← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 115

Sashe 57

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baba Salihu bana bukatar kazo inda nake kayi hakuri dan Allah neman da nake maka asirince yau yazo karshe ga hoton ka d'ana dauko nan da niyar cigaba da cigiyar da adu'a da nake akan Allah ya bayyana mun kai.
Ashe nine kabari inata wahalar banza..
Pls kayi nesa dani ban zama da mutum mara gaskiya da Amana...

Sossai jikin Baba Salihu yadau zafi Jin furucin sheik hakan yasa ya kalli drever cikin tsawa yace nace ka bude motar Ko.
Sossai Drever ya razana ganin yanda Baba Salihu ya rikide lokaci daya..
Hatta Dattijo yayi mamakin ganin sa a wannan yanayin..

Cikin hanzari drever ya bude masa murfin motar.
Shigewa wa yayi tareda rufo kofar da karfi cikin Daga murya yace Muje Ko ?
Babu bata lokaci drever ya jasu zuwa gun Sheik.
Koda suka iso baba Salihu Allah Allah yake yafita motar.

Ana gama daidaita parking cikin dan hanzari yabude motar tareda nufar cikin gidan..
Drever n'a biye dashi abaya bayan ya ajiye motar..
Waigowa yayi cikin damuwa yace nuna mun dakin da ubangidana yake..
Bega ma rufe bakin sa ba yaji muryan Malam Isa Aminin sheik n'a fadin.

Baba Salihu gamu nan shigo mana yana mai bude masa dakin..
Cikin Azama ya nufi dakin bakin sa dauke da sallama.
Kallon dakin yake yanda komai n'a dakin yake musamman babu wani tarkace aciki.

Alkur'an yagani ajiye da carbi yana ta zuba idanu inda ze ga sheik.

Malam Isa cikin sakin fuska yace bismillah zauna mana nasan mutumin naka kake zuba idanu Ko ?
Baba Salihu Murmushin dole yayi yace eh fa yana ina ne..
Jin karar bude kofar bandaki yasashi yin shiru Kallon sheik yake yanda fuskar shi take jike Alamun Alwala ya dauro..
Cikin rawan Murya yace Sheik barkda da fitowa.
Yawwa yabashi Amsa atakaice tareda wuce shi ya zauna kan dadduma yana jan carbi.

Baba Salihu yazama yayi kusa da sheik har suna face din juna.
Carbin dake hannun sheik yasa hannun shi yakama.
Hakan yasa sheik dago Idanun sa yana kallon sa yana kallon Abunda yake shirin yi..

Baba Salihu ciki rawar Murya yace Sheik dan girman Allah katsaya ka saurareni.
Gabadaya sheik saida yaji jikin sa yayi sanyi tunda yakira sunan Allah..
Cikin hada rai yace Fadi abunda zaka fadi ina da abun yi yanzu.
Malam Isah yace haba sheik ka ringa hakuri mana koma meye aiyariga yafaru.

Kallon sa ya maida akan baba salihu cike da mutuntawa yace fadi abunda kakeson fadi.

Bakaramin dadi Baba salihu yaji ba dan ya karfafa masa gwuiwa...

Cikin muryan tausayi yafara magana yace sheik tunda n'a bar gidan ka nan gabon nazo.
Saboda n'alura idan har nace zankawo d'ana to yan gidan mu zasu samu labarin inda nake..
Inada mummunar tabo da Aka goga mun wanda y shine yayi sanadiyar barina kasar mu.
Nashigo garin kano.
Da niyar duk inda wannan shahararren Malamin nan yake nan zan zauna Ko Allah zesa in rage dadin dayafito dani Daga gidan mu....
Wannan dalilin yasa n'a bazama neman gidan ka har aka min kwatancen tsohon gidan ka ya sheik...

Ranar d'ana fara tozali dakai bakaramin dadi naji ba ina fadin yau gani ga Malamin d'ana fi so da kauna da nake yawan sauraren tafsir din sa....

