← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 115

Sashe 62

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yarima yana karasowa wajen yagaida Ànty cike da ladabi.
Salma ganin sa yasa tafara sakin Murmushi gaishe shi tayi ciki ciki ya Amsa mata..
Asiya tace Rahama mu tafi Ko.
Yarima yace ku dakata jirgin da zamu personnel ne.
Inbahaka muka ce zamu bi n'a nijeria a Lagos za'a sauke mu..
Bega m'a rufe bakin sa sai ga

SAMAD AIR PLAN
PERSONNEL

Yasauka hakan yasa gabadaya wajen cikin mamaki suke kallon wannan jirgin banda Aminu da Faruk dasu suka San komai..
Rahama karanta sunan jirgin take tana maimaitawa acikin zuciyar ta..
Su Ko Ànty da su Asiya 'da Salma duk mamaki yacika su..
Abubakar yace MashaAllah yana kallon Yarima dake kokarin yin gaba wajen wannan jirgin cikin burgewa yake tafiya wanda yaja hankalin ila' irin matan da mazan dake wajen airport din suna ta Fadin MashaAllah musamman Ganin Rahama gefen sa..

Cikin yan zaman wajen Airport din take fadin ai wannan da kuke gani Jikan Sarki ne.
Jirgin sa personnel inhar zebar kasar nan..
Dayan tace Amma kaman Jirgin bata kasa Nigeria bace ance nashi ne nakansa ai ya taka Arziki 'matashi ne yanda ya shahara wajen gina kasuwanci da kwarewa akan Ayyukan da yasa agaba...

Koda suka iso wajen Jirgin juyowa yayi dan yiwa Abubakar sallama taré bashi Umarnin motar su Akira drever sa yazo yadauka..
Abubakar yace InshAllah zan sanar masa cike da girmama juna suke sukai Musabaha

Bakin su dauke da Adu'a suka Shiga Jirgin Rahama tana kokarin zuwa wajen anti ta zauna wani kallo da yayi mata n'a kishiga taitayin ki hakan yasa tazauna gefen.sa.
Tsit kakeji babu mai magana acikin su Ko wanne yana ta karanto Adu'oi kariya Daga ubangijin sa...

Kusan minti goma suka dauka kafun Jirgin ya keta Azo cike da kwarewar drever..

Abubakar jikin Asanyaye yadawo cike da kewar Ànty ga Abba baya nan gashi Mama yau ta baci tsakanin su tunda harda Mari..
Hanyar sa ta barin filin Airport din yaci karo da Samira yarinyar dake son Samad.
Cikin yauki takaraso tace dazun kamar kaine nagani tareda wasu maza uku..
Abubakar ya hada rai yace eh haka ne me yafaru ne ?
Murmushi yake tayi tace daman cikin su akwai wanda nakeson gani wannan dan balaraben nan akan wani hoto da yake nema..
Abubakar cikin gajiya da sauraren ta yace wai ku matan yanzu meyasa bakuda Aji ne bakwa jiran a nemeku kai Allah ya wadaran naka ya lalace wlh..
Yarima Samad kikeso Ko.
Toshi da Matar sa.
suka wuce da à bokan sa.
Gefen ta yaraba yana kokarin wuce ta.
Tasha gaban cikin magiya kamar zatai kuka tace haba dan uwa meye laifina dan naso shi..
Wallahi inason sa Samad din nan..
Ta dalilin ka nasan sunan shi ka taimaka mun..

Abubakar beko tsaya bin ta kanta ba yayi gaba yana buga uban sauri yana tsuki cike da takaicin halayen yan matan zamanin nan..

Ita Ko sakaka take kallon shi cikin sanyin jiki ta lalubo wayar ta tareda ajiyewa Faruk sakon voice kamar haka..

Meyasa kaki bari mu hadu tun ranan d'ana ganku.
Yau gashi n'a hango ku kafun nakaraso kun wuce takai karshen zancen tareda rufe datar ta.
Maida wayar tayi cikin jakar ta....

