← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 115

Sashe 43

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yarima Samad wani unguwa sukaje rijiyar lemu daidai wani babban Massalacin yan Darika ya paka motar sa..
Faruk bude murfin motar yayi yana kallon yanayin unguwar.
Aminu shima fitowa yayi yace kaga la'asar takusa.
Kallon Samad sukai da Alamun jira yake su bude masa kofa.
Faruk y abude masa yace maza kafito inrufe motar.
Kasan yanzu za'a tada Sallah.
Samad yace to l'imam munji tareda yin gaba dan d'auro Alwala.
Ciki sauri sauri sukai Alwala suna shiga Massalacin aka tada Sallah.
Bayan sun idar ne suka dan zauna yin Azkarai..
Aminu duk yarigasu fitowa Daga Masallacin..
Suna fitowa suka same shi atsaye yana jiran su...
Samad kokarin bude murfin motar yake yaji sautin muryan mace Daga bayan sa.
Firgita yayi dan Jin muryan yayi Daga sama.
Nan da nan ya tsuke fuskar sa babu digon Mutunci ya fuskance ta..
Yace keee...
Wai meyasa ku yaran matan yanzu Sam bakuda kamun kai ne..
Kin tsaya mun a ka.
Fadawa zaki yi ajikina ne
Kallon banza yabita dashi tareda bude murfin motar yashiga.
Su Faruk da Mamaki suke kallon Yarinyar dan sunga batada makusa amma matar shi tafita kyau.
Kwabe baki sukai ganin yanda boss ke ta zuba ruwan masifa.

Wata matashiyar yarinya ce wacce ta dade tana kallon hoton Samad a labaran duniya kuma ta dade da fadawa kogin son sa har gidan su kallon zautaciyya ake mata fadi sukeyi duk arzikin uban ki bekai n'a yarima Samad ba.
Yan uwan ta da iyayen bata shawara sukai data hakura da shi dan ba Ganin shi zatai ba har Abada ba....
Hawaye sun cika Idanun ta dan ko tunda ya tsare ta da ruwan masifa bakin ta mutuwa yayi Daga tace Assalam alaikum shikenan cibi yazama kari..
Ganin har sun shige mota ne suna kokarin barin unguwar.
Tayi saurin tarar me napep tace dan Allah bi bayan bakar motar cen mercendez...
Tayi mai nuni da hannun ta.
Inna ce zan tsaya daukar mota ta zasu bace mun da gani tafada cike da damuwa akan fuskar ta.
cikin Jin tsoron kada tarasashi lokaci daya..
Me nepep juya akalar keken nasa yayi yabi bayan su.
Bama nisa sukai ba daidai gidan Alh umar mai salula sukai parking din motar tasu..
Cikin sauri Faruk yabude wa Samad kofa.
Kokarin dauko zanen Daga cikin motar yake Idanun sa yayi har ba da yarinyar tana kokarin fitowa Daga napep din..
😳😳

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
09069080725
3/21/22, 07:44 - Nuriyyat: 4️⃣7️⃣

Tana kokarin fitowa Daga napep din...

Tsaki yayi yana maganar zuci.

