← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 115

Sashe 46

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Rahma tace kash nade t'aso ku babu shiri my kani sannu da zuwa.
Kallon Docto tayi tace mu je tayi gaba suka take mata baya dukan su.
Dakin tashiga bakin ta dauke da sallama ganin har yayi barci.
Ta karaso wajen gadon ahankali take shafa fuskar sa wanda yasa ya bude Idanun sa..
Yasauke su akan ta yana kallon coffe dake hannun ta yana turiri..
Shigowar su Farruk da Docto yasa tafara kokarin mika masa coffe..
Babu musu yakarba ahankali yake sha.
Yana lumshe Idanun sa Alamun yaji dadin sa dan cikin sa yayi dumi sossai.
Kokarin ajiye kofin yake hakan yasa Rahama tayi sauri karba Daga hannun sa sannu take ta jero masa akai akai cikin tsananin damuwa.
Docto Ishaq matsowa yayi kusa dashi tareda duba sa cike da kulawa.
Kallon Docto suke yanda yake ta abu daya tun dazu.
Faruk cikin Kosawa yace Docto kagano matsalar dake d'amun sa ne har Amai yayi hade da mugun abu acikin sa
salati Docto yafara yace subuhannalah acikin nasa..
Aminu yace kwarai kuwa tareda kunna masa hoton daya dauka..
Cikin tashin hankali Docto ke kallon hoton cikin damuwa yace nidai gaskiya à iya fahimta ta wannan ciwon bana asibiti bane..
Zan masa allurar daze yasamu barci sossai yatashi da karfin jikin sa.
Magunguna ya fiddo Daga jakar sa.
Ya mikawa Rahma...
Hannun biyu biyu ta karba..
Wayar ta ne yasoma ring tana dubawa taga Abba ne..
Cikin hanzari ta Daga wayar tareda karawa a kunne cikin sanyi murya tagaishe shi Dagacen bangaren yace kin kira harna kwanta barci yau da wuri n'a kwanta..
Sa'adatu tace Mijin ki babu lafiya har Abdul jalil yaraka docto gidan naku..
Rahama tace eh Abba sunzo jikin ma dasauki tana son tayi wa Abba bayani ganin mutane à dakin yasa tafasa...
Abba yace Allah yakara lafiya ku kula dashi dan Allah kinji yata.
InshAllah ta furta tareda yin sallama ta ajiye wayar.
Docto da Abdul jalil sallama sukai masu akan zasu koma..
Rahama godiya tayi musu '' su Faruk da Aminu rakiya sukai masu.
Kudi Faruk yadauko da niyar sallamar docto amma fur yaki yace ai yiwa kaine karsu damu.....

Rahama gyarawa Samad kwanciya tayi tareda rufa masa blanket ajikin sa..
Zaune takoma tayi tagumi tuna abunda ke gabanta yasa ta tashi tareda dauro Alwala tayi shafa'i da wutri..
Alkur'an mai girma ta dauko ta bude tafara karanta shi cike da nutsuwa muryan ta na tashi tana karatun tana kallon Samad dake motsawa a gadon sa.
Faruk da Aminu sake dawo wa cikin dakin sukai ganin Rahama na karatu shikuma barci yake hakan yasa suka juya dan zuwa nasu dakin..
Aminu yace kaga ikon Allah Ko badan yarinyar nan ba ya zamuyi dashi wlh iyaka mukai shi Asibiti ayi ta magani daban cuta daban..
Faruk yace kasan kwanakin baya sanda baka gari wlh yayi ciwo sossai dan har nacire rai akan ze tashi.
Ba d'are ba rana haka muke kuka nida Mamy da kannen sa.....
Aminu yace subuhannalah andade ana ruwa kasa n'a shanyewa kenan.
Yakamata mu kira Mamy à sanar mata da abunda ke faruwa cewar Aminu..
Faruk yace hakane kuma tareda lalubo wayar sa ya dannawa Mamy cikin sa'a kuwa ta Daga hakanan taji batada nutsuwa banda bugawa babu abunda zuciyar ta takeyi.
Cikin rawar murya tace Faruk ina fatan dai lafiya Ko.
Farruk yabata labarin abunda ke faruwa cikin tsananin tashin hankali tafara kuka tace shikenan d'ana ze mutu.
Hawaye shar à Idanun ta.

Farruk yace Mamy hakuri zakiyi ai yasamu kulawa sossai gun matar tasa kinga itace silar fitar mugun ajiyar dake cikin cikin sa.
Mamy tace ina matar tashi take 'Faruk yace tana dakin su inkai mata wayar ne ?

