← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 115

Sashe 52

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rahama tace nidai ce banda lokaci Asiya ga karatu ga aikin gida '' be zama lallai inba whsap lokaci n'a ba.
Amma in ina free Tabbas zan hau ayi hira..
Asiya tace hakane kuma Allah yasamu adanshin ku.
Ameen tabata amsa cikin muryan dake nuna kasala tace Asiya ni zan kwanta Daga haka sukai Sallama.
Kokarin hayewa gado take taji ring din wayar ta hakan yasa ta saurin dubawa ganin nombar Sheik ne ke yawo kan screen din wayar..
Cikin hanzari ta Daga.
Bakin dauke da sallama.
Sheik cikin Jin dadin Jin muryan ta yace diya ta dafatan dai kina lafiya.
Lafiya lau tabashi amsa.
Abby nayi miss dinka inason inzo gida inkawo maku ziyara.
Murmushi yayi yace Rahama ta basai kinzo ba kisha zaman ki ni gobe ma tafiya zanyi nida Amini n'a..
Rahama tace Abby tafiya kuma ina zakaje tafada cikin yanayin damuwa.
Sheik yace walimar aure ne a kasar Gabon kedai kiyi muna adua dalilin kiran naki kenan..
Rahama numfashi ta fesar tace Allah ubangiji yakaiku lafiya yadawo daku lafiya..
Ameen summa Ameen suka amsa...
Daga haka sukaci gaba da hiran su yana kara mata haske kan abubuwan da suka shige mata duhu......

Kashe Gari.

Bayan ta idar da Sallah Asuba zaune takoma kan sallayar ta tana azkarai.
Alkur'an tadauko zata fara karatun ta taji karar buga kofa..
Hakan yasa ta ajiye akan dardumar ta tareda nufar kofar dakin à hankali ta murda handle din kofar.
Tareda budewa kallon shi take yana sanye cikin farar jallabiya da hula akan sa.
Tsintar murya tayi yana Fadin lokacin Sallah haryawuce n'a mance ban tashe ki ba.
Cikin sanyi murya tace ai nayi sallah.
Durkusawa kayi tayi cikin ladabi tace ina kwana ya karfin jiki..
Ciki ciki ya amsa mata da lafiya lau.
Kokarin rufe dakin take ya zuba mata zararan Idanun sa masu kashe garkuwan jikin yan mata..
Yace ina tsaye bakin kofar zaki rufe ?
Yi hakuri n'a zata zaka wuce ne kara bude kofar tayi tana nuna masa hanya ya shiga.
Shiga dakin yayi sai bin dakin da kallo yake har Idanun sa suka sauka kan wannan akwatunan lefen..
Kallon su yake yana ciza labban sa.
Cikin isa da izza yace wannan kayan kinfara Amfani dasu ne ?
Girgiza masa kai tayi Alamun A'a.
To karki kuskura kiyi Amfani da nasan kina jin dadin zaki saka kayan da wani kato yasiya to ni agida n'a ba'a wannan tsarin ina fatan kin fahimce ni.
Gyada masa kai tayi.
Yace wannan kayan zan adauke su Aba mabukata.
Su kuma gold din saida su zanyi inkai kudin gidan marayu.
Rau Rau take kallon sa a zuciyar sai fadi take to saime daman akwatunan basu dameni ba.
Kallon ta yake yace kina magana ne ?
Naga labban ki n'a motsawa...
Girgiza kai tayi Alamun A'a gaskiya ba abunda nace..
Good ya furta kindaiji abunda nace lefe dakaina zan hado miki kwanan nan ki shirya anjima Muje super market ki duba kayyayakin da kike so..
Daga nan Muje kasuwa insaimiki atamfofi da lace material.
Kinsan zamu tayi Ko.
Tafiya ta maimaita a fili.
Tana mai kallon sa..
Daga mata gira yayi Alamun hakane.
Shiru tayi tana tunanin to ina zasu je ne wai Allah batason barin garin su...
Dawo da ita cikin tunanin ta yayi ta hanyar fadi zamuje garin kwatano dake ki shirya nan da kwana uku masu zuwa..
Kallon réaction din yake yanda yaga zallan damuwa..
Cikin yin kasa da murya tace Allah yakaimu.
Ameen ya amsa mata cen ciki tareda baro dakin nata.
Itako Rahama tunani tashiga meyasa sai yau ze gayamata zasuyi tafiya ''
Tafiyar mai bata kusa ba oh Allah yazanyi rayuwa garin da ba nawa ba bantaba fita kasar nan ba.
Iyaka ta Lagos.
Yau gashi anzo mun da bakon Al'amari.
Daukar wayar ta tayi tareda kiran ànty ta sanar mata ànty nuna mata tayi bama tasan da zancen ba tace kwatano kuma zakije Rahma kiyi hakuri aure ne babu inda bekai ya mace amma InshAllah gobe da kaina zanzo karki wahalar da kanki kice zakizo gida nafison sai kin shekara Sannan kizo kinji Ko daughter.

