← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 115

Sashe 8

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

IKILIMA ADAM
(Kyauta daga Allah)

Paid Book ne
Vip 300
Spécial 500

Acct nomba 3115484026
ikilima adamu first bank
Ko kuma Katin MTN
Banason Vtu

Idan kinbiya kina iya turo shaidar biyar ki 'ta wannan lambar 09069080725

Book 1️⃣1️⃣

Tafiya sukai mai dan nisa kafun suje rijiyar lemu.

Daidai wani babban masallaci juma'a sukai parking motar' nasu.

Yarima kansa aduke yake batareda yasan Sun iso ba.

Faruk daidaita parking d'in motar' nasu yayi tareda zagayowa yabude wa Yarima Samad mota.

Dago Kai Yayi YACE am sorry ashe har mun iso...

Laptop dake kan kafafun nasa ya ajiye kan kujerar motar' tareda dauko médical glass d'in sa yasa .

Ba karamin kyau shigar dayayi ya amshe shi sajen nashi lub lub kwance Akan fuskar shi Yana sheki .

Cikeda da izzar sa da cikar haibar sa yasauko daga motar' .

Tsaye yake yanata kallon yanayin unguwar da tsare tsaren gine ginensu.

Kallon massalaci dasuke sallah juma'a yayi yanayin tsarin massalacin kwarai yaburge shi.

Faruk yace Samad mutafi mana kasan akwai ayyukan da zamuyi a kamfanin da kakeson kabude ko.

Marwan dake gefen nasu tsaye yace Amma kuma ai yakamata mu koma gida tunda kullum sai munje massalatai amma shiru kakeji babu amsa yanzu kila ma baya kasar nan 'mune muke wahalar banza.

Aminu cikin bacin rai yace wlh kaide Marwan ko ya'akai dan bakin cikine kullum bakason ci gaban mu.

Waima dole ne saika fito kazauna gida mana haba.

Duk kasashen da muke yawon zuwa kaine kullum kake mita adaina yawo neman Wanda baya rayé .

Taya kasan baya raye Kenan kasan wani abune akan mutuwar sa.

Haba dan Allah idanunsa Sun kada ji yake kamar yakama Marwan ya shake masa wuya saiya daina numfashi.

Yarima Samad duk ihun da Aminu yake kan sa harya fara sarawa kwata kwata beson hayaniya.

Ganin Aminu Yaki Bari sai masifa yaketa zubawa

Hannu ya daga alamun ya isa

Shiru kakeji Dukansu babu Wanda yayi magana.

Mai gadin massalacin ne yazo gaban su cikin girmamawa Yana fuskantar Samad YACE ranka yadade wani taimako za'a baku ne.

Aminu ya amshi zancen da eh wani bawan Allah Muke nema Allah yasa kasan shi.

Mai gadin YACE to Allah yasa nasan sa ya sunan sa.

Faruk YACE sunan sa.

Alhaji salihu turaki

Jinjina sunan mai gadin massalacin yayi yace gaskiya bansan shi banma taba jin suna me kama da nashi ba.

Yarima samad yakaraso gaban sa cikin idanun sa dasuka kada jajir jin amsar mai gadin yabasu

Amshi wannan Kati nane
Nombar wayata nakai dan Allah duk sanda kasamu labari Akan wannan sunan ka Kira ni.

Namaka Alkawari siya
Maka gida da mota.

Mai gadi ya girgiza kwarai dajin Alkawarin gida da mota kallon Katin dake hannun sa yayi.

Yaga

Anrubuta Yarima Samad salihu Turaki.

Tareda adresse d'in gidan sa da nombar Waya.

Faruk yace muna iya komawa cikin motar direct kamfanin zamu nufa muga Meye tsare tsaren da Aka fara.

Yarima Samad cikin gamsuwa da Hakan yakoma motar nasu...
.

Daidai suna fita layin .

Daidai da isowan Sheik dan gabatar da sallah la'asar.

Kallon motocin Sheik yake .

Jikin Lambar motar anrubata Yarima Samad.

Mai gadi yace Ranka yadade wayannan mutanen bincike sukazo yi.

Sheik dake kokarin daukar buta dan yin alwala yace Akan mekenan suke bincike...

Nuna masa Kati da yabasu yayi tareda sunan Wanda sukace suna nema...

Sheik yace basu nuna maka hoton sa.

