← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 115

Sashe 56

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana kokarin dagota Daga kwancen cikin sanyin murya yace meyake samun ki ?
Daman bakida lafiya ne ina ke miki ciwo duk yajero mata tambayoyin a jere lokaci daya.

Ita Ko batasan yanayi ba sai mutsu mutsu take hakan yasa lissafi ya kunce masa.
Kokarin daukar ta yake dan kaita daki saiya tuna da wannan d'octo family din su.
Wayar Rahama yadauko yashiga contact list din ta.
D'octo hamza ya rubuta saiko yaga nombar tafito.
Copy nombar yayi à wayar sa tareda danna masa kira.
Cikin sa'a bugu daya yadaga kasancewa bakuwar lamba.
D'octo yace dawa nake magana ne ?
Samad cikin damuwa yace Abdul Samad ne.
Mijin Rahama diyar sheik Imam yakarashe zancen yana kallon ta.
Dagacen bangaren yace au to nagane ina fatan dai lafiya Ko.
Samad yace Rahama ce tana fama da zazzabi tundazu sai mutsu mutsu take takasa bude Idanun ta.
Docto dake sauraren bayanan sa yace tanada ciki ne ?
Bakaramin kidima yayi ba Jin wannan tambayar ya maimai ta azuciyar shi.
ciki kuma Daga nace tana zazzabi sai tambayar banza.
Afili yace Ah Ah Docto batada ciki.
OK to yabashi Amsa gani nan zuwa ainasan gidan naku Daga hk ya katse wayar.
Zama yayi a gefen tana yana kallon ta.
Ta daina mutsu mutsu da take amma sai nishi takeyi a hankali.

Su Faruk à hanyar su takai Asiya gida suka isheta da surutu sai Murmushi take tana kallon Windows motar motocin da suke wuce wa take kallo.
Faruk yace Asiya !
Na'am ta amsa cike da kulawa.
Yace Amshi wayar nan kigani wannan hoton kokin San ta à unguwar ta ku.

Leka kansa yayi bayan motar tareda mika mata wayar.
Hannun biyu tasa ta karba '' kallon screen din wayar take hoton da ta gani bakaramin Girgiza ta yayi ba '' bakin ta na rawa tace kamar zanen Rahama ne wayayi mata.
Faruk da Aminu kallon juna sukai suna Murmushi.
Faruk yace nima dai naga suna yanayi da Rahama.
Amma kuma ze iya zama ba ita bace din.
Asiya ta numfasa tana kara kallon hoton dakyau har da zoomin din sa.
Zazzakar muryan sukaji tana fadin wannan dai zanen hoton Rahama ne Ko shakka babu.
Kuna taré da ita agida har wani neman ta kuke
nifa bangane ba ku fahimtar dani pls tana me kallon keyar Faruk dake zaune a kujerar zaman banza.
Faruk yaci gaba da magana tareda ba Asiya labarin wannan hoton Samad da ya dade shekara da shekaru yana nema.
Asiya tace to ku kyaleshi mana tunda ya kasa yarda itace ai wataran dole ya yarda inma be yarda ba shiya sani saiya bita a mafarkin ya Aure ta..
Kune m'a kuke biye masa.
Faruk yace to aidole mu biye masa dan mu m'a inmunzo da tamu tabarar tare dashi akeyin komai.
Yanada sa abu aransa ne
Mafarkin sa kamar wahayi yake Asiya.
Shiyasa inda ya nacewa Abu dawuya be cimmasa ba.
Aminu yace kwarai kuwa ai tabe tabe haka yake fa.
Asiya tace waye kuma tabe tabe ne ?

Faruk da Aminu suka bushe da dariya.
Aminu yace Yarima Samad inkiyar sa ne Tabe Tabe au baki sani ba.

