← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 115

Sashe 20

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamy banda dariya babu abunda take tace au airport dinma sai kun nuna halin ku.

Khadija da Ahmad cike da Jin dadi suka gaisa da kowa.

Wani mayatacen kallo marwan ke jifan khadija dashi har yana cijje laban sa.
Yana tunanin yanda zeyi ya sameta cikin ruwan sanyi.

Motocin da aka kawo suka shige ciki kai tsaye gidan Samad suka nufa .
A hanyar su Ta zuwa masaukin su mai martaba yakira Dr Abdullahi ya sanar masa da zuwan sa da inda yasauka cike da farin ciki yace yana nan zuwa duba su....

Washe gari babban rana kuma ranar farin ciki ahlin gidan sheik '
Da
Gidan Dr Abdullahi.
Gidan su Al' amin.
Kowannen su yana Alfahari da zuwan wannan ranar.

Bangaren Al'amin

Al'amin Sam baya son zuwa daurin auren nan.
Dakyar Abban sa ya lallaba sa suka tafi.

Gidan sheik yau da farin ciki aka tashi anata hada hada hada farfesun n'ama n'a yan daurin aure tuni aka fitar dasu 'dan karfe goma za'a daura auran.

Rahama banda faduwar gaba babu abunda zuciyar takeyi.

Ànty data fito dakin ta sanye take da farin lace riga da zani hannayen ta sun sha zanen lallai bakaramin kyau tayi ba.
Dakin da rahama take ta nufa.
Sallama dauke a bakinta tashiga dakin.

Kallon Rahama take da kulawa tace yata wai har yanzu me makeup din nan bata zo bane.
Rahama cikin sanyin murya tace ànty yau kwata kwata wallahi nakasa gane kaina gabakidaya.
Shiyasa banma kira me makeup ba Ta fada cike da damuwa.
Ànty samun wuri tayi tazauna kusa da Rahama suna fuskantar juna tace haka kowa yake amma tunda naga har kinkasa boye damuwar ki gayamin ya kike ji.
Nan da nan Rahama tafara bata labarin yanda takejin zuciyar ta n'a mata matsifaffen harbawa

Jim ànty tayi har ta bude baki zatai magana wata kanwar ta tashi go tace ànty sa'adatu neman ki ake yi kizo kibada inda za'a zuba jallof din shinkafar ta fada cike da bukatuwa.
Ànty tace Muje tareda yiwa Rahama maganar zata dawo.

Dan wajen daurin aure kowa ya hallara manyan abokan sheik ne da basu karaso ba su ake jira à daura.

Kamar anjefo salma Daga sama haka tafado dakin su' dube dube take cikin jakar ta tadauko wannan maganin da malam isa yabata sakawa tayi cikin brezia tareda daukar wayar ta da kudi 'sauri sauri take tana kallon agogon hannun ta.
Dayasha zanen lalle.
Ganin time n'a tafiya uban sauri take ta zubawa kasancewa duk mazan gidan babu kodaya duk sun tafi wajen daurin auren.

Bangaren Yarima Samad sun sha farar shadda harda babban rigar Dayasha aiki gun kwararren tela takalmin sa half cover sossai shigar tayi mishi kyau dan yau shine rana ta farko à rayuwar sa dayayi shiga ta mussaman har yanzu dai faduwar gaba yakeji.

Faruk da Aminu da marwan suma kusan kayan iri daya suka sa.
Nan dai Faruk ya ringa daukarsu selfie da babbar wayar sa iPhone.

Sossai Samad yadara a hotunan wanda ya bayyana zallar kyawun sa.
Da cikar haibar sa.

Kokarin fita suke yace wa marwan kashiga ciki ka gayawa mamy ita da khadija su tafi gidan Dr Abdullahi inda ake taron.

Dan tuni mai martaba ya hallara wajen daurin auren inda wuri ya amsa gayyatan manyan manyan kasa harda larabawa motoci kuwa sun gama cika unguwar dashi kamar sallah idi haka jama'a sukaita hallara ana zaman jiran babban aminin sheik wanda shine waliyin Rahama.

