← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 115

Sashe 64

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yarima zaune cikin motar banda kallon Rahama ba abunda yake yi cikin kasa da murya yace..
Da mun shiga Masarauta inason duk inda nasa kafa kibini karki yarda ki canza hanya in ba nine nace ki tafi ba..
Gyada masa kai tayi cikin gamsuwa.
Hannun ta ya rike cikin nashi yana murzasu ahankali ba daman tayi magana tana tsoro...
Cikin yin kasa da murya yace dazun wani Adu'a kika karanto ne bakaramin dadin sa naji ba..
Murmushi tayi wanda yasa kuncin ta lotsawa tace adu'a ce wanda ke dauke da babban kariya gani nayi kamar ciwon naka yanada Alaka da iska shiyasa nayi hakan.
Murmushi yayi yace nagode Rahamatullah..

Shiru tayi tana cigaba da kallon hanyar da suke bi..

Motocin daidai Masarautar tayi parking babu bata lokaci Masu gadi suka bude kofofi..
Motocin suka shigo ciki. zuwa parking space..
Nan da nan Masarautar ya karade da gudan tsoffafi bayi n'a cikin Masarautar yayi daidai da fitowar hadimai da bayi da kuyangu.

RAHAMA bakin ta dauke da Adu'oi ta sauke kafafun ta cikin masarautar.
Wanda yayi sanadiyan wani kara Daga Sama nan da nan Garin ya hade wani iska ke kadawa mai cike da ni'ima wanda yake nuna hadari n'a d'af da sauka..
Dan duk wani shukoki dake wajen iska nata kada su...

Yarima Samad kai tsaye suka cusa cikin Masarautar da Aka kawata shi....
Rahama cikin Azama take bin Samad a bayan ta..

Suna shiga Daga ciki Bayi sukayi layi daya suna sanye cikin uniforme din Masarautar ran su aduke..
Sukace ya Barka da zuwa jikan Sarki '' Barka da zuwa Amaryar Yarima..
Wuce su yayi batareda yayi musu magana ba..
Rahama n'a ganin yayi gaba ta take masa baya..

Su Ànty da Asiya da, salma tuni Su Bayi suka wuce dasu sashin da bakin Masarautar ke sauka...

Yarima Samad kai tsaye Fadar Sarki ya nufa bakin sa dauke da Sallama yashigo..
Ganin sa bakaramin Girgiza mutanen wajen yayi ba mussaman Abban Marwan da Abban Maryam da wasu n'a kusa dasu sossai suka razana basu gama gigicewa ba...
Sallamar Rahama ne yasa kowa awajen tashi tsaye suna kallon takun da take yi har ta iso kusa da mijin nata..
Risina tayi kasa kanta aduke tagaida mai Martaba..
Cikin Jin dadin gaisuwar ta
Mai Martaba yace Madallah da zuwan Amaryan Samad..

Abdul Samad kallon mutan dakin yake cike da izza dan yasan suna jiran suji abunda ze furta..

Alhmdulilah Allah yakawoni gida lafiya tareda matata Rahama..
Dafatan Masarautar nan zasuyi mata biyayya kamar yanda ake min..
Ku sani duk wanda ya bata ran ta..
Uhmm ni yatabo kuma babu sassauci tattare dani awannan karon sossai n'a shirya muku ban ware kowa ba..
Duk wanda ya tsargu dashi nake...

Kowa wajen tsit yayi Ahmad dake zaune kusa da Marwan kowanne su yanata juya kalaman sa.
Shi Ahmad yayi nazarin sa amma ya kasa gano inda habaicin Samad ya dosa..
Shiko Marwan tsaf ya gane hardashi a cikin jawabin Samad...
Abban Marwan sossai yake ta jinjina kalaman sa shida Abban Maryam kowa awajen da abunda yake sakawa aransa...

Mai Martaba shi kansa yayi matukar mamakin yaron da yake shiru shiru magana ma be dameshi ba shine yau yake ta fadin zance yasan akwai wata akasa..

Rahama ita kam kalaman sa sun matukar daure mata kai takasa gane inda ya dosa...
Maganar sa ne yadawo da ita duniyar tunanin data fada...

Cike da ladabi kamar bashi yagama zuba musu rashin ido ba yamikawa kowa hannun wajen sukai musabaha..

