← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 115

Sashe 71

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salma cikin bacin rai tabar wajen.
Tafiya take bata gane inda take sa kafafun ta dan bakin cikin Karima..
Samun wuri tayi gefe daya tazauna taringa rusa uban kuka ita kadai zaune...
Faruk da Aminu ne suka shigo ganin Salma tana kuka bakaramin Daga musu hankali yayi wajen ta sukayi Aminu yace wannan kamar kanwar Rahama..
Faruk yace ita ce mana koba ka gane ta ne..
Cikin damuwa Faruk yace wai Salma haryanzu jikin ne Ko mu koma Asibiti ne...
Girgiza kai tayi tace A'a cikin sheshekar kuka.

Aminu yace to laifi akai miki ne..
Girgiza kai tayi tace wai ni yanzu ace ban isa inje sashin yaya ta saida izinin su Ko n'a baiwa.. Tana matse hawaye Daga Idanun ta...
Faruk dake kallon ta cikin kwantar murya yace.
Wace baiwa ce ta hanaki shiga sashin su Yarima...

Aminu yace nasan dai bewuce Karima Ko..
Salma tace itace mana bakuga rashin mutunci data shuka mun ba.
Harda mun sharri wai nazo da mugun abu...
Nidai wlh aduba lamarin nan dan so nake inga Rahama zamu tattauna wasu maganganu ne..

Aminu yace to Salma banda abunki yanzu d'are ne fa''kuma nasan Yarima yana ciki' suna taré kinga Amarya ce.
Ki hakura zuwa gobe sai kije Ko....
Salma kara sautin kukan ta tayi tana bubbuga kafa kamar karamar Yarinya....

Aminu yace yi hakuri Salma bara a kira Yarima Samad a sanar masa dazuwan ki..
Komu da muke à bokan sa gaskiya
in bata kama dole ba.
Bama zuwa sashin sa da daddare sai inhar shine ya gayyace mu...
Yanzu ma da kika ganmu ba wajen sa muka zo ba..
Gun Mamy zamuje......
Faruk yace wai ina Asiya ne...
Salma dake matso kwalla tace tana ciki nabar ta '' tana waya da wani....

Nan da nan Annurin dake kwance kan fuskar Faruk ya dauke yahade rai cikin muryan sa data canza kala lokaci daya yace yanzu tana wayar ne..?

Salma tace eh mana saita kwana tana waya wani lokacin ma zata kai karfe hudun d'are Sannan ta kwanta shiyasa bata gajiya da barci safe....

Aminu Sam maganar Salma batayi masa dadi ba... Yace Amma Salma bekamata ki fadi haka ba.. Ance kafadi Alkhairi kokayi shiru.....

Salma dake kunkuni tace gayamin sharri acikin zance na Daga ya tambayeni n'a bashi Amsa to meye laifina..
Aminu yace bakida laifi kodaya.

Bara inkira Samad asanar masa da zuwan ki dan yabada damar abude miki hanya kije Ko...
Sossai taji dadin haka aranta har ta shirya irin wulakancin da zatayi wa Karima idan zata bude sashin Yarima.....

Wayar tayi ring har ta gaji Sannan Yarima ya Daga...
Dagacen bangaren yana makale jikin Rahama tana zuba masa shagwaba ya kyaleta... Bata so
Yace Aminu yadai harkun shigo ne..
Aminu yace Tabe Tabe gamu nan nida Faruk zamu sashin Mamy.
Muka iske Kanwar Matar ka tana kuka wai Karima taci zarafin ta tahanata zuwa sashin naku.....

Yarima Jin an anbaci kanwar Matar sa yasa............

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah...

Yawwan comment Yawwan typin.....
3/21/22, 07:51 - Nuriyyat: KANWATA

7️⃣0️⃣

Yasa shi tashi tsaye yace karta ga laifin Karima dan doka ne aka kindaya mata '' amma kuma maganar cin zarafi zanji dalilin daya sa tayi hakan...

