← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 115

Sashe 101

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwantar da kai yayi Alamun ban hakuri yace natuba Mamy.
Babu bata lokaci suka d'au hanyar zuwa bohikon dukan su harda su Faruk da Aminu da Karima 'su Khadija ana Murna za'a je gun kaka ziyara..
Samad Sam beso Rahama ta shiga motar su Mamy ba..
Ba haka yaso ba..

Faruk duk jikin sa a mace tun lokacin da Samad yasoma bashi labarin Karima..
So yake ya kalleta dakyau'' cike da mamaki..
Aminu Da Samad kadai ne ke fira a motar ' su biyu ke bayan kujerar mota..
Faruk n'a Tuki Ahmad nakusa dashi a gaba..
Shi Ahmad murmushi yake akan Asiya Sam haryanzu Ko waya betaba hadasu ba..
Yana lissafin yanda zeci gidan ta badai shi ta zaga

Wata zuciyar tace Anya Ahmad yin haka ba kuskure bane 'inka sake ta zaka samu matsala da iyayen ka kuma ka basu' kunya..
Tabe baki shiyakadai yana maganar zuci yace uhmm to koda na saketa din Ko sunyi fushi n'a kwana biyu ne zasu huce...

Samad dake kallon keyar Faruk Yace kai kabi damu à hankali fa karka jefamu cikin rami kajawa mata ta asara...
Darawa Dukansu motar sukayi harda Ahmad.
Aminu yace kai Tabe Tabe tunda kayi aure shikenan bamu da ta kan mu ka ishe mu ka gallabe mu..
Nima dai auren nan zanyi inhuta haba dan Allah..
Faruk dake murmushi yana Tuki yace meye dan mun mutu iyaka dai tayi maka takaba da ankwana biyu ta samu wani mijin ta aura...

Sossai Yarima Samad ya Girgiza Jin wai zata samu wani mijin ta aura.

Yace dan bakin cikine kai Faruk ta Allah ba takaba ga Kabari n'a ga n'a Rahama InshAllah taré zamu mutu..
Sossai suka d'ara haka sukayi ta fira har suka isa garin bohikon....
Kai tsaye gidan Liman Ahmad suka nufa..
Iske shi sukayi waje yana koyar da dalibai.
Ganin motocin su yaga tambarin gidan Sarauta yasan eh lallai bakin kwatano ne suka iso.....

Nan da nan ya sallami dalibai tareda koma ciki..
Koda suka iso.
Parkin space suka paka motocin su...

Lale Lale Lale cewar *Iya Gari* kakar su Samad wannan sunan ake kiran ta àgarin Asalin sunanta Amina....

Samad bakin sa dauke da murmushi yace Iya Gari lallai matar nan bakya tsufa..
Tabe baki tayi tace taya zan tsufa kuna ta dankaromin kishiyoyi harda maigida n'a Ahmad shima kishiyar zemin..
Dariya suke nan da nan suka nufi masaukin su..

Firdausi Autar su Mamy ce tafito Daga dakin ta aguje tanufo Mamy ta rungume ta '' tace anty Habiba kin zama me iyali.
Kallon Rahama take wacce suke gaisawa da Iya Gari tana mata tsiya akan ta kwace mata miji....

Firdausi tace kai kai wannan ce Matar Samad kamar nasan fuskar nan..
Rahama juyawa tayi tana kallon Firdausi tace '' la la anty fiddo kece..

Sossai Firdausi ta rungume ta '' tace Rahamatullah wai dan Allah dagsk kece matar d'ana '' shiru tayi tana murmushi..

Yarima Samad yace Mama firdausi kinsanta ne..
Kwarai kuwa nasan Rahama Abdurrazak.
Mun hadu da ita Asaudiyya ita tana karatu ne''nikuma munje umra' sossai ta ringa koyamin karatu 'katuna wataran muna waya dakai lokacin inacen' 'har nacemaka wallahi wata yar karamar yarinya ta burge ni sossai ga tarin ilimi akan ta har daurani take akan karatuna' nace maka 'nima da Allah zesa yata Aisha zata zama kamar ta danaji dadi.
Kacemin ai abun rabone da dagewan iyaye...

Yarima Samad cike da Jin dadi yace kwarai kuwa natuna ashe itace uhmm Allah yayi kunsake hadewa' à matsayin yar ki..