Asiya tace uhmm bansani ba to ina sunan ya samo Asali ne tana kokarin mika wa Faruk wayar sa..
Farruk n'a karban wayar ya ajiye gaban sa yace.
Eh to wannan sunan ya samo Asali ne t'a dalilin kawar ki Rahama.
Asiya zatai magana
Aminu yace dan Allah manta dashi sunan ya samo Asali ne tun kuruciyar sa dan yacika yawan tabe taben ababen marmari.
Dariya Asiya mai fidda sauti Asiya tayi tace uhmm nidai banson kuna tsokanar mijin Aminiyata inajin kunyar ku.

Faruk da Aminu sukace Ah son kai Ko to munyi shiru.
Aminu rike da baki yace lallai ta nuna mana yan uban ci.
Ita dai Jin su take tana dariya....

D'octo Hamza da sallama bakin sa ya shigo kayataccen falon da be isan sa kallo.
Samad dake tsaye akan Rahama kallon D'octo yake cike da mutuntaka sukai musabaha.
D'octo yace wai me ke damun Rahama ne ?
Yarima yace zazzabi dai yake damun ta..

D'octo Hamza kokarin duba Rahama yake cikin kwarewa da sanin makaman aiki.
Yana duba ta yadawo da kallon sa Akan Yarima Samad yace wannan ba wani lalura bane..
Dan zazzabi ne kuma ze sauka InshAllah.
Kiran Sunan Rahama Docto ya shiga yi hakan yasa ta dan bude Idanun ta kadan ta kuma rufe wa
Kara kiran Sunan nata yayi wanda yasa takara bude Idanun ta tasauke su akan sa.
Cikin yin kasa Da murya yace Rahama meyake damun ki
Ba komai tabashi Amsa cikin kasalalliyar murya.
Doctor hamza ya kalli Yarima cikin son Fahimtar dashi yakamata akirawo wata Nurse mace ta duba ta da kyau.
Yarima yace to ai babu matsala akirawo ta.

Doctor hamza dannawa Nurse din kira yayi cikin gaggawa tareda yi mata Kwatance gidan Yarima..

Jigum Yarima da docto sukai a zaune suna jiran karasowar docto din.
Itakuwa Rahma sossai takeji felin n'a saukar mata ''
Tambayar kanta take wannan wani bakon yanayi ne haka ya ziyarce ta lissafi ya kunce mata.

Wayar Docto ne yasoma ring yana dubawa yaga nurse din '' fuskar shi dauke da fara'a yace zahra har kin iso ne kina daidai ina yakarashe zancen yana kallon Yarima ''..
Yarima kallon sa yake yana mai Alamun da hannun ta iso.
Kada masa kai yayi da kai tareda katse wayar.
Kallon Yarima yayi cikin sauri yace zanje in shigo da ita.
Yana fita yarima ya tallafo Rahama tareda zaunar da ita kallon Idanun ta yake yanda duk ta birkice lokaci daya..
Be San lokacin da bakin sa yafara furta sannu ba cike da iya furta lafuzan.

Kallon mai cike da ma'anoni yakewa Rahama dan yau ne karo n'a farko daya sata agaba yana kallo.
MashaAllah yafurta acikin zuciya '' besan maganar ta fito fili ba.
Fadi wannan yarinyar ashe haka take da kyaun gaske komai nata is normal bakin ta hancin ta.
Kallon tsafta yake bin ta dashi yana kallon kwayar Idanun sa da suke son tuno masa da wani abu n'a cikin mafarkin sa.

Sallamar d'octo da Nurse ne yadawo dashi Daga duniyar tunanin daya fada.
Bismillah yafada cike da kulawa yana kallon wannan matar da take sanye cikin fararen kaya nasu n'a likito ci.
Yawwa ta furta babu bata lokaci taje gaban Rahama tana kallon ta tace baiwar Allah Ko zamu iya shiga da ciki induba ki..
Yarima Samad dake kallon Nurse din yace bangane ku shiga Daga ciki ba.
Itama Rahama kallon da Samad yakebin Nurse din dashi shi take mata..
Nurse rike da baki dakuma sanin makaman aikin ta tace inban dubata ba taya zansan damuwar ta..
Yarima ya karbi zancen da batada wani damuwa fa karki damu basai kun shiga Daga ciki ba..
D'octo hamza shi lamarin Samad yafara daure masa kai shi kansa yaki bashi damar ya taba jikin Rahama saidai yace yafadi inda ake so ya taba din..
Kallon Nurse din yayi Yace Zahra kawai ki duba ta anan tunda a dakin bazeyu ba
Yarima Samad yace nimadai haka nagani dai.

