← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 115

Sashe 113

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shugaban Adalai cike da izza yafito Daga cikin masarautar magoya bayan sa..
Duk suna biye dashi a baya...
Basu bata lokaci ba dukansu wajen tafiya kotu ba..
Ko kan su isa cen..
Fulani da Maman Maryam da saratu duk suna cen......

Kowa yana kotun hatta Alkalin yana zaune kawai shugaban Adalai ake jiran karasowan sa..
Abban Maryam shida Amaryar sa suka iso kotun...
Liman Bohicon mahaifin mamy da Firdausi da Yaya Auwal da Sani duk kowa ya kama waje yazauna..

Koda shugaban Adalai ya shigo hakan yasa gabadaya kowa wajen y tashi tsaye hatta Alkalin saida ya tashi..
Kujerar da shugaban Adalai ze zauna akai baya cikin jerin wayanda kowa yazauna tashi daban take tasha ado sossai irin n'a yan sarauta......
Yana zama kan kujerar kowa yazauna hadda Alkali muh'd Haruna....
Mamy kallon mijin nata take kamar wani bakon mutum sossai yayi mata kwarjini a idanu musamman dataga yazauna yaja girman sa.....

Me bayani dake zaune tashi yayi yasoma magana yayin da yan jaridu suna daukar bayanan sa da caméra da lasifika.....

Kamar yanda kuka sani taron shari'a ne za'ayi tsakanin shugaban Adalai da wasu mata guda uku....

Wanda suka hada baki wajen cutar dashi..
Cikin su akwai yar matar sa..
Akwai matar kanin sa..
Sannan da baiwa.

Alkali gyaran murya yayi yace Ko akwai lauyan wanda yake kara...

Yarima Samad tashi tsaye yayi yace ya mai girma mai shari'a gani nan..
Sunana Abdul Samad Salihu Turaki...
Nine lauyan mai kara..

Alkali yace akwai lauyan masu kare wanda ake kara...

Me bada bayanai yace babu yamai girma mai shari'a...

Alkali rubuce rubuce yayi Sannan ya Dago kai yana kallon Samad yace lauyan mai kara muna sauraren ka...

Yarima Samad cike da takama yafara bayanin duk abunda yafaru zuwa abunda suka bugawa mahaifin sa...
Sossai kotun tayi tsit babu abunda kake ji sai karar fanka...

Alkali sossai ya jinjina Al'amarin yace lauyan me kara Ko akwai tambayoyin da zakayi wayanda ake zargi
Yarima Samad gaban nasu ya isa yana kallon Maman Maryam yace kotu tanason tasan sunan ki..
MAMAN MARYAM.. Tace sunana Farida Ahmad.
Mata ce awajen Garba..
Yarima yace Ko zaki iya fadawa kotu dalilin daya sa kuka kulla wa shugaban Adalai sharri..
Maman Maryam ajiyar zuciya tasauke tana kallon mijin nata dake zaune kusa da Amarya sa...
Tace nayi hakane da inason mijin kanwata...

Gabadaya kotun zazzare idanu sukayi hatta Abban maryam din..
Yarima Samad yace shine kika zabi ku kulla masa sharri..
Tace A'a nayi nayi ya rabu da habiba ya aureni yaki amincewa '' shine nayi masa haka dan in tozarta shi yaji bakin cikin danake ji inna bude idanuna ina ganin sa da kanwata alhalin Nice nakeson sa tun farko shine ya zabe ta yabarni...
Mamy fashewa da kuka tayi sossai a wajen....

YARIMA Samad yace mungode malama Farida...
Gaban Fulani yakoma ita ma ya bukaci ta gayawa kotu sunan ta......
Fulani tace Sunana Salamatu bashir...

Yarima gyara Tsayuwar sa yayi yana kallon agogon hannun sa yace...
Ko zaki gayamana dalilin dayasa kuka kulla wa shugaban Adalai sharri..

KUKA ta saka sossai tace.. Tace wallahi hassada ce Saboda banaso yaci gaba da mulkin nafison ta dawo hannun mijina da d'ana...
Yarima Samad murmushi yace mungode Farida....

Gaban Saratu ya nufa yace Sarki yawo yau dai Allah yakawo ki nan zaki iya gayawa kotu sunan ki...

Saratu Muhd tafada ataikaice...

