← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 115

Sashe 107

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nan Mamy ta basu labarin Abban Karima tsohon shugaban kasar Niger Muhammed yusufu.
Yazo daurin aure...
Cike da murna Samad yace kai kai Dole mu dawo gobe nasan yazo daukar iyalin sa kuma karima ta nan.
Mamy tace kai bakaga zuwan sa yanda garin gabadaya ya karade da firan zuwan sa..
Duk firan da suke Baba salihu yana jinsu sossai muryan Mamy yake ratsashi ji yake kamar yayi tsuntsuwa ya ganshi a gaban ta...
Ga kuma murna zuwan shugaban kasar Niger dinnan hakan bakaramin dadi yayi masa ba..
Yarima n'a gama waya da Mamy yadawo da kallon sa akan Abban su dake Jan carbi yana tasbihi..
Ahmad cike da kosawa ya ajiye carbin yace Abba yanzu yakamata kadan bamu lokacin naka ''.
Kallon sa yake yana murmushi yana cigaba da Jan carbin nasa...
Ganin Yarima shima yataho ze daura Daga magiyan da Ahmad ke masa 'yasa shi ajiye carbin..
Kallon su yake cike da kauna yace karkuga naki magana tunda n'a iso gidan..
Hakan danayi yana Daga cikin Adalci mutum ya iya bakin sa acikin dunban jama'a inda baze rasa masoya da makiya ba...
Inason kuje Kuyi Alwala kuzo muyi sallah tare..
Gobe sonake ku koma ku kadai kwatano...
Cikin zazzare idanu Yarima Samad yace ina wallahi bazeyuba Allah bazanyi kaffara ba...
Ganin yanda launin dan nasa ya canza lokaci daya '' ya tabbatar masa babu wasa a tare dashi..
Shiru yayi yace to Aje Ayi Alwala...

Cen Gidan Sheik kuwa bayan kowa ya watse..
Kara hada kan matan nasa yayi yamusu Nasiha...
Mai ratsa zukata..
Maman Salma tace uhmm duk wannan surutun ita karama ce ya isheni da ji haka..
Ai karamin abu baya zuwa gidan miji.
Bare wanda ya taba aure abu Shiba sabo ba....
Hassana kada kai tayi tana jinjina kalaman mama...
Ànty shiru tayi ba tace uffan ba..
Sheik cikin son kawar da zancen yace..
Yawwa Amarya tashi Sa'adatu ta miki jagora...
Ita hauwa da bakin naki ambasu masauki..
Cikin hanzari hassana ta tashi dan takosa tabar falon '' bin bayan anty tayi suka haura kan matakalan step..

Yana ganin wucewar du anty yadawo da kallon sa akan Mama.
Yace ke yanzu wace irin mace ce ke kina zubar da girman ki a Idanun kowa..
Wannan matar nifa n'a auro ta..
Bada ita zakiyi ba dani zakiyi babu dalilin daze sa kina jifanta da kalamai marasa dadi....
Ko kin manta manzon Allah tsira da Amincin Allah da bazawara ya fara..
Mama tace ai shi tashi bazawarar saida aka sabun ta masa ita..
Kai kuma fa...

Sake da baki yake kallon ta yace Eh lallai kin iya bada Amsa....
To zanshiga ga ledan nan kazar ki ce A'ciki..
Iyeh me zanyi da kaza naga Ko adaren farko n'a dakai balangu ka kawo..
Murmushi yayi yace uhmm Kodai amaimaita daren Farkon ne.
Ita hassana tahakura da mijin a yau.....
Juya masa keya tayi Shiko ya ajiye ledar yace uwar gida natafi saida Safe ki kula da kanki da adu'oi kariya....
Kai tsaye ya nufi dakin hassana iske su yayi zaune Ànty n'a mata hira..
Isowar sa yasa shi fadin iye har fada aka bude yau adakina....
Ànty tace daman kai nake jira intafi...
Kallon hassana tayi tace to Amarya n'a tafi saida safe..
Hassana tace Ah Ah tun yanzu zaki tafi dan Allah ki tsaya...
Sheik yace Muje Sa'adatu in raka ki daki nasan kina taré da gajiya....
Ànty tace yi hakuri Amarya wallahi Agajiye nake 'zanshigo da safe InshAllah...
Sheik ajiye kazar hassana yayi da wasu abun tabawa...
Yarike n'a Anty a hannun sa sukayi bangaren nata....
Koda suka isa dakin nata..
Yace Sa'adatu nagode da kulawa Allah yasaka da Alkhairi...
Sa'adatu ina Alfahari dake cikin iyalina 'kin taka Rawar gani..
Azuciyar sa sai fadi yake Sa'adatu n'afi son ki akan Ko wace mace aduniya banda mahaifiya ta...

