← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 115

Sashe 13

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bude idanun ta dasuke lumshe tayi tareda gyara zaman ta dukar da kai tayi alamun afuwa ga ànty.

Cikin sanyi murya tace anti wlh Adamsy yaban tausayi ina kuka ne halin daze shiga akaina.

Wanda ni zan shiga bedameni ba.

Anti shikenan zanbar gidan mu.
'labarin aurena ban tabaji koda à novel bane ace mijin dazan aura uban sa yaje yadauko sa.

Inada kyakyawan zato akan baba salihu amma dukan mu'

Bamusan daga ina yafito ba

Abba kadai yasani cikin kuka tace yanzu ànty in yakawo yaron nasa kukaga bamai tarbiyya bane shikenan babu wanda zehana à daura auren.

Numfashi ta fesar zataci gaba da magana.
Ànty ta dakatar da ita.
Da hannun

Pls Rahama narokeki kicire duk wani tunani aranki Allah yana sa ne dake kuma InshAllah auren nan ze zamo Alkhairi atare dake karki damu da rashin sanin wanda zaki aura.

Kedai kisa aranki bauta zakije Ko yaya mijin naki yake kiyi masa biyayya.
Kinji Ko ?

Gyada kai tayi alamun gamsuwa.
Tareda kwanciya jikin ànty.

Cikin rarrashi anty keta bata shawarwari masu kashe jiki.

Ahaka barci yayi awon gaba da Rahama batareda ta shirya ba.

Gyara mata kwanciya tayi tareda tofe ta da adu'oi kana ta rufa mata blanket tabaro dakin tareda rufo mata kofa.

Daidai corrido daze sada ta da dakin nata taji muryan Salma alamun waya takeyi a sirrince.

Ganin anty yasa ta rikice tareda tura wayar cikin Brézia.

Rau Rau da idanu take kallon anty alamun rashin gaskiya sun bayyana atare da ita.

Wuce ta anty tayi tana Girgiza kai tsoron magana takeyi uwarta tace sharri ake mata.

Abba yazo wucewa tawajen ganin Salma a wajen bakaramin shock yashiga ba.

Wayar yafara ruri tana kawo haske.

Nan take taji hantar cikin ta ya kada ganin sheik na kokarin....

Karku manta Paid book
Kubiya ku cigaba da karatun sa har a gama.

Taku har kullum kyauta Daga Allah
3/20/22, 22:34 - A'ish: *🌟🌟 KANWATA🌟🌟*

Paid book ne

300 vip

500 spécial

Àcct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ko kuma Katin MTN
Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

1️⃣7️⃣

Sheik cikin hanzari yakaraso gaban baba salihu tareda rungumar sa.

Cikin kuka yake fadin na shaku dakai dan uwa kazamo tamkar fitila a cikin ahlina kanada dadin zama kyakyawan zuciya.

Sassauta rungumar dayayi wa baba salihu yayi tareda kallon sa cikin idanu hannayen su tsarke cikin juna.

Yace yanzu inka tafi yaushe zaka dawo karka manta dudu bikin bekai sati uku ba.

Baba salihu karfafawa sheik gwuiwa yayi akan zedawo nan bada jimawa ba.

Har bakin titi suka rako sa duk wani kudaden sa aikin gadin dayake musu. sheik yamika masa.

salihu dakyar ya masa kudin saida yaga ran sheik yabaci sannan ya amsa yaita zuba godiya.

Suna kallon sa ya tari me napep yashiga sunata daga masa hannu yana daga musu harya sukai nisa.

Sheik jiki asanyaye suka koma gida.
Abubakar yace Abba yanzu daya tafi wani mutum ne na amana zaka samu yaringa tsare mana gida.

Sheik murmushi yayi irin tasu ta manya yace aiyanzu tsaron gida yadawo hannun ka.

Abubakar ya ce laa !
Abba nikuma ayyuka na fa ?

Sheik yace hakuri zakayine kaga ba dadewa zeyi ba kafun biki zansamu mana me gadi.

Aishi baba salihu koya dawo gaskiya bazeyi gadi ba.

S'aide kasuwanci dan yazama surikina.
Abubakar girgiza kai yayi cikin gamsuwa da zancen Abba ' Suna isowa gida yayi sashin sa.

