← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 115

Sashe 38

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rahama zuwa tayi gaban Salma dake kallon su cikin Mamakin ganin Yarima Samad din ganin shi take kamar cikin larabawa yafito yanda fatar jikin sa ke fresh '
Bakin sa take kallon yanda leben sa yake jajir. '.
Rahama ta dawo da ita Daga tunanin ta tahanyar shafa fuskar ta tace kanwaty yajikin naki.
Salma tace naji sauki amma Idanun ta nakan Samad.

Rahama Kallon Ànty take tace waimeke damun Salma ne.
Ganin su Samad na wajen yasa Abba fadin inaga Maleria ce da taifot saidai result yafito zamu ji..
Sannu Rahama ke jero mata tace wai ina mijin Salma ne.
Mama tayi Jim tace yaje yadawo.
Cike da tausayawa Rahama ke kallon yanda Salma ta rame sossai..
Samad yace Abba daman munzo da niyar zuwa wajen naka sai mukaji kuna Asibiti..
Cikin Jin Dadi sheik yace au to nagane nanma ya isa ya muka iya da kaddarar cuta sai hakuri..
Samad ahannun yasa cikin Aljihun sa yazaro bandir din dubu dari ya ajiye gaban Ànty yace gashi babu yawa ayi hakuri..
Sheik yace anyi haka kuwa d'ana yana Murmushi yace amma kudin sunyi yawa ka rage su..
Fauk yace karka damu ya sheik imam '' kudin Asibiti har ku gama zama yadauki nauyin sa.
Adu'arku yake nema dan shima yazama dan 'ku.
Sossai Samad yaji Dadin bayanin Faruk.
Tashi sukai da niyar zasu fita.
Samad ya kalli Mama yace uwata zamu tafi Ko zan iya zuwa gobe gidan naku dan inga hoton.
Sheik yace karka damu zanturo Abdul j'alil yakawo maka.
Samad kallon Rahama yake yaga Alamun ba son tafiya take ba.
Sheik n'a Lure da kallon Rahama dayake yi.
Haka yasa yayi gyaran murya yace Rahama tashi kuje Ko tunda anyi ziyar hankali yakwanta.
Samad ya karbi zancen da A'a ka barta akwai inda zamu je inmun dawo zamu biyo mu dauke ta yakarashe zancen tareda fita dakin.
Abokan sa suka take masa baya.
Sheik godiya yashiga yi musu bisa kokarin sa da kyautatawan su.
Sheik dawowa cikin dakin yayi yazauna yana kallon Rahama Sam bega Rama tattare da ita ba.
Yaga tadanyi haske.
Cikin damuwa yake ba Rahama labarin abunda yasamun Salma.
Salati ta fara tana kallon Salma tace Amma Abba mijin ta beda imani yanzu yana ina haka.
Sheik yace inazan sani.
Saidai Allah yakyauta ya tsare gaba.
Salma cikin kuka tace nidai bazan koma gidan shi dukana yake yi tareda nuna musu shaidan dukan.
Ganin jikin ta da zanen bulala.
Mama tace subuhannalah harda duka tace kwarai kuwa.
Sheik yace ai bazan raba auren ba koda zaki koma ba yanzu ba Salma sai kinyi watanni agida InshAllah.
Salma taji dadin furucin Sheik har ta murmusa Rahama tace Abba Ko zata dawo gidana da zama ne.
Dasauri ànty ta katseta ta hanyar fadin A''à bazata je ba akan me zata zaune miki gidan miji..
Ran Mama da Salma yayi mugun baci hakanan su ka shanye abunda tayi musu..
Sheik yace Sa'adatu ai gaskiya kika fada da auren wani bazaki je gidan wasu ba ki zaune musu ba saidai ziyara.
Rahama tayi shiru tana sauraren su.
Sheik tashi yayi yace to zanje sai bayan isha'i zandawo Daga haka yabar dakin.
Sheik nafita Mama taringa jifan Ànty da kallon banza.
Ita Ko ànty hakan bedamun ta inhar akan gaskiyar ta ne.

*************************

🇧🇯 Kwatano.

Karima ce tasamu wani sirrintance waje tareda zama ta kunna wayar ta.
Nombar Samad ta danna wa kira.
Tayi ring kamar baza'a Daga ba.
Jin an Daga yasa ta sakin ajiyar zuciya.
Cikin kasa da muryan ta tace ya shugaba na Yarimar Gheuzo baiwar ka Karima ce..
Dagacen bangaren yace Karima sai yanzu kika samu damar kirana tace kayimun Afuwa tareda risinawa kamar tana gaban sa.
Abdul Samad yace inason ki samun idanu sossai akan Marwan.
Da shige da fitan sa.
Idan drever na yana nan ki masa sakon nan shine zeringa bin sahun Marwan har fulani 'da Abba Marwan.
Ina fatan kin fahimta tace naam ya shugaba.
Yace ke cikin gida ne zaki min aiki taimako ki shine zekai ni da nasarar gano baiwar nan data gudu Saratu.
Cike da gamsuwa Karima tace InshAllah zanyi yanda kace.
Har ze katse sai jiya yi tace ya shugaba na.
Ya matar taka take.
Shiru yayi na wani lokaci kafun yace tana lafiya Karima..
Karima tace Ranka ya dade karka zo garin nan da ita harsai Allah ya azurtaku da haihuwa.
Cike da Mamaki yake nazarin kalaman ta yace Karima banfahimce ki ba
Ki dan ban haske.
Har ta yi tunanin bazata gaya masa ba sai ta tuna irin kaunar da take masa.
Cikin raunin murya tabashi labarin abunda yafaru a yan kwanakin nan..
Ya Girgiza matuka da Jin zancen nata.
Cikin dauriya yace kada ki damu Karima ni wannan be dameni ba.
Matata kuma zanzo kwanan n'an wajen wani shari'a bazan zo da ita ba.
Sossai Karima taji dadin bayanan sa.
Daga haka sukai Sallama.

************ ****** *******

🇬🇦 Gabon

Hajiya Assana ce zaune kan sallaya bayan ta idar da Sallah Daga hannayen ta sama tayi tana rokon Allah ya mallaka mata zuciyar baba Salihu kuka take iya karfin ta..
Diyar ta mai suna hauwa ce tashigo cike da mamaki take kallon uwar ta tana kuka ta durkushe gaban ta tace Mama haryanzu baki daina kukan mutuwar baba bane.
Adua'a yake bukata.

Girgiza kai tayi tace hauwa Ba wannan kukan nake ba yata.
Cikin tsananin damuwa hauwa ta tallabo fuskar uwar ta tana goge mata hawaye jiki asanyaye tace mama Ko baki yarda dani bane.
Hajiya hassana dago jajayen Idanun ta tayi tana kallon yar ta tace niko nayarda dake hauwa ta'''...
Hauwa ta numfasa tace to dan Allah gayamin damuwar ki inbada maganin ta intayaki da adua

Zaunar da hauwa tayi tace akwai wani bawan Allah mai suna Alh Salihu turaki wlh nakamu da son sa banajin zan iya rayuwa babu shi.
Hauwa tace Alhaji Salihu turaki daya dai d'ana sani dan gidan Sarauta ne fa tafada cike da zare idanu.
Mamar ta tace ya'akai kikasan haka daughter tareda share hawayen ta.
Numfashi hauwa ta fesar tace mama nasan shi kiyarda wani dattijon yana gidan sa.
Agun jikokin sa nake samun labarin sa ance Sarki ne a garin kwatano.
Amma wasu dalilai yasa yasauka kan karagan mulki.
Hajiya Hassana tashi tayi Daga zaune tana ciza yatsar ta tace yanzu nagane dalilin dayasa yaki Amsar tayi n'a.
. Hauwa tace menene dalilin mama ''
ta tsareta da manyan idanuwan ta.

Hajiya hassana tace inhar Salihu turaki ne uhmmmmmmmm

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/20/22, 22:34 - A'ish: KANWATA

Akwai channel dîna KYAUTA TV kushiga ku danna mun.

Subcribe

Comment

Share

Like

Littafin kaikajawa kanka audio yana kan channel dîna saina jiku.

Littafin nan kudi ne Inkin ganshi a wajen group dîna na sata.
Inkin bukata ga nomba.
09069080725.

4️⃣3️⃣

Hajiya Hassana tace inhar Salihu Turaki ne uhmmmmm nasan sunan sa tunda dadewa '' Saboda mummunar labarin daya karade a duniya akan sa.
Hauwa ta zare Idanun ta tace mummunar labari kuma wannan Salihin mutumin.
Hassana taku tayi taje wajen Windows dakin nata maida kallon ta tayi à wajen tace ke bazan iya gayamiki wannan labarin ba harsai na binciko gaskiyar Al'amarin.
Hauwa kallon bayan uwar take fuskar ta dauke da damuwa tace taya zaki gano abunda ke boye bayan kina nan shikuma garin su kwatano ne.
Dariya mai sauti hassana tayi tana buga kafafun ta kasa tareda waigowa tadawo kusa da yar ido cikin ido take kallon ta tace kwatanon zanje InshAllah indai bashida hannun akan abunda naji to wallahi zan sama masa mafita.
Hauwa tace la'ila rike da baki tace mama ki rufa mana asiri '' ki hakura da Salihun nan banjin dadin damuwa da wanda be damu dake ba da kike yi akarshe yazo be aure ki ba.
Murmushi mama tayi tace baby n'a zanyi ne Dan Allah dakuma kaunar da nake masa '' kimun adua dan Allah karki fitar da sirrina Ko kanin ki kada ki gayamasa ga inda zanje.
Kinji Ko !!
Gyada kai tayi Alamun gamsuwa Idanun ta cike da kwalla ta rungumi uwar ta cikin sanyin murya tace Mama Allah yasa kada kiyi zuwan banza nasan ke uwa tagari ce dan Allah ki kara rike mana martabarki da mutunci ki ina Alfahari dake uwata.
Kuka ya kwace mata tana shafa kan hauwa tace nagode daugheter tare da manna mata kiss 💋 a goshin ta..

*************************

Baba Salihu zaune adakin kamar yanda yasaba ya kunna wannan cctv camera yana kallon abunda akai uhmm Samad yafada à zuciyar sa nasan ka bakada sauki fa 'tunanin mafita yake y' hakan yasa ya dauko babbar wayar dake gefen nasa ya danna kira gun mai bashi labarin Samad..

Cikin damuwa yace dafatan kowa lfy.
Yabashi amsa da lafiya lau ne.
Dan numfasawa baba salihu yayi yana taune lip din shi.
Yace nalura kamar Rahama bata Jin dadin zama da Samad '' Dagacen bangaren yace shima yaso ya fahimci haka amma zekara sa idanu yaga ne gaskiyar Al'amarin.
Baba Salihu cikin damuwa yace bana son mahaifina yabar duniya banyi tozali dashi ba..
Idanun sa cike da kwalla.
Kasa jure wayar da suke yi yayi tareda katse wayar y azauna yana kuka iya karfin sa.
Tuno abunda yasuka wuce shekara da shekaru yake cikin kunan rai yace waze wanke ni a idon duniya..
Ya zanyi mahaifina yaga haske na..
Daga HANNAYEN SA SAMA yayi cikin kuka yana rokon sassauci a rayuwar sa....

Ita Ko hajiya Hassana ta shirya tsaf har airpor yayan ta suka rako ta zata tafi kwatano.

Suna Airport har jirgin nasu ya tashi sararin samaniya.

Hauwa da kanin ta jiki asanyaye suka koma gida
.

🇳🇬 KANO

Sai bayan isha'i suka koma asibitin dan dauko Rahama daidai da dawowar Abubakar da Abdul jalil 'cikin Jin dadin ganin Samad sukai musabaha dashi'
Abubakar yace mijin Rahama Ko ?
Chapter 38 · 0% Book details