Dauko zanen yayi suka nufi jama'ar dake wajen bakin su dauke da sallama Farruk yace dan Allah tambaya nake.
Cikin su wani yace Allah yasa mun sani.
Dan Allah muna neman Alhaji Salihu Turaki.
Cikin mutanen da suka iske zaune yace gaskiya bana tunanin a wannan unguwar yake.
Yarinya da tabiyo karasowa tayi tana fuskantar Faruk tace wa kuke nema ?
Farruk yace ke yar unguwar nan ce ?.
Tace eh mana tana me kallon Samad daya juya mata baya yana magana da wasu.
Faruk yace Alhaji Salihu Turaki muke nema.
Yarinyar mai suna Samira tace ayya bansan wannan sunan à unguwar nan ba.
Amma sunan yamin kama da sunan wani Sarki à kwatano.
Muna gani a jaridu.
Faruk yace eh to bashi bane.
Zanen hoton ya nuna mata kota San me kama da wannan..
Samira tace eh tabbas nasan nataba ganin fuskar nan a rijiyar zaki.
Makarantar d'ana bari ne..
Sunan yarinyar nan na mance gaskiya.
Faruk yace dagaske kike dan Allah bamusan wasa fa.
Tace wlh dagaske nake maka yar uwar ku ce.
Cikin zumudi Faruk yasamu Yarima Samad da yaketa tambayar sunan mahaifin sa da zanen hannun sa.
Yace kai dan Sarki Albishirin ka yau burinka daya ze cika saura daya.
Da sauri Samad yabar wajen da yake yace musu ya gode.
Dawowa yayi wajen Faruk yace bani insha mana.
Faruk ya nuna Samira yace kaga wannan yarinyar tace tasan zanen nan à rijiyar zaki....
Samad kallon rashin yarda yake mata yana kallon zancen ta amatsayin karya ne dan tasamu suyi magana ne tayi hakan..
Kallon ta yake yana nazartan ta cikin yin kasa da murya yace kin tabbatar da kintaba ganin wannan zanen..
Eh nataba gani nasan ta munyi makaranta daya.
Aminu yace tana nan batayi aure bane Ko tayi ?

Samira tace gaskiya bansan wannan ba saide naje n'a bincika..
Numfashi Samad ya fesar yana kallon ta yace wlh inkikai wasa da hankalina zaki sani kalleni da kyau banson araina mun wayau.
Fuskar sa a murtuke.
Faruk yace haba Samad tunda tace ta santa ai bazatai karya ba...
Samira tagama lura yanzu duk abunda tace ze mata dan yana son yaga wacce yake nema da Jan ido.
Cikin Jan aji itama tace n'a tafi naga sai bin ku nake kuna dizgani gaban mutane.
Aminu ne yasha gabanta yace haba wane mu '' yanzu ki bamu nombar wayar ki.
Tareda mika masa wayar cikin Jin dadi ta karba tasa masa nombar wayar ta.
Samad be bar abunda yakawo su ba yacigaba da tambayar Salihu Turaki kowa saiyace besan shi ba.
Dawowa yayi wajen su Aminu ganin yarinyar ta tafi ajiyar zuciya yasauke.
Yace yww Faruk wancen yarinyar kaga tafiyar ta Ko ?
Dan kada ta sake biyo mu.
Farruk yace eh ta tafi amma n'a karbi nombar ta nabata nawa tunda tace tasan ta.
Make kafada Samad yayi yace oh wannan matsalar kuce wlh karka sakoni koda wasa karka nuna mata gidana wlh.
Maganar zanen hoton.
Inka shirya ta raka ka inta kaika kai kuma saika kaini inaga haka ze fi.
Aminu yace kwarai kuwa hakan yayi Yarima.
Maganar neman baban ka Samad Ko zamu canza kasa ce.
Samad kallon sa yake yace meyasa kace haka Aminu.
Numfashi ya fesar yace jikina yana bani yana rayé kuma baya cikin Nigeria.
Wahalar da kanmu à banza muke nifa à ganina.
Faruk yace gaskiya ne wlh àdai duba lamarin nan.
Kokuma musa rokon Allah akan a duk inda yake Allah ya bayyana shi.
Samad yace na fahimce ku hakan ma mafita ce babba.
Aminu gyara Tsayuwar sa yayi yace to me ze hana kasa matar ka Rahama taringa tashin d'are tana rokon ubangiji yayi gaggawa bayyana inda yake a tunanina.
Kuma surukin ka mahaifin ta babban malamin ne koshi mu nema yasa mu a adua mana duniya fa da fadi cewar Faruk taya zamu gansa cikin dumbu jama'a bayan bamu San inda yake ba..
Sossai Samad yayi Amanna da bayanan su.
Yace to muje kai tsaye gidan sheik imam basai ankoma gida ba..
Cikin gamsuwa da bayanan sa suka bude masa murfin motar baya..
Shiga yayi
Suma suka shige motar. suna Dagawa jama'ar wajen hannu Alamun godiya da kulawar da suka basu.

