← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 115

Sashe 41

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kallon shi take cikin mamaki take kallon sa tace aida tazo da ka ganta ahmadu ya akai ne tana mai tsareshi da idanu.
Numfashi ya fesar yace kawai de nazo wucewa ta wajen dakin Mama fulani naji murya kamar nata.
Mama fulani kuma Mamy ta maimaita tace A'a badai Maman maryam ba to me ze kawo ta gidan nan bata shigo sashi n'a in banda abunka tafada cike da rudani.
Ahmad yace uhmm yana iya zama banji daidai ba '' Mamy wai yaushe Samad zezo da Amarya tasa ne.
Khadija tayi caraf ta karbi zancen tace wlh Haba Mamy ace yayi aure amma haryanzu baze dawo kasar shi ba yo me yakeyi àcen din tafada tana me turo baki gaba.
Mamy tace to iyayena kun gama mun fada rike kunnen ta tayi tace korafi be karbu ba.
N'aga dai duk kunada lambar wayar sa amma kun tasani agaba da magana inba tsoro ba kirashi mana kai Ahmad.
Dariya yayi saida kuncin sa ya lotsa yace Mamy kinsan zan iya gayamai kawai dai amsar daze bani shi nake tsoro.
Oho ni kuka raina kenan céwar Mamy tana kokarin tashi dan shiga kitchen.
Khadija tace Mamy wlh banson ki tashi inhar kina mun tausa...
Mamy Murmushi tayi tace uhmm yar auta ai tashi zaki yi mu shiga kitchen tare..
Ahmad yace Mamy Muje in tayaki mana tunda ita ta kasa tashi gaba yayi Mamy n'a dariya ita Ko sai zumbure zumbure takeyi.
.
Ahmad ne ke feran doya dan yau Mamy tace doya da miya zasuci da miyar kaza....
Yanka doyan har doyan yankewa yake hade da bawon.
Mamy dake juya naman ta akan wuta ta juyo tana kallon yanda Ahmad ke ta dawaniya da doya.
Rike da baki tace yau naga ikon Allah aka ake feran doya.
Da Yarima ne habawa tuni ànwuce wajen..
Khadija da yanzu t'a shigo kitchen din banda dariya babu abunda take '' dago kai yayi suka hada Idanu.
Tayi masa gwalo sossai ya ciza bakin sa yace dani kike tace eh din kai fa.
Aiko bin ta yayi aguje.
Mamy rike da baki tace yau n'aga shashanci kullum basa girma ne.

Shiko Ahmad har daki yaki bita tana kokarin shiga bandaki ya j'awo daman be wanke hannun sa ba aikuwa ya shafa mata kaikayi wani uban tsalle khadija ta doka aguje tafada bandaki tsutsa jikin ta tashiga yi..
Banda dariya babu abunda yake yi harda rike ciki yabar dakin.

Abunka da farar mace nan da nan fatar ta yayi jajir ruwa take ta sakar wa kanta tana ayyana aranta wlh saita rama...

************************

Drever Samad ne ke ta zarya à compound din gidan Karima yake jira.
Jin takun ta yasa yakoma da baya baya suka koma parking space..
Cikin kasa da murya tace Ali drever yaya kasamu wani labari akan su Abban Marwan kuwa.

Gaskiya bansamu ba yabata Amsa cikin yanayin damuwa amma sainake ganin kamar sun fi mu wayau fa.
Karima tace kamar ya..
Numfasawa yayi yace duk sanda zanbi bayan su wuri daya kullum suke zuwa su dawo.
Cikin yanayin damuwa Karima tace to amma inda suke tsayawa kasan inane.
Kada kai yayi Alamun A'a.
Karima tace nex time ka tafi dani akwai abunda zan duba.
OK karki damu yabata amsa cikin yin kasa da murya yace ke ga Marwan cen zuwa maza kibi ta baya..
Babu bata lokaci tabar wajen cikin hanzarin ta kallon ta yake Harta bace masa da gani.

Marwan ne yakaraso wajen yana kallon sa cikin tuhuma yace Ali me kake yi anan kai kadai.
Murmushin dole yayi yace au daman aikena Mamy tayi shine natsaya duba motar da zan fita dashi.
Wani kallo Sama sama yake jifan Ali dashi yana yatsine fuska.
Yace kai ai Mamy bakowa bace a gidan nan bace matar barawo..
Firgit ya yajuyo yana nanata kalaman sa.
Bangane Matar barawo ba yabashi amsa.

Marwan yace zaka gane ne inhar aka kore su Daga masarautar nan kujira kuga abunda zebiyo baya.
Wuce shi yayi yana huci.
Ali cikin tsananin damuwa yace zasu bar Masarautar to su koma ina kenan wa'iyazubillah..
Dole yasan abun yi.
Yafada tareda neman layin Samad be same shi ba...