Mamy cike da Jin dadi tace MashaAllah abu yayi..
Wai ina yaya Auwal ne.
Da Sani..
Bata gama rufe baki ba sai gasu '' sun taho harda baban nasu...
Cike da. Jin dadi suka kara gaisawa da mamy.
Abban su sossai yaji dadin ganin su.
Yace yau dai Samad yazo mun da Amarya kuma babu wanda ya isa yatafi da ita..
Yarima Samad sossai ya d'ara yace uhmm banga kana aiken kudin cefane ba..

Liman Ahmed kallon Rahama yayi yace ke Rahama kullum bakina Jin alert awayar ki ba..
Cikin zazzakar Muryan tace Ko yanzu ma sun shigo kudin.....
Gabadaya dakin dariya suka sa...
Bayan sunyi ciye ciye dukan su..
Rahama tabi Firdausi zuwa dakin nata..
Sossai Samad ya takura..

Sai bayan Ish'ai Liman Ahmad yakira dukan yayan sa harda Su Faruk da Aminu ' Samad da Ahmed.
Cike da nutsuwa kowa ya zazzauna kasa.
Yace yawwa game da maganar Farida ne..
Gaskiya yarinyar nan ta cuceni ta cuci kanta nabata tarbiyya Allah ne shedata' kuka yake sossai yace shine zata janyo abunda ze bata martaban gida ni Liman.
Duk hukunci da Aka zartan akan ta babu ruwana wlh ita tajawa kanta..
Sannan zancen Maryam zata dawo nan hannuna tunda mahaifiyar ta bata gida 'kuma naji ance uban nata yayi aure..

Auwal yace hakane gaskiya gwamma ta dawo hannun ka.
Zatafi samun kulawa kuma zata nutsu..

Sannan maganar mijin Habiba da baya kasar nan shekara shidda.
Anya wannan zaman me billewa ce banason abunda ze kawo mace ta fada halaka..
Dan haka asan abun yi...
Yarima Samad yace Liman mun gano inda yake..
Nan ya shiga bawa liman labarin abunda yafaru a masarautar da dalilin barin gidan nasa dakuma inda yazauna 'dakuma inda yake ayanzu..

Sossai Mamy ta Girgiza Jin wai aikin gadi yayi agidan su Rahama....
Kuma yanada masaniya akan inda yake amma be sanar mata ba..
Tabe baki tana kallon shi

Tace kai Samad kasan inda yake shine kabarni a duhu.
Kuma har gidan su Rahama yazauna Daga kai har ita babu wanda yataba fadamin..
Yarima yace ita kanta Rahama batasan shine ubana ba saida taga hoton sa..
Kuma kinsan batada surutu bata fiye magana ba..
Inhar ba annemeta da zancen bane..

Firdausi tace hakane Tome zata ce miki kina uwar mijin ta..
Faruk yace gaskiya ne kam bazata ce komai ba Inde Rahama ce..

Nan. Dai. Fira ya bârke tsakanin su
Liman yace maryam gobe yakeso ta taho bohikon din in bikin khadija ya tashi taje tadawo....

Sun zauna suna ta tsara yanda zasu yi shagalln bikin Ahmad da Khadija..

Kwanan su uku àgarin duk dangi saida aka zazzaga da Rahama '' masu zuwa ganin ta kuwa makil kasancewar ta diyar sheik Abdurrazak....

Karima kuwa sossai taringa bin Rahama duk inda zata sa kafa à garin.
Duk yanda Faruk yaso Samad yabashi labarin Karima abin yaci tura yabar shi sai sun koma kafun su tafi Kanon ze matsa masa dan yaji labarin komai..

Koda Maryam ta iso bohikon Liman Ahmad '' cikin Almajiran masu daukar karatu wajen sa yayi masa Al'kawarin bashi auren Maryam 'sadaki da iyayen sa kawai yake bukata..

Maryam tayi kuka harta godewa Allah yanzu itace aka bada auren ta kamar mara yanci' uhmm.

IYA GARI NAN NAN TARINGAYI DA Mamy da Rahama '' ita da yayan ta firdausi da Auwal da sani..
Suma sunce zasuje biki.
Amma iyakar kwatano.

