← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 115

Sashe 76

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Labarin abunda yafaru yaje kunnen Mamy dan kuskus akaitayi acikin masarautar..
Cikin tashin hankalin daya bayyana a fuskar mamy '' barin dakin ta tayi tareda fitowa nan falo '' ta iske Ahmad zaune yana kallon vidéo a tiktok sai washe baki yake musamman wata big baby da taketa tikan rawa cikin wakar turanci tana sanye cikin riga da mini siket ga karin gashi cike akan ta '' tazubo shi '' 'ko' 'ina sassan jikin ta motsawa yake..
Cibiyar ta yatsurawa idanu' '' yana Murmushi ''

Sam hankalin sa yayi nisa besan da fitowar Mamy ba...
Sai ji yayi ta wabce wayar Daga hannun sa''cikin fada tace baba n'a yaushe ka zama hkne kai bazaka bar rayuwar yahudu da nasara ba da rayuwar Arna ba' 'meye ribar wannan vidéo da kake kallon' 'cikin Daga murya take fada sossai Ahmad ya tsorace yau Mamy da kanta take hawar shi da fada haka.
Cilla masa wayar sa tayi akan kafar sa..
Tace maza kashe wayar nan biyoni kaji abunda Yafaru da Karima baiwar Samad..

Cikin tsananin Mamaki yace Ah Ah meya same ta cikin gigita yake magana dan Sam baya Jin ze iya yafewa wanda ya taba Karima..
Tashi yayi yakama hannun mamy cikin damuwa yace Muje Ko Mamy..

Yayi daidai da fitowar Hassana Daga kitchen Ahmad n'a ganin ta yadaure fuska cike da takaicin Mamy n'a wajen yace mata ina kwana..

Lafiya lau tabashi amsa.
Kallon Mamy take tace naji kuna maganar Karima Allah yasa lafiya Ko...
Nan Mamy tashiga bata labarin abunda yafaru '' '.
Ahmad bejira yaji karshen labarin ba..
Cikin zafin nama da saurin sa kai tsaye dakin iya firdausi ya tafi...

Hassana cikin tausayawa Karima tace gaskiya ba'a kyauta mata ba..
Cikin yin kasa da murya tace yawwa mamy yau nakeson inje babban kasuwar kwatano Tokpa zanje indan yi siyayya kinsan gobe tafiya ta..

Mamy cikin rashin son Rabuwa da hassana dan sun Saba tace haba hassana yanzu baki Daga tafiyar ba...
Hassana Murmushi ta sakar mata tace Mamy tunda nazo banga mijin naki ba '' daman ya rasu ne '' ko baya zama garine...

Mamy cikin tsananin mamaki take juya kalaman hassana Girgiza kai '' tayi tace Ah Ah be mutu ba..
Idanu ta tsurawa hassana tace nayarda dake zanbaki labarina '' amma da sharadi...

Hassana cikin Jin dadin saukin kan Mamy tace meye sharadin InshAllah zan yi...
Mamy gyara Tsayuwar tayi tana fuskantar Hassana tace saikin gayamin abunda yakawo ki '' masarautar mu''

Kina gayamin gaskiya nima zakiji gaskiya abunda kika tambaya...

Hassana sossai tayi mamakin Jin furucin Mamy..
Cikin tsananin kaduwa tace kibari Muje mu duba Karima' 'mu dawo Ko..

Ahmad koda ya isa dakin iya Firdausi iske Karima yayi tana barci ga bandeji fari duk an nannade mata kai...
Hannun ta dauke da kalula ana mata karin ruwa..
Iya firdausi cikin kasa da murya tace Ah Yarima Ahmad kaine..

Eh nine yabata Amsa atakaice ina zuwa kawai ya furta '' be tsaya bata lokaci ba kai tsaye yayi Sashin Fulani cikin azzama..
Yayi daidai da fitowar Mamy da hassana cike da mamaki suke kallon inda Ahmad din yashiga...

Mamy cikin gigita tace Yaron nan yanda yake tafiya ba lafiya bane '' mu take masa baya....

Ahmad da kafafun ya bankada kofar Fulani ya bude '' maida kofar yayi yarufe tareda danna mata key...
Fulani zaune take tana yagan cinyan kaza...
Bata Ankara ba '' sai ji tayi anbuga mata uban naushi abaki '' kashin kazar...........