Aminu yace OK gara haka ai.
Ya za'ai tashigo ne tace tanason ganin yayar ta..
Murmushi Samad yayi yana kallon Rahama dake kokarin rufe jikin ta da bargo '' yace uhmm kudai bata hakuri nima ina nan fitowa ni kadai yanzu.
Mu hadu Sashin Mamy.

Aminu yace Tabe Tabe saika zo din Daga haka ya katse wayar..
Kallon sa yadawo akan Salma yace kindaiji abunda yace '' hakuri yake baki akan bazaki samu ganin Rahama a yau ba.
Sai dai gobe.....
Kallon sa yamaida akan Faruk yace kai kuma menene damuwar ka naga tunda akai maganar Asiya ka canza Daga yanayin ka

Faruk yace Ah Ah ba haka bane yanzu dai Muje Sashin Mamy din..
Barin Salma sukayi awajen zaune..
Ganin lallai suma sun raina mata wayau ya za'ai tana kanwar matar gida zasu taka ta..

Saida ta Share minti goma zaune bayan tafiyar su Faruk.
Tashi tayi jiki asanyaye zata wuce masaukin su...

Jin karar takun takalmi yasata waigawa taga me zuwa...
Caraf Idanun su ya tsarke cikin juna ita da Samad wani kallo yake bin ta dashi masu tarin ma'anoni....harya iso gaban ta batasani ba dan ta shagala da kallon sa....

Tsintar muryan sa tayi yana Fadin Salma mekikeyi anan ke kadai..
Bama tasan yana magana ba Sam hankalin ta baya kusa 'ta shagala da kallon sa..

Da Mamaki yake kallon yanda ta kura masa idanu... Sunan ta data ji ya Ambata da karfi yace Salmaaa firgit tadawo hayyacin ta.. Cikin Jin kunya tafara Murmushi yake.
Shiko kawar da kan sa yayi Daga kallon ta..
Yace mekike yi anan maza ki wuce daki '' banason yawo fa..
Kin ce kinason magana da yayar ki naga kusan wuni kukayi da ita a yau..
Dan haka kibari gobe zata zo da inda kuke..
Wannan kallon da kike yawan yimin n'a menene yafada tareda rungume hannayen sa a kirji.

Cikin Jin kunyar kalaman sa da rikattatun Idanun sa daya zuba mata akaran farko n'a rayuwar ta..

Cikin sanyin murya tace meye A'ciki danna kalle ka kaifa mijin yaya ta ne..

Samad dake nazartan kalaman ta yayi shiru cen kamar baze magana ba..
Har ta cire rai sai taji yana fadin eh lallai ni mijin yayar ki ce...
Wannan ba hujja bace kiyi ta kallona har in tsargu da kaina.
Dan haka inason Daga yau ki daina inba da wata manufa kukeyi ba.....

Salma da bakin ta ya mutu tace nidai bada wata manufa nakeyi ba''
Saide kaine baka yarda da kanka ba..
Cak yatsaya da shirin tafiya da yakeyi..
Waigowa yayi yana kallon ta tun daga kasa har Sama
Kamar ya banyarda da kaina ba''' Daga nace miki kidaina abunda beda amfani
ke Kanwata ce inna sameki da kuskure to zan hukuntaki daidai da abunda kika aikata koda khadija ce haka zan mata kisa ki rubuta ina binki bashi daya karki bari yazama uku kinji Ko ya saki wani shu'umin Murmushi tareda barin wajen cikin isa da izza...

Kallon sa take harya bace mata da gani lallai ta yarda yarima duk yanda take tunanin sa ya zarce ta..
Yana bin ta bashi daya take ta maimaitawa tome yake nufi kenan rasa me bata amsa yasa
Jiki babu kwari tayi hanyar dakin nasu...
Bakin ta dauke da Sallama ta shiga dakin iske Asiya da Ànty suna karatun Alkur'an tare..
Sallamar ta yasa suka katse karatun suna mata kallon ina tafito..

Cikin inda inda tasoma kame kame uhmm daman ina tareda su Faruk ne dan ciwon ciki n'a ya tashi...