Rahama tasamu kyautuka agun yan uwa da à bokan arziki....

Karfe biyu suka baro garin cike da kewa....

Sai bayan la'asar suka isa kwatano dayake babu nisa sossai.....

Suna isa gida.
Kai tsaye kowa yayi sashin nasa...

Faruk hango Karima yayi tana ta buga uban sauri zata wuce dakin nasu..

Muryar sa ta sinkayo yana fadin dakata dan Allah....

Cak ta tsaya gaban sa cike da ladabi tace naam yaya Faruk gani...

Kallon ta yake cikin idanu yakura mata idanu 'sossai ganin mugun kyawun ta dabe taba lura ba saida ya firgita shi yau ne karo n'a farko da yayi mata kallon tsafta...

Kallon dayake bin ta dashi yayi yawa hakan yasa tace uhmm yaya Faruk inajin ka kayi shiru sonake inje inyi sallah...

Dawo da nutsuwar yayi yace yawwa Karima.

Daman ke yar Shugaban Kasar Niger ce..

Cikin zazzare idanu take...........

Taku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:56 - Nuriyyat: 9️⃣5️⃣

09069080725

Cikin zazzare idanu tace ina kaji wannan zancen..

Sake da baki take kallon sa zuciyar ta na tsananta bugawa..

Murmushi yayi yace yanaga duk kin rude Daga tambaya..

Daga bakin dabe mun karya naji kema kinsani..

Shiru ne ya ratsa n'a wasu dakiku tace kabari shugaba n'a inyabani izini zan gayamaka..

Tabe baki yayi yace nima ai shugaban naki ne nida shi duk daya ne Karima...

Hakane yaya Faruk '' to kabari zuwa dare n'a nutsu inka dawo zanbaka labari...

OK to Allah yakaimu ya furta tareda barin wajen itakuwa tawuce cike da mamaki ya akayi Yarima Samad yagaya masa.

Bayan Isha'i kuwa saiga Faruk yakara dawowa wannan karan Gun Samad yatafi direct.
Koda ya isa sashin Yarima ya iske shi zaune a falon sa shikadai système n'a gaban Idanun sa sanye yake da médical glass.
Yayi zurfi acikin aikin da yakeyi hakan yasa beyi saurin Jin Sallamar Faruk..

Dafashi yayi yace kai Tabe Tabe wai aikine yatashi haka..
Dago kai yayi yana kallon Faruk yace kai yada zuwa gidan masu aure awannan time din..

Faruk darawa yayi yace naji dai dan iska gunka nazo.
Bismillah Samad yace yana nuna masa wajen zama..

Hakan yasa Faruk y azauna yana fuskantar Samad dake kokarin rufe système din sa..

Uhmm inajin ka kazo ne akan tafiyar mu Kano ne..

Faruk yace Duka dai amma abu n'a farko shine kaban labarin Karima daka fara bani munje bohicon kaki karasa mun sauran bayanai....

Yarima Samad cike da mamaki yake kallon sa yace kai kai yanzu kan wannan zancen kasa harna rufe système dîna bangama aiki ba..

To meye dan karufe système din kai din ma ai gulma ce bawai aikin zakayi ba...

Ni dai gayamin kaine saurare..

Idan naki gayamaka meze faru ne ya tsare sa da idanu..

Uhmm Aikuwa inkaki gayamin babu inda zanje kuma wallahi baka isa ka tashi Daga nan ba.
Zanga ta inda Rahama zata ganka..

Jin haka Yarima Samad yace uhmm tunda kace haka zauna inbaka labari nasan ba mutunci ne dakai ba saika aikata abunda ka fada din yanzu ni nayi hankali banson banje naga sahibata ba...

Kamar yanda nagayamaka Karima ba baiwa ce diyar shugaban kasar Niger 🇳🇪 ce..

Shugaban Adalai yace kasar niger wajen wani taro da Aka gudanar n'a sarakuna..
Bayan anwatse taron 'gidan Shugaban kasar ya sauka maimakon Hôtel.
Cewar shugaban kasar Alh Salihu yawuce zama hôtel Saboda irin Adalcin sa.....
Bayan ya isa fadar shugaban kasa yasamu masauki me kyau cike da kulawa...
Chapter 101 · 0% Book details