Gyada kai tayi cikin gamsuwa da bayanan ànty sallama sukai.
Inda Ànty ta ajiye wayar Domin zuwa hadawa sheik break da dawuri zasu tashi...

Bayan kowa ya karya agidan sheik ya tara s'u yace to Allah yayi zan tafi dan Allah azauna lfy da juna.
Kallon Salma yayi yace ke banson yawo inbada izinin mijin ki ba.
Abubakar yace Abba kaide gayamata fa dan naga tafita wlh zan gyara ta saidai in mijin nata ne yabata damar fita yakarashe zancen yana mai daukar jakar sheik ze fice waje.
Mama tace amma dai Abubakar bakada kunya kenan ni ka daukeni uwar banza kenan kana nufin zanbar Salma tayi abunda taga dama ne kaine me hankali kaika iya magana Ko ?
Rike da baki Abubakar ke kallon uwar sa yace haba Mama wai ina ruwan ki da sha'anina da kannena ne naga dai bake kadai bace agidan n'an akwai ànty ita bataji zafi ba saike.

Mama tace taya za'ai taji zafi tasan zafin haihuwar ya mace ne akasa ta tsinta.
Sheik yaji haushin kalamin ta hakan yasa yafi ce Daga gidan.
Bin bayan shi Ànty da Abdul jalil sukai suka bar Mama da Salma.
Kofar gida sheik yace to sa'adatu mun tafi Allah ya kaddara saduwar mu
Adu'a ta fara masa cikin sanyi murya tace Allah yakaika lafiya yadawo dakai lfy yatsare ka.
Ameen suka amsa tashi yayin da drever ya bude masa mota ya shiga...
Abubakar da Abdul jalil shiga motar sukai suma.
Ànty n'a tsaye tana kallon su har motar yabar unguwar tana ta Daga musu hannu.
Komawa Daga cikin gidan tayi.
Nan inda tabar mama da Salma nan ta same su mama n'a ganin ta takara sautin muryan ta.
Tace ke Salma ki abunda ranki yake so tunda baya nan duk inda kike so ki je wlh banga uban da ze hana ba kuma wata munafukar taje ta gayamasa zata fuskanci hukunci Daga gareni.
Salma shewa tayi tana taba hannun ta tace yawwa mama shiyasa nake sonki.

Kada kai Ànty tayi tareda barin wajen cikin hanzarin ta...

Cen airport Aminin Sheik zaune yana jiran sa ganin karasowar yasa ya nufi inda su sheik suke.
Babu bata lokaci aka fara kiran suna hakan yasa sheik bin bayan Aminin sa cikin sauri.
Abdul jalil da Abubakar kallon su suke suna Daga musu hannu har suka shige jirgin....

Kasar Gabon.