Kallon sa yadawo kan Mai Martaba yace tsoho me Ran karfe zamu shiga Daga ciki kasan sai mun leka kowani sashi n'a gidan nan kafun Muje masauki...

Mai Martaba yace gaskiya ne wannan..
Samad n'a tashi Rahama itama tashi tayi...
Direct cikin gida suka nufa inda hadimai ke take musu baya....

Cikin Azzama Karima ta karaso wajen bakin ta dauke da Murmushi tace ya shugaba na Barka da zuwa..
Kallon ta yake yana Murmushi..
Cikin Jin dadi tace Gimbiya Rahama Barka dazuwa wannan gida me Albarka..
Rahama kada mata kai tayi yanda Samad din yayi...
Karima cike da ladabi tace..
Ya shugaba na..
Gimbiya Fulani tace sashin ta zaku fara zuwa shine Al'adar gidan nan duk Amaryar da Aka kawo itace farkon ganin ta...
Murmushi yayi yace Babu matsala..
Hakan yasa sukai Sashin Fulani....

Ita Ko Fulani tagama shirin ta tsaf cikin shigar Alfarma.
Murmushi takeyi mai cike da Ma'anoni..
Sallamar Yarima rike da hannun Rahama ne.
Ya sata tashi tsaye zumbur...........

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah

No editin maneji
3/21/22, 07:46 - Nuriyyat: *KANWATA*

NB
Pls masu mun korafi akan wannan Littafin kan bana sakin zancen wajen kwanciyar Samad da Rahama...
Addini Akwai Alkunya dole wani abun kanayi kana dan sakayawa bazan iya fitowa koro koro ina sakin zance ba dan wannan littafin bansan iyakar inda yake yawo ba duk da Paid book.. ne
Amma zanyi iya kokarina ganin n'a isar da sakon da nakeson isarwa cikin Aminci da kwanciyar hankali..

09069080725

6️⃣1️⃣

Cike da Mamaki take kallon hannun Rahama da Samad ya rike gam..
Karasowa Falon yayi suka iso har tsakiyar Falon.
Rahama kan ta na aduke cike da ladabi tana kokarin risina dan gaishe da Fulani dasauri Samad ya dago tana fadin haba Amarya ta ya za'ai ki durkushe kasa kawai dan gaishe da mutum da Adam irin ki wannan kamar sujjada ce kuma Allah kadai akewa haka..

Sai kuma wayanda ake matukar Jin kunyar su da girmama su..
Kallon Rahama yayi wanda kanta ke aduke cike da takama yayi wani kasaitaccen Murmushi wanda ke bayyana kamalar sa yace..
Wannan Matar baba n'a Ma'ana kanin Mahaifina..
Wani bangaren kuma abokiyar wasa ta ce shiyasa kikaji n'a hanaki yi mata wannan gaisuwan...

Kallon Fulani yake yace mun hadu da Karima ta idar mun da sakon sashin ki ne nafarko inda yakamata infara zuwa.

Jawo Rahama yayi tareda rungume ta ajikin tanason kwacewa tana tsoron abunda zebiyo baya inhar sun bar dakin tasan halin sa babu sauki wani fanin..

To gamu munzo ki bamu abunda zaki bamu yana kallon fuskar dauke da Murmushi sabanin da idan yashigo dakin ta cikin hada rai yake..

Jin tayi shiru ne t'a Gaza magana banda tafasa babu abunda zuciyar takeyi ji take kamar ta kurma ihu tace wayyo à kawo mata dauki irin wannan cin fuskan haka da Samad yayi mata tunda take arayuwar ba'a taba yi mata kwatan kwacin sa ba...

Cikin d'Anne Fushin ta tace Ayya Sannu dazuwa Yata dan yaye Alkyabba nan muga fuskar ki mana.
Mufa iyayen ki ne..

Samad yace kwarai kuwa kune sahun farko ma a iyayen bakiga wajen ki muka fara lekowa ba.
Saboda kina cike da zalaman son ganin danki da Matar sa Ko.
To gamu yakara matse Rahama ajikin sa..

Shiru tayi tace uhmm Samad nayi murna da zuwan ku dafatan kun iso lafiya..
Keko Amarya ki saki jikin ki nan gidan ku ne...

