← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 115

Sashe 49

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Mamy wannan matar fa na hadu da ita a zongo rannan dan taji ance Daga gidan sarauta nake shine fa ta biyo ni har da cemin in kai ta gidan mu"

Mamy tsarkan dake wuyar ta gold ce Hatta agogon hannun ta na gold ne kallo daya nayi mata tsab nagane bawai taimako take nema akwai wata manufa akasa"

Sossai Mamy ta gamsu da bayanan sa.

Kara matsowa tayi kusa dashi tareda kama hannun sa cikin nata tana murzasu, kallon shi take tace maganar ka gaskiya ce wani lokacin tunanin ka sai yafi nawa zurfi.

Amma kuma matar nan bana tunanin tana da wani mugun nufi amma zan sa idanu sosai a kan ta kai kuma karage tsanar da kake nuna mata pls"

Ka ringa gaishe ta kaji my son?

Murmushi yayi wanda ya bayyana zallan kyawun sa yace "InshAllah Mamy zan kiyaye"

Tashi yayi yace "to ni dai zan fita"

Fatan Alkhairi Mamy tayi masa.

Tana kallon sa har ya bar dakin Girgiza kai ta ke yi tace "uhmm ko shi Samad ya zamantakewar sa da iyalin sa?

Daukar waya tayi ta kira Samad.

Cikin hanzari ya d'aga yana zaune kan kujerar office din sa a'lamun tarin aiki gaban sa.

Mamy tace d'ana ya kake ya gida.?

Lafiya lau ya Bata amsa still dai hannun sa dauke da biro wayar hans free ya sata tare da ajiye ta kan tebur yana rubuce rubucen sa.

Mamy tace "ina diyata Rahama?

Kalau take ya bata amsa.
Mamy cikin zakuwa tace Samad wai ME maman maryam tace maka ne?

Cikin raba hankalin sa gida biyu yace" Mamy cewa tayi inzo da Rahama dan su ganta"

Gaban Mamy yayi mugun faduwa tace "tokai amsar me kabata ne?

Samad ajiye biron hannun sa yayi tareda daukar wayar yacire hans free ya kara ta a kunne.

Yace nace mata zamu zo taré in har zan zo zaman kotu Inshaa Allah.

Nifa mamy na kusa komawa kwatanon da lokaci kadan yarage..

Mamy da gaban ta ya tsanan ta bugawa tace "bangane ka kusa dawowa ba?

Ajiyar zuciya ya sauke ya na mai shafa sajen shi da suka kwanta lub lub a fuskar sa ya ce "Mamy naga ai har yanzu Burina be cika ba dole zamu cigaba da adu'ar Allah ya bayyana shi"
.

Barin kanon baze tsaida kamfanin d'ana bude ba komai zecigaba InshAllah dan zan ringa zuwa duba abubuwa kuma inacen ma ina tafiyar da komai kar ki damu..

Ajiyar zuciya Mamy ta sauke tace Allah ya taimaka ya kuma kawo ku lafiya ka gaidamun Rahama"

Cikin Jin dadi yace" za taji mamy Daga haka sukai Sallama"

Sai karfe hudu suka baro kamfanin Samad.

Kai tsaye babban super market Aljazeera suka nufa,
Suna parking din motar nasu yayi dai-dai da wata bakar mota ta paka.

Wanda ke cikin motar ta cikin madubin motar take kallon Samad.

Samad kokarin shiga wannan Super market din yayi Idanun sa yayi masa tozali da wannan matar da take kokarin boye kan ta a cikin motar.

Mutuwar tsaye yayi ya kasa tafiya cikin zafin nama ya juyo.........

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:44 - Nuriyyat: KANWATA

09069080725

5️⃣2️⃣

Cikin zafin nama yajuyo zeyi wajen wannan bakar motar '' hango Yarima Samad yasa wannan dattijuwar fisgan motar ta aguje cikin sauri tabar wajen, aguje ya karaso amma ina har tana kokarin hawa titi.

Cikin ihu yake kiran Faruk da Aminu wanda tuni sun shige super market din..
Ba tare da yajira fitowar su yashiga motar à 360 ya fisgi motar ya take mata baya '' yana tuki cikin zakuwa daya cimma ta...

Wannan dattijuwar lura da yana bayan ta yasa ta canza hanya wacce bana gidan su ba '' kwana taringa bi dashi har tayi sa'ar bace masa da gani.

Su Faruk da Aminu aguje sukai waje 'ikon Allah Faruk ya furta yace" Yakira mu Ko ina yatafi ne?
Aminu zaro wayar sa Daga Aljihun rigar sa ya danna Yarima kira.

Samad da ransa yake b'ace ya daga cikin Kosawa yace ku jirani gani nan tafe tareda katse kiran...
Aminu rike da baki yace" Kaga nine nakira shi amma beban daman magana ba, amma yafadi nashi ya katse..
Faruk yace meyace maka ne? Yatsare shi da idanu...

Cewa yayi mu Jira sa yana yarfe hannayen sa cikin takaici..
Isowar Yarima yasa sukai gunsa tun kan yagama parking din motar.
Daga zaune cikin motar ne ya leko kansa waje cikin dan b'acin rai yace" Kungama ne kufito da kayan Muje.
Faruk yace" Inafa muka gama nagadai kaine kayi ihun kiran mu.
Dafa kai Samad yayi yace" Oh My god babu bata lokaci yafito cikin motar gaba yayi suka take masa baya har cikin super market din..