Nazamo ma'aboci zaman massalacin da kake bada sallah ne Saboda kai '' har Allah yasa tausayina acikin zuciyarka kasancewa kullum kana ganina a sahun farko a massalaci..
Shiya kawo yarda da Aminci harka dauke ni Gadi gidan ka.
Nine nashiga rayuwan ka ya sheik Imam wlh dan inkawo haske acikin Rayuwata ka yafemin boye maka Asali na da nayi...

Ninan Sarki ne a garin kwatano '' masarautar gheuzo..

Sheik Da Aminin zumbur suka Mike daga zaunen da suke cikin........

Ayi hakuri wannan ma ba Admin tayi typin ba.
Dan batada time.
Comment da sharhi shi ze sa insan kunji dadin typin dîna sai inkara yi muku nex page inkara mata send ta tura muku
.
Membre cikin yan spécial grp À.
Sa'adatu.

Labari da tsarawa na.
IKILIMA ADAM
KYAUTA DAGA Allah.
3/21/22, 07:45 - Nuriyyat: KANWATA

LITTAFIN NAN KUDI NE INKIN GANSHI A WAJEN GROUP DÃŽNA NA SATA NE

Inkina bukata ga nomba
09069080725

5️⃣7️⃣

Sheik da Aminin sa zumbur suka Mike Daga zaunen cikin kidima.
Kallon Baba Salihu suke suna maimaita Sarkin kwatano cike da mamaki sheik yace kana nufin kaine Alh Salihu Turaki danaji mummunar labari akan sa wanda ya Girgiza dumban jama'a.
Kasashen waje har Saudiya saida tayi tsokaci akan wannan labarin daya bazu..

Kamar antaba zuwa cigiyar wannan sunan naka a unguwar mu tabbas amma bansan Ko suwaye ba..

Cikin kuka yace sheik nine wlh nasan zakaji haushina nasan zakaji meyasa ka yarda dani tun farko nasan kana nadamar kusanci daka samu tattare dani..
Kuka yake mai tsuma rai yace Sheik wlh Abun da ake zargina ban aikata ba.
Sharrin magauta ne ya sheik ka fahimce a lokacin nasan inna fito maka a mutum ba lallai bane ka saurare ni ba. dan duk wanda yaji labari dole ne yadau hakan take.
Bisa shedar da shaidu suka bada ya sheik..

Sheik cike da tausayawa yake kallon Baba Salihu shida Aminin sa.
Dafa baba salihu yayi yamasa Alamu ya tashi.
Yana tashi tsaye cikin kuka Sheik ya rungumi baba salihu yace karka damu ni daman tun farko danaji wannan labarin ban dauka ba dan bana yarda da labarin ance babu gamsarshiyar hujja.

Malam isa cikin tausayin Baba Salihu shima zuwa yayi inda suke rungume da juna yadaura hannun sa akan su tareda rugumar su.
Cikin saisaita murya yace InshAllah Baba Salihu nida Sheik Abdurrazak zamu taimaka maka da iya karfin Adu'ar mu..
Sakin su yayi tareda samun waje ya zauna hakan yasa suka saki juna hawaye farin ciki Sheik yakeyi dan bakaramin dadi yaji ba ganin Baba salihu yabiyo su yazabi yayi masa haka dan ya nuna masa bacin ran sa ne akan guje masa da yayi..
Duk da yanada kyakkyawan fahimta dashi yasan ba mutumin banza bane....

Sheik fuskantar baba Salihu yayi yace meyasa meyasa kana matsayin Sarkin Adalai kazo à matsayin kaskantaccen mutum cikin Jin zafin haka aransa.

Baba Salihu cikin kuka yace baka kaskantar dani ba zama dakai yakoya mun yanda ake rayuwa da jama'a zama dakai ya nuna mun taka tsatsan akan komai n'a rayuwa.
Shiyasa nacanza salon Rayuwa ta..

Sheik kallon dake kallon sa cike da tausayawa yace To ai mijin Rahama jikin Sarki ne n'a yanzu cikin yayan yan uwan ka ne ?
Kasa da kai Baba salihu yayi yace ya sunan mijin Rahama ?
Sheik Yace Abdulsamad ne inaga inhar ban mance ba.
Aminin sheik yace kwarai kuwa sunan sa ne.
Baba Salihu shiru yayi cikin kasa da murya yace nine uban Abdul Samad.
Sheik zazzare idanu yayi yace kenan wannan yaron adu'a dayasa ayi masa akan mahaifin sa Allah ya bayyana sa.
Kaine kenan sossai yaba baba Salihu labarin yanda sukai da Samad.

meyasa ka boye masa kanka danka ne fa !!