Nurse tana me kallo Idanun Rahama tsaf taga wutar félin ne a Idanun ta Saboda tasaba Amsar wannan case din..
Cikin hikima tace baiwar Allah wani abinci ne kikaci n'a karshe..
Yarima zeyi magana d'octo yayi masa hannun Alamun yayi shiru.
Tsitt kakeji sun zuba mata idanu aji amsar ta.

Ita Ko Rahama cikin muryan ta da baya fita tace banci Abinci ba.
Sai ruwan lipton Sam batason Samad yaji tunda ya kasa ya tsare.
Nurse din kallon Samad da d'octo tayi tace dan Allah ku je koda compound din gidan ne akwai tambayar da zan mata ba lallai bane ta amsa a gaban ku ba..

Fita sukai Samad ba haka yaso ba.
Cike da kwarewa tayi mata tambayoyin da suka sa ta gano Zumar da maganin da tasha ne matsalar.
Kallon Rahama tayi cikin kasa da murya tace kinsan meye damuwar ki kuwa.
Girgiza kai Rahama tayi.
Nurse Murmushi tayi tace ai sha'awa ce ke damun ki kinje kindau Ko aiki dan haka zanwa mijin ki bayani..
Cikin tsoro da fargaba Rahama zatai magana.
Ganin Samad kamar anjefoshi Daga Sama yashigo cikin saurin sa docto ya take masa baya.

Kallon Nurse yake yace gayamin me matsalar amma tundazun kuna abu daya haba dan Allah yafada cike da gajiyawa..
Nurse dago kai tayi tana kallon sa tace babu wata matsala dake samun ta.
Baka biya mata bukatar aure ne.

Kalamar Nurse bakaramin doka zuciyar shi tayiba saida gaban sa yabada ras '' Rahama da docto kallon Nurse suke.
Rahma muryan ta na rawa kamar zatai kuka tace haba Nurse ya zaki ce haka nifa nasaba yin dan zazzabi haka kuma yasauka shine dai besani.
Takarashe zancen kamar zatai kuka..
Yarima Samad dake kallon ta sake da baki yace Nurse nifa bana fahimtar yaren da kike magana akai yayi hakane dan Rahama tayi tunanin begane me Nurse take nufi ba dan yaga tsantsar tsoro a Idanun ta..

Nurse tace au baka gane abunda nake nufi..
Yarima yace aikuwa bangane yanzu dai rubuta mata magani basai n'a gane ba..

Ajiyar zuciya Rahama tasauke duk da yanayin ta sai karuwa yakeyi.
Samad sallamar docto da Nurse yayi inda yabiya kudin aikin ta.
Ta tafi cike da godiya da irin biyan da yayi mata mai tsoka.

______________________________

Gabon 🇬🇦

Baba salihu sai safa da marwa yake yana kallon agogon hannun sa....
Dattijo n'a gefen cike da tausayawa yake kallon baba Salihu yace kayi hakuri ranka ya dade InshAllah komai zezo da sauki..

Jin Horn din wannan drever da yakai su Sheik masauki yasashi tunkarar mota '' cikin rawan murya yace tunda Allah yakawo bude mana mu shiga mana..
Drever shiru yayi ya kasa magana..
Baba Salihu kallon sa yake yace yadai nace kabude mu tafi kaki magana..
Cikin saisaita muryan sa yace Ya shugaba na.
Wannan bakon yabani takarda wai inbaka...
Hannun sa na rawa ya karbi takardan..
Abunda yafara bashi tsoro shine ganin hoton sa daya bari àcen kano.
Sai, wannan wasikar

Bude takardan yayi yasoma karantawa kamar haka.
Chapter 56 · 0% Book details