Sashe 63
Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karima cikin Kosawa da yawan tambayoyin hassana
tace nima bazan San dalilin sa kawai yace ga yanda yake so..
Nikuma yazama wajibi in masa biyayya..
Hassana tace kwarai kuwa hakane Allah yasa mudace..
Karima tace Ameen tareda rufo sashin Samad tayi gaba.
Hassana nabiye da ita abaya tana mamakin yanda akai duk zaman ta gidan ta kasa gane kan komi sai juya mata hankali Karima takeyi.
Jakadiya taki bata damar suyi magana kullum sai ce mata take gobe gobe har yanzu goben taki zuwa..
Tafara sarewa da lamarin gidan dan haka tasa aranta da angama taron zata tafi garin su...
Fadar mai Martaba cike yake da dunban jama'a.
Inda Abba Marwan ke zaune kusa da mai Martaba suna kwasar gaisuwa agun baki..
Roban Faro ya dauko hannun sa cike da ruwan maganin kamar n'a gargajiya.
Cikin yin kasa da Murya yace ya Abby ga maganin ka fa.
Yakamata Ace kasha kafun taro yayi taro Saboda lafiya ka...
Mai Martaba kallon sa yake cike da fara a yace kabar shi zuwa d'are nasha dan indan nasha jiri yake sani kasan maganin hausa akwai karfi kuma gani da taro banson inkasa sakewa da jama'a yakarashe zancen yana sauraren kirarin da fadawa ke masa..
Kallon Waziri yayi yace yanzu saura minti Ashirin su karaso maza à tafi da motoci zuwa daukosu wanda Yarima ze shiga da Amaryan dafatan motar tana redy Ko..
Waziri yace eh ranka shidade yana redy...
To maza Atafi nakosa inga zuwan su gidan nan..
Abban Marwan yace maza Waziri a je acika Umarni kasan d'ana zezo da Matar sa..
Cikin hanzari Waziri yafita..
Abban Marwan yace to bara inje in ajiye maganin zuwa d'are sai inkawo maka Ko..
Mai Martaba yace Ah Ah kabarshi zanshiga ciki dashi..
Badan ransa yaso ba yace kai ALLAH YA TAIMAKI Sarki to zanje indawo..
Mai Martaba yace ina zakaje kuma A'a kada kaje Ko nan da cen..
Sossai Ran sa yabaci tareda gyara zaman sa suna kwasar gaisuwa...
Fulani daidai fita wajen gari wajen wani jeji tayi parking din motar ta...
Tana fitowa tarufe motar tareda nufar wannan jejin cikin saurin ta cikin kwazazzabai take buga uban sauri ga ciyayi ga ramuka haka take ta jefa kafafun ta cikin tsoron wannan wajen har Allah yabata nasaran karasowa wajen bokan dake zaune nannade da kafafun sa...
Dariya yasoma saida ya firgitata ta gigice ganin yanda launin sa ya canza lokaci daya..
Zama tayi cikin tsoro da fargaba tace n'a iso boka.
Kallon ta yake da jajayen Idanun sa kamar wuta ya fiddo wata katuwar kwarya gaban sa...
Yace yanzu gayamin me kikeso ayi ne dan haryanzu be kusance ta kinga babu Alamun samu ciki tattare da ita bare.
Mai Martaba yafadi mugun kudurin sa...
Dadi taji aran ta tace eh tunda be kusance ta kenan dai aikin ka nakyau ace suna zaune gida daya inda babu kai nasan da yanzu tana dauke da ciki..
Boko yace kwarai kuwa mune nan muka hana shi kusantar ta..
Itama muka sa mata girman Kai
zasu ci uban su..
Kwaryan dake gaban sa yazubawa ruwa.
Yace dan leko ki gani..
Hakan yasa Fulani tashi Daga zaune tana kallon wannan ruwan..
Zare Idanun ta tayi ganin Samad Samad da Matar sa suna kokarin sauka Daga cikin jirgin..
Kallon Matar Samad take Amma Alkyabba dake kanta ya hana taga fuskar ta..
Cikin tashin hankali tace boka gasu nan fa..
Dariya yayi yace yanzu me kikeso ayi masa...