Sheik yakarasa gida iske salma da Rahama sun shirya cikin kayan su na makaranta zasu wuce dan yau shine rana ta karshe zana jarabawan su.

Kiransu yayi zuwa dakin nasa.

Mama tace haba sheik kazo sai magana nake maka kana shareni wa'azi kakeyi agari amma agidan ka.

Akwai gyara wallahi

Zainab matar hussain dake cin abinci saida ta dago kai tana kallon tijara irin na Mama.

Be bi takanta ba yawuce dakin sa yana girgiza kai.

Yana shiga Rahama da salma suka take masa baya.

Sallama dauke abakin su.
Suka shiga samun wuri sukai suka zauna.

Kallon su yake nawasu dakiku yana nazartan yanayin su.

Yalura salma duk takosa tabar dakin yanayin zaman nata yake kallo.

Gyaran murya yayi yace
Rahama kina sane nabada auren ki ko ?

Kanta aduke ta amsa cikin cool voice nasani abba tabashi amsa a takaice.

Inason pls amatsayin ki n'a yarinya me hankali ki tsaida hankalin ki.
Waje daya nasan kinsan bazan taba miki zaben tumun dare ba.

Rahama dan Allah karki bani kunya nasan akwai wani wanda kikeso kidauka yashigo rayuwarki ne bisa kaddara narokeki yata.

Jikin Rahama yayi mugun sanyi cikin raunin murya tace Abba zanmaka biyayya wallahi Ko mahaukaci kaba ni amatsayin miji zan zauna dashi bare ace mutum mai hankali d'à nutsuwa karkai yi shakku akan tarbiyyan dakabani bazan bari kaji kunya ba InshAllah.

Dadin kalamanta bakadan suka dada ran sheik ba guntun hawayen dake fuskar sa ahankali yake kwaranya Dadi yakeji aransa da Allah ya bashi ya mace mai nutsuwa da hankali.

Fuskantar Salma yayi yace to na dawo kanki.

Nasan halayenki salma naso inmiki zabin mijin aure amma nalura hakan baze yuba ina son ki gabatar da wanda kikeso dan arana daya nakeson auran daku keda yar uwarki.

Salma kanta akasa banda bugawa babu abunda zuciyarta yakeyi.

Cikin tsoro da fargaba tace Abba ni Adamu nakeso.

Kusan atare abba da Rahama suka dago kai Suna kallon ta.

Abba yace wani Adamun kenan ?

Cikin tsoro ta furta dan anbassador libya.
Gaban Rahama saida yabada ras wani sashi na zuciyarta tace to ai gwara ya auri
*KANWATA*

Tunda yarasani kukan zuci take Ta yanda zata auri wanda bataso.

Abba yace Adamu daman saurayin kine.

Turo baki tayi gaba tace ai daman ni yafara gani yana so.

Rahama tashiga tafita ganin taraba mu.
Gashi ita kanta ma ba auren nasa zatayi ba tana murguda baki da hararan Rahama.

Abba Ransa yabace.

Yace ke dakata nan bankira ku ba dan ayita faden zancen banzaba.
Kituro adamun yazo inason ganin sa.

Kuna iya tafiya karkuyi latti.

Jiki asanyaye Rahama ta tashi banda kuka babu abunda zuciyarta yakeyi.

Akan hanyar su ta makaranta babu wanda yakewa dan uwan sa magana.

Salma tsaki kawai taketa jerowa Sam Rahama taki kulata dan gabadaya hankalin ta nakan makaranta da zasu je.

Mai gadin makaranta sai washe baki yake ganin Rahama mutumiyar sa.

Sai magana yake mata dakyar tabashi amsa tashige ciki..

Suna shiga aji aka fara zana jarabawan Sam Rahama rubutu Takeyi amma Sam hankalin ta

Baya kan abunda take zanawa dandai ilimin a kwanyarta yake d'à saidai tayi asarar damarta t'a karshe da taimakon asiya tadawo tunanin ta harta gyara inda tayi kura 'kurai.

Har suka tashi break Sam bata da tsukuni auren nata daya saura satî biyu kacal shine yake daga mata hankali.

Yazan yi ni Rahama inyi zaman aure d'à wanda bansan halayen sa ba.

