← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 115

Sashe 103

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kuma kinsan da haka ne kike son ki hana '' gayamin Ko matar batayi miki bane...
Tun Farko da kin nuna mun bakyaso inna gamsu da hujjojin ki zan iya hakura innemi Zabin Allah.....
Kinsan banda kamar ki Rahama duk acikin yaya na.
Akan ki zan iya yin komai 'nasan kinada tarbiyya bazaki so muyi abunda mutuncin gidan mu ze zube ba..

Rahama tace hakane Abby n'a karka Adamu' itama wannan din Allah yakawo ta da Alkhairi..

Ameen ya Allah ya furta yana mejin kaunar yarsa n'a kara ruruwa acikin zuciyar sa...

Daga haka sukayi Sallama...

Shiko Sheik Hassana ya dannawa kira..

Yace Amarya bakya laifi koda kin kashe karen gida n'a..
Murmushi tayi Daga zaune tace my husband ai cewa ake koda na kashe dan masu gida..

Darawa yayi yace Ah Ah dan baki kashe bane dakin ni awajena kinyi laifi my love.
Uhmm yanzu de jibi daurin auren mu karfa kisa aranki Daga ke babu kari 'duk lokacin d'ana samu dama zan cike' inkuma banyi ba to haka Allah yatsara...
Tabe baki tayi Daga zaune tace haba angon hassana 'kai Adali ne Ko goma ake yi nasan zakayi adalci uhmm kaide wani abu sai jibi ranar daurin aure naji bakin cikin da bazaka zo ba..

Kiyi hakuri Amarsu ta angon ta' akwai wata diya ta Asiya 'da kanin mijin yata Rahama ze aura' kuma Nine n'a jagoranci komai n'a auren nasu..
Am sorry kinji baby n'a yakashe murya.
Hakan yasa ta Jin kanta à nishadi 'tace uhmm yawuce tunda ka kawo uzuri..
Amma fa nazo zamu d'au hotuna zafafa nidakai.
Sossai ma zamu dauka yabata amsa.
Amma ki tabbatar da hijab jikin ki kafun muyi hoton kinsan irin wannan hoton yawo suke a social média' 'kuma ni gida n'a ba' a yafa mayafi hubby kizo da hijabai in sun miki karanci zan hadaki da Sa'adatu zata dinko miki..
Uhmm naji my love dîna uban yaya n'a sirrin zuciyata 'mai gyara tunani n'a me sani farin ciki...

Sheik cire hular kansa yayi yana dan shafa kansa' 'wani kayataccen Murmushi yayi yana ayyanawa aransa uhmm shima yazama karamin yaro yau....
Amarya ta ina godiya sossai zan shiga Daga ciki..

Uhmm yanzu har ka gaji da hira dani..
Ah ah banki mu kwana chat ba' yau ina dakin Sa'adatu 'kuma ita bata son jira' gara in je kinsan yau da gobe duk wajen ta nake jibi kuma ina tareda sweety n'a..

Sossai ta dara katse firan yayi da Fadi ki tabbatar kinyi mafarki na.
Da haka sukayi sallama.
Kai tsaye dakin Ànty ya nufa iske yayi zaune tace Abban Rahama 'kaga yanda kayi kyau kuwa...

Allah Ko Sa'adatu tunda muke ban taba miki kyau ba sai yanzu..
Kai kasan kullum ina gaba wajen yaba kyawun halittar ka..
Shiyasa nake adua Allah yasa in haifo mai kama da kai kamar Rahama...
Sossai ya dara yace yawwa dan matso zanwa baby n'a adua kinsan jiya ina dakin Maman Salma 'babu damar ayi adu'ar..

Hakane ta furta tareda matsowa yana tofa adua tana lumshe idanu..
Nikam nace bara inbaro dakin nan kada Sheik ya hango yaci ni tara.....

Asuba ta gari......

Kashe Gari.

Kwatano.

Tunda sassafe masarautar gheuzo ta tashi da Ayyuka tareda baki ta Ko ina daga garuruka harda gyare gyare ake yi inda sarakuna zasu sauka cikin su harda Sarkin kano.....

Yarima Samad dasu Ahmad 'da Rahama' tsab suka shirya '' su Faruk da Aminu sammako sukayi dan zuwa jidan akwatunan lefen sukai airport.....
Mama Firdausi wanda da ita za'a tafi 'tsaf suka shirya tareda wasu yan uwan nasu Daga bohicon..
Karima tace baza'a abarta abaya ba duk suna cikin matafiya...

Khadija harda kuka wai bada ita za'a je ba..
Yarima Samad yace kije ina gobe daurin auren ki' muma jibi zamu dawo InshAllah da Amarya.
Mamy da Mai Martaba Adua sukayi masu 'da fatan Allah ubangiji yakai su lafiya..
Abban Marwan tuni yawuce aiport dan dole yakamata ace ga kanin uban Ahmad a wajen daurin auren.....

Basu bata lokaci ba Samad Personnel air plan.
Jirgin nasu ya Daga sararin Samaniya.......
Sai Kano...

🇬🇦 Gabon

Hassana tasha lalle hadadde tayi wani fresh tasha gyara tsaf harda maganin tsaida Brest tasha dan haka boob din ta yakoma kamar sabuwa
Magungunan gyara ba'a cewa komai gidan nasu ancika tun à ranar aka fara daura tukunya ana sauke wa...
Me kitson dakewa Hassana kitso tace 'saidai aturawa sheik hoto yagani yabiya ta....