Eh kai mata wayar nan dan Allah.
Cikin sauri sauri ya nufi dakin iske Rahama yayi zaune inda yabarta karatu takeyi hartayi nisa tsitt kake Jin dakin banda sautin muryan ta da kamshi turare babu abunda ke tashi adakin...
Cike da kulawa yace Madam Samad mamy zatai miki magana yafada yana me mika mata wayar.
Amsa tayi tareda ajiye Alkur'an à gefen ta cike da girmamawa ta gaida Mamy ta amsa da lafiya lau ya me jiki.
Tace yaji sauki Alhmdulilah.
Mamy shiru tayi tana nazarin tayanda zata bullo mata..
Cikin sassaita murya tace diyata Rahama ta amsa da naam tana me maida hankalin ta akan abunda take shirin fade.
Mamy tace dan Allah kisa idanu sossai akan sa '' ki taimakeni yanda Allah yataimake ki Rahama.
Dan Allah karki ringa nesa d'ashi indai yana gida Ko baya gida ki ringa bin diddigin sa.
Rahama cikin sanyin jiki tace InshAllah Mamy zan kula.
Cikin Jin dadin Amsar ta Mamy tace Allah yayi miki Albarka nasan dai yayi barci Ko
Rahama da Idanun ta na akan sa tace eh yasamu barci sossai ma.
To dan Allah karki kiyi nisa dashi koda cikin d'are ne.
Maganar Mamy bakaramin tada mata hankali yayi ba ita da take shirin ta shimfida bargon ta akasa tunda yau kwana ya kamata adakin sa..
Mamy tace dafatan dai kingane abunda nake nufi..
Rahama tayi shiru bata bata Amsa ba..
Mamy tsab ta lura Rahama tana Jin kunyar ta sossai Daga haka sukai sallama.
Ajiye wayar tayi gefen gado ganin Faruk yafice..
Cikin sanyin jiki taje ta murzawa dakin key tareda dawowa cikin dakin.
Samad da yanzu yafarka amma be bude Idanun sa ba. Kallon ta yake yanda take ta safa da marwa acikin dakin.
Zam Zam n'a hannun ta wanda ta juye a kofi yaga sai adu'oi takeyi ba kakkautawa tana gamawa ganin ta nufo inda yake lumshe Idanun sa yayi kamar me barci.
Yana Jin yanda take shafa masa ruwan adua ajikin sa har zuwa fuskar.
Taci gaba da shafa masa har zuwa wajen marar sa daidai hannun ta na kokarin..............

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:44 - Nuriyyat: Uhmm masu fitar da novel.
Masu jiran n'a sata ayi kusha zaman Jiraa dakyau fa.
😏

5️⃣0️⃣

Hannun ta na kokarin taba Samad din tayi saurin zame hannun cikin Jin tsoro 'kallon ta yake jiyayi kamar su shekara ahaka dan duk da ciwon da yake ji hakan be hana shi Jin félin n'a t'aso masa.
Kallon ta yake yanda take kokarin ajiye ruwan hannun ta.
Blanket ta rufa masa.
Kallon fuskar sa take taga eh lallai barci yake..

Uhmm kaga mutum dan beda lafiya duk ya saki jikin sa saikace karamin yaro '' komai sai anyi masa ni yanzu inama zan kwanta ne tafada afili kallon bakin gadon tayi tace uhmm bara indan kwanta anan kafun ya tashi
n'a farka karya ganni tana me kokarin sauka Daga kan gadon tayi dan canza kayan jikin ta zuwa n'a barci.
Kayan barcin ta dauka direct bandaki tashiga dan saka su.
Murmushi yayi ganin ta tafi bandakin yana cikin tunanin maganar yarinya nan da suka hadu à rijiyar lemu yake
so yake ya tambayi Faruk akan tabbacin zancen nata
Wata zuciyar tace masa tokai Samad idan kaga zanen hoton ka da ka dade kana nema ya zakai da Rahama.
Murmushi yayi azuciyar fadi yake ita Rahma *KYAUTA DAGA ALLAH* CE.
Wancen muradin raina ce.

Ahaka har barci barawo yai gaba dashi..
Tana fitowa Daga bandaki cikin sauri sauri taje tasamu wajen cen karshen gadon takwanta.
Tunanin mafita take yi so take taji tarihin Yarima Samad '' kasa kwance tayi tareda zama ta zabga uban tagumi lallai abunda tagani bakaramin tada mata hankali yayi ba.
Koma wanene tana tabbacin asiri akai masa.
Oh lissafi ya kwace mata so take tasan tasan komi game da Yarima Samad wa zan tunkara kenan take tambayar kanta.
Wata zuciyar tace haba Rahama ke kuwa kike da wayanda zasu baki labari tiryan tiryan.
Khadija ce ta fado mata arai Girgiza kafafun ta takeyi lallai ba shakka badan d'are yayi tabbas da na kira khadija dan inji Ko tasan wani abu game da yayan nata.
Ahaka barci barawo yai awon gaba da ita..
***********************

Alarme din wayar sa ne yasoma kara '' ahankali ya bude Idanun sa tareda sauke su akan ta barci take amma da ka kalle ta sai kayi zaton Idanun ta biyu.
Harda gajiya suka dirar mata lokaci daya...
Sauka Daga kan gadon yayi yana tafiya babu kuzari a tattare dashi amma tabbas yaji sauki sossai akan jiya..
Jin karar bude kofar bandaki ne yasa arazane ta farka.
Cikin hanzari ta nufo sa.
Cikin muryan barci tace ina zakaje ne tana murza Idanun ta.
Kallon ta yake cikin yin kasa da murya yace bakiga time din Sallah yayi bane batareda yajira cewar ta ba ya shige.
Ta kai minti biyar tsaye inda yabar ta kallon kofar bandakin take.
Ko me ta tuna tajuya zuwa dakin nata.
Àcen tayi sallah tana idarwa ta tazauna yin azkar saida haske yafito Sannan ta fada bandaki tayi wanka da ruwa mai zafi dan sanyi ake yi ba kadan ba..
Shiko Samad yau adakin nasa yayi sallah anan kan darduma barci yayi awon gaba dashi.

Faruk da Aminu sanye suke cikin farar jallabiya hannayen su cikin Aljihun rigar su.
Daga massalaci suke.
Aminu yace anya Samad ya tashi kuwa.
Yakamata mu kyaleshi zuwa anjima tunda matar sa tana nan.
Takun tafiyar Rahama yasa hankalin su yadawo akan ta.
Ina kwana tace musu a mutunce suka amsa mata da lafiya lau.
Chapter 46 · 0% Book details