***********************

🇧🇯 Kwatano

Tun safiyan Ranar gabadaya kasar ta dauka zancen auren Yarima Samad dunbum jama'a Mamaki sukayi sossai hakan yasa Airport din Cadjehoun inda *SAMAD AIR PLAN* yake sossai wajen yacika da dunbun jama'a.

Yan Jaridu gidan redio da télévision kowani sashi na kasar sun halatta a wajen.
Dakarun sojoji da yan Sanda sun iso da hana faruwar rikici awajen.
Dan mai Martaba yace kada taron jama'a nan yasa SAMAD fita hayyacin sa.
Shi kwata kwata baya son hayaniya......
Sossai airport yasha gyara da ado anyi décoration din All din wajen ga wani glove da aka sanya wacce take bada kaloli kala kala tareda Rubuto suna akasa duk me wucewa saiya tsaya ya kalla Inda wutar ke rubuta.

Welcome Abdul Samad _Rahama.
Happy Mariage life..
Wannan kenan...

Masarautar gheuzo bakaramin Jin Dadi ne masoyan Samad suka tashi dashi ba..
Anyi girke Girke kala kala.

Saratu Murna awajen ta ita da Mamy dasu Ahmad da khadija ba'a cewa komai..
Maman Maryam da Maryam sammako sukai zuwa masarautar dan gani da idon su yanda àbun ze kasance..
Hajiya Hassana sossai tashagala wajen taya Mamy delicious girki wanda Abinci Samad ne da Rahama n'a mussaman ne.

Kallo daya zakaiwa Mamy ka hango tsatsar Farin ciki tattare da ita..
Tasha ado kamar babu gobe..
Su Ahmad da Khadija sun kure àdaka cikin kaya kala daya tsadaddan shadda.
Maman Maryam dake zaune tana kallon rawan jikin da ake tayi..
Tace Mamy bara inje inyiwa Fulani Allah yasanya Alkhairi kinga ana zaman târe Ko..
Mamy tace gaskiya ne yakamata dan ita ma uwa ce Agun Samad...

Cikin hanzarin ta Mamy tayi hanyar dakin Fulani da sallama bakin ta
tashiga iske Fulani tayi sai Safa da Marwa takeyi acikin dakin..
Cikin gigita Fulani ke kallon Maman Maryam tace kina ganin wannan dan iskan yaron yana kokarin zuwa masarautar mu da Matar sa..
Maman Maryam tace gayamin menéne Mafita cikin tsananin tashin hankali take kallon Fulani....

Fulani nuna mata kujera tayi suka zauna tace ke yanzu yakike tunanin wannan abun zata kasance.
ke kenan kinringa Asara kenan duba lamarin nan fa..
Ya za'ai Samad yaki Auren Maryam kuma ki kyaleshu shidin wa..

Maman Maryam tace yakikeson Ayi yanzu tafada tana ciza labban ta.

Cikin kukan takaici Fulani tace wallahi saina kashe Samad uban shi ma saida muka ga bayan sa saboda mugun halin sa..
Wallahi shi karamin Alhaki ne yayi kadan Alkur'an harya sani zubda hawaye 😩 Saboda taurin kansa..
Ita matar tasa tsinanniya kwana uku nabata da kafafun ta zata bar kasar nan wlh shegiya hauka zan manna mata irin n'a Surukin ta.
Maman Maryam tace yanzu kina ganin zamuyi nasara kuwa..
Abban Marwan da Marwan din da suka shigo dakin kamar an jefo su cikin tashin hankali.

Suke kallo Fulani da duk tabi ta rude..
Marwan yace Fulani ance fa sun kusa karasowa kuma gobe ne za'ai babban taron da ba'a taba kamar shi ba a masarautar nan..
Ni wlh Samad dinnan ba kashe shi za'ai ba ahuta yakarashe zancen yana huci kamar kumurcin zaki...
Abban Marwan cikin iya salon sa da dabarun sa yace A'a basai ankashe shi ba yin haka zekawo zargi acikin Masarautar nan.
Mafita daya ce à barsu suzo din agama taron lafiya..
Bayan an watse ne zamu san yanda zamuyi dasu amma wane su manta da yan iska..
InshAllah Marwan Saika yi aure kuma kaine zaka haifo jikan FARKO...

