← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 115

Sashe 14

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa gidan saida suka zabura Jin yanda salma ke ihun neman taimako.
Sheik dorina yaketa zabga mata Ko ina ajikin ta.

Kuka take kaman ranta zefita tana fadin natuba wallahi bazan sake ba.
Wayyo Abba kirjina zafi.
Wuyana zan mutu !

Mama dasuketa buga kofar itada ànty amma ina Ko sauraren su beyi ba.

Hussain yace wlh kada fa zuciya ya debeshi yakasheta nasan yaya Abdulrazak akwai hakuri amma fa da ransa ya bace baya gudun abunda zebiyo baya.

Zainab matar hussain cikin damuwa tace maza kanemo wani abu aballa kofar nan.

Babu musu ya tafi sai gashi dake da gatari hannun sa kokarin buga kofar yake.

Sheik yace dakata zan bude yana bude dakin aguje suka shiga ciki.

Mamaki ne yakamasu ganin Sheik sharkaf kaman wanda aka watsawa ruwa zufa ne ke sassafo masa ta ko'ina ajikin sa.
salma nakwance kaman wata gawa takasa tashi sautin kukan da take rerawa ahankali yajawo hankalin su akan ta.

Mama cikin kuka tace Salma laifin me kikai masa da harya zabi yamiki mugun duka.
Zabura tayi taje gaban ta tana huci sama sama.

Na tabbata da Rahama ce Ko Abdul jalil baza taba musu wannan muguntar ba.

Karfa kamance salma jinin ka ce fa kai ne ubanta.

Tsawar da Sheik ya daka
Mata ba ita kadai duk dakin saida suka razana.

Cikin kunan rai yace wallahi nayi nadaman hada zuri'a dake Aisha Sam bakida hali bakida tarbiyya tsawon shekaru nawa nadauka ina hakuri dake wallahi badan umarnin mahaifina bane kada in sake ki duk rintsi duk wuya da bakikai wannan lokacin à gidana ba.
Saboda ke zanje makarfin nan duk yanda zanyi sainayi yaban daman sakin ki.

Sakaryan banza duk abunda salma takeyi da sa hannun ki.

Ni uba ne dole ne infita nema Ko harkokin gabana kune iyaye mata tarbiyya Daga hannun ku ake dauka shi uba hakkin sa ne yadaura iyalin sa kan kyakyawan turba kuma Allah yasani ina yi.

Kallon su hussain yayi Idanun sa sun kada goge hawayen dake kwaranya kan idanunsa yayi dawani kyalle yace ku duba Rahama dan Allah waze kushe halayenta Saboda tasamu riko hannun uwa tagari.

Kamar ni wallahi salma tayi kadan ta zubar min da mutuncina à idanun duniya wallahi.

Nan yashiga basu labarin abunda tayi salati duka dakin yadauka.

Cikin kuka Rahama tashigo tarike kafar Abba dan Allah kayafe mata.

Karka yanke mata hukunci cikin fushi Abba.
Hannun yasa yadaga Rahama Ta fada jikinsa tana kuka, bubbuga bayan ta yasoma yi.

Yace naji zancenki Rahama zanyi tunani akan abunda yadace.

Kallon hussain yayi yace inason karinga sa mun idanu akan shige da ficen yaran nan.

Hussain yace babu matsala zanyi adaiyi hakuri da ita yaya
zamani ne da muke ciki yanzu sai du'ai.

Mama cikin kuka tace shikenaan yau sheik ya gama cimun mutunci a idanun jama'a.

Har ni kake cewa zaka saka inka sake ni gayamin wa zan aura ai tun kuruciyata zakai haka bayan zu ba.

Kama Salma sukayi da taimakon Rahama suka kaita dakin nasu.

Kowa ya watse zuciyar sa babu dadi.

**************

Daddy Adamsy tareda mommyn sa suka Iso gidan.
Cike da damuwa kwance akan fuskarsu 'hango Adamsy kwance kan 3ster idanun sa a lumshe.

Cikin kuka momy ta rungume sa mamaki ne yakamashi ganin iyayen nasa agaban sa.

Daddy a jiyar zuciya yasauke yana kallon dan nasa Cike da tausayawa.

Wai Adamu wannan wace yarinya ce haka da har samun ta zemaka wahala gayamin wane ne ubanta.

Adamu mamakin ganin iyayen nasa zuwan bazatan da sukai masa.

