← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 115

Sashe 77

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rike da kugun sa yake kallon Su Faruk yace muna iya tafiya naso inje gidan Su Faruk ingaida iyayen nasa kaima Aminu mu biya naku gidan '' Daga baya zankai Rahama ta gaishe su...

Faruk yace Ah karka damu wani uzurin yana gaban wani naga kamar Mamy ke neman ka Muje dukan mu.
Ko zuwa gobe saikaje gidajen namu aiba bakon waje bane a wajen ka...

Yarima yace godiya nake Abokaina dawo.da kallon sa kan Hajiya zulai yayi yace wannan sirrin da kike dashi kina tabbaacin zaki sanar mun komai kowani zaki gayan ki boye wani...
Hajiya zulai cikin tsananin mamaki yanda yake zaro zance.
da yayi magana inyayi shiru zaka ce bashi bane yayi kalamin ba...

Tace Yarima wannan hakkin da Aka kwace mun ka karbo mun wlh hadda hakkin daure wa karya gindi shine Allah ya nuna mun ishara ina nufin Nina boye Saratu agida n'a watan uku Sannan ta bar kasar ''...

Cikin razana suke kallon ta dukan su''yarima innaliahi kawai yake ta maimaitawa acikin zuciyar sa..
Yace hajiya zulai maganar mu dake mai tsawo ne...
Tunda nasan gidan naki nan da kwana uku innagama uzurin gabana zamu zo nida Abokaina harda Mata ta...

Sossai taji dadin furucin sa Daga haka sukayi sallama...
Faruk motar Samad ya shiga '' Shiko Aminu yaja t'asu motar da suka zo da ita kotun....

Ahanyar su Yarima Samad yace kaga yanda Allah yake ikon sa Ko...
Wannan matar tayi Al'kawarin zata gayamana inda Saratu take InshAllah mun kusa kawo rabin matsalar gidan mu...
Faruk yace gaskiya kam hakane.....

**************************

Kano
.

Mama ita da Aminiyar ta zaune gaban wani tsohon malami yana jan carbi dago kai yayi yana kallon su..
Yace Aishatu gaskiya wannan matar saita haihu kuma tagwaye ne acikin nata mace da namiji...
Abu daya zakiyi shine kisa mata guba acikin abinci taci ta mutu..
Koko kisa mata maganin daze barar mata da cikin nata cikin ruwan shan ta...
Amma asiri baze kamata ba dan tanada kariya sossai tattare da ita bata wasa da karatun Alkur'an..
Sannan adu'oi koda yaushe cikin su take '' 'mijin naku shima ba'a iya samun sa..
Maganar gaskiya yafison wancen matar' 'ke kuma yana tausayin ki ne a matsayin matar da mahaifin sa yayi masa zabi kuma ya haramta masa rabuwa dake....

Sai maganar Diyar ki Salma kuna son akashe wannan auren' 'shi abune me sauki' '' saide mijin nata yanzu da gaske yana son Salman ya tuba akan laifin sa na baya...
Yakuka. Gani dago kai. Yayi yana. Kallon su....

Aminiyar Mama ajiyar zuciya ta sauke cikin yin kasa da murya tace ai kawai araba auren nan...
Akwai wanda zamu hadata dashi wani Alhaji Ibrahim bushasha...
Sossai Malam yayi mamaki yace Alhaji Ibrahim baya kasar nan fa...
Aminiyar Mama ta kwace zancen hannun malam tace yana garin mana '' 'har waya muna yi dashi...
Shiko shiru yayi yana Girgiza kai yaso yayi magana amma Aminiyar mama bata bashi dama ba...

Mama tace uhmm nidai araba auren so muke yazo har gida yabata Takardan saki har uku...
Malam yace babu matsala cikin da take dauke dashi ya zakuyi...

Mama ta kalli kawar ta tana jiran amsar ta...
Kawar tace kawai Malam a barar da cikin me zatayi da wani ciki Ana neman wani sabon miji........

Malam yace uhmm gaskiya bazan iya lalata cikin ba '' Amma zan iya raba auren Daga haka dai sukayi abunda zasu yi.
Ya sallame su...

