← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 115

Sashe 44

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salma n'a komawa gida Ànty ta tareta tace karki damu da Abunda yayi tashin balaga ne ke kuma kisan matsayin sa.
Ki girmama shi.
Mijin ki ne Aljannar ki n'a tafin kafar sa.
Hannun tayiwa Ànty Alamun ya isa haka tana kunkuni tace ainasan da haka Rahama ce bata sani ba tana cen gidan da ba'a son ta..
Fuuuuu tawuce cikin dakin su..
Ànty da mamaki take kallon ta tace wai ita wannan yaushe zatai hankali ne.
Uhmm Allah yashirye ki tafurta tareda barin wajen...

**********************
Sheik zaune kofar gidan sa shida Aminin sa Isa.
Suna tattauna tafiyar da zasuyi zuwa kasar Gabon.
Gwanati ta gayyace shi zuwa taron walimar daurin auren diyar shugaban kasar Gabon.

Parkin din motar da akai daidai kofar gidan nasa..
Murmushi Sheik yayi ganin anrubuta Samad ajikin motar.
Aminin sa yace kamar surukin ka kobashi bane yana kallon Samad dake kokarin fitowa Daga motar.
Sheik yace eh shine ashe ka gane shi.

Eh mana dole in gane shi kasan wajen daurin auren nan jinai yana fadiwa mai martaba wani Samad din za'a daura wa aure..
Sheik yayi Murmushi yace au Ko ni ne hakan zancen daga zuwa daurin aure sai ta juye dani..
Fuskar su dauke da Murmushi suna kallon Samad dake tunkaro su
Shida abokan sa..

Cike da nutsuwa suka karaso kan su akasa suka durkuse kasa cikin ladabi suka gaida sheik da Aminin sa.
Sossai suka amsa musu cike da fara'a.
Sheik. Yace kace munada manyan baki.
Muje Daga ciki Ko.
Tashi sukai tareda Aminin sa.
Sukai ciki Samad da abokan sa suna bayan su.
Direct dakin baki yakaisu tareda ajiye musu ruwa da lemu a gaban su..
.
Yarima Samad yace sheik imam mungode sossai da karramawa..
Sheik. Yace anzama daya ya Rahama take ?.
Cikin Jin kunya yace tana lafiya lau.
Aminu ne yayi gyaran murya yasoma yiwa sheik bayanin dalilin zuwan nasu...
Sossai sheik da Aminin sa suka jinjina Al'amarin

Sheik yace yanzu kimanin wata nawa baku ganshi ba.
Yarima Samad cikin yin kasa da murya yace shekaru biyar kenan har muna neman n'a shidda..
Kada kai sheik yayi yace eh lallai andade Allah ya bayyana shi.
Dukan su da Ameen suka amsa.
Kallon Samad yayi yace karka damu zamu tayaka da adua.
Kaima ka dage har tashin d'are karkayi wasa dashi.
Samad yace InshAllah.
Adu'oi yarubuta masa masu muhimmancin
Jikin wata farar paper.

Masu karatu inkuna bukata zan turo muku very important wlh..

Mika masa yayi yace sadaka kada kayi wasa dashi d'ana zakaga haske.
Sannan kasa Rahama ta tayaka nasan batada sanya wajen sallah d'are.
InshAllah za'a mata magana Daga haka suka tashi har wajen mota sukai masu rakiya shida Aminin sa.
saida motar t'asu tabar unguwar Sannan suka juya shida Aminin sa..
Suna yaba hankali da nutsuwa irin ta jinin saurata basusan dawan garin ba.. *************************

🇧🇯

Hajiya Hassana daidai kofar masarautar mai mashin ya ajiye ta....
Ta sallame shi tareda nufo kofar masarautar gheuzo.
Kallon yanayin tsarin gine ginen su take yi yanda aka kawata wajen sossai..
Gwanin ban sha'awa.
Kwankwasa kofar tayi yayi daidai da ana kokarin budewa Yarima Ahmad kofa zefi ta yana cikin motar sa.
Sauke glashin motar yayi yana zare idanu ganin hajiya hassana da yayi cikin hanzari yafara......