*************************

Al'amin tunda Salma tabar gidan sa saiyau yasamu yazo gidan nasu.
Sheik yayi masa fada sossai da waazi da illan cin Amanar iyaye hakuri yabashi yace yarufa masa Asiri kar jama'a gari suji.
Sheik yace uhmm Al'amin kenan kai kana tunanin bansan halin da kake ciki bane kasan Allah gafurum rahim ne ba'a shiga tsakanin bawa da mahallincin sa.
Zancen Salma ta koma bema t'aso ba.
Duk yanda Al'amin yayi sheik yace babu wannan zancen fur yakiya akarshe yace to kana iya zuwa kasamu Salma inta amince saiku koma inkuma taki saidai kabarta zuwa nan gaba.
Jiki babu kwari Al'amin ya shiga Daga ciki.
Dan ganawa da Salma.
Mama n'a ganin sa habawa tarufe sa da masifa dan iska shege la'ananne yanda ka cutar mun da yata InshAllah kaima zaka wulakanta.
Sossai Al'amin yaji haushin mugayen duar da take tamasa cikin rashin kunyar sa yace Mama karki sake zagina fa dan kina tunanin kinban jakar yar ki aini wallahi diyar kishiyar ki Rahama naso abani dan bata samu tarbiyya ba..
Ànty cikin sauri takaraso wajen tana kallon yanda Al'amin ke zazzaga wa Mama ruwan jaraba.
Ànty tace habawa Al'amin rashin kunyar ka haryakai ka zagi uwar matar ka.
Sunne kai yayi yace kiyi hakuri maman Rahama wlh matar n'an batada mutunci ne.
Kuka Mama ta saka iya karfin wiwi tace Abubakar kana ina ne.
Yau ga dan iskan surikin zamani.
Abdul jalil dake shigowa cikin gidan yace ai bayanan yafita lafiya kuwa ganin Al'amin yanda yake cika yana batsewa..
Mama tace wannan dan rainin wayon ne mana yazo waishi ze tafi da Salma.
Abdul jalil ya mikawa Al'amin hannu sukai musabaha kallon Al'amin yake yace kayi hakuri antina bazataba koma yanzu ba.
Salma ce tafito Daga dakin ta sanye take cikin doguwar hijab har kasa..
Karasowa wajen nasa tayi tana masa kallon tara saura kwata..
Bismillah tace masa sukai zauren gidan nasu.
Gyara Tsayuwarta tayi tana kallon sa Daga kasa har sama.
Tana karkada kafa.
Amma wlh kacika dan rainin wayau Al'amin harkai kana tunanin zankoma wannan kazamin gidan naka kurkuku wanda a agidan namu Ko me gadi yafishi mukami..
Wlh ka yanka mun takardan Saki wawa lusarin namiji.
Al'amin banda tsuma babu abunda jikin sa yakeyi yace nine lusarin lallai zan tabbatar miki da hakan.
Zancen saki kuma ai babu shi tsakanin mu dansai n'a wulakanta ki kamar yanda kika mun..
Murmushi yayi me kama da ciwo yace eh daman nasan ke jarabbabiya ce shine nazo indaukeki muje in rage zafi karuwar gida kawai..
Salma zata Daga hannu ta mare sa Abdul jalil ya rike mata hannu'.
Girgiza kai yakeyi yace antina kada kiyi haka komai lalacewar sa mijin ki ne iname baki hakuri ki shanye koma menene yayi miki.
Kallon sa yamaida kan Al'amin yace kaikuma kaine shugaban ta intayi kuskure ka gyara mata ta hanyar nasiha yakarashe zancen tareda fita Daga gidan yabarsu nan..
Kallon shi suke har ya bace musu da gani.
Salma tace ni zanshige wataran zamu hade ai.
Tana hararan sa tabar wajen sai wani yauki take yau gâta isassa.
Kallon takun tafiyar yake yace ai Salma ban dandani zumar ki ba har yanzu sonake ki shigo hannun n'a.
Zan canza miki gida fita Daga gidan yayi yana tunanin yanda wasan ze kaya tsakanin su..
Chapter 43 · 0% Book details