Marwan yace Abba kana ganin haka zeyu kuwa naje wa Mai martaba da zancen inason aure.
Cémin yayi wai banda Sana'ar rike mata Saboda Allah aiko Auren gâta ana iya mun wani Arzikine beda shi..
Abban Marwan yace karka damu shi mai Martaba nashi mai Sauki ne n'alura maganin sa yagama Aiki zan kara masa sabon jiko bara ma yanzu inje inhada masa kafun taro yayi taro yaki saurarena yakarashe zancen tareda fita dakin cikin Azama..

Fulani da Maman Maryam binsa sukai da kallo harya fice..
Marwan shima fita yayi dan zuwa ya shirya kafun su Samad su iso...

Ita Ko Maman Maryam tace yanzu bara inkoma kada Kanwata taga n'a dade tayi tunanin wani Abu..
Fulani tace babu matsala je ki zan nemeki..
Tana fita Fulani da sheke da wani mugun dariya tace Shasha wawiya jibe ta Ko kunya babu wai yar uwar ta takewa Hassada Saboda mijin kanwar ta be zabe ta ba...

Ko me Fulani ke nufi da wannan Kalaman kudai muje zuwa fans...

Tsaki taita je rowa shegiya kina tunanin in ma auren ne zan yarda Samad ya auri yar ki ne..
Wallahi saide ya Auri.
Diyar Ànty n'a bilkisu mai gadon zinare.
Daukar wayar tayi ta dannawa bokan jeji waya..
Bugu daya ya Daga wayar cikin kukan munafuncin tace yanzu kana ganin yaron nan zeyi Abunda d'ana be aikata ba.
Wai meyasa kuka kasa iyawa dashi ne karamin Alhaki...

Dagacen bangaren Boka yace haba ya zakice haka zan baki Mamaki badai sun kusa sauka ba kedai zubawa sarautar Allah idanu kiga yanda wasan zekaya..

Inason duk. Halin da ake ciki yanzu kizo nan kisameni..
Fulani tace kasan akwai taro fa kada anemeni arasa..
Boka yace karki damu zan dauke hankalin kowa akan ki kedai kizo akwai aikin da za'ai mai zafi zafin ta.
Cikin yarda da zancen sa tace gani nan shiryawa yanzu zaka ganni tareda katse wayar tana dariyan mugun ta...

Baiwar ta Asabe tashigo cike da ladabi tace ya shugaba ta..
Kallon banza take bin ta dashi kiyi magana kin wani dukar da kanki...

Cikin Rawan Murya Asabe tace daman sonake inje Sashin su Mamy in tayasu aikace aikace taron baki shiyasa nazo neman izini..

Wani kallo Fulani ke bin ta dashi masu tarin ma'anoni cike da jin haushin ta dakuma tuna fita zatayi.
Yasa tace eh babu damuwa kuje Kuyi aikin ai yau ranar Murna ce..

Cike da Jin Dadi tabar dakin itako Fulani dakin ta.
Ta nufa dan shirya wa cikin hanzarin ta....

Karima zuwa tayi Sashin Rahama da Samad room freshner ta fesa ta kunna turaren wuta gabadaya sashin har cikin masarautar yadau kamshin mai dadin shaka..
Kokarin fitowa take taci karo da hassana itama cikin ado tasha babban Shadda ajikin ta..

Kallon Karima take tace harkin fito ne ?
Karima tace eh na fito ya 'akai ne t'a tsareta da idanu..

Hassana tace babu komai n'a zata zan dan tayaki aikine.
Karima tace A'a aina gama kuma kinga shugaba n'a yau ze iso.
Baya kaunar yaga wani ya tayani aiki rannan m'a dan be nan ne kuma inason abokiyar fira shiyasa mukai taré...

Hassana tayi Murmushi irin t'asu ta manya tace Karima kenan yanzu shi kwata kwata beson yaga wani yana taya ki aiki to Saboda me ?
Chapter 62 · 0% Book details