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:44 - Nuriyyat: 4️⃣8️⃣

Cikin hanzari yafara kiciniyar bude kofar motar sa '' cikin azama yataho gaban ta kallon ta yake tareda sauke fask mask dake fuskar sa.
Baiwar Allah me kike nema ne wai dan Allah.
Meyasa ku mutane bakwa gane maula ba sana'a bace yakarashe zancen yana nuna mata hanya data wuce Daga nan..

Hajiya Hassana cikin dan bata rai yaro karami n'a gayamata kalamai daya zo bakin sa, tace uhmm kai Ahmad ashe haka kake maganar mutane gaskiya ne kenan..
Kallon rashin fahimtar inda zancen nata ya dosa ya fara yace bangane zancen mutane ba wani abu akace miki nayi..
Gyara Tsayuwar tayi tace, kwarai 'kuwa an gayamin kana da girman kai sabanin yayan naka.
Kuma ni ba maula nazo yi kai kanka kasan nafi karfin haka..
Kallon ta yake yanda ta hada rai take gayamai maganganu.
Daga kasar Ghana nake.......
Aiki nake nema kuma a gidan sarauta nakeso dagaske nake maka ba maula nazo ba ka yarda dani
Wani kallo yake bin ta dashi masu tarin ma'anoni ''
Kinga dan Allah banason shishigi
Bama bukatar ma'aikata à masarautar.
Tunda angaya miki inada girman kai meye n'a tsaida ni yakarashe zancen tareda komawa wajen motar sa.
Kallon banza yake ta bin ta dashi.
yana shiga motar yakara gaba
kallon sa take harya fita layin.
Karasawa wajen kofar shiga masarautar tayi taci Sa'a khadija ta fito yiwa kawar ta rakiya.
Inawuni tace musu kallon ta suke suke..
suka amsa mata da lafiya lau ne.
Tareda wuce ta.
Kawar khadija tace wannan matar kuma Daga ina tana kwabe baki.
Khadija tace ina zan sani nima hk nagan ta..
Ciki gaba da tafiyar sukai inda suka tsaida me napep.

Kawar khadija n'a hawa napep
Khadija tajuyo da nufin komawa ciki.
Hajiya Hassana ta tareta cikin damuwa kwance a fuskar ta tace dan Allah baiwar Allah ki taimaka mun inshiga masarauta aiki nake nema kudina ne suka kare Daga nazo neman mahaifina gashi inason komawa kasar mu Gabon kudin jirgin da gindin sa yazauna hôtel din d'ana sauka yau kudina zekare bansan ya zanyi ba insuka koreni ba..
Khadija tace subuhannalah wayyo baiwar Allah kinban tausayi.
Kin buga gidan ne ba'a bude miki ba ?
A'a ina dai kokarin bugawa naga wani matashin saurayi yafito a mota kin saurarena yayi inaga sauri yake.
Khadija tace Ayya haka yake kiyi hakuri nasan yaya Ahmed ne, zan taimaka miki InshAllah bara inshiga ingayawa Mamy intaban izini zanshigo dake takarashe zancen tareda barin wajen...

Hajiya Hassana tace uhmm Allah yasa ta amince dan wannan bukata ta shine farkon nasara ta InshAllah..

Khadija n'a isa sashin Mamy ta iske ta tayi uban tagumi batayi wata, wata tace Mamy n'a wai haryanzu bazaki rage damuwa ba.
Kinga wata bakuwa awaje ta bata labarin yanda sukai tace kuma fa Ahmad kin sauraren ta yayi yawuce.
Mamy tace gaskiya be kyauta ba ki je ki shigo da ita muji me tazo dashi.

Cikin Jin dadi ta tafita wajen
Dan ta shigo da hajiya hassana.

*************************

Fulani da Abban Marwan zaune suke fuskokin su dauke da damuwa.
Marwan cikin bacin rai yace wlh Mamy kashe Yarima ya kamata muyi da matar sa.
Kokuma a raba su.
Idan anje miki ya kusance ta karkiyi Gardama wallahi.
Cikin takaici Abban Marwan ke ta huci SAMA YACE AI INSHALLAH baze kusance ta ba dan haryanzu beda karfin sha'awa ajikin sa.