Baba salihu tashi Daga zaunen yayi yayi taku daya zuwa biyu tareda kallon kofar waje hannayen sa goye abaya yace..
Nazabi inboye musu Saboda samun labarin danayi Sarki Turaki n'a neman sanin inda nake rayuwa ganin hakane yasa nafara boye musu inda nake naki yarda d'ana ya ganni dan ina tabbacin inda har ya ganni to me martaba yagama sanin inda nake..

Sheik da Aminin sa kallon suke cike da tausayawa sukace karka damu ai InshAllah zamu taimaka maka.
Da taimakon Rahama yana kallo baba salihu daya kura masa idanu..
Sheik yace kwarai kuwa Rahama InshAllah zata warware duk wata kulli dake cikin gidan nan.

Baba Salihu cike da yarda da kai yace kaga yanda Allah ke ikon sa Ko daman yan Ameen sun Amsa shiyasa koda na gujewa kawo d'ana.
Allah yabashi ta wani silan '' kayi hakuri ya sheik nasan kaji zafin hakan danai Amma banyi da niyar cin zarafi ba.
Saidan inada yakinin Adamu yanason Rahama nasan shi zaka ba inhar kaga bandawo ba.

Sheik dake goge Zufan daya keto masa cikin tsananin tausayin Baba Salihu '' 'shima ya furta abunda yaji wannan drever yakira shi dashi.
Yace ya shugaban Adalai kayi hakuri bisa abunda nayi maka a filin airport.

Baba Salihu saurin katseshi yayi da fadin wannan sunan yayi min nauyi dayawa a bakin ka nafison Jin kana kirana da baba Salihu narokeka kaci gaba da fadin haka.

Aminin sheik yace Ah Ah ai girman ka ne kuma ba'a canzawa tuwo suna kai Sarkin Adalai shin za'a iya samun Sarkin da yayi Adalci irin naka kuwa Ko mahaifin ka dake kan karagan mulki dalilin shugabancin ka ne ake cemasa shugaban Adalai.
Amma ya tafka babban kuskure ta ya za'ai ace ya yarda da zancen zirr....

Baba Salihu cikin kwantar da murya yace bana tunanin mahaifina ya aikata mun abunda yayi mun ne da sanin sa nasan dai akwai wani Abu akasa wanda gano gaskiyar lamarin Alhakin yana akan wata baiwa wacce take gun mata ta..
Sossai suka Shiga tattauna yanda zasu bullowa lamarin nan dan akwai lauje cikin nadi..

*************************

KANO.

Sai kusan karfe tara suka Faruk suka dawo gida bayan sun sauke Asiya..
Karasowa falon sukai ganin Samad zaune kusa da Rahama kallon ta yake babu Ko kiftawa.
Faruk yace haba sai sallama mukeyi ina ka kai hankalin ka ne..
Samad firgit ya dawo hayyacin sa Murmushi yake yayi yace Au har kun dawo dafatan kun sauke ta gida ya tambaya cike da kulawa..

Aminu dake kokarin haurawa sama yace eh kalau muka kaita tabe tabe..
Tareda cigaba da tafiyar sa...
Samad kallon Faruk yayi dashima zebi bayan Aminu yace kai kuma ina zakaje ne wancen dan iskan yatafi kaima zaka bishi ne ?

Faruk cikin tabe baki yace to inzauna nan inmaka me kana tareda da matar ka Ko sanin shigowar mu bakai ba yakarashe zancen tareda bin matakalan step cikin saurin sa.

Yarima kallon sa yake harya shige dakin nasa maida kallon sa yayi akan Rahama wacce ita ba barci take itakuma Idanun ta basa bude..

Kallon ta yake n'a wasu yan dakiku be Jira wata wata ba yakaita dakin nata tareda dire ta akan gadon ta..
Chapter 57 · 0% Book details