Fahimtar abunda ke cikin ransa ne Abba yace abokin ka hamza shine ya sanar mana dan haka inajin ka yar wacece ?

Cikin yin kasa da kai yace diyar sheik Abdurrazak kabeer hizqeel makarfi ce.

What ?

Daddy ya furta yana zazzare idanu kallon mommy yake kin Ko gane wanda yake fade kuwa.

Girgiza kai mommy tace Alamun A'a amma kaman nasan sunan à duniyar social média.

Daddy cikin farin ciki yace wannan shaharraren malamin addinin nan da yasha gwagwarmaya da kafurai ta dalili sa dayawa sun tuba.

Kuma masani akan wayewar zamani indai har shine uban nata gaskiya Adamu kaikasan abunda kagani harka nace masa kabari Allah yakaimu gobe zaka kaini gidan nasu.

Adamsy duk da haka be gamsu zesamu rahama dan sarai yasan halin sheik kan Alkawari inya dauka baya canjawa.

Kallon su yakoma kan hamza dake sauko wa kan matakalan step.
Bakin sa dauke da murmushi yakaraso falon cike da ladabi ya gaisheda iyayen Adamsy fuska asake suka amsa masa.

********,****

Washe gari

Asuban fari sheik yaringa bin dakin kowa yana bubbuga kofa Alamun su tashi lokacin sallah yayi.

Rahama daman idanun ta biyu gyara zaman ta kan sallaya tayi tareda soma tashin salma dake barcin wahalan dukan da tasha hannun Abba.

Cike da so da kaunar salma tasata agabanta tana kallon yanda take barci ahankali kwance.

Har ta tashi zata je sakeyin sabon Alwala ta tsinkayo muryan salma cikin barci tana fadin wayyo ni fa baku isa ku rabani da Adamsy ba.

Shinake so.

Dawowa Rahama tayi ganin sai shure shure salma keyi à gadon tana gurnani.

Tashin ta tayi arazane ta farka tana mika kokarin komawa barcin take Rahama ta hana

Haba salma inzaki kwanta nace kiringa yin Alwala amma Sam bakiyi
Gashi saikiyita mugayen mafarkai kina gurnani.

Salma wani kallon banzai take jifan Rahama tsakii tayi tace banda munafunci ina ruwan ki da barcina..

Rahama kyaleta tayi tawuce dan gabatar da Alwala.

Bayan ta idar da sallah ne tazauna tanata azkar.

Kallon salma dake barcin t'a Ko sallah batayi ba.
Saida tabi kowani daki tayimusu barka da asuba tareda yin ayyukan da tasan aikinta ne.

Babu ganda Ko kiwuya takama aiki tagyara Ko ina na gidan tsaf tareda kunna turaren wuta har dakin Abba takai.

*****************

Yarima samad wanka yafito daure da towel iya kugun sa.

Cikin hanzari yakashe wutar dakin domin Al'adar sa ce inze sanya kaya saiya kashe wutar dakin.

Wani yadi mai masifan kyau yasaka royal bleue bakaramin kyau yayi da shigar ba takalmin sa harf cover yasanya tareda zuwa gaban mirrow mai kadan yadan murza à hannayen sa da fuskar sa..

Sauri sauri yake yi dan zeje bauchi kaiwa abokin sa ziyara tareda bincike akan Abban nasa.

Ahanzarce yasauko kasa ganin su Aminu da marwan 'faruk kowannen su à shirye yake.

Suna ganin yasauka faruk yace pls Yarima samad dan dakata mana saurin me kakeyi baka karya ba.

Kallon agogon hannun sa Yarima Samad yayi cikin marairaice fuska yace am sorry bari in mun isa cen bauchi naci.

Kada mu makara time fa yakusa tareda cigaba da tafiya suna take masa baya...

***********

Abba zaune yana koyar da karatun Alkur'ani agidan nasa.

Rahama 'da abubakar
Abdul jalil da hussain.
Salma kadaice bata zo ba.

Cikeda kwarewa yake karanto surorin Alkur'ani
Dukan su hannayen su dauke yake da Alkur'ani mai girma.

Time to time Rahama tanata kallon agogo.
Cikin yin kasa da murya cike da ladabi tace.

Abba karfe goma ne zamuje airport yin bukin jirgin Lagos.

