← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 115

Sashe 22

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Eh kinbata lokaci kinsan yamma tayi ya kamata ace mun shirya ki dan Abba yace za'a zo daukan ki da Anyi sallah isha'i.

Rahama saida gaban yafadi Jin za'a zo daukan ta azuciyar ta sai fadi take nashiga uku Ko wane ne mijin nawa.

Kallon anty tayi lokaci daya Idanun ta suka ciko da kwalla tace to ànty bara nayi sallah sai inshirya.

Asiya dake mata kallon so da kauna da tausayin aminiyar ta cikin sanyi murya tace bara inje gida insanar zanbiki gidan mijin naki dan acen zan kwana da safe Ko zuwa yamma In Allah yakaimu sai indawo gida.
Cikin nutsuwa take maganar.

Cike da gamsuwa da bayanan ta anty tace hakan ma yayi kinga kinsamu kidan tausasa mata zuciya kinsan abu da zafi zafin yake yanzu azuciyar ta.

Asiya wucewa tayi Rahama tace saikin dawo dan Allah karki dade.
Gyada mata kai tayi cike da tausayawa.

Anty tace gaskiya Rahama kinyi dacen kawar arziki kinga yanda take kuka sossai dazun kuwa da akace anfasa daurin auren ki da Adamsy andaura da Abdul samad.

Rahama sunan Abdul samad taketa juyawa cikin zuciyar ta dan sai yanzu tasan sunan mijin da aka aura mata.

Yayar ànty tace ai abunda Asiya tayi Allah ne kadai zebiyata ance sai hali yazo daya ake abota.

Ita wancen me bakar kafa ai batada kawayen arziki tana kallon salma data dukar da kanta kasa.

Rahama n'a idar da sallah nan da nan aka shiga shiryata me makeup Anty takira dakyar Rahama tayarda akai mata makeup din saida taga ran Anty yabaci Sannan ta amince.

Wani hadadden shadda gezner n'a kwatano wanda akalla kudin sa zekai kimanin dubu dari.
New design ne new fashion.

Riga da siket akai mata shaddar maroon color ne yasha ado da goldin color bakaramin kyau yayi mata sossai ajiki ba.
Dayake tanada tsayi ga ta farar mace mai cikar halitta bob.
Ga hip

Nan da nan wannan dinki yazauna mata dass a jikin ta tareda fitar dawani sirritancen kyawun Rahama wanda yasa dakin sukaita ihu suna shewa hade da tafa hannayen su.

Suna ta fadin azo aga Amarya Rahama wallahi saide haushi saide à mutu.

Salma bakaramin tashin hankali tashi ga ganin yayar ta yanda tasha kyau harta gaji gashi sai habaice habaice suke ta jifan ta dashi.

Cikin zafin nama takaraso inda suke tace wallahi kunji kunya bandaku sakarkaru ne taya zakuyita habaice habaice inba tsoro ba kufito fili mana tana magana cikin bacin rai.

Kuma Rahama da kuke karewa kune bakusan wacece ba to wallahi karuwar gida ce bari ku gani.

Sake da baki kowa ke kallon ta cikin dakin. dauko wayar tayi ta shiga whsap tareda nuna musu hoton da Rahama tana kwance kan wani.

Anty karban wayar tayi tana kallo zoomin din hoton tayi taga eh lallai maganar salma hakane amma ahoton yanuna kamar faduwa sukai.

Tsaki take ta jerowa tareda je fa mata wayar ta.
Tace wannan hoton yana Daga cikin mugayen halayen ki ke ce kika dauka dan ki bata mata suna.
Kuma Daga gani kindauka ne dan ki nuna zallan kiyayya ki agareta dadina da Abun kema dai andaura miki aure ki tafi mun gani Ko zaki iya zaman auren tafada cike da Jin haushin ta.
Mu wallahi yanzu muka fara ganin kimar ta da darajan ta.

Rahama da duk abunda ake tana jinsu banda kuka babu abunda take yi.
Azuciyar ta sai maimai ta kalmar karuwan gida da salma ta fada take.
Afili kuma kallon su ànty tayi tace ku barta da halin ta ni bazan ce mata komai ba.
Tayi magana cikin raunin murya da tafasan zuciya.
......