Yau tun safe baba salihu yake ta faman hada kayan sa.
Ze bar kasar zuwa kasar Nigeria kano..

Duka wata daya zeyi yakoma Gabon..
Sai kiran su yake airport din suna kara jaddada masa jirgin kano besauka ba.
Data sauka za'a sanar masa yazauna cikin shiri..

*************************

Masarautar gheuzo.

Mai Martaba zaune cikin shigar sa na sarakuna gefen sa waziri ne.
A damar sa Abban Marwan ne zaune dirshan cikin muryan roko yace Allah ya taimaki Sarki ataimaka ayiwa Marwan aure yaga wacce yake so..
Mai Martaba kallon sa yake cikin dattako yace Marwan ne za'ai wa aure yaron da Ko aikin yi beda shi.
Abban Marwan yayi kasa da murya yace cikin tsoron mahaifin sa yace mai martaba aiyasamu aiki Samad compagny à kano taré suke aiki nan ze koma yaci gaba da aiki.
Mai martaba yace A'a yaje ya nemi aikin kansa yayi inda gaske ne meyasa Abdul Samad be fadamin ba.
Abban marwan yace kila ya Manta ne amma tabbas taré suke aikin dashi aka bude kamfanin.

Mai martaba yace naji zanyi magana da Samad inji kanun labarai.
Bakaramin haushi Abban Marwan yaji ba yafadi magana amma ace masa sai anbincika cikin dan bacin rai yace nina tafi mai martaba saina jika.
Daga haka yafi ce cikin Jin haushin su..

Mai martaba kallon waziri yayi yace inason afara tarawa gidan nan Saboda ayi shela domin sanarwa jama'ar masarautar nan gangarumin taron da za'a hada n'a tarban Matar Samad 'sashin da zata zauna ita da mijin nata agyara musu à canza furniture komi n'a dakin.
Sannan lefen da masarautar ta hada akwatuna 24 su zama ready.
Zamuyi taron bikin namu n'a musamman nan da sati biyu InshAllah kafun nan bangaren mamy zata zauna.
Waziri cikin bangirma yace ya shugaban Adalai InshAllah yanda kace haka za'ai.
Jakadiya ce tashigo cikin bangirma tace ya shugaba Mama karama tana neman ai mata iso wajen ka.
Allah ya taimakeka Sarki mai ran karfe.
Kallon ta yake.
Waziri yayi caraf yace Jakadiya sarki yabada dama à shigo da ita.
Cikin rawar jiki tabar fadan.
Kalllo bayi da kunyagu take kowa n'a hidimar gaban sa sanye suke da uniforme din masarautar.
Ganin Jakadiya yasa suka fara gaishe ta.
Tareda rusuna kai.
Hajiya Hassana cin karo sukai ita da Jakadiya.
Kallon kallo suka Shiga yiwa juna.
Hassana da Murmushi ta gaida jakadiya ta amsa mata cikin sakin fuska tana tambayar kan ta Ko wannan ce bakuwar da Akace masarauta tayi..
Jakadiya tace dan Allah Ko kece bakuwar gimbiya Mamy.
Murmushi tayi tace eh Nice, Sunana Hassana dafatan n'a sameku lafiya inason abokiyar hira a masarautar nan...
Jakadiya tace ai indai wannan ne kinsamu zan hadaki da baiwar Samad Karima..
Hassana cikin Jin dadi tace dan Allah hadani da karima.
Jakadiya ta kalli cikin kunyagu dake kai kawo cikin masarautar ta bada umarnin a rakata gun Karima tareda yin gaba dan isar wa Mama karama sakon mai martaba...

Kunyaga takai hassana har dakin Karima iske ta sukai zaune Alamun wani muhimmin abu take ganin su yasa ta zabura.
Tafara in n'a in n'a ciki yake tace ke Daga ina haka ai wannan bakuwar Mamy ce.
Hassana Murmushi tayi tace eh nina ce akawoni.
Chapter 52 · 0% Book details