← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 115 OF 115

Sashe 115

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Wani uban Kara Rahama tayi ta tsalle tana Girgiza salma wacce Idanun ta suke akafe..
.sheik na hawaye yasa hannun sa yarufe mata idanu yana kuka...

Nan da nan yadau wayar sa yakira ambulance din yace musu su koma dan tarigamu gidan gaskiya........
Ànty kuka take sossai Mama duk tabi tarikice..
Koda labari ya isa wajen Shugaban Adalai basu bata lokaci ba wajen bin jirgi ba shida mamy...

Wayyo Rahama kuka take ana rirriketa Yarima Samad da shima kuka yake yaja ta rike ta yana kokarin dauke ta akan gawar Salma....

Babu bata lokaci mata suka dauki Salma sukayi mata wanka..
Mama kuka take sossai ganin gawar yar ta abun soyuwar ta kuka take sossai take tace yata n'a cuce ki n'a cuci rayuwar ki.
Rahama kam sumewa tayi hakan yasa aka kwantar da ita Asibiti ana sanya mata ruwa.....

Wajen Karfe biyar aka sallaci gawar Salma inda aka samu cinkoson mutane..
Sossai anty take kuka itada Mama da hassana....

Bayan kwana uku da rasuwar Salma.
Rahama ta farfado ta koma silence magana daya zaka mata zata fashe da kuka..
Mamy da shugaban Adalai rarrashin ta suka dinga yi suka nuna mata babu soyayyar data wuce taringa binta da adu'a.....

Rayuwa ta sauya abubuwa sun canja..
Haka ake ta gudanar da rayuwa cike dajin Dadi.
Har Allah yakara bawa Rahama haihuwa inda suka haihu lokaci daya da hassana...

Rahama ta haifo ya mace wacce ta sanyawa Suna Salma tana kuka sossai rungume da hoton su n'a kuruciya itada kanwar ta....

Hassana ta haifo dan ta Namiji wanda suka sanyawa suna Salihu sossai ake murna...
Mama zuwa tayi tarungume Ànty cikin kuka tace Sa'adatu kanwata dan Allah kiyafemu n'a cutar dake tunda aka kawo gidan n'a.
Ànty tace n'a yafe miki nima kiyafemin zaman taré.......
Sheik sossai yaji dadin ganin duk sun hada kai.. Cike da kewa Salma duk yaji gidan ya rage masa dadi be kasawa dayi mata adu'a....
Har yana nadaman korar daya taba yimata sanda tazo gidan sa da gyale...

Rahama da Samad komawa sukayi kwatano inda sukaci gaba da rayuwar su cike da Jin dadi.
Yarima Samad samun aiki yayi inda yake shirin barin kasar shida Rahama zasu koma égyte da zama...

Shugaban Adalai sossai yake gudanar da mulkin sa bisa Adalci da tausayin talaka..
Mamy sossai tayi wani haske tayi fresh itada mijin nata....
Mama karama da kanta taraka Karima har kasar su Niger ziyara....

Asiya da Ahmed tamkar tagwaye haka suka koma...

Bayan Sati daya Samad tafiyar t'asu ya tashi shida Rahama....

Tamma bihamdulillahi
Anan nakawo karshen wannan littafin ina rokon Allah yasa mu amfana da abunda ke ciki...

Sakon gaisuwa ga duk masoyana..
Inayin ku...

Allah kayafemun kurakuraina...

Allah kasa muga farkon Ramadan lafiya muga karshen sa lafiya...

Duk wanda nayiwa laifi akan book dinnan dan Allah ya yafemun dan Adam agizi ne..

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah

IKILIMA ADAM..

Marubuciyar kaikajawa kanka

Da kuma Kanwata..

Saimun hadu à book dina maisuna RUDANI da kuma Rai daya..
Kai dagaji kunsan n'a musamman ne dan ya zarce KANWATA..

Ku daure kuyi comment wayanda basa yi dan inji ra'ayoyin ku akan Littafin nan......
Chapter 115 · 0% Book details