🇬🇦 Gabon

Baba Salihu zaune shikadai adakin sa yana tunanin yanda ze gana da yarima Samad.
Wata zuciyar tace inkai haka aika tonawa kanka asiri kazauna dai matsayin da kake ciki shize fiye maka..
Karar wayar sa yadawo dashi cikin hayyacin sa.
Yana Daga wayar yayi sallama.
Dagacen bangaren yace ya shugaba gaskiya abubuwa suna tabarbarewa fa.
Cikin kaduwa yace banfahimta cikin tsoro da fargaba yake magana Dagacen bangaren yace gaskiyar magana dole ne.
Yarima Samad yakoma kwatano da zama.
Yawon da yakeyi dan neman ka ya isa haka.
Sannan akwai wani zanen hoton wata Yarinya daya zana suna yanayi da Rahama har yanzu ya kasa gane cewar wannan zanen itace matar dayake aure..
Idanun sa sun rufe ya shugaba N'A.
Baba Salihu cikin damuwa yace wai haryanzu Yarima n'a yana bibiyan wannan hoton mafarki nasan shine yahanashi aure.
Dagacen bangaren yace aibe hakura ba rannan matar shi muka bar asibiti muka shiga gari da wannan zanen hoton ka kadai ne beda shi shima dan Mamy tahana ne.
Baba salihu ya numfasa yace turomin hoton zanen ingani.
Sannan dole yakoma gida aikin sa na kano Ko babu shi komai ze tafi daidai InshAllah..
Daga haka sukai Salama..
Baba Salihu cikin yanayin damuwa yake tuno Mamy yace baiwar Allah na cutar dake shekara biyar.
Kuka yake sossai tareda durkushe a kasa.

************************

🇳🇬

Kano.

Salma sossai taji sauki har aka basu Sallama.
Bayan sun dawo gida akai ta shigowa gaishe ta da jiki harda iyayen Al'amin.
Shiko Al'amin Ko gezau bezo ba.
Sheik zaune kusa da Salma yace mata sannu ta gyada m'asa kai.
Kallon ta yake yace MashaAllah yanzu tunda kin dawo gida banda yawo kinsan aure n'a kanki..
Wayar sa ce tafara ring yana dubawa yaga nombar Rahama ne.
Cikin Jin dadi tace Abba ygida ya jikin Salma.
Amsa mata yayi taji sauki.
Shiru ne ya ratsa tsakanin su.
Sheik yace Rahama ta
Tace naam Abby.
Yana ga kinyi shiru gayamin mêke faruwa ne.
Salma Jin furucin Abba dadi taji tana tunanin Ko itama duka tasha gun mijin nata.

Jin sheik n'a salati yace Rahama garin yaya kika bari iska ke damun ki agidan auren ki.
Ke ce fa kikewa mata ruk'iya yau shine karamin abu ze gagareki maza ki farka in barci kike ki yaki da kanki.
Dagajin labarin nan shaidanun Aljanune...
Sossai Rahama ke Zufa tace Abby ka kara turomin wasu adu'oi masu karfi..
Abba yace yanzu kuwa aikina WhatsApp da layin nan tace eh inayi Abba..
Daga haka sukai Sallama.
Ran Salma inyayi dubu ya tashi tace chab ashe ma baduka tasha ba....
********

*************************

Yarima Samad Daga shi sai Rahama kadai ne agidan.
Kallon ta yake ta gefen idanu yanda taketa kai kawo a kitchen...
Uhmm taita yawo da katon hijabi acikin gida saikace matar mamaci.

Ita Ko Rahama à Nutse tagama girkin nata.
Ta gyara kitchen tsaf..
Abinci ta jera kan dinner table kamshin Abinci bakaramin tadawa Yarima Samad hankali yayi ba

Yana son yayi magana ya kasa.
Kallon ta yake da mamaki bayan zumbulelen hijab dake sharan kasa da tasa.
Har nikaf taje dakin nata ta dauko tasa tace azuciyar ta zakaga karyan,wulakanci dani kake zancen..
Kokarin daukan remote yake yi dan canza tasha yaga tadawo falon ta zauna banda bakin kwayar Idanun ta babu abunda yake gani.
Cikin kidima yace keee ina zaki je?
Kallon shi take tacikin nikaf din tace hanyar waje kaga nayi ?
Maida kallon ta akan TV tayi.
Sake da baki yace bayan katuwar hijab din nikaf kika sako.
Tace kwarai kuwa kaine ka koyamin in akwai namiji awaje in suturce jikina.
Kaman ce rannan adaki cemin kayi indai na yawo tsirara inda namiji adaki yo meye laifina takarashe zancen tareda maida kallon ta kan TV.
Tashi Daga zaune yayi yana cijje labban sa cikin tsawa yace ciremin hijabin nan tareda nufota ta gadan gadan cikin zafin....

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:43 - Nuriyyat: 4️⃣6️⃣

Gadan Gadan cikin zafin nama zafin nama yake kokarin cire mata hijab itakuwa gam tarike tana fadin please ka sake hijab din wuya wayyo ànty zecire mun wuya..
Jin karar knocking Daga waje yasa ya cika ta tareda komawa kan kujerar sa yace waye ne cikin bacin rai.
Aminu yace dan iska to mune harda kulle mu a waje.

Tashi yayi yana tafiya yana tsaki murda handle din kofar yayi ya bude kofar.
Faruk da Aminu kallon shi suke yanda yake ta cika yana batsewa shikadai.
Kusan atare suka shigo falon '' Faruk yace Madam ke ce anan kallo kike ne ya jefo mata tambaya yana kokarin hawa kan matakalan step shida Aminu.
Chapter 41 · 0% Book details