Ahanyar su ta komawa gida Mama tace nidai inason Sa'adatu wannan cikin jikin nata ya bare wallahi niban haifi tagwaye ba itace zata haifa...

Kawar mama tace karki d'amu kamar jibi zasu dawo Ko '' sha kurumin data dawo ki sanar mun...
Cike da Jin dadi suka taba hannun ita da Mama.....

Sheik zaune kofar gidan nasa yana kallon ta inda Mama zata taho dan tafita babu izinin sossai ransa ya baci....

Zaune yake yana nazarin ina take zuwa ne. Kullum tunda yadawo bata zauna ba...
Kukan zuci yake yace Abbana mahaifina kaine ka hadani da Ayshatu nasan rabon yaya ne ya koka tsakanina da ita...

Amma tunda n'a aure ta banji dadi ba '' 'ya Allah kashirya min Aisha ta''' adua yake sossai A'cikn zuciyar sa...

Hango ta Daga nesa ita kadai tana tahowa yasa shi maida kallon sa akan ta...

Cikin. Tsoro da fargaban ganin mijin nata a kofar gidan nasu...
Jiki babu kwari ta karaso, wajen tana kokarin wuce shi...
Taji yana fadin Aysha dakata dan Allah karki dauke ni sakarai mana...

Cak ta tsaya cikin sanyin jiki ta juyo tana kallon sa ''...
Bakin sa n'a rawa yace Daga ina kike kuma da izinin wa kika fita sossai ya hada ransa...

Cike da tsoro tace magani naje siye...

Maganin me kike je siye yana kallon ta cikin ido...

Cikin yin kasa da murya tace maganin haihuwa mana''' naga tun akan Salma bankara haihuwa ba...
Saboda tsabar mugun ta shine ka nemowa Sa'adatu maganin haihuwa nika kyaleni Saboda baka yayi n'a. .
Cikin kukan Borin kunya tace dan niba fara bace irin ka shiyasa ba'a sona...
Baka nemana a shimfida sai inhar Nice n'a nema....

Sake da baki Sheik yake kallon ta har dariya ta subuce masa besaniba.....
So yake yayi dariya amma ganin ta yasa yadaure...

Uhmm Ayshatu kenan ya furta cikin Jan sunan ta.
Yace me kike so inmiki wanda ban miki ba...
Kinzo kina kawo zancen shirme mara tushe...
Bana kwanciya dake uhmm dukan zancen banza kike yi ayshatu...

Kishin naki ne ya motsa Ko haihuwa ta Allah ce shike ba wanda yaso kuma ya hana wanda yaso...
Keda Allah yaba arzikin yaya wasu suna nan basu haihu ba kuma sun zauna lafiya...
Bâri kiji maganar gaskiya aure zankara kwanan nan InshAllah..

Mama jin kalaman sa tayi kamar ànbuga mata guduma akai...
Cikin zazzare idanu tace aure kace fa
..
Cikin yarda da kai yace eh mana kona wuce yin aure ne..
Dan haka maganar haihuwa kishirya Inkinada Rabo sai Allah yabaki..
Cike da takaici yawuce ta ya shige cikin gidan nasa yana juya kalaman n'a baya kwanciya da ita...

Zama. Yayi kan. Kujera yana Girgiza kai. Yace oh Allah mata iyayen sharri duk abunda kake musu wataran zasu ce baka taba tsinana musu komai ba...

Barin wani tunanin yayi tareda dauko Alkur'an mai girma yasoma karantawa.......

*******************,***

Kwatano...

Sossai Mamy take ta yiwa Ahmad fada akan abunda ya aikata '' '
Koda ya Yarima ya shigo Jin labarin abunda Ahmad yayi besa yaji haushi ba kuma be masa fada ba...
Zaune yake yana kallon yanda Mamy ta zage. Tana fada iya gaskiyar ta...

Saida yaga tagama ta zauna yace Mamy hakuri zakiyi damu fa..
Dan n'a Ahmad kadan ne akan nwa yanzu ma dakin Fulanin da marwan zani...