Kafun nan su hussain Hassan 'Abubakar sunata rabon lemuka masu sanyi kowa wajen saida ya samu yajika makoshin sa' suna jiran adaura adawo bangaren ciye ciye.

Bangaren salma mai napep din daidai kofar gidan Adamsy yasauke ta sanye take da nikaf à fuskar ta 'sallamar mai napep tayi.
Daidai bangon gidan nasu ta tsaya.
Nan da nan tadauko wannan kwallin Daga cikin jakar ta.

Waige Waige takeyi tana adua Allah yasa Adamsy bewuce ba.

Aiko waigowan dazatai taganshi sunfito da abokan sa' sunci fararen shadda wai tsiya suke masa yana dariya.

Wani yaro ta hanga takira sa yazo tace yaje yakira mata angon cen..
Ba musu yatafi yasanar masa.
Adamsy da mamaki kwance akan fuskar sa ya ga wacce ke kiran shi sanye take da nikaf à fuskar ta.

Ce m'a abokan sa yana zuwa yayi tareda tunkarar inda take.

Ganin ya doso inda take cikin azzama tayi saurin shafa kwallin nan à Idanun ta.

Yana karasowa suka hada Idanu gabadaya
Yafara ganin taurari dishi dishi yake ganin ta.
Idanun sa na juya masa.
Kallon ta yake cikin yanayin daya kasa tantancewa n'a menene.

Murmushi kasan zuciyar ta
A fili kuma fuskar ta cike da damuwa tace yaya Adamsy hakika ni me kaunar ka ce bazan bari acuce ka ba.
N'a gayamaka Rahama yar iska ce amma baka yarda ba.
Yaudai ga sheda nan.
Badalar da tayi à jiya. shiyasa inka kira wayar ta bata dagawa sai taga dama..

Adamsy daya koma kamar tabbabe agabanta yace muga shedar dakike dashi yana kallon ta cikin idanu.

Kunna wayar tayi tareda nuna masa hoton Rahama kwance akan wani.
Kallon wayar yake cikin tashin hankali.
Gaban sa yayi mummunan faduwa Azabure ya furta A'a Rahama bansanki da haka 'ya zaki min haka yana kuka mai tsuma rai.

Salma ganin abokan sa hankalin su yadawo kan su yasa tajuya tabarshi wajen tsaye.
zuciyar ta cike da farin ciki tabar wajen.

Nan da nan Idanun Adamsy suka kada jajir banda hoton wanda Rahama ke kwance kansa babu abunda yake gani à Idanun sa.

Wani uban kara yasaka wanda yajawo hankalin jama'a gidan bikin da abokan sa sukayo kansa suna tambayar lafiya kuwa cikin tsananin damuwa kwance a fuskar su.

Cikin tsawa yace wallahi billa'l'azim nafasa auren nan kuma babu uban daya iya sa ya daura shi Ko andaura saina kwance shi yana musu nuni da hannun yanda ze datse auren.

Abokan sa suka ce haba ai zancen banza kake baka tashi fasa aure ba sai ana sauran yan mintuna adaura kai ma kasan zancen banza ne wlh daya Daga cikin abokan ke magana ransa à bace.

Shiga motar Adamsy yayi suma suka shiga dakansa yaja motar aguje yanata sharara uban gudu kaman ze tashi sama..

Nan gidan su Adamsy jama'a sunata jujjuya kalaman wai yafasa auren labari yajewa mommy da take cen zaune cikin baki harda mamy zaune suna taya ta rabon abinci.

Firgita tayi dajin mummunan labarin nan.
Lambar Adamsy take kira amma Sam baya dagawa..
Haka yasa tasoma kiran n'a Daddy sa shima taron jama'a yasa besan ana kira ba.
Cike da damuwa ta kalli mamy da mama karama tace wannan yaron tun haihuwar shi zuwa yanzu be taba konamun rai irin n'a yau ba.

Jibi yanda yasamu auren nan dakyar amma yace yafasa zama tayi dirshan kan kujera tana goge Zufa nan da nan hawaye yacika Idanun tace ace ranar farin cikin ta shine ze zama bakar rana agareta.