Fulani tace so nake akashe masa mazakutan sa kawai...
Wani katuwar karamar maciji tana kusa dashi hannun yasa tareda dauko ta a cillata awannan ruwan ta tafi...
Yayi daidai da Saukowar Samad Daga jirgin sama daidai da shigar wannan macijin À marar sa...
Samad Wash ya furta awajen dafe da marar sa yana kokarin faduwa..
Hannun Rahama tasa ta tallafosa kallo daya tayi masa ta gane abunda ke damun sa...
Cikin Azama suka dan matsa Daga gefe su Ànty n'a bayan su cikin damuwa Ko wanne su...
Adu'oi tafara karantowa masu zafi wanda rabon ta da tayi su tun tana gidan iyayen ta.
tana gamawa takama wajen da taga yarike tayi masa tofi..
Sub sub sub wannan macijin yafita aguje jikin Samad tareda komawa inda aka turo shi....
Shiko Samad n'an take yamike yace karku damu fa ciwon yatafi..
Cikin tashin Hankali fulani dariyar ta yakoma ciki tana zazzare idanu ganin dawowar Macijin Daga ita har boka saida..........
*Ta ku har kullum kyauta Daga Allah*
3/21/22, 07:46 - Nuriyyat: KANWATA
09069080725
IKILIMA ADAM
KYAUTA DAGA ALLAH
6ï¸âƒ£0ï¸âƒ£
Saida suka tsorata.
Boka yana kallon yanda macijin ke ta wusil wusil kamar ze mutu ya dade haka Sannan boka ya watsa masa wani ruwa yauki kamar kubewa hakan yasa yayi tsit ya kwanta lamo yana maida numfashi...
Fulani da take agigice Idanun ta nakan macijin tace wannan wace irin yar Asiri ce wannan..
. Boka yayi dariya me kama da ciwo yace ke karki damu wannan yarinyar da Ayar Allah take Amfani..
Nikuma namiki Alkawari duk sanda take cikin Jinin Al'ada à sanar mun a lokacin ne zanyi nawa aikin yar iska har ta isa m'a..
Babu Mamaki baban ta nasha turawa mutane Aljanu akaisu magani wajen su har kasar kwatano bakiga yanda yake kona mana Aljanai ba..
Ina nan da haushin uban ta Ko babu ke ni zan yake ta.
Fulani ajiyar zuciya ta sauke tana kallon boka tace to yaushe zan dawo ne yarinya nan fa.
Wallahi banason ya kusance ta..
Boka yace kinadai gani da Idanun ki mun tura ta maido mana.
ABU daya zakiyi ki taimaki kanki kafun n'azo da nawa aikin.
Kisan hanyar da zaki bi.
Ki nesan ta shi da ita.
Har tsawon kwana bakwai lokacin zata kasance cikin Jinin Al'ada.
Zanyi Amfani da wannan damar wajen cimma manufar mu..
Fulani cikin takaici tace naji boka ni zan tafi banson su rigani isa gidan takarashe zancen tareda tashi cikin tsaurin ta tabar jejin tareda nufar inda motar ta yake ta hau babu bata lokaci....
Shiko boka zaune yake yana jinjinar Al'amarin Rahama ita wace irin yarinya ce haka dan matuka ta mugun bashi tsoro kasa nunawa Fulani yayi.....
Filin Airport Samad n'a karasowa tsakiyar filin wajen hannun sa cikin n'a Rahama.
Ko d'ar beji ba bare kunya haka yakara manne hannun Rahama da nashi su Asiya da Ànty kallon ikon Allah suke suna Murmushi dan Sam yaki basu daman suyi magana da ita tunda suka t'aso..
Ita Ko Salma gabadaya hankalin ta yayi mugun tashi ganin yanda yake ta kara manne wa yayar ta..
Kan kace me gabadaya ma'aikatan sa suka hallara gaban sa..
Secretaria, manajoji, PA, da kananan ma'aikata Ko wanne su layi yayi sanye cikin uniforme din aikin su..
Hada baki sukai wajen Fadin.
Welcome Sir.
Kada kai yayi yana Murmushin ganin kowannen su lafiya..