Kash wlh ban tambaya ba.

Dan nasan Wanda suka nema bama a unguwar nan yake ba.

Daidai da isowar baba salihu shima yana sauri karya rasa Sallah.

Yaji Sheik n'a fadin

To ai a unguwar nan Kaf.

Babu wani Alhaji salihu Turaki .

Gaban baba salihu ne ya tsananta bugawa cikin dakiya yakaraso wajen nasu yanayin sa ya canja jiki babu kwari.

Buta yadauko yayi Alwala Sheik yace dan hanzarta mallam salihu yanzu zan tada sallah .

************

Bayan kwana biyu.

****

Rayuwa ta sauya sossai agidan iñda mama da Anty suka zama kamar kawaye damacen Anty saukin Kaine da ita mama ce ke nuna mata tsantsar kiyayya duk da boye halin Nata tayi dan tasamu Sheik yasauko daga yajin dayai mata .

Duk ranar kwanan ta 'falo yake kwanciya hakan ba karamin bakanta Ran mama yake ba.
Amma ta shanye ...

Cikin hanzari Rahama tafito toilet daure da towel ajikin ta 'agogon dake makale bangon dakin nasu taga Karfe takwas saura kwata.

Batare da Bata lokaci ba '
Tashirya tsaf cikin Kayan makarantar ta 'hijabin makarantar tasu bleu color dashaya guga tasaka cikin hanzari.

Salma sai wani cika take' tana batsewa Ganin yayar tata tayi shiga me kyau .

Cikin hanzari sukayiwa iyayen nasu sallama Domin yau zasu fara jarabawa.

Adamsy yashigo aji kasancewa yau shine zefara musu jarabawar .

Baza idanunsa yaketayi a makaranta dalibai nashigowa amma sam bega Rahama ko kanwarta ba 'rasa nutsuwar sa Yayi.

Harya shiga ajin ya kalli dalibai dakowan su ashirye suke tsaf dan afara .

Asiya kawar Rahama yakira yace tasameshi awaje babu musu...

Tafito tana kallon yanayin sa Daya canja.

Zararan idanun sa masu kashe garkuwan jikin Yan mata ya zuba mata .

Tareda tambayar ta meya Hana Rahama zuwa makaranta ne kuma yau jarabawa ta karshe.

Zata Budé baki t'ayi magana saika ga

Rahama Sun kunno Kai itada Salma.

Tafiyarta yake kallo Wanda wasu zasu iya cewa n'a takama ne 'amma itakuma wannan yanayin halittar ne 'ko ina n'a jikin ta n'a motsawa .

Kafarta sai ta daga Daya Ta tsaigaita sannan tasauke dayan .

Bakaramin tafiya da imanin sa tafiya ba....

Harsuka karaso gaban sa cike da ladabi ta gaishe shi .

Kunya ne yakamashi Ganin ta tsareshi da idanu.

Lfyalau yabata amsa tareda juyawa ajin .

Rahama da asiya da Salma da bakin ciki ya dabaibaye mata zuciya .

Ganin kallon da adamsy kewa Rahama..

Kusan karfe goma Aka fito brek ...

Asiya da Rahama zaune suke karkashin Wata bushiya suna tattauna yanda lecture da zasuyi nex

Tsintar muryan adamsy sukai tsaye akansu.

Yace bedace dake ba Rahama kizauna ke kadai batareda masoyin naki ba.

Murmushi asiya tayi Ganin Rahama tasha mur lokaci Daya.
Zama yayi gefen su.

Rahama n'a kokarin tashi .

Asiya tariko hannun ta pls dan girman Allah dawo ki zauna kinsan wulakanta dan Adam baya cikin dabi'ar ki.

Bawan Allah nan yanason ki Rahama yakamata kibashi dama.

Adamsy yakaraso gaban Rahama tareda durkeshewa akasa Yana kuka mai taba zuciya...

Dan Allah Rahama zuciya ta tana azabtuwa saboda Rashin kulawar dakike bani zan iya mutuwa Akan ki dan Allah ki kauna ceni.

Rahama jikinta yagama yin sanyi takalli Asiya tace pls kigayamai yatashi kada idanun mutane yataru Akan mu.

Wallahi Rahama bazan tashi ba agabanki ba saikin ce kin amince dani.

Kallon asiya tayi tana kwabe fuska ranta abace.
Asiya daga mata Gira tayi alamun ta amince kawai.