Kasar Gabon.

Baba salihu zaune yake gaban talabin sa yana kallon tashar Arewa 24

Lumshe Idanun sa yayi yana tunanin halin da sheik ya shiga n'a rashin dawowar sa.

TV nata aiki shikadai batareda ya maida hankalin akai ba 'remote yadauko yana kokari kashe TV yaga wani.
Sanarwa.

Yaji ana gabatar da labari da dumin dumin sa.
Shahararen malamin Adinnin nan mai suna sheik Abdurrazak kabeer hizqeel makarfi.

A yau Ranar juma'a aka daura auren yayan sa ga kadan Daga ciki dafatan masu kallo suna biye damu.
Dan Jaridan ke fade alaman gabatarwa

Baba salihu daya shagala da kallon TV sakin remote yayi Daga hannun sa tareda gyara zaman sa.
Ya tattara nutsuwar sa wajen kallo.

Hasko vidéo daurin auren dayaga anyi yanata baza idanu koze hango sheik acikin su.
Ganin mai martaba acikin vidéo bakaramin tashin hankali ya shiga ba.
Afili yace Abba meya kaika kano 'batareda ya rufe bakin sa Yaji ana fadin andaura auren Rahama da angon ta Abdul samad.
Bisa sadaki dubu dari.

Salma tareda angon ta Al'amin zumbur ya Mike Daga zaune yanata safa da marwa cikin tsakiyar falon.

Banda wasi wasi babu abunda zuciyar sa take yi yace to ainaji Adamu zata aura ya akai aka fasa auren kuma wani Abdul samad ne me sa'a haka daya samu Rahama.

Kuka yake da iyakar zuciyar sa yace sheik ban kyauta maka ba.
Bancika Adali ba gashi bankawo d'ana ba Sannan Rahama bata auri wanda takeso ba.

Toshi wane ne wannan Abdul samad din yake tambayar kansa.
Cije labbansa yayi yace shikuma Abbana waya gayyace shi daurin aure.

Rasa me bashi Amsa yasa ya danna kira gun me bashi labari.

Wayar nata ring ba'a daga ba zama yayi kan kujera tareda dafe kansa dake masa ciwo.

Yace shekara nawa rabon da inga fuskar mai martaba saiyau yau ma din a TV
Uhmm inama ace zan iya danaje gareka mai martaba ya fada cike da raunin murya.

dattijon gidan sa yataho gaban sa tareda durkusawa yace ya shugaban Adalai mai tausayin talaka.
Naganka cikin matsanancin damuwa kozaka iya fadamin damuwar ka.
kansa adauke yake.
Cikin tausasa murya yake magana.

Baba salihu ya kalle sa. Yace haba malam Musa nace kadaina durkusa min Daga masa hannu yayi Alamun ya tashi Daga durkeshen da yayi.

Kallon dattijon yake wanda zasuyi tsara ashekaru kokuma ya girme sa.

Yace bismallah zauna.
Zama dattijon yayi suna fuskantar juna.
Baba salihu à jiyar zuciya yasauke yace bari inbaka labarin wani butulcin d'ana aikata à kano.

Dattijon kallon sa yake yana jujjuya kalaman sa yace ranka yadade ina sauraren ka.
Tareda maida hankalin sa akan sa.

Dan numfasawa baba salihu yayi yabashi labarin sheik da auren daya amince zebashi dakuma dalili baro kasar.

Dattijon yace ya shugaban Adalai ai wannan ba butulci bane kaddara ce haka Allah yatsara wannan yarinyar bazata auri danka ba kuma bazata auri wanda take so ba.

Naka kawai kabisu da Adua.
Sossai baba salihu Yaji dadin kalamin wannan dattijon da kansa yadauko lemukan kwali Daga frij din falo tareda tsiyaya musu à cup ya mika masa.
Shima yana shan na hannun sa.

Dattijon mamakin saukin kai irin n'a baba salihu yake duk da yasan shi jinin sarauta ne amma saukin kan nasa yayi masifar yawa.
...