Cike da ladabi suka fara gaishe da Rahama..
Itama din yanda taga Samad yayi hakan tayi tsab take lura da duk wani motsin shi..
Su Faruk suna karasowa wajen sukace bismillah Yarima mu tafi.
Kokarin wucewa suke kowane Ma'aikaci suna ta koran jama'a cikan da akai yasa Samad yayi burki Daga inda yake yaki motsa kafafun sa..
Sojoji da yan sanda ne suka fara watse cinkoson da akai ta hanyar maida mutane cen baya..
Yan Sanda uku ne suka zo wajen su Yarima tareda nuna musu hanyar da zasu bi..
Kai tsaye sukabi hanyar gabadayan sossai.
Rahama da yan uwanta suke kallon wannan glove din dake rubuta welcome.
Abdul Samad Rahama.
Happy mariage life..
Sossai wannan abun ya burge Rahama bakaramin dadi taji ba har ta nuna afili duk motsin ta Samad yana kallon ta yasan ta shagala da kallon wannan glove din dakuma décoration din da akai da sunan su...
Daidai Mafitar Aiport din.
Cikin Sauri sauri bayi suka fito Daga cikin motar masarauta tareda zuwa shimfida dogon carpet gaban su...
Wanda yake dauke da sunan Ango da Amarya..
Cike da takama da izza Samad ke taka wannan carpet din shida Rahama bayi suna ta watsa kyalyalin dake a hannun su a duk inda zasu sa kafafun su.
Bakaramin burge jama'ar wajen wannan tsarin yayi ba...
Hakan yasa yan Jaridu da sukai ta daukan hotuna da vidéo direct
Kokarin shiga motar su cikin yan Jaridu ya karaso wajen lasifika n'a hannun sa..
Yace Barka da isowa dan Sarki jikan Sarki '' mun samu labarin ka daura aure a garin kano kuma gobe za'ai taron biki....
Yarima gyara Tsayuwar sa dan basu Amsa.....
Yayi daidai da cen kasar 🇬🇦 Gabon din Baba Salihu da Sheik da Malam Isa suna gaban Akwatin TV suna kallon tashar Canal 3 daya Daga cikin tasoshin kwatano..
Direct suke kallon shirin da ake nunawa kai tsaye a filin Aiport din
Sheik bakin sa dauke da Murmushi suke sauraron jawabin Yarima Samad..
Inda yake Fadin.
Eh nayi aure a kasar Nigeria wannan surprise ne nayiwa yan kasata kwatano..
Dan Jarida dake dauke da lasifika me dauke da tambari canal 3 yace.
Ko zaka iya gayamana yanda akai ka hadu da gimbiyar ka..
Yarima gyara kallon dan jaridan yayi hakan yabasu daman kawo lasifikan daidai saitin bakin sa..
Cikin isa da muryan sa mai dadin sauraro..
Yace n'a hadu da Mata ta Rahama ne a filin airport yana me kallon ta..
Wannan haduwan da mukai zuciya ta takamu da son Mata ta abar kauna ta...
Gabadaya wajen aka dauki tabi.
Yace kuma ba shine ranar farko d'ana fara hadu da ita ba '' 'ranar farko shine Ranar da muka kwanta rashin lafiya alokaci daya Saboda muhimmancin soyayya dake tsakanin mu da ita..
Rahama Rahma ce à gareni yakarashe zancen tareda shiga motar itama Rahama ta shiga aka rufo masu kofa.
Tsaf yarima yasan wannan daukar da akai musu duk duniya zata gani harda magautan shi dole yazabi wannan hanyar domin kauda tunanin su akan sa..
Sheik da baba salihu bakaramin dadi sukaji ba ganin yanda Yarima yayi bayani sai Fadi suke Alhmdulilah Alhmdulilah tareda daukan lemun da suka zuba akofi suna sha cikin Jin dadin ganin yayan su..
Bakaramin dadi sheik yaji ba ganin Ànty cike da kamala tana Murmushin Jin jawabin Yarima Samad..
Kwatano..
Nan da nan motocin masarauta suka bar filin airport din..
Suka d'au babban titin daze sada su da masarautar ghuezo..