← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 115

Sashe 108

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yarima kallon agogo yayi ganin lokaci n'a tafiya yace Rahama kizo mu tafi zanje tarban Saratu ne da za'a kaita airport...
Wa zaki samu daze zauna wajen nata....
Rahama cike da damuwa tace Amjad kawanta ce jinina ce....
Nafison inzauna da ita...
Dan Allah kabarni...
Hada rai yayi yace bazaki zauna ba..
Tare zamu bar Asibitin nan...
Kiran Abubakar yayi wanda yake cen yana kuka yace Dan Allah yaya Habu ka taimaka kazo Asibitin nan badan Halin ta ba dan Allah zakayi....
Dakyar Abubakar ya yarda yazo Asibiti koda ya Iso har ankaita dakin hutu..
Kannen Sheik hassan da hussaini ne suka rako sa Asibitin..

Suma kam cike da damuwa suke jinjina Al'amarin nan...

Yarima Samad barin Asibiti yayi da Rahama kai tsaye suka fara shirin barin kasar..

Ita Ko Salma tanacen kwance batasan inda kanta yake ba...

Hussaini da Hassan da Abubakar sai safa da marwa suke yi ganin shirun yayi yawa..
Fitowar babban docto ne yasa dukan su suka nufo sa....
Hussain yace likita dan Allah ku mana bayani ya zancen yarinyar da akayiwa cs....
Akasalance likitan ya kalle su yace ku biyoni office dîna....

Kai tsaye suka take masa baya....
Koda ya isa dakin zama yayi kan kujerar sa tareda sanya médicale glas yana yan rubuce rubuce akan file me dauke da Sunan Salma Abdurrazak....
Yana kai karshen rubutun nasa yayi sign à karshe tareda dankwala wannan penti bleu dake gaban sa akan pepper.
Bakajin komai sai ajiyar zuciyoyi..
Dago kai yayi yana kallon su yace Kune yan uwan Salma watau abunda yake Faruwa shine.
Wannan gubar data shaka yayi afectin din mahaifarta 'ya kone d'uk wasu kwayayan halittar ta... Dan binciken mu ya nuna bazata sake samun haihuwa ba..
Kuma cikin dake jikin ta' 'shima numfashin sa ya tsaya daman cikin dudu wata hudu zuwa biyar ne..
Munyi nasarar cire mata cikin Daga jikin...
Kuma Allah yataimake ta da matsalar ta tsaya iya nan da ace tasha guban ne babu abunda ze hana ta mutuwa....

Gabadaya dakin sai Zufa ke keto musu kamar wayanda suke cikin rana duk karfin Ac dake dakin....
Abubakar bakin sa na rawa yace docto babu abunda za'iya yimata ta haihu zuwa nan gaba....
Kada kai likita yayi yace Ko ina za'a je bazata haihu ba''amma kasan hikima ta ubangiji yana iya canza komai fatan d'ai Allah yabata lafiya....
Mika musu takardan yayi yace duk magunguna da za'a siya mata suna nan...
Yanzu tana dakin hutu..
Zuwa la'asar zata iya farfadowa....
Ruwan lipton da suga zaku tanadar mata..

Jiki Asanyaye Abubakar sukayi musabaha da docto tareda masa godiya taré suka bar dakin da su Hussaini...
Koda suka fito sun iske Ànty da yayar ta..
Ganin su yasa suke nufe su hankali tashe.
Kuka ànty take tace Salma bakyajin magana kash da wannan bakar rana....
Abubakar bata labarin duk abunda docto yace yayi...
Salati suka dauka suna taba hannu ita da yayar ta ta...
Wayar Abubakar ne yake ring yana dubawa yaga mama ce...
Cikin hanzari ya Daga tareda barin wajen da suke..

Mama tace Abubakar Salma ta kashe ni '' tasa mijina ya koreni Daga gidan sa...
Shegiya tsinanniya yau ta sani zubda hawaye...
Abubakar yace Mama ina rabaki da mugayen kalamai..
Bata labarin abunda ke Faruwa yayi nan da nan tafara kuka tadaura hannu akai tace '' shikenan yanzu Salma bazata sake samun ciki ba....
Wayyo Allah nashiga uku Dan Allah ka kula da Salma '' taya zanyi magana da Rahama ne....
Na cutar da ita 'yarinyar nan bata taba nuna fushin ta akaina...
Wayyo ni Aishatu n'a cutar da wanda yafi kowa kaunata aduniya Abdurrazak.

Abubakar cikin kwantar da murya yace Mama tun lokacin da muke son ganar dake gaskiya nida Abby akan Yanda kike daukan Alakar Rahama da Salma kwata kwata kinki bamu dama...
Abby tunda kikaga yaki bari kizauna 'tura ne yakai shi bango shekara da Shekaru ake abu daya..
Cikin kuka tace Dana Dan Allah kaci gaba da tausar mun zuciyar baban ka narokeka..
Daga hk sukayi Sallama....
Yana gama wayar da ita sai ga Shugaban Adalai da Sheik sunzo Asibitin harda Hassana....

Abubakar tarban su yayi tareda yi musu jagora zuwa cikin Asibitin..
Koda suka isa 'Sheik da Shugaban Adalai gun likita suka nufa..
Bayanin da yayiwa su Abubakar shiyakara yiwa su Sheik..
Salati suka fara dukan su...
Sheik n'a Girgiza kai yana kuka yace Salihu'' Aisha ta cutar dani kuka yake sossai...
Wanda hakan ya daga hankalin docto din ganin babban malami yana kuka to abun azimun ne....
Rarrashin sa suka farayi...
Sheik yace' badan nayi Al'kawari bazan saki Aisha duk rintsi to da babu abunda ze hana ni yin haka nasan girman Al'kawari..
Kallon Shugaban Adalai yayi yace t'aso Muje dakin da Aka kwantar da ita muganta...
Koda suka isa dakin iske ta sukayi tana kwance fuskar nan nata yayi fayau '' numfashin ta sama sama yake fita.....