Samad tabe baki yace yace tunda bazaki bamu wurin zama ba tomu zamu zauna sakin Rahama yayi ja zata suka zauna kan kujera..
Tareda daura kafar sa daya kan tebur..
Lemun dake kan tebur din yazuba a kofi ya sha yana lumshe idanu...
Amarya zaki sha yana kallon Rahama kofi à hannun sa kada masa kai tayi Alamun A'a..
Fulani takai kololuwa wajen bacin rai tace.
Kuna iya tafiya sashin Mama Karama kartaga har yanzu baku shigo ba...

Samad yace Ah karki damu meye n'a ta dan n'a tsaya wajen uwata.
Kefa uwata ce babu matsala inna kwana anan..
Duk yanda Fulani take tunanin saukin kan Samad ashe ya zarce tunanin ta...
Tashi yayi tsaye hakan yasa Rahama itama tashi tsaye..
Fulani tace Au Amarya bazaki bâri inga fuskar ki ba.....
Sossai Rahama ta Kosa taji meye tsakanin Samad da Fulani..
Yaye Alkyabba tayi..
Fulani saida ta tsorata dan ganin kyawun yarinyar kamar ita tayi kanta batayi zato Ko tsammanin zesa mu.
Mata irin ta ba.
KADA kai tashigayi tace.

Lallai Samad ka iya zabe uhmm koda yake ba zabin ka bane.
Zabin Mai Martaba ne fa kila ya lura céwar kana shirin lalacewa shiyasa yayi maka auren Matar da wani yace yafasa dauka...
.
Bakaramin zafin kalaman ta Yarima da Rahama sukaji ba..
Shiko Samad cikin nuna rashin damuwa akan zancen ta..
Yace bakisan Ance wani hanin da Allah baiwa ce..
Shiyasa naki Aminta da tayin bikisu da kikayi mun..
Allah ya musanya mun da Mafi Alkhairin Mata...
Shiko wanda yafasa auren ta..
Matsayin sa ne bekai ya aure ta ba..
Shiyasa Allah ya canza lamarin.
Ni nabiya Sadaki aka daura Ko ince Mai Martaba yabiya..
Kinkosan Abunda ake cewa auren Sadaka kuwa ?

Saika fada fitsarrare tana huci sama sama..

Ai auren Sadaka shine auren dako sadaki baka biya ba aka tura maka.
Bayan mun biya kinga kuwa mun siya ne da kudin mu..
Gashi gobe za'ai shagalin biki ina fatan dai kinyi gayyata yakarashe zancen tareda kama hannun Rahama suka fice Daga dakin nata..

Banda Safa da Marwa babu ABUNDA fulani keyi cike da mamaki yau itace Samad ya disga agaban matar shi..
Eh lallai dole indau Mataki shegu tsinannu.
Ya auro Aljana irin sa dangin matsiyata

Samad direct sashin Mama karama suka nufa..
Ganin su yasa cike da fara'a ta tarbe su..
MashaAllah MashaAllah
Kishiyata Rahama yau dai Allah ya hadamu zamuga waye gwarzo agun maigidan namu...
Samad sossai yake dariya yace Mama karama aikece uwargida duk wacce tazo tana bayan ki..
Rahama cike da ladabi ta durkushe domin gaida Mama karama..

Sossai ta yaba da hankali da nutsuwar Rahama
Komai nata cike da nutsuwa takeyin sa..

Rahama cikin Kosawa tayi kasa da murya yanda mama karama bazata jiyo ta ba..
Tace pls incire wannan kayan nauyin dake jikina ya isheni wlh..
Kallon ta yake cikin hada fuska yace aiko bazaki cire ba harsai mun koma sashin mu....
Abincin da Mama karama ta jera musu ne yajawo hankalin sa wajen Fadin kai gaskiya bazamu ci Abinci yanzu ba sai Anjima kisa akirawo Karima tazo ta dauki Abinci takai sashi n'a..

MAMA KARAMA tace inkai bazaka ci ba saika hana matar ka..
Zazzakar muryan Rahama taji tana Fadin n'a koshi Mama..
Suna gama abunda zasu yi suka baro sashin Mama Karama..
Chapter 64 · 0% Book details