Afili kallon ta yayi yace ga ledar ki' hannu bibbiyu tasa ta karba tana godiya tace uhmm. Wannan kazar har ka tunamun baya...
Cikin tsigar wasa yace Ko inzo a maimaita ne..
Tace A'a baniso akaiwa Amarya..
Daga haka sukayi Sallama yafi ce kai tsaye dakin Hassana..
Ita Ko bandaki ta shiga domin yin wanka......

Sheik koda ya isa dakin iske Hassana yayi har ta canza kaya tasaka n'a barci...
Nan da nan ya umarce taje ta dauro Alwala suyi nafila...
Babu musu taje ta dauro koda ta dawo iske shi tayi yana Jan carbi...
Yana ganin ta basu bata lokaci ba wajen tada Sallah ba....
Bayan sun idar sukayi ciye ciye abaki yaringa bata...
Daga nan salon ya canza..
Aranar dai hassana ta jinjina wa Sheik ta Daga masa hannu.
Bayan ya samu kansa ne Daga duniyar Daya tafi yace Hassana tace naam..
Yace ke ta musamman ce...

Asiya zaune ita da Rahama.
Suna hira 'tunawa tayi Salma tace tana neman ta..
Hakan yasa ta kira Samad ta sanar masa..
Dan yace mata duk abunda Salma zatayi ta sanar masa..
Cikin tsoro yace Ah Ah Rahama karki je zanmiki bayani gobe da safe inna shigo...
Jin haka jikin ta yayi sanyi sossai...
Dawowa tayi takwanta kusa da Asiya dake shirin barci....
Wayar Rahama ne yasoma ring tana dubawa taga Ahmad ne...
Babu bata lokaci ta Daga
Tace kanina ya gajiyar taro...
Alhmdulilah yabata Amsa..
Ina kawar taki take ne yana mai lumshe Idanun sa saiyanzu ya tabbatar wa kansa abaya cen bawai kiyayya bace yake mata soyayya ce...
Dan bata wayar zan mata magana kinsan gobe da wuri zamu koma...
Rahama tace Ayya Amma nidai abarni inyi Sati daya...
Inafa bazamu yarda ba wallahi... Kafarmu kafar ki...
Dariya tayi tace Ah abun yakai haka..
Tace yama wuce haka bakada labari ne....

Mikawa Asiya wayar tayi tace amshi angon naki yana son magana dake...
Jin haka Asiya ta tashi Daga kwance cike da ladabi tace yaya Ahmad inawuni...
Murmushi yayi yace lafiya lau kanwata...
Rasa me ze ce mata yayi Saboda artabun da suka sha da ita.
Wani kunyar ta ne ya lullube shi yace daman n'a kira inji Ko kina lafiya ne..
Lafiya lau nake tabashi amsa atakaice.. Tace to zan dan kwanta saida safe kenan...
Babu yanda ya iya hakanan sukayi sallama shida ita.......

Kashe Gari....

Bayan Sallah Asuba Sheik da Hassana yayi karin kumallo '' hassana tace uhmm m'y love bakada dama fa...
Murmushi yayi yace to ke din ce cakwala dadi...
Daga haka sukayi ta zuba love adakin kamar bazasu fito ba...

Mama tana kasa tana kallon agogo ganin har goma be fito ba...
Tana jijjiga tana cika.
Shigowar Salma ne yasa ta maida hankalin ta akan ta....
Mama tace subuhannalah Salma meyake damun ki ne...
Cikin Rawar murya tace Mama wallahi guba nasawa Rahama a cikin abinci '' jiya..
Naita jiran ta tazo taci bata zoba..
Hannun nawa ya taba robar 'cike da mantuwa nasa hannu abaki n'a..
Shine tunjiya nake fama da matsanancin ciwon ciki ga Al'amin adakin sirrin nasa ya kwana....
Caraf kalaman ta akan kunne Sheik..
Cikin zabura ya karaso falon yace Salma guba kika sawa yata Rahama cikin abinci..
Ina Abinci yake yafada a matukar razane...
Bakin ta narawa tace wallahi Abba n'a ba.
Karen gidan nan..
Aguje sukayi farfajiyar gidan ganin Karen sukayi kwance a mace bakin sa duk kumfa...
Innaliahi wa'inna il rajun ya shiga maimaitawa yace yanzu Salma rashin Imanin ki yakai ki kashe rai...