Adua sukayi mata sossai kafun subar dakin.

Wayar Sheik ne yafara ring yana dubawa yaga Samad ne.
Dagawa yayi 'Dagacen bangaren Yarima Samad yace Sheik Imam agayawa Abba shikadai ake jira anan Filin airport din......
Sheik yace gamu nan zuwa yanzu' 'kace anzo da Saratu Ko..
Samad yace eh gatanan da ankwa zaune kusa da Yusuf Sani Yaro dayazo shida Matar sa...

OK gamunan zuwa ya furta tareda katse kiran...
Suna Fitowa Sheik ya kalli hassana yace Hauwa yar ki tabi su Rahama airport tace da ita za'a je..
Hassana tace eh da ita za'a je wai gun Mamy zata zauna tace...

MashaAllah ya furta babu bata lokaci ba suka bar Asibitin tareda barin Ànty da hassana 'da su Abubakar da hussain da suke masu Adua Allah yakaisu airport lafiya....

Cen Filin jirgin Shugaban Adalai n'a isowa gabadaya wajen kowa ya tashi hatta masu wucewa da wayanda ke zaune'
Sake da baki suke fadin wannan kamar shugaban Adalai ne sarkin da ba'a samu irin sa acikin zamanin da muke ciki ba..
Surutu ya barke a filin airport din....

Basu bata lokaci ba kai tsaye suka Shiga Jirgin Samad Personnel...

Koda suka tashi Daga garin kano...

Awa uku sukayi jirgin nasu yasauka à babban filin airport....
Daman Yarima Samad yacewa Mamy duk abunda take tabari ita da mai martaba duk suzo tarban su....
Mai Martaba yayi matukar mamakin Jin haka amma yace bara yaje yagani me yakeson nuna masa.....
Kasantuwa mai Martaba yazo Filin airport din..
Gabadaya wajen ya hargitse da jama'a hatta yan Jaridu ba'a barsu abaya ba..
Dan daukar bayanai ba.....
Duk inda Sarki ke jefa kafarsa '' waziri da fadawa da bodygar suna biye dasu abaya...
Ita kuma Mamy bayi da jakadiya duk suna biye da ita...
Daukar su Video ake har suka isa bakin jirgin suna jiran fitowar su Samad din.....

Yayi daidai da yan Jaridu duk sunyi layi suma sun kafa caméra din su dan daukar wayanda zasu fito ajirgin duk da basu sani ba.....

Daga Cikin jirgin Shugaban Adalai sukace yafara fitowa....
Hakan yasa Cike da nutsuwa yake tafiyar sa mai daukan hankali tafiya mai nuna izza da Mulki tattare dashi...
Yana cire kafafun n'asa kamar baya so takawa...

Kafafun sa ya fara fitowa sannan gangar jikin sa....

Cike da Zallan Mamaki babban Dan Jarida yake kallon sa yana taka step din jirgin yace wannan ai Shugaban Adalai ne....

Jin Furucin nasa yasa Mai martaba da Mamy Dago kansu Arazane cikin gigita suke kallon sa yana saukowa..
Mamy...........

Taku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:57 - Nuriyyat: KANWATA

09069080725

https://youtube.com/channel/UCCb-59DLAXr2BDMl3XJQvIA

Dan Allah channel dîna KYAUTA TV nan à sama kushiga ku danna mun subcribe 👆🏻

Saina jiku Masoya n'a...

Akwai Sabon Littafina wanda ze zomu ku da Zafi zafin sa..

Mai Suna *RUDANI* kai Dagajin sunan kunsan akwai akwai abubuwan masu ruda kwakwalwa 'dakuma ban Al'ajabi..
Wannan littafin tsaf n'a shirya wajen baje basira ta..
Kunsan Alkamila baya rubuta shirme.

KYAUTA DAGA Allah.

Shalelen Jarumai writ associat...

Masu bukatar tallah hajar su suna iya tuntuba ta wannan nombar dake sama..

9️⃣9️⃣

Mamy zazzare idanu tasoma cikin kidime take murza Idanun ta '' tace Ah Ah ku dubani kada Aljanu ne suka kama ni....
Jakadiya tace shugaba ta ba Aljanu bane 'uban yayan naki ne da kansa kike hangowa..
Mai Martaba cikin hanzarin yana gudu har yana tuntube kadan yarage yafadi..
Baba Salihu yataho aguje yatareshi yafada jikin sa....
Kuka ya saki yana Fadin d'ana Ashe kaine babban bakon da akace nazo n'a gani..
Kuka yake sossai yakara rungume dan nasa...
Koda Yarima suka iso wajen kallon su suke bakin su dauke da murmushi.
Yarima yace Mai Martaba ka sake shi mana har mu isa gida nan duk motsin mu a social média yake yawo...
Sassauta rikon da Yayiwa Salihu yayi yana goge kwallan da suka gangaro Daga Idanun sa....
Mamy Mutuwar tsaye tayi tana hawayen Farin ciki kallon sa take kamar sabon abu da bata taba gani ba..
Cikin takun sa mai cike da izza da tsantsar mulki yakarasa gaban ta...
Yace Habiba ta Salihu..
Ba mafarki kike ba nine nan mata ta.
sossai wajen yadauki shewa gun yan kallo da yan jaridu da yan gani da idanu dansu karar...
Chapter 108 · 0% Book details