Saratu kina iya gayawa kotu meyasa kika aikata mugun aiki..

Bakin ta narawa tace Wallahi Fulani da Farida suka sani sunce inhar ban aikata ba zasu kulla min sharri sata kuma nasan hukunci sa a masarautar...
Akarshe da na nemi intona Asiri sai sukasa akasheni shine dalilin guduwa nabar masarautar......

Alkali dake saurarann nasu yace kotu ta gamsu cewar Anyiwa Shugaban Adalai sharri ne dan haka kotu ya wanke sa...

Fulani anyanke miki zama gidan Yaro tsawon shekaru 15..
Kema Farida haka..
Ita kuma Saratu bisa turasasa ta da sukayi shekara goma zatayi..

Gabadaya kotun tadauka da ALLAHU Akbar...
Mamy zuwa WAJEN farida tayi kafun awuce dasu tace yar uwa n'a yafe miki duniya da lahira kuka take. Sossai ta rungume Farida.....

Kallon ta tamaida kan Fulani tace kema n'a yafe miki..
Hakama Saratu.....
Sossai kotun ya tashi da hayaniya sai cece kuce ake yi...
Abban Maryam zuwa yayi gaban Farida yace yanzu gidan Yari zaki je koda zaki fito wallahi kin tsufa baki moriya dan haka n'a sake ki...
Kuka ta fashe dashi tana fadin wayyo kaicona...
Nan da nan aka fara bawa shugaban Adalai hanya ta bisa jagoran jami'an tsaro.....

Kusan kowa Agajiye suka dawo gida..
Liman Bohicon sossai yayi kuka kuma Yayiwa Yarsa Farida fatan Allah ya kaddara saduwar su...
Kuma Yayiwa Shugaban Adalai murna da samun yanci..........

Bayan Sati biyu bikin Su Faruk ya gabato inda su Rahama da Samad da Asiya sune kirjin biki..
Sossai suka gyara Karima ta koma kamar ba ita ba....tasha gyara sossai wajen mamy ita da hauwa...

Hauwa zaune kusa da Mamy cikin zazzakar muryan ta tace uhmm Mamy nidai da za'a bar nawa bikin saina kara girma...
Mamy tunstsirewa da dariya tayi tace to Saboda me hauwa'u n'a...
Uhmm nidai wallahi banason rabuwa dake Alkur'an tana kwabe fuska cikin shagwaba..
Murmusawa Mamy tayi tana shafa kanta tace karki damu ai mijin daze aure ki da mijin Karima duk anan masarautar zaku zauna '' Shugaban Adalai yace Sam baze iya nisa dasu ba dan abokan arziki ne wanda suke wa Samad so n'a tsakani da Allah...
Wayyo Mamy dadi kashe ni cewar hauwa
Cike da ni nishadi suke firan su.....

Wannan karan sossai masarautar takara amsar gayyatar baki Daga nesa dana kusa...
Yan uwan hassana duk sun hallara Daga Gabon...

Hassana ita da Sheik suka zo bikin kasancewa cikin anty ya tsufa shiyasa aka barta agida..

Mahaifin Karima da mahaifiyar ta Iya Firdausi sossai sukayi tsantsani da jama'ar su zuwa wajen daurin auren yar su...
Faruk da Aminu da Marwan wannan ranar babu kamar su dan kaya kala daya suka saka anko farar shadda harda Samad da Ahmad

Sadakin daurin auren nasu Samad ne yabiya kowani ango millions daya...
Sheik sossai yasamu tarba mekyau musamman wajen shugaban Adalai nan nan yake ta yi da sheik..

Sheik shine yayiwa Faruk wakilin ango....
Sossai wajen daurin auren nan yatara dunban jama'a harda manyan manyan kasar irinsu Shugaban Kasar kwatano patrice Talon duk da Arne ne saida ya halacci wannan gagaramin taron..

Faruk zoga murna awajen sa shida Aminu mussaman d'a sukaji ance nan masarautar zasu zauna murna fal acikin su bazasuyi nisa da Samad ba...

Sai kusan karfe shidda n'a yamma aka kai Amare kowacce dakin mijin nata..
Hauwa tayi kuka sossai dan batayi zaton aure nan kusa ba...
Hassana tace haba yata keda zakiyi murna koba komai kina kusa da Mamy..da kalamai masu taushi suka rarrashe ta....