Kano.

Yarima Samad dakyar aka shiga dashi cikin gida yayi daidai da shigowan mai martaba da su mamy da khadija da Ahmed.

Mama karama tana gaba.
Sani baban marwan yanata buga uban sauri dan ji yake kamar ze mutu dan bakin ciki
Yace kashin shi yabushe tunda aka daurawa Abdul samad aure.

Cikin hanzari ya shiga gidan tareda kama hannun dan sa Marwan suka shige dakin sa.
Domin zantawa.

Faruk nan tsakiyar falo suka zaunar da Abdul samad.
Sunata buga masa baya Alamun rarrashi.
Aminu yace Kayi hakuri wallahi Alkhairi ze zame maka wannan auren.

Jajayen Idanun sa da suka kada ya dago yake kallon Aminu cikin rawan murya yace Alkhairi ne kace Ko yana me watsa masa mugun kallo.

meyasa baka bari andaura auren dakai ba sha sha kawai wallahi natsani wannan auran.
Bari kuji kaida Faruk kune ku rirrikeni da karfin tsiya dan naso inje n'a murje bakin waliyin Amaryan kuka hana to wallahi kuma kun ciyo bashi.

Kokarin tashi yake zeshige dakin sa.
Yaji muryan mamy ta buga masa uban tsawa saida kowa cikin gidan ya firgita dan basu taba ganin ta cikin wannan yanayin ba tunda suke.

Cikin Azzama takaraso falon cikin bacin rai tace kai uban wane ne da zaka ce sai abunda kake so shi zaka samu.
Tana me tsare shi da Idanun ta da suka kada Daga fari zuwa ja.

Cak Yarima Samad ya tsaya yana sauraren kalaman mamy da Sam basu sassauci a ciki.

Taci gaba da magana cikin bacin rai da Daga murya tace kai harka kai mai martaba ya zartan da hukunci akan ka.

Kaja da maganar sa har kana kokarin zuwa kunyata shi gaban dunban jama'a dan kawai yace adaura maka aure.

Wai ma in tambayeka kai à zaton ka haka zaka kare rayuwar ka batareda aure ba.

Kayi kuskure Samad tun wuri ka canza tunanin ka.

Umarnin da zanbaka yanzu shine maza ku dau motoci guda goma kuje daukan Amarya kuma wallahi tallahi kaje har wajen uban Amaryar ka. ka gaishe su tareda nuna musu farin cikin ka.

Cikin zazzare idanu Samad......

Taku har kullum kyauta Daga Allah

Ku daina fitar mun da littafi.

Duk wacce taci karo da littafin nan awajen groupe dîna.

To duk n'a sata ne.

Inkinada bukata ki tuntubeni 09069080725

Wayyo masu fitar mun da novel bazan gaji da fadi ba kuyi hakuri ku daina.

KYAUTA TV channel YouTube dîna pls dan Allah ku shiga ku danna mun subcribe.
3/20/22, 22:34 - A'ish: KANWATA

Akwai channel dîna KYAUTA TV kushiga kumun subcribe.

Littafin kaikajawa kanka
Audio yana kan channel dîna saina jiku.

Littafin nan n'a kudi ne
Inkin ganshi a wajen group dîna na sata ne.
Inkina bukata ga nomba
09069080725.

2️⃣8️⃣

Cikin zazzare idanu Samad ke kallon Mamy kuka ne kawai beyi ba amma da duk Alamu yanuna soya ke yayi kukan dan gani yake bakaramin dauriya yayi ba tundaga wajen daurin auren har zuwan sa gida.

Mamy gaba tayi tanata fada khadija nabiye da ita abaya.

Mai martaba da mama karama kallon Samad suke yanda yakoma karamin yaro bilhakkin kuka yake da iyakar gaskiyar sa.

Dafashi mai martaba yayi cikin Rarrashi yace Abdul Samad aure fa ba mugun abu bane yarinyar nan da aka aura maka ita wallahi tanada tarbiyya karka kayi bakin ciki da auren ta yakai jikana abun sona.
Chapter 22 · 0% Book details