Fulani tace injiwa ya gayamaka haka bakada labari ne.
Bokan daji cewa yayi wallahi rannan kadan yarage be kusance ta saida suka sauya mata halittar ta zuwa n'a kunama shine dalilin dayasa be aikata abunda yayi niya ba.
Dankali Abban Marwan ya furta nan take wani Zufa ya keto masa duk sassar jikin sa..

Kiyi hakuri Fulani in Allah in Allah ya yarda da matar tasa zezo..
Ai kinga kwanaki da Samad zeje kano Mai martaba yayi na'am da tafiyar sa yanzu kuma yafara Jin haushin haka har yana mummunar furuci akan Yaya Salihu..
Wlh koda mai Martaba kadai da ita shegiyar matar Samad zamu iya rusa su gabadaya.
Nifa har Mamys sonake tabar masarautar nan to zaman me takeyi ne yafada cikin Daga murya...
Fulani ta d'ara tace kai ai Mamy da kake gani muguwar icce ce bakar munafuka ce ai yanda mijin ta yabar Masarautar nan InshAllah itama tana ji tana gani zata barshi bari har surukarta tazo ni Fulani wlh saina nasa sun zama abun tausayi acikin masarautar nan....
Dariya Marwan yayi yace nima dai yanzu naji bugu.
Har labari yazo mun wai Mai martaba yana son ya Nada Yarima Samad à matsayin Sarki kiji fa.
Yana kallon uwar sa.
Dafashi sukai shida Fulani suna bubbuga bayan sa Alamun rarrashi.
Kwantar da hankalin ka Marwan InshAllah Burin su baze cika ba...

**********************

Da sallama bakin su suka shigo Sashin Mamy khadija n'a gaba Hajiya Hassana nabiye da ita abaya....
Mamy dake zaune tana canza channel ajiye remote din hannun ta tayi fuskar ta dauke da Murmushi tayi sannun ki da zuwa ga waje nan ki zauna.
Hajiya Hassana neman waje tayi à kasa ta zauna cike da ladabi take gaishe da Mamy..
Mamy tace dan Allah tashi ki koma kan kujera.
dan Allah kiyi hakuri à kan abunda Yarima Ahmad yayi miki..

Hajiya Hassana Murmushi tayi tace haba ai yaro da nakowa ne wlh bakomai bane '' Inkika duba wani bangaren yanada gaskiya yanzu mutum ba abun yarda bane..
Kuma zama kasan yayi min dadi kada ki damu nagode da kulawa.

Mamy tace hakane kuma Amma kasa kyakyawan niya InshAllah baza'a ci galaba akan ka ba...

**************************

Gabon 🇬🇦

Cikin tashin hankali baba Salihu yake kallon computer dakin nasa..
Ganin hassana hankalin sa yayi mugun tashi yace wannan matar me take nufi ne wai haukar taje tafadawa mata ta Ko sotake ta tona mun asiri asan inda nake..
Wata zuciyar tace tome abun damuwa kawai kabar kasar..
Yace A'a kozan ban kasar nan sai nayi yanda za'a yi wannan matar ta dawo Gabon InshAllah
Ransa a matukar bace yakira me bashi labari.
Bugu daya ya Daga..
Dagacen bangaren yace ya shugaba naji muryan ka sai a hankali..
Baba Salihu yayi masa bayanin matsalar daya kunno kai
.
Jinjina Al'amarin yayi yace kasan dai ina kano Ko amma akwai wanda nayarda dashi anan kwatano kuma amintaccen yarima Ahmad ne zansashi yasa idanu akan ta.
Batareda yasan dalilin yin haka ba.
Cikin. Gamsuwa da bayanan sa baba Salihu yace pls ka taimaka mun dan banson duk shirina yatashi à banza ta dalilin ta..
Daga haka. Sukai sallama.
Kasa zaune yayi yanata safa da marwa a dakin nasa..
*************************

🇳🇬 KANO

Horn sukai mai gadi ya wangale masu gate....
Parking space suka ajiye motar..
Faruk ya zagayo dan budewa Samad mota
Sai gani yayi ya bude amma be fito ba.
Ya saura acikin motar be fito ba
Aminu yace, wannan lafiya kuwa shibe fito ba.
Faruk yace ka kyaleshi Sarauta ce ta motsa naga dai yanzu yagama waya.
Chapter 44 · 0% Book details