Ànty tace yanzu akwai wanda ya tambayeki inda kika fito.
Girgiza kai tayi tace A'a..
Asiya dake tabe baki tace to ai yawo beda amfani agareki kina matar aure kardai sashin Rahama kika je dan Allah kibarta ta huta da mijin ta 'karki kashe mata aure..

Salma da Ranta yagama baci tace au nice ma zan kashe mata aure..
Innayi haka meye riba ta..
Asiya tace ribarki shine kiga kun rasa dukan ku.

Ma'ana ta rasa Yarima kema kinrasa kinga babu wanda yake dashi cikin ku..
Salma zatayi magana Ànty tayi mata hannun stop..
Tace ke me kike tunani ne bamusan lagon ki ba..
Kin hana Adamu auren Rahama yanzu zaki kashe mata auren ne...

Nidai nasan take taken ki bewuce kiga kin rabata da gidan Sarauta nan...
Wallahi kika kuskura kika kashewa yata aure uhmm wlh ko ubanki be isa yarabani dake ba..

Tunda nake dashi bamu taba fada ba amma akan haka zamuyi inhar yace ze daure miki gindi..
Salma sai hura hanci takeyi cikin tsananin bacin rai tace zato zunubi ne koda yazama gaskiya...
Banda zuciyar ku babu Allah taya zakuyi mugun tunanina akaina...
Auren nata da Adamu mugun halin ta yasa ya fasa auren ta....
Bata karasa fadin abunda zata ce ba taji anty ta wanke ta da gigitaccen mari wanda yasa nan da nan tafara ganin taurari..
Ànty zata kara mata marin Asiya tarike hannun ta tace kiyi hakuri InshAllah zata canza halin ta....
Karmu biye mata muzama irin ta..

Salma rushewa da uban kuka tayi hakan yasa tadau wayar ta takira mama cikin sheshekar kuka ta sanar mata da abunda anty da Asiya sukayi mata..

Dagacen bangaren mama tace shegu yan iska d'angin matsiyata sun je maula aidole su wulakantanki.
ita Rahama dan uban ta tunda tayi aure sau daya takirani kuma Koda zata tafi yakamata tazo tamun sallama ki rabu dasu wallahi har Rahama sainayi maganin ta....
.
Salma cikin Jin dadin kwantar mata da hankali da Mama tayi tace mama.
Wai ina Abdul jalil ne.
Mama Tace shege baya wuni gida tunda yaga shegiyar uwar sa bata nan
a hanse free Salma tasa wayar yanda su Ànty zasu ji abunda suke fade...
Ita Ko Ànty banda kukan zuci babu abunda takeyi...
So take ta sanarwa sheik gaskiya ya raba masu gida ita da Mama Ko kuma ita takoma gidan su tazauna har asamu mafita hakanan takeji zuciyar ta be aminta da komawa gidan nan ba..

Salma suna gama wayar ta katse tanata jijjiga jikin ta tace uhmm kalan dangi kawai..
Dukan ku babu wanda ya hada jini da Rahama..

Ànty tace ninan n'a hada jini da Rahama Saboda inkikaga Abdul jalil to kamar kinga Rahama ne suna mugun kama.
Jinina da nata sun gwauraye wuri daya.

Asiya cikin bacin rai tagama karanta sakon Faruk daya shigo wayar ta...
Dago kai tayi tana kallon Salma tace wawiyar banza watau sharri kika kulla mun wajen Faruk meye ribarki algunguma...
Inkina son shi kije ki kashe auren naki sai inhada ku aure....

Ànty tace ke kuma meya hadaki da Salma ne tana kallon Asiya da Ranta yake abace..
Asiya taba Ànty labarin abunda Faruk ya fada mata,..
Cikin takaici Ànty tace Asiya karki damu matar mutum kabarin sa kalaman sa karsu bata miki rai kidai bashi hakuri.
Ke KUMA SALMA kindai bani wlh halinki sai ke shasha......
Chapter 71 · 0% Book details