Mamy sukai ta rarrashin ta suna bata hakuri tareda bata karfin guiwar InshAllah Daddy sa bazasu saurare shi ba.

Bangaren Adamsy ikon Allah kadai yakaishi wajen daurin auren Ko daidaita parking motar beyi ba.
Yafito a ujajan cikin uban sauri, yan jaridu sunata barka da zuwa ango inaa Ko kallon inda suke Sam beyi ba.

Yanata cusa kan sa cikin dumbin Al'umma.
Kasancewa ansan shima angon ne yasa akai ta bashi hanya.

Yana isowa aka gama daurin auren salma da Al'amin.
Sun gyara zaman taré da fadin yanzu za'a daura auren Adamu da Rahama ina waliyin ta aminin sheik, ya bayyana kansa...

Ku dakata cikin tsawa wanda yayi sanadiyan kallo yakoma kansa..

Cikin ihu yana huci sama sama yace karku daura auren nan nafasa banayi.

Dr Abdullahi zumbur ya Mike tsaye yace wannan wani irin zancen banza ne adamu kake fadi bainin nasi.
Cikin tashin hankali yake magana.

Adamu
Cikin kuka yace nace kada adaura wallahi idan kun daura anan wajen zanmata saki uku n'a rantse da Allah.
Yana haki muryan sa ya disashe.
Sheik wani Zufa ne ke keto masa ta Ko ina cikin rawan murya yace adakata daurin auren nan.
Kunji furucin sa dan haka ni uban Rahama n'a hakura.

Yana kokarin cewa kowa à tashi Daga wajen daurin auren tunda andaura auren salma da Al'amin.

Mai martaba ya dafa sheik da waliyan ango yace ku dakata.

Kowa wajen hankalin sa yadawo kansa zaro bandir din kudi yayi Daga cikin aljihun sa naira dubu dari yace gashi sadaki ne.

Kallon sa sheik yakeyi da Idanun sa suka kada.
Yana masa kallon kudin menene ?
Mai martaba yace adaura auren Rahama da jikansa Abdul Samad.

Yarima Samad duk abunda akeyi wajen daurin auren bedame sa ba Jin an ambaci sunan sa cikin tsananin tashin hankali ya..................

Saimun hadu à Paid book.

Yan spécial group À Da B jinjinar bangirma à Gare ku.

Hakama yan normal grp ina Alfahari daku.
Domin saidaku muke cimma duk wata nasara.

I love my fans

09069080725
3/20/22, 22:34 - A'ish: Kanwata

2️⃣6️⃣

Cikin tsananin tashin hankali yake kallon mai martaba muryan sa na rawa yace wani jikan naka kenan 'Sam yama mance cikin taro suke..

Mai martaba yace inaga kai kadai ne Abdul Samad a masarauta.

Mai martaba beko bi takan yarima samad ba ya tsaya yanata kokarin shawo kan sheik daya amince adaura kawai.

Aminin sheik Isa
yayi wa sheik magana yabari kawai adaura kodan su fita kunyar jama''à da aka tara.

Sheik yace wa Aminin sa banki zancen ka ba shin wane ne yaron kuma ya tarbiiyyar sa yake.
Nifa ba neman kai nakeyi da yata ba.

Suna gama tattauna da sheik.
Aminin Abba ya tunkari mai martaba yace uban Amarya ya amince adaura.
Sheik mamaki ne kwance akan fuskar sa ganin ba haka sukayi da Aminin sa ba.

Nan da nan yan daurin aure suka gyara zaman su 'Aminin Abba yamika sadakin hannun Abba.

Dr Abdullahi banda kukan zuci babu abunda yakeyi.
Jin za'a daura da jikan sarki yasa yadanjin saukin abunda ke damun sa.

Yarima samad da hankalin sa yayi mugun tashi kokarin tashi yake yace wallahi badashi ba abokan sa suka rirrike shi suna kokarin barin wajen dashi.

Daidai fita filin daurin auren yaji ana sanarwa ta cikin lasifika.

Ana fadin Alhmdulilah andaura Auren Rahama da angon ta Abdul samad bisa sadaki dubu dari.
Chapter 20 · 0% Book details