Bayan kwana biyu da bikin iya Firdausi suka koma kasar t'asu cike da kewar Mamy da Karima..
Dan Karima tayi kuka sossai Faruk yace mata karta damu zasuje taré ziyara dan wannan rarrashin ta dan samu sukuni...

Kowa ya watse Alhmdulilah har Sheik yakoma tareda hassana Amarya..
Koda suka isa sun iske anty babu lafiya jikin nata radau yadau mugun zafi....
Yayar tace kusa da ita tana shirin kaita Asibiti dan Salma dake kwance haryanzu babu lafiya dan wannan kuban yayi nasarar taba zuciyar ta...
Kwance take tana kallon yanda su Sheik suka rikice dan kai Ànty Asibiti......
A gaggauce suka isa..
Likitoci sukayi ca à kanta inda kai tsaye suka nufi blok da ita....

Koda babban likitan yafito samun sheik yayi da zancen dole saidai ayi mata CS sheik ganin halin da take ciki cike da rudewa kada ya rasa matar sa yace Ayi mata aikin su gaggauta...

Sossai likitoci suka rufa akan ta suna kokarin yi mata aiki... Saiga nakuda tazo da karfin ta wanda yasa tana nishi ta jefo yar ta '' katuwa 'wani sabon nakudan yakara tashi kankace me ta sake haifo ya mace' likitocin cike da Al'ajabi ganin wannan karamin cikin nata ta haifo yan biyu mata masu kama da Rahama sak komai nasu iri daya...
Kuka suke tsala wanda hakan ya tabbatar wa sheik har angama opération din.
Babban Burin sa yajikin sa'adatu yake.....
Koda likitar yafito cike da Zufa da kuma gajiyar wahala da suka sha akan ta..
Bakin sa dauke da Murmushi yace Sheik matar ka da kanta ta haihu ta haifo tagwaye mata...
Sheik bakin sa dauke da Murmushi yace MashaAllah MashaAllah tagwaye nasamu.

Agurguje ya nufi wajen hassana da yayar anty ya sanar musu da batun haihuwa yaya biyu..
Cike da Farin ciki hassana tace wayyo abun dadi tagwaye ta haifa MashaAllah.
Sheik zumudi yasa shi kiran Shugaban Adalai ya sanar masa haihuwa har Rahama saida yakira ya sanar mata...
Cike da Jin dadi tace Abby zanzo suna...
Ah Ah Rahama kiyi zaman ki naji ance kema kina hanya Allah yaraba lafiya '' Rahama cike dajin haushin hanata zuwa tace Abby naji ance ranar suna za'a daura auren yaya Abubakar..
Sheik yace kwarai kuwa haka muka tsara.....
Dan Jim tayi yace lafiya kuwa Rahamatullah..
Bakin ta dauke da damuwa tace dan Allah dan zatin ubangiji Abby kadawo da Mama sossai take kuka.....
Jikin sa a mace yace Rahama tunda nake dake baki taba rokona wani abu ba kasancewa n'a mahaifin inna ce Ah Ah ban miki Adalci ba '' daman inada niyar dawo da ita nabar ta ne ta dan sha iskan gida..
Nan yakwashi abunda yafaru da Salma yafada mata..
Sossai take kuka tace yanzu Abby Salma bazata sake samun ciki ba.
Innaliahi wa'inna il ai rajun take ta maimaitawa...

Sheik yace wannan Aya ce agare ta da duk mai irin halin ta...
Karki damu ana gobe suna zan dawo da mahaifiyar ki...
Daga hk sukayi Sallama...

Kwanan su daya à Asibiti aka sallame su..
Sossai Ànty tayi murna da samun yaya mata..
Ranar suna yara sukaci sunan Hassana da hussaina...

Hassana kam ba'acewa komai Saboda tsabar murna an mata takwara aranar sai fadi take yaran hannun ta zasu ringa wuni da anyaye su sunzama nata..
Ànty tace InshAllah nabaki yan biyun nan sossai sheik Kéjin dadin mu'amalar hassana da Sa'adatu..
Misalin karfe hudu aka daura auren Abubakar Sadik tareda Amarya sa Zahra sossai gidan yacika da murna haihuwa data aure..
Chapter 113 · 0% Book details