Bansan ya yake ba 'bansan Addininin sa ba.

Murya Adamsy ta tsinta dake tsaye yana kallon ta.

Sanye yake da boyel bleue color hular sa bleue sai baza kamshi yake.

Haba Rahama bedace dake ba kizauna ke kadai anan ba' batareda abokin hira ba.

Dago jajayen idanun ta tayi ta kalleshi tareda kauda kanta gefe.

Tashi tayi daga Wajen shan gabanta yayi yace haba babu fada meyakawo gaba gimbiya.

Salma takaraso inda suke tana murmushi kai bakasan dalilin fushin ta ba.

Girgiza kai yayi yana kallon salma dake wani kashemai idanu karasowa gab dashi tayi har sunajin numfashin juna.

Abba yayi mata miji wanda bakai ba bikin saura satî biyu.

Adamsy nan da nan idanun sa suka kawo ruwa Sam ya manta da zancen bada auren Rahama da Abba yace yayi.

Rahama kasa jure tsayuwar ta nan tayi.

Barin wajen tayi cikin sheshekar kuka mai tsuma zuciya.

Adamsy zebi bayan Rahama salma tasha Gaban sa.

Pls karka bita dan bakula ka zatayi ba tayiwa Abba alkawarin haka.

Iname baka shawara tunda ka rasa Rahama ka aureni.

Firgit haka yaji kalaman nata kamar saukan guduma kallon tara saura kwata yake jifanta dashi.

Afili yafurta aure ni dake salma yana nuna kansa da yatsa.

Wallahi kin makaro Ko ke ce autar mata nahakura dake non-sens kawai.

Tubar da miyau yayi akasa tsukii yaja tareda barin wajen yana mejin tsanarta à cikin zuciyar shi.

Ikon Allah ne kadai yakai adamsy gida.

Awaje ya paka motar sa 'kai tsaye gida ya nufa tafiya yake kamar dan maye.

Ko kallon me gadi dake gaishe shi be yi ba.

Hamza dake zaune yana kallon TV arazane yadago kai yana kallon adamsy dake kokarin faduwa.

Cikin hanzari ya tarosa cikin gigita yace Adam

Meyake damunka ne Adamu.

Budan bakin adamsy yace...

Ta ku har kullum kyauta daga Allah
3/20/22, 22:34 - A'ish: *🌟🌟 KANWATA🌟🌟*

Paid book ne

300 vip

500 spécial

Àcct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ko kuma Katin MTN
Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

1️⃣9️⃣

Ganin sheik n'a kokarin saka hannun sa cikin rigar ta ze zaro wayar.

Kokarin guduwa takeyi ya damko Hannayen ta 'wani irin wawan riko yayiwa hannun ta tareda wucewa da ita kai tsaye dakin nasa.

Suna shiga yaja kofar yarufe wayar yazaro ajikin ta yana kallon yanda take ring saman screen din wayar anrubuta Al'amin.

Daga wayar yayi tareda sa hansfree kasa kunne yayi yana sauraron abunda yake fadi.

Dagacen bangaren yace haba salma kinfa yimun Alkawari zaki mallaka min budurcin ki.

Naga yanzu lokaci yayi da zaki bani hadin kai inason nanda sati daya.
Muje hôtel pls wallahi abukace nake tunda yaketa zuba be lura da Sam salma bata amsa masa ba saida yakai ayar zancen nasa kallon wayar yayi yaga dai baa kashe.

Cikin fushi yace 'kindaukeni mahaukaci nikadai sai magana nake kinshareni.

Sheik bakaramin tashin hankali ba yashiga t' yanata nanata zancen budurci acikin zuciyar sa.

Afili kuma kallon wayar yakeyi yana kallon Idanun salma data fita hayyacin ta lokaci daya.

Gyaran murya yayi yace da uban salma kake magana kajira kaga abunda zebiyo baya.

Al'amin ba karamin tashin hankali yashiga ba. Kallon wayar yakeyi yace shikenan ze tona mana asiri yazan yi in iyayena sukaji wannan zancen.

Sheik da Idanun sa suka kada jajir kyawawan maruka guda uku yadauketa dashi wanda hakan yasa ihun ta.
Ya karade ila'irin gidan gabadaya.
Chapter 13 · 0% Book details