Hakane fa yayinda sheik ya ce to maza tashi ki je.
Salma tarakaki.

Ungo wannan wayar tareda mika mata wayar salma daya kwace akwai layi ciki 'nasaka duk yanda ake ciki ki kirani.

Cikin gamsuwa ta tashi tareda zuwa jan salma suka tari me napep à daidai kofar gidan su.

Suna fita layin yayi daidai da shigowar motar Adamsy da iyayen sa..

Basufi Akallah minti shabiyar ba sai gasu airport.

Cikin sauri sauri Rahama ke tafiya kada time yawuce tasan ba zasu karba ba.

Yarima Samad à ujajan yake sauri dan kada su rasa jirgin safiya.

Daidai da wani karfe Rahama tasa kafafun ta.

Karfen makale hijab din Rahama yayi wanda ya jata da baya baya.

Tana tangal tangal zata fadi yayi daidai da zuwan Yarima samad à ujajan karo sukai Ta saki wani kara tareda fadawa jikin sa wanda hakan yasa shi faduwa dukan su à kasa.

Rahama n'a saman shi.

Marwan cikin shu'umin murmushi yadau wayar sa hoton su yadauka à haka.

Salma ciki....

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah

Karku manta Paid book ne

Free yakusa karewa
3/20/22, 22:34 - A'ish: *🌟🌟 KANWATA🌟🌟*

Paid book ne

300 vip

500 spécial

Àcct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ko kuma Katin MTN
Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

*Taurari biyu kuma Matasan marubuta masu tasowa Sunzo muku da dadadan wanda zai nishad'antar daku masoya wannan Matasan marubuta ba kowa bane illa: 𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼,,𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈(𝙠𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝 ) Sunzo muku da sabon novels masu suna.

*𝙈𝘼𝙈𝘼𝙉 𝙉𝙐𝙎𝘼𝙄𝘽𝘼* tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝘿𝘿𝘼𝙍𝘼 𝘾𝙀)

𝙄𝙆𝙄𝙇𝙄𝙈𝘼 𝘼𝘿𝘼𝙈( 𝙆𝙮𝙖𝙪𝙩𝙖 𝙙𝙖𝙜𝙖 𝘼𝙡𝙡𝙖𝙝) tazo muku da littafin (𝙆'𝘼𝙉𝙒𝘼𝙏𝘼)
Kai dajin sunan labarin ma kasan basai an tambaya ba.

*(K'ADDARA CE)*
*Dandano! Dandano!!*

Hanan meye lefin mu dan muna cikin garin Saudiya? Muma bayin kammu bane K'ADDARA CE ta kawo mu cikin Saudiya. Hanan mai muka yiwa mutane suke jifan mu da mummunan kalma?. Cikin masifa Iman Ta zaburo bata yi magana ba ta damk'i hannun Sultana Tace" Ke Sultana muje ki nuna a hanyar shara-mansoor d'in Uban waye ya fad'i miki wannan maganar yau saina wuk'ance shi fuuu suka bar Hanan anan tasaki baki...

*K'ANWATA*

*Dandano!Dandano!!*

Mama kina ganin Abun da Salma taimin? Kin kasa mata magama. Jijjiga Mama take yi tana kuka mai tsuma rai..Mama ta d'ago jajayen idanun ta da suka ciko da kwalla Tace Rahama kiyi Hak'uri kanwar kice... Sharr! sharr!! Idanun ta suke zubar da kwalla da radadi had'e da zallar bakin ciki,take kallon sama ta daga hannayen ta sama tare da fad'in. Ya Allah ya Allah ka gana ganin Abun da K'ANWATA taimun ya Allah ka..

Ga maru buk'atar wannan novels d'in zasu iya tuntub'ar wannan numbobin. 09069080725 our +966599791573

Nomal. guda d'aya N 300 ne

guda biyu N 500 ne

Special guda d'aya N 500 ne

guda biyu N 1000 ne

Zaki iya biyan kud'in ki ta wannan hanyar. 3115484026 Ikilima Adam first bank

2️⃣1️⃣___2️⃣2️⃣

Mamy tace inajin ki kinyi shiru tsareta da idanu tayi.

Maryam cikin kasalalliyar murya tace mamy yarima samad baya sona wlh.

Zazzare idanu khadija da mamy sukai sake da baki suna kallon ta.

Kamar ya baya sonki mamy ke tambayar ta.
Chapter 14 · 0% Book details