*************************

Salma kallon à gogo tayi bayan ta idar da sallah tana me kara bin gidan da kallo '' kowa ina tsaf yake cikin kwabe baki tace" Wai Anty Rahama kinada Y'ar aiki agidan nan ne?..

Kallon Rashin fahimta Rahama ta bita dashi tana kokarin kwashe kwanukan da suka ci Abinci..
Salma numfasawa tayi tace eh naga gidan nan yamiki girma sossai ya kike yi wajen aikin gidan nan ke kadai? Nasan bazaki iya ba ko kinada masu yi ne?..
Murmushi Rahama tayi tace" kanwaty ai ba wani aiki bane agidan nan me wahala.
Kwabe baki Salma tayi tana taunan chiugum karas karas a bakin ta.
Yayi dai-dai da shigowar Samad da su Aminu cikin dan sauri sauri Yake tafiya. '' Caraf Idanun sa ya tsarke d'ana Salma tsuke fuska yayi taré da barin wajen cikin dan hanzari.
Salma kallon shi take tana Ayyana to laifin me taimishi ya tsaneta..
Faruk da Aminu falon suka karaso cikin sakin Fuska suke kallon Rahama da Salma tareda yi musu sannu,
Suma sashin su suka nufa ba b'ata lokaci.
Salma dake kallon ikon Allah tace uhmm kedai Ànty Rahama kinada aiki babba Wallahi.
Rahama tace name kenan? Cikin son Jin abunda zata ce..

Ai dole ince haka gida duk katti ke kadai ce Mace a cikin su '' Sannan da dukan Alama Mijin nan naki dan bakin rai ne Wallahi, jibi tunda nazo yanda yake ta Jin haushina ....
Hadiye sauran maganar tayi Jin takun saukowa Daga kan matakalan step.
Gaban ta ya shiga dukan uku uku ganin Yarima azuciye yasauko kasa yana kokarin kaiwa Salma mari, Aminu yayi caraf ya kama hannun.
Hannun Yarima rawa rawa yake Saboda tsabar bakin cikin bekaiwa Salma mari ba.

Aminu cikin kasa da murya yace" Waime Yarinyar nan tayi maka ne haka?.
Cikin b'acin rai ya kalli Salma bakin sa na rawa yace suwaye Katti agidan nan?
Faruk shima zare idanu yayi yace katti kuma ? Yana kallon Yarima.
Samad yace" Wannan Yarinyar batada mutunci wai mune katti acikin gida...
Bakin Rahama na rawa tace" Yi hakuri badakai take ba wani firan muke.
Samad Beko bi takan Rahama ba dan ita kanta haushi take basa.
Direct kitchen yazarce.
Rike da kugun sa yana kallon yanda aka gyara wajen tsaf kamar ba'ai aiki cikin ta gaba.
Frij ya bude yadauko lemun champagne ,🥂 kwalba guda, ya karaso falon iske Salma yayi har ta fice Rahma zata bi ta dan rakiya, '' muryan shi taji yana Fadin Inkika kuskura kafarki tabar falon nan da sunan Rakiya uhmm sauran basai n'a fada ba..
Cak Rahama ta tsaya Idanun ta cike da kwalla tadawo itako Salma Jin furucin sa yasa tabar gidan cikin saurin ta..
Tana buga uban sauri wanda yaja hankalin mai gadi, kokarin bude mata gâté yake amma koda ta Iso bankade shi tayi yana kokarin faduwa.
Subhanallahi ya furta, wannan Mahaukaciya kuma Daga ina? Tsuke bakin sa yayi kada aji shi tareda zama kan kujerar sa yana Girgiza kai...

Salma tarar me napep tayi Unguwar Malam isa tayi masa Kwatance.
Babu bata lokaci akai Unguwar da ita, yana sauke ta ta sallame shi tareda fadawa kai tsaye Gidan malam isa.
Sa'a taci Malam isa yafito zeje Unguwa, yana Ganin Salma ya gane ta yace" Amarya bakwa laifi mu shiga Daga ciki..
Suna shiga dakin malam isa ya zauna itama zaman tayi dirshan Idanun ta cike da kwalla.
Kallon ta yake yace" Nasan mèke tafe dake.
Cikin mamaki tace" Ina ga ba muyi maganar damuwa ta dakai ba yanzu nashigo...
Malam isa bushewa da dariya yayi wanda saida dakin ya amsa yace" Tun jiya nasan da zuwan ki a yau
Kuma matsalar ki daya ne kinason mijin yayar ki.
Kinje gidan yaita miki wulakancin Ko ba haka bane?
Hakane ta furta cewa Salma..
Malam isa yabuga kasar dake gaban sa yace" Ke Salma wannan auren ba zamu iya raba shi ba kamar yanda muka raba wancen ba.
Cikin rashin fahimta Salma ke kallon shi ya za'ai kace bazamu iya ba malam?
Cikin kuka take magana tace" Malam bakasan radadin danakeji ba inna bude idanuna naga wai yaya ta ce take auren wannan balaraben sai inji kamar in kashe kaina malam..

Kallon ta yake yanda take zaro zancen yasan har cikin zuciyar ta take fiddo zance..
Salma yakira sunan ta atausashe !!

Na'am tabashi amsa tareda dago kai suna kallon juna.
Chapter 49 · 0% Book details