Muje zuwa.

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:52 - Nuriyyat: 7️⃣5️⃣

09069080725

Kashin kazar dake hannun ta faduwa yayi kasan carfet '' cikin gigita ta dago kai take kallon Ahmad dake shirin kai mata wani dukan '' kaucewa tayi cikin neman hanyar guduwa tace Ahmad haukar naka ya tashi ne daman baka samu lafiya ba..
Wani wawan rikon da yayi mata yasa cikin zazzare idanu tace Ahmad ka mance Koni wacece nifa matar kanin uban ka ce...
Me nayi maka ne '' da har zaka saka hannun à jikina takarashe zancen cikin kukan da yazo mata...

Ahmad dake huci sama sama cikin dagawa yace uban me Karima tayi miki kika sabanta mata rayuwa zan babbalaki nima duk hukunci da za'a dauka akaina adauka n'a yarda zanjure '' cigaba da bugun Fulani yake ta '' ta Ko ina sai ihu take tana neman ceto..

Mamy da Hassana suna ta bubbuga kofar cikin ihu take magana tana fadin Ahmad kabude kofar n'an bakajina ne..
Ina bemasan tanayiba '' ihun Fulani ya karade dukan Masarautar.

Labari yaje kunnen Mai Martaba da Abban Marwan ga Ahmad n'an yanata bugun Fulani '' bugun bana wasa ba.....
Hakan yasa Sarki ya tura waziri yaje à balla kofar koda suka je kokarin su n'a balla kofar '' Mamy tace karku balla kamar ya tsaigaita da bugun nata '' 'cikin ihu tace babana dan Allah bude kofar nan' 'cikin tashin hankali take magana dan sossai Ranta yake abace...

Daga cikin dakin yana Jin muryan Mamy yakara damkar Fulani tareda kai mata naushi a bakin ta nan da nan bakin yaringa tsiyaya da jini..

Razannannen kara ta saki' 'kuka mai cike da tsoro Idanun ta sun canza launi zuwa ja' '' hannun tasa ta taba bakin nata taga jini yabi hannun ta cike da rudewa take kallon Jinin tana kallon Ahmad dake tsaye yana kallon ta '' hannun yayi mata alamu cikin Daga Murya yace Inkika kuskura kikayi tari anan wajen saina taka ki..

Hannayen tasa ta toshe bakin nata tana zazzare idanu..
Jin karar buga kofar yaki karewa yasa ya nufi inda kofar yake..
Cikin hanzarin sa ya bude kofar caraf Idanun sa ya tsarke cikin juna shida Mamy cikin bacin rai Mamy ta Daga hannun zata mare shi..
Hassana tarike mata hannun cikin magiya tace dan Allah karki mare shi Mamy ''
Waziri da bayi da hadimai da kuyangu harda Abban Marwan cikin hanzarin su suka Shiga dakin...

Ita Ko Mamy kallon Ahmad take cikin tsawa tace dan rainin hankali kashige ciki kajira ni ina zuwa make kafada yayi Alamun oho Ko ajikin sa '' tunda yayi abunda ran sa yake so beki duk wani hukunci da za'ai masa ba....

Ahmad nawuce wa '' 'Mamy taja hannun Hassana sukayi cikin dakin Fulani koda suka Shiga iske fulani sukayi ana ta jero mata Sannu..
Abban Marwan rike da roban ruwan dumi yana gasa mata bakin nata...
Sai Wash take fadi tana ciza labban ta..

Cikin kidima Mamy ke kallon yanda Fulani takoma cike da rudani ta karaso gaban Fulani cikin muryan ban hakuri tace dan Allah Mama Fulani kiyi hakuri '' wallahi tallahi bansan ya akayi yaron nan Bejin magana ta ba...