Bari kuji yadawo da kallon sa akan Mama yace koda Salma tayi Asiri dan adamu kada ya auri Rahama inada masaniya 'dan inda take zuwa makotan su ne sukazo sukaban labarin anga yata wajen...
Ta aikata babban kuskure ta ruguza farin cikin dunban mutane tasa yayar ta cikin damuwa Daga baya Allah ya wanke ta...
Shirun da nayi a wancen lokacin bawai yana nufin bazan iya daukar mataki bane...
Saidai kawai nayi shiru ne saboda anason karinga yiwa mutum uzuri...
Ance hali Zane ne..
Tabbas Salma wajen uwar ki kikayi gado...
Kallon Mama yayi rai abace yace a yau dinnan nakeson ki barmin gidana...
Yayi daidai da karasowar Baba salihu da Yayan nasa harda su Faruk da Abban Marwan... Su mama Firdausi da sauran su...
Sunzo daukan Asiya...

Ganin Mama tarike kafar sheik tana magiya da kuka yasa cikin hanzarin su suka karaso wajen...
Ita Ko Salma sai ihu take tana fadin cikina 'cikina cikina.....

Ihun nata caraf ya sauka akan kunne Rahama da Asiya harda Ànty à ujajan suka fito ganin Abunda ke faruwa...
Abubakar da yaji abunda yafaru salati suka fara tareda mutan gidan gabadaya......

Rahamaa kuka tasoma mai tsuma rai tace Salma menayi miki ne.
Salma mena tare miki kikeson kiga bayana...

Cikin dauriya Salma tace Rahama ni baki taba mun laifin komai ba..
Mama ta nuna min duk abunda nakeso shi zanyi babu me hanani..
Mama ta nuna mun kada in yarda ki fini da komai dan kina yar Gidan Ànty...

Nikuma nasa wannan araina tun ina yarinya nasha Alwashin bazan taba yarda ki wuce ni ba...
Saima ki dawo kasa ta..
Inada bakar zuciya da banson in bude idanuna inganki Rahama...

Gabadaya kowa wajen yadau Salati 'yarima Samad da Al'amarin yabashi tsoro..
Kama hannun sheik yayi suka koma gefe yace dan Allah yabari akaita Asibiti....
Sannan yabashi labarin d'uk abunda yafaru àcen kasar su...
Sossai Sheik ya Girgiza yace Ah Ah yarima Samad bazan kai SALMA Asibiti ba..
Abubakar yace wallahi baza'a kaita ba saide ta mutu anan wajen....

Ganin da gaske suke yasa YARIMA Samad shida Rahamaa suka ciccibe ta zuwa Asibiti..
Koda suka isa umergency aka tafi da ita...
Likitoci sukayi ca à kanta.
Babban likita yace wannan yarinyar wanna iskan guban ya kashe abunda ke cikin nata..
Dole cs za'a mata..
Yarima Samad yace a mata tareda sa hannu...

Rahama kuka take tana adu'a Allah yasa ayi nasara...
Samad rungume da ita yace InshAllah za'ayi nasara hubby n'a...

Cen gidan kuwa...
Kowa gidan antaru anata ba sheik hakuri akan ya kyale Mama ta zauna yace Sam ba wanna zancen.
Shidai be saketa ba.
Ci da shan ta ze ringa aika mata..
Amma fa saitaje makarfi ta zauna saiya nemeta...
Kuka take sossai Ànty ganin ba abunda zata iya ne yasata yin shiru tunda ya rantse tasan bazeyi kaffara ba....
Mai hakuri inyayi Fushi to babu kyau.....

Baba Salihu shima sossai abunda yafaru ya taba zuciyar sa....
Chapter 107 · 0% Book details