Zazzakar muryanta ya tsinta tana fadin katashi n'a amince .

Wani tsalle adamsy ya d'Oka tareda tashi yabar wajen cikin zalama.

*******

Amina tace Salma kinkosan ABUNDA ke faruwa kuwa '

A'a saikin fada inajinki!

Wallahi Adamsy da Rahama soyayya suke n'a ban mamaki ke dazun zokiga yanda ya diririce Akan ta harda dukawa akasa.

Wani katutun bakin cikine ya ziyarshi Zuciyar ta 'wasu zafafan hawaye ne suka silalo mata a kuncin ta.

Soyayya fa kikace ...

Taku har kullum kyauta daga Allah

Karku manta paid Book ne

09069080725
3/20/22, 22:34 - A'ish: *🌟🌟 KANWATA🌟🌟*

🔔📚

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌�*

MARUBUCIYAR

*Amince Dani*

*KAIKAJAWA KANKA*

Yanzu kuma gani dauke da

*KANWATA*

IKILIMA ADAM
(Kyauta daga Allah)

Paid Book ne
Vip 300
Spécial 500

Acct nomba 3115484026
ikilima adamu first bank
Ko kuma Katin MTN
Banason Vtu

Idan kinbiya kina iya turo shaidar biyar ki 'ta wannan lambar 09069080725

Book 1️⃣2️⃣

Ankusa gama free Book

Soyayya fa kikace

Nashiga uku ni Salma me natsaya kallo da har yayata zata samu saurayin da duk fadin kanon nan bantaba ganin Wanda yakaishi haduwa ba.

Dafa Amina tayi cikin kuka' tace yazanyi ne Amina wlh inason shi.

Kuma wallahi bazan taba barin Rahama ta aureshi ba 'uban kuturu yayi kadan bare n'a makaho.

Asiya kwabe baki tayi tace to me Zakiyi bayan aikin gama ya gama 'da dukan alamu itama Rahama tanason shi wlh.

To ina saurayin naki Al'amin yake ne.

Tsaki Salma ta jero Al'amin fa kikace in ana maganar Mazan kwarai pls kidaina sako shi.
.nidai kiban shawara yazanyi ne.

Asiya tadan numfasa kamar me lissafin tace nasamo mana mafita Daya ce.

Abu daya ne kawai kifito a mutum ki gayamai masa kina kaunar sa.

Inhar bé baki hadin Kai ba 'uhmmm munada hanyoyi dayawa.

Tafa hannu sukai Salma tace shegiya kawata shiyasa nake mugun sonki wlh.

Amma wannan tsinanniya yayar tawa mai farar kafa ' yo aidole ince mai farar kafa wlh duk inda zata sa kafa 'to nice da faduwa ina dalili tana Jamin bakin jini.

Wallahi badan mama tahaifeta ba 'da tuni nasan yanda nayi Aka koreta gidan nan.

Uhmm Salma Kenan yar uwar ki ce ta jini ki sassauta mata mana .

Aji suka koma hankalin Salma sam baya jikin ta ta lula duniyar tunanin adamsy.

Minti arba'i suka dauka kafun da bisani Aka tashi .

Rahama daukar jakar Salma tayi tana murmushi tace m'y kanwaty muje ko yau naga ko kulani bakiyi ba tunda mukazo skul.

Harara ta watsamata andai ji dashi tun dazun da idanun naki yarufe Akan Adamsy bakisan dani ba saï Yanzu.

Sakaka da baki asiya da Rahama sukai suna kallon ikon Allah 'amina dariya tabushe dashi tana gyara safar kafarta tace anty Rahama ki rabu da Salma fa aljanun ta ne suka tashi.

Kusan Dukan su dariya suka kyalkyale dashi Wanda hakan ya Sosa Ran Salma 'hawaye suka gani idanun shar shar .

Rahama tarufe tace my kanwati ke bakisan Wasa bane 'pls kiyi hakuri wallahi zolayar ki muke...
Zumburo baki tayi waje tafice gaba abinta.

Rahama tace kinga Asiya banga tazama ba tunda Salma tafice wlh karta kiramun ruwa bangama warkewa ba.

Dariya asiya take' saï da kuncin ta ya lotsa.

Kallon Amina tayi tace muna iya tafiya ko tunda tagudu tabi yar uwar ta.
Chapter 8 · 0% Book details