Harara Fulani take watsawa Mamy cikin dauriya tace uhmm daman kin turo shi ne ya karasa ni ko''' bayan kinsa dan naki yanada mental problèm ba daidai yake ba..
Abban Marwan dake cikin Jin haushin Mamy cikin Daga Murya yace kinzo kiga Ko mata ta bata karasa bane Ko..
To wlh kujira kiga abunda zebiyo baya inban da rashin hankali Mata ta ze buga '' yaro mara Tarbiyya irin uban sa...
Ran Mamy yakai kololuwa wajen baci tace uhmm Ai mijina shi kuwa keda Tarbiyya kasan ance Albasa batayi halin ruwa ba..
Ahmad danka ne duk zagin da zakayi masa akan ku ze koma amma InshAllah shi Allah ze wanke sa''bana goyon bayan sa dan kowa bewuce kuskure ba...

Takarashe zancen tareda kama hannun hassana dake shirin magana ta katse ta ta hanyar Jan ta suka fice...

Waziri cikin tsananin mamaki yace Ah Ah Fulani kinga ikon Allah ashe haka Yarima Ahmad yayi miki mugun ta'asa...
Barin su yayi dan zuwa sanarwa Sarki yanda àbun ya kasance....

Sarki n'a zaune cikin jama'ar sa yana sauraron dawowar Waziri...
Isowar Waziri yasa Fadawa suka bashi hanya ya iso gaban Sarki cike da za kuwa yaringa bashi labarin yanda sukaga Fulani...
Salati Sarki yayi cikin tsananin damuwa yace Amma dai Ahmad wuyan sa ya isa yanka tome dalilin daya sa ya mata wannan dibar haukan...

Gangami ya nemi ayi masa iso '' 'babu bata lokaci Sarki yace ashigo dashi....
Cike da girmamawa ya shiga jerowa Sarki kirari..
Allah yataimaki Sarki Yarima Samad yabada umarni ahukunta Karfin iko' 'kuma harna aiwatar Saboda sanin dokokin masarautar nan..
Bisa laifin dukan Karima da yayi cikin umarnin Fulani akan ta hana ta makullan sashin Yarima' 'shine Marwan yace ahukunta Karima yana kai karshen labarin.
Gabadaya wajen suka dau Salati..

Sarki cikin gyaran murya yace da dai ba Karima bace wata baiwar ce zan iya magana' '' iya firdausi da Karima '' yarima ne ya Fanshe su Daga masarautar zaria Nigeria dan haka banda ikon shiga wannan zancen...
Duk abunda Ahmad yayi wa Fulani abu daya zan iya shine in hana shi kada ya sake amma adokar masarautar nan babu hukunci akan wanda yadauki hukunci akan antaba baiwar sa.....

Iya Firdausi itama baiwar Yarima Samad ce bansan yanda àbun ya juye takoma sashin Fulani ba....
Gangami yace Allah yataimaki Sarki zankoma daman dukan zancen kenan daya kawoni Daga haka yafi ce...

.........................................

Yarima Samad '' cikin murnan Nasaran daya samu a kotu kan wannan matar da Aka d'Annewa hakkin ta...
Takardun ta da komai ya mika mata..

Cikin kuka mai tsuma zuciya tace Yarima nagode Allah yasaka maka da Alkhairi yanda ka taimakeni InshAllah zan taimaka maka...
Cike da mamaki Faruk da Aminu suke kallon ta...
.
Yarima yace bangane zaki taimaka mun ba..
Hajiya zulai '' cikin d'Anne kukan dayazo mata '' tace ina masaniya akan wannan baiwar da kake nema shekara da shekaru d'ana...

Cikin zazzare idanu Yarima ke kallon ta cike da nazartan kalaman ta yace wace baiwar kenan kike magana akan ta..
Hajiya zulai cikin yarda da kan ta tace Saratu mana baiwar Mahaifiyar ka habiba ''...

Yarima Samad cikin hada rai yace kinsan inda Saratu take kika kasa gayamin '' to ya akayi ma kikasan ina neman ta
ina da ayar tambaya akan ki....
Faruk da Aminu dake tsaye wajen suna sauraron su''sukace kwarai kuwa zancen ka haka yake Yarima....

Zatayi magana wayar Yarima tasoma ring' 'yana duba wayar yaga Mamy ce hakanan yaji faduwar gaba cikin dauriya ya Daga wayar ta...

Dagacen bangaren tace inafatan kagama abunda kake inason ganin ka yanzu gidan nan bata jira cewar shi ba ta katse wayar...
Chapter 76 · 0% Book details