Sallamar Rahama da Khadija ne Asiya da Salma suna biye dasu yasa kallon sa yakoma kansu...
Ganin Rahama n'a cikin su yafara kokarin dawowa hayyacin sa amma ina yariga da yadau zafi hakan yasa bekara.kallon inda suke ba....

Cike da ladabi Rahama da Asiya da salma suka gaishe da Mamy amsa musu tayi cikin yin kasa murya tace Rahama har kin iso '' 'nuna musu Kujera tayi da su zauna hakan yasa suka zazaauna Ko wanne su yayi shiru..
Ita Ko Rahama satar kallon Yarima Samad take da sam hankalin sa baya kanta....

Mamy cikin son dakatar dashi tace bangane n'a Ahmad kadan bane me kake nufi Abdul Samad ta tsare da idanu...

Ganin ya tashi tsaye hannun sa dauke da katuwar d'orina yace Mamy babu ruwan ki...
Cikin Daga Murya duka wayanda ke falon saida suka tsorota ganin yanda jikin sa yadau rawa sossai kamar mazari..
Cikin zafin nama yajuya à fusa ce ze wuce kokarin taré shi Mamy take yi..

Ita Rahama cikin hanzarin tabi bayan sa ganin yanda yake zuba uban saurin sai fadi take Amjad Amjad Amjad....

Tsaya dan Allah dan Allah katsaya Nice Rahama..

Cikin.............

Ta ku har kullum KYAUTA Daga Allah
3/21/22, 07:52 - Nuriyyat: 7️⃣6️⃣

09069080725

Nice Rahama cikin hanzarin ta da zafin nama amma ina yayi nisa sai buga sauri yake kafun isowar sa labari ya isa wajen Fulani ga Samad shima zuwa '' Fulani cikin hanzarin ta canza daki tareda kulle kanta tacewa bayi karsu ga inda take...

Koda Samad ya iso yana ta dube dube '' 'cikin tsawa yake kallon bayin yace ina Shugabar ku take....
Bakin su n'a rawa sukace bamu inda ta tafi ba' '' yayi daidai da karasowan Rahama da Mamy...

Rahama kama hannun sa tayi cikin takaicin ashe haka ya iya fada '' 'tace haba Amjad dan Allah kayi hakuri duk da bansan mêke faruwa ba.
Ganin Mamy zatayi magana yafi ce Daga dakin direct dakin Marwan ya shiga..

Marwan kwance yake yana Waya da Yarinyar da yakeso ya aura...
Kamar Daga Sama yaji antake masa hannun sa dake rike da wayar da karfi wanda yajawo fashewar wayar à hannun sa''nan da nan hannun ya amsa Alamun gocewa...

Cikin gigita yadago kai ganin Yarima' Samad ne akan sa Idanun sa '' babu annuri..
Wannan dorinar yake ta lafta masa ta Ko ina yana magana cikin ihu yace n'a rabaka da Karima da kasan wacece ita Sam bazakayi mugun tunani akan ta ba...

Karima ba baiwa bace '' tsagaita maganar sa '' yayi yaci gaba da bugun Marwan yana ihu iya karfin sa...
Mamy da Rahama ne sukayi nasaran shigowa dakin '' 'cikin tsawa tace daman haka kuke kaida Ahmad bakuda mutunci''' kuma inhar rashin mutunci naku ya motsa bakwajin bari..
Yanzu dan Allah ni me kuka daukeni mara amfani kenan inhar baka daina bugun sa ba''' wallahi zanbar muku gidan naku'''.

Cak Yarima ya tsaya kamar an dasa shi '' cike da nadama ya juyo yana kallon yanda Mamy ke '' kuka '' cikin rarrashi yace dan Allah Mamy karkiyi fushi damu '' fushin ki '' 'musiba ce à gare mu..

Bansan yanda akayi n'akasa iya contrôle din kaina ba....

Shiko Marwan da Allah yacece shi be jigata ba''' yafara neman hanyar barin dakin...

Mamy dake kallon sa cikin kalan tausayawa tace d'ana Marwan dan Allah kayi hakuri'' Nice Mamy dinka kasan bazan taba yarda Samad ