← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 115

Sashe 39

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Murmushi yayi yace eh nine.
Ah yanzu kuka zone mu shiga Daga ciki mana.
Aminu yace Ranka ya dade ai munzo daukan Rahama mu kazo yi yafada tareda yin gaba.
Abubakar yace bismillah Muje cike da dokin son ganin Rahama yashiga dakin.
Yana shiga ya iske ta tana karatun Alkur'an.
Kallon ta yake yanda take karatu a natse yace *KANWATA* inkinkai Aya ki dakatar ga mijin ki yashigo...
Samad da suke bakin kofar shida à bokan sa kallon ta suke hartakai Aya..
Rahama tace la la Yaya ABU ashe dai zamu hadu daman ina takaicin tafiya ban ganka ba.
Abubakar cikin Jin dadi yakama hannun ta cikin nashi yana matsama tareda dafata suna Face din juna.

SAMAD RANKA IN YAYI DUBU YABACI YASAN YAYAN TANE UWA DAYA UBA DAYA..
Faruk ya lura ransa yabaci murya à tausashe yace yaya ABU sauri mukeyi dan Allah..
Abubakar yace babu matsala.
KE RAHAMA TASHI KU TAFI KINJI KO..
Kallon Ànty take dake barcin Gajiya gashi Mama taje gida ta dawo..
Rike hannun Salma tayi tace my kanwaty mun tafi Allah yakara lafiya.
Nikaf dinta ta sanya tareda nufar hanyar fita.
Shiko Samad tuni suka bar dakin suna cikin Mota suna jiran ta.
Sai cika yake yana batsewa wannan yarinyar yar rainin hankali ce.

A rainin wayau ne tashanya mu 'mu yaran Tane tana cen tana murza hannun namiji.
Kallon takun ta tana tahowa yasa kallon sa yakoma akanta.
Karasowa tayi tareda bude murfin motar..
Ta shiga ta inda yake zaune.
Matsawa yayi Daga gefe yana bubbuga kafa Alamun zamu je gida zaki sani.
Faruk drever d'insu yayi har gidan nasu.
************************

England.

Adamsy ne yake Chattin da Asiya ta whsap.
Cikin tsananin damuwa yayiwa Asiya voice yace wallahi Asiya har gobe inason Rahama da Yarima ze sakar min ita danafi kowa farin ciki wallahi nakasa sukuni.
Asiya cike da nutsuwa tabashi Amsa tace babu abunda yafi karfin adua..
Ka yaki shaidan acikin zuciyar ka Rahama yanzu Matar wani ce kasa m'a ranka hakuri.
Zan baka adu'oi da zasu taimakeka...

Adu'oi dayawa tayi masa audio tareda tura masa.
Adamsy dake kwance saman gadon sa mai laushi yace Asiya naji bayananki InshAllah zan aiki dashi.
Asiya tace to yaushe zaka dawo ne munyi miss dinka.
Murmushi yayi yace ai garin babu dadi babu Rahama daman Saboda ita nashiga koyarwa a wannan makarantar t'aku
Uhmm Asiya tace kenan mu ba mutane bane.
Yi hakuri Asiya ai kodan son da kike ma Rahama zanzo
Wai ina bakar munafukar kanwar Rahma take.
Asiya tace indakwai sunan da yafi wannan kana iya kiranta dashi Algunguma aitayi aure a ranar n'a tsani me bakar zuciya ace yayar ki uwa daya uba daya.
Uhmm in'nice Rahma nida ita har Abada wlh saide ita Rahama zuciyar yafiya gareta yanzu za'a mata abu anjima zata ce ta yafe.
Adamsy yace dabi'un ta da hankalin ta suna Daga cikin abunda yajawo hankalina akanta Ko banza nasan yaya n'a zasu samu tarbiyya.
Asiya tace haka ne wlh tamasu raino Daga uba nagari uwar dakin ta mutumiyar Arziki da tawakali.
Ahakadai suka cigaba da hira itada Adamsy sun shagala sossai..

**************************

Yarima Samad a gajiye suka karaso falon nasu.
Faruk ya fada kan 3tsr yace Wash munsha yawo kuma babu nasara.
Aminu yace wlh babu nasara fa amma wataran zamuyi nasara.

Yarima Samad kallon su yake yana kwabe baki yace kudai anyi ragwaye wlh jibi yanda kuka baje kan kujera yakarashe zancen yana hawa kan matakalan step.
Tuni Rahama ta shige dakin nasa.
Sauri sauri take tacire kayan jikin ta.
Turo kofar da akayi ne yasa cikin hanzari tamaida hijabin ta ajikin ta.
Zama tayi akasa tana latsa wayar ta.
Da sallama bakin sa yakaraso falon kallon ta yake yanda ta na de kafafun cikin hijab.
Wuce ta yayi yafara rage kayan jikin sa.
Haka kawai yaji kamar tana kallon sa.
Ya waiga yaga hankalin ta nakan waya.
Uhmm yace wannan Yarinyar zan gyara mata zama mu tasa Yawon da bamu shirya ba.
Gyaran murya yayi wanda yajawo hankalin ta akan sa.
Ke taso ki je ki hadamun ruwan wanka gaki kin fito babban gida.
Amma Sam bakida wayau.
Kallon shi take shima itake yake kallo yanajin bugawar zuciyar sa yana tsananta duk sanda yayi tozali da ita.
Ko karya nayi miki ne ?
Banda son a taba ki babu abunda ke burgeki.
Hararan ta yake tana tsaki.

Tashi tayi Daga zaune tana ciza labbansa ta suka bushe.
Azuciyar ta sai fadi take uhmm shi kullum laifi ake masa babu rana ta banza da baze ce ga wani abu ba.

Kai tsaye toilette din ta fada tana kokarin hada masa ruwan wanka.
Taji taku a bayan ta.
Bata kawo komai aranta ba taci gaba da hada ruwan.
Dagowar da zatai taga abu gabanta tsaye cikin bakaken kaya.
Idanun sa kwala kwala kamar kwai.
Soma ja da baya tayi yana kusanto ta.
Ta kai karshen....

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah.

Zakuga ina typin be tsawo sossai ciwon idanu nake in ina kallon screen din wayar ji nake kamar zasu fado
3/21/22, 07:43 - Nuriyyat: KANWATA

Akwai channel dîna KYAUTA TV kushiga ku danna mun.

Subcribe

Comment

Share

Like

Littafin kaikajawa kanka audio yana kan channel dîna saina jiku.

Littafin nan kudi ne Inkin ganshi a wajen group dîna na sata.
Inkin bukata ga nomba.
09069080725.

4️⃣4️⃣

Ta kai karshen bangon dakin tafara adu'oi tana tofa masa tana adu'oi cikin aro jarumta tace me kake nema dani ne ?
Nufosa tayi tacire tsoro nan da nan yafara ja da baya batt ya bace Daga bandakin.

Ganin yabace be sa ta daina aduar da ke bakin ta ba ta nayi cikin Daga murya.
Yarima Samad mamaki ne yacika shi Jin muryan ta ita kadai a bandakin.
Daga shi sai dan gajeran wando jikin sa cikin hanzarin sa ya shiga bandakin ganin gabadaya hankalin ta baya kansa adu'oi take ta zubawa tana magana tace yakai mummunar halittar nan dawo nan bangama dakai ba yaka gudu.
Sai gashi ya bayyana gaban yanata susa jikin sa na masa kaikayi.
Murya cen sama take jiyo wani murya mai amo hakan yasa ta Daga kanta sama.

Keee Rahama wlh inkika cutar da dan aikena namiki Alkawarin nadama a rayuwar ki.
Samad dake tsaye yana kallon ikon Allah rike take da kugun ta Idanun ta sun kada sunyi jajir 'bejin komai sai tashin muryan ta.
Jin muryan ta yayi tana Wani buga uban kara hade da dariya tace bakuda abunda zakuyi maganina Ko mu gwada yanzu ne suratul bakara tafara karantowa da karfin ta wannan Aljanin dake gaban barin wajen yayi' '' Shiko me magana Daga Sama yana ihu fadi yake Rahama ki dakata Ko kin hanani wucewa hanyar dazanbi nawuce wuta nake gani.
Rahama bako ta saurare shi ba cigaba da karatun take tana kara sautin muryan nata.
Wani irin kara yayi Daga cen Sama yace Inkina yiwa darajar Manzon Allah SAW ki bar karatun nan wlh natuba najanye kalamai n'a.
Tsaigaita karatun tayi cikin fushi tace gayamin me nayi muku kuke neman takura mun.
Dagacen bangaren yace wallahi turomu akai.
Rahama cikin zafin rai da batasan tanadashi ba tace zaka gayamin gaskiya Ko sai nayi kasa kasa dakai.
Wani huci Sama Sama yake yi yana nishi yace anturomu ne Daga baban Maryam.
Yana fadin haka yabar wajen cikin tsananin wahala.
Nanata kalamin nasa takeyi tace baban Maryam kuma.
TA MANCE À BANDA KI TAKE.

JIN MURYAN ABDUL SAMAD YANA FADIN KE LFY KIKE..tareda tsareta da idanu cikin damuwa.
Ajiyar zuciya tafara suke wa tana kallon sa.
Kamo hannun ta yayi sukaje daki tareda zaunar da ita bakin gado yace Rahama wai meke damun ki gayamin.
Kallon shi take tace anya gidan nan bana Aljanu bane.
Kallon ta yake yace kamar ya fa gidan Aljanu.
Uhmm abubuwa ban tsoro nagani harda cemin wai baban Maryam yaturo su.
Abdul Samad cikin tsananin tashin hankali yashiga Jin zancen nata..
Ya Salam ya furta cikin Jin tausayin ta yakama hannayen ta yace Rahama ba gidan Aljanu bane.
Shaidanun mutane ne da shaidanun Aljanu sune suke takura mana.
Tunani yake cikin zuciyar shi yace karfa Yarinyar mutane tasamu matsala Saboda ni.
A'a Rahama bazan bari acutar mun dake ba.
Maganar zuci yake yana kallon yanda take ta ajiyar zuciya.
Besan sanda ya jawo ta ya rungume ba.
Itako kasa fita Daga jikin nasa tayi dan wani dumi taji yana ratsata kamshin jikin sa take shaka hade da lumshe Idanun ta.
Tana tunanin to wannan abun shi menene shi taya akai suka shigo rayuwar ta, tunani take tasan duk a d'angin nata babu baban Maryam.
Kara shigewa jikin sa tayi wanda hakan ya sakar masa da kasala.
Cikin dauriya yace bara inje inyi wankar Ko ?
Sam t'ama mance shi ta runguma harda make kafada zatai kukan shagwaba.
Kallon bakin nata yake nan take Yaji wani yarrr.
Ajikin sa.
Chapter 39 · 0% Book details