Daukan hoton sukayi' 'shi kuwa Sheik yana cen yanata hada hada tarban bakin sa da suka zo Daga nesa irin su saudiya' Soudan...

Ganin sakon nata ta whsap ya shiga cikin hanzari..

Cin karo yayi da wannan tsalelen kitson nan..
Cikin.

Muje zuwa

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:56 - Nuriyyat: KANWATA

09069080725

9️⃣6️⃣

Cikin Rawar hannu ya bude hoton 'Murmushi yayi Aminin Sheik dake zaune kusa dashi yace dan lubaiya nima' ka koya mun wannan soyayya haka...

Dago kai Sheik yayi yana Kallon sa 'yace in soyayya ne kaine malami koka mance nan kake zubawa da Uwargidan ka Sa'adiya....

Malam Isa yace uhmm ai yanzu tarage kula dani' 'wai yaya' ' hidimar gida....

Uhmm saika lallaba ta ahaka kasan bata son kishiya Ko.....
Malam Isa yace anya nima ba karawa zanyi ba..

Sheik yace Gaskiya karka kara kasata ahanya kana da rauni bana tunanin zaka iya contrôle din mata fiye da daya..

Su Mata da kake gani in mutum yayi wasa sai sukai shi ga halaka...

Adalci shine babban abun dubawa 'dayawa maza cikin sai su ringa fadin ai zanyi Adalci inada kudi' inada kaza 'duk aikin banza ne' indai kaiba Adali bane 'dukiyar ka bazata kare ka ranar gobe Alkiyama ba.....

Kai kasan cewar n'a kara aure ne saboda matsalolin uwargida ta..
Da kuma inada yakinin zanyi Adalci.
Har kwanan gobe banyarda Sa'adatu ta raina ta Ko babu komai itace farkon shafi n'a rayuwa ta.
Iyayen ta nake dubawa sun mun halarci ' koda mukayi aure' mahaifin ta saida yaban dubu dari biyar kyauta yace in jari...
Yace wlh ba yabani bane dan ina auren yar sa.
Yabani ne dan mutunci iyayena dani kaina kada in duba dan yamun kyauta Aisha tamun laifi Inkin hukuntata...

Alhmdulilah wannan kudin tazamo silar Arziki duk da Allah ke azurtawa 'amma wannan kudin sun mun rana kafun in zama wani abu saida silar su...

Kwanaki ma har tafara goran ta mun akan tsohon gidan' wai itace sila 'dariya tabani kasan mata ba'a biye musu.
Bare in kishi ya motsa....

Shin zaka iya rike mata biyu kuwa ka zauna kayi nazari' babu ruwan ka da wane yayi 'nikaina danayi taimakon Allah nake nema..

Sossai jikin Malam isa yayi Sanyi yace zankara aure Sheik amma sai nan da shekara biyu haka lokacin' mun sake gida.....

Sheik maida kallon sa yayi akan wayar sa '' ganin stick da hassana ta turo n'a tagumi Alamun Ana jira ya bada Amsa..

Rubutu 'yayi yace MashaAllah tabarakallah kitso ya wanku' wanka tabi jiki....
Maza kema ki goge wann hoton awayar ki kada à dauka ayi ta turawa....
Me kitso abata dubu hamsin ta turo Àcct nomba yana gama fadin haka yasauka online din.....
Kai tsaye tashi sukayi dan zuwa Tarbo su Rahama ance sun taho... Abubakar ya hango shida Abdul jalil suna sanye cikin jallabiya hash color..

Dadin ganin su yayi ganin sun tunkaro inda suke.....
Abdul jalil yace Abby zamuje mu nuna wa masu kawo shanaye gidan nan sunce basu gane Kwatance ba..
Sheik yace to maza katafi kaji Ko...
Dawo da kallon yayi akan Abubakar yace ya angyara masaukin baki Ko.....
Abubakar yace anyi komai Abby saidai fatan ayi taro lafiya a watse lafiya.
Iyayen yarinyar da nake nema sunce zuwa monday suke son aturo...

MashaAllah Sheik ya furta to Allah yakaimu...
Koda Abubakar din yawuce yace uhmm yaron nan duka shekaru 22 gare shi amma aure yake '' koda yake nima shekara 21 gareni aka mun aure ina wata kasa...
Barin wani tunanin yayi ya shiga tsabgogin gaban sa......
Koda su Rahama suka iso tayi harba da Sheik rungume shi tayi sossai.....

Cike da Farin ciki yace haske n'a harkin iso..
Murmushi tayi tace Abby kaga yanda kayi kyau kuwa.... Naji dadin ganin ka '' bara in shiga ciki nakosa inga Mama....

Aguje ta fada gidan tana dube duben inda zata ga Mama hangota tayi zaune Dagacen gefe ita kadai Alamun ta fada duniyar tunani...
Rungumar da Rahama tayi mata ne yadawo da ita cikin hayyacin ta...
Tace la la Rahama ta yaushe a gari wayyo Allah dadi yata Idanun ki kenan zauna mana.....
Chapter 103 · 0% Book details