← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 115

Sashe 27

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kusan lasa'ar Anty sukayo ayari tareda yan uwan Mama da yan uwanta da kawayen su 'harda makwaftan su.
Abubakar taré dashi akazo Abdul jalil yabiyo shi sossai wayanda basu zo kawo Amarya ba suka saki baki suna kallon tsaruwar gidan.
Mamy daman tasan dazuwan su kyakyawan tarba sukai masu tareda mommy Adamu dan tazo ta taya su amsar baki.
Girki me Rai da lafiya Mamy t'asa akai musu cike da babban kula.
Abubakar yana shigowa bayan sun gaisa da surukan kanwar shi ya nemi ayi masa jagora har dakin Rahama.
Asiya takaishi Rahama n'a ganin sa aguje taje ta rungume shi tana murna tace yaya dan Allah ka ringa zuwa ina ganin ka kwana daya bakaji yanda naji ba.
Murmushi yake harda hawaye yace Rahama ta kenan wayagayamiki haka akeyi aini yayan ki ne koda kanin ki ne.
Bazeyu kullum aringa gani n'a à gidan ki ba hakan zubda mutunci ne kin gane Ko my kanwaty tareda shafa fuskar ta yana mejin son ta da kaunar ta 'ina kyakyawan mijin naki yake ya tambaya cike da kulawa.
Shiru tayi tace bansan inda yake ba tana turo baki cikin shagwaba' ' dariya yayi yace uhmm shagwaban nan dai tana nan ba'a daina ba.
Uhmm tace yaya wai ina Salma take tafada cike da kewa shiru yayi yana tunanin anya Rahama ba irin matan Aljanna bace kuwa yanzu ace duk wannan bakin cikin da ta shayar da ita à jiya amma yau tana tambayar ta.
Murmushi yayi a fili yace tana gida aikin San mijin nata saiya kama haya Ko ince dangin sa zasu kama mishi sai su tare ' ya sallam tafurta tace amma meze hana Abba yakama mashi daki su zauna nasan zaman kadaici ze dame t'a.
Abubakar kallon ta yake yanda duk ta damu yace kwantar da hankalin ki ai sun ma kama daki kaya kawai ake jira yafadi hakane dan tabar zancen Salma dan haryanzu cike da Jin haushin ta yake
Sun dade suna hira kafun yayi mata sallama ze tafi kuka tasoma tana fadin yanzu shikenan zaka tafi kabarni yaya n'a gayamin yaushe zaka dawo. Yace inaga saikin haihu Ko kuma kinzo gida.
Kalmar haihuwa daya furta take ta juyawa tace uhmm wai haihuwa sai dai a gidan marayu zan samo yaya in rena dan wlh ina sha'awar reno.
Tare suka sauko Daga kan matakalan step din ita da Abubakar sannu da zuwa tayima bakin ta da suka ba je suna cin abinci a falo kallon Ànty tayi da take waya tana fadin kalan labulayen da za'a kawo wa Rahama wuce su tayi tabi bayan Abubakar ta same shi jikin mota yana kokarin budewa 'kallon shi take Idanun ta cike da kwalla tace inka je ka gaida Abba da Mama zuwa t'ai ta rungumeshi tana kuka sai Rarrashin ta yake' yayi daidai da shigowar motar Yarima Samad tun Daga nesa yake hango Rahama rungume da wani da besan Ko waye ba.
Parking din motar yafito ta gefen idanu yake kallon su saida yazo daidai su yayiwa Abubakar hannun sukai musabaha cike da Jin dadi Abubakar yace kanina dan Allah ga kanwata Amana.
Yarima Samad cikin Jin haushin su yace bakada matsala yanzu kazo ne ya tambaya.
Abubakar yace eh bandade ba kuma yanzu zan tafi.
Abdul Samad yace dan Allah ka gaidamin surukina sheik imam
Yana kokarin shiga Daga cikin gidan kai tsaye yashige gidan yana tunanin hukuncin dazeyiwa Rahama akan rungumar Abubakar da tayi yarinya babu kamun kai kana magana tana kada kai kaman kadangariya mtssss yaja tsakiii kasa karasawa falon yayi ganin baki cike duk sunyiwa falon kaca_kaca da abinci kokarin barin falon yake ànty ta hango shi kuma ta tabbata shine mijin Rahama dan yanda aka suffan ta ma ta shi.
Ànty tace haba Surikina ya ka tsaya bakin kofa ne
Shigo mana duk nan iyayen ka ne fa 'cikin sanyin jiki yakaraso yana kallon yanda suka maida masa gida kamar gidan dambe à ladabce ya gaishe su' Mamy data fito Daga dakin ta tace kaga wannan itace uwar rikon Rahama Ma'ana matar baban ta tana me nuna masa Ànty cike da girmamawa yasake gaishe ta yana kokarin barin falon.
Sai bayan isha'i suka tattara zasu tafi 'Abdul jalil be gaji da ganin Rahama ba dan tunda suka zo yana manne da ita a daki dakyar ànty ta tsawata masa akan yazo sutafi aizekara dawowa Asiya ta tattara inata inata tana kuka Rahama n'a kuka tace shikenan Asiya zaki tafi kibarni kaicona daman haka aure yakesa zukata kuka dan Allah karki tafi kuka suke sossai Aguje takama kafar Ànty dake kokarin shiga mota tana kuka iya ranta tace ànty kema tafiya zakiyi kibarni wayyo uwata shekara da shekaru ajikinki nake kwana ke ce fitila mai haska duhun dake cikin zuciyata shikenan Farin cikin n'a yakare ànty.
Cikin kuka ànty tace Rahama banso kika sani kuka ba tunjiya nake ta kokarin daurewa nakasa inaganin kamar yawuce a yau shine zaki kara sani kukan kiyi hakuri Abdul Samad shine rayuwan ki yanzu duk abunda ze je yadawo karki taba Daga murya akan nasa zakiyi nasara InshAllah takarasa zancen tana kokarin shiga mota..
Kuka take sossai har motar su yabar haraban gidan jiki asanyaye tadawo cikin gidan iske Mamy da mijin nata kadai ne a falo khadija da Ahmed duk sun tafi sun kwanta dan suma sun tara gajiya.
Falon tadawo ta nemi waje kasa ta zauna tana watsa da yatsun hannun kewar khadija take da bata kwanta ba data taya ta kwana gashi batasan dakin nasu ba '' bare taje ta taso ta.
Falon shiru banda karar message din WhatsApp babu abunda kakeji 'kallon shi Mamy take yanda ya karkata hankalin sa kan wayar hannun sa gaban sa ledan kaji ne da juice da Mamy ta sashi dole ya siyo su.
Mamy da barci yafara dibarta ta kalle shi tace ina kayan da ka amso Daga gidan Dr Abdullahi sunce lefe ne Ko' ' eh yabata amsa suna À mota mance su nayi yafada ba tareda ya dago kai ba.
Katashi kuje ku kwanta d'are yayi Ko kallon Rahama take da duk tsananin tsoro yakamata me Mamy take nufi daki daya zata kwana da wannan mutumin uhmm wayyo Allah anty ze zalinceni maganar zuci take dawo da ita cikin tunanin ta yayi yace tashi Muje Ko tareda yin gaba dakyar ta tashi dan ta lura Mamy kallon ta take cikin Jin kunya tabi bayan nashi ita Ko mamy daman jira take su tafi gaban Idanun ta dan tasan halin nashi shiyasa takara kwana dan tagyara masa zama.
Kashe wutar falon tayi tareda wuce wa dakin nata cikin kasala.

Abdul Samad tunda suka shiga dakin banda safa da marwa babu abunda yake yi kallon ta yake yanda ta rakube jikin bangon dakin
Tunanin maganar da Mamy tayi masa lokacin daze je siyo kaji.
Girgiza kai yayi cikin zuciyar sa yace ina Mamy n'a bazeyu ba saidai ki gafarceni Ko hadani kwana daki daya da ita bakaramin kokari nayi ba.
Barin wani tunani yayi tareda shiga toilette yayi wanka yashirya cikin kayan barci saida ya Haye gadon yakwanta yana kokarin rage hasken dakin yahango ta inda yabar ta nan tsaye.
Cikin bacin rai yace ga kaji nan Mamy t'asa in siyo miki karma kiyi tunanin wani abu kin wani tsaya kaman an kafaki awajen yafada cike da fada to dan Allah karki cinye ni danye wannan kallon haba yayi yawa mana.
Ita dai Rahama kallon sa take tana son ta koma dayan dakin data kwana jiya dan batasan inda zata kwananta anan ba.
Kokarin fita take har ta murda handle din kofar tana kokarin sa kai cikin zafin nama zata tona mai Asiri ya kamo hannayen ta masu taushi da tsansti wani yar yar haka yaji tsikar jikin sa na tashi sakin hannun ta yayi.
Yace ki wuce ciki nace Ko dauki bargo gashi cen ki shinfida a kasa ki kwanta ''
Yafada cikin fushi.
cikin hanzari da tsoron sa ta hau gadon tana kokarin dauko bargon hannun yakai.....

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah

NB.
Nasan dayawa basu San duk Ranar juma'a bana postin din littafin kanwata ba.

Sai mun hadu Ranar asabar acigaba da comment da sharhi
3/20/22, 22:34 - A'ish: KANWATA

Akwai channel dîna KYAUTA TV kushiga ku danna mun.

Subcribe

Comment

Share

Like

Littafin kaikajawa kanka audio yana kan channel dîna saina jiku.

Littafin nan kudi ne Inkin ganshi a wajen group dîna na sata.
Inkin bukata ga nomba.
09069080725

3️⃣3️⃣

''' kokarin dauko bargon take hannun ta yakai kan wayar sa dake dake Ring kan screen din wayar anrubuta Maryam '' maimaita sunan take cikin zuciyar ta 'shiko ganin ta tsaya ne yasa shi fadin me kike yi ne da bazaki sauko ba Daga kan gadon ba.
Daga dauko bargo yakarashe zancen yana mata kallon tuhuma.
Jin karar wayar ne yasa shi zuwa daukar wayar ganin Maryam ce me kiran ya so ya katse Ganin Rahama yasa ya Daga. ....
Daga cen bangaren ta rushe da kuka tace yanzu yaya Abdul Samad aure kayi ' me ye laifina dan n'ace inason ka dan Allah kaduba lamarina wlh inason ka''' soyake ya rufe ta da fada amma ganin Rahama yasa yace haba baby n'a meye ze dameki dan nayi auren Sadaka kedai kinsha kurumin ki aini naki ne har Abada karki damu kanki kinji Ko amma pls kibari gobe zamu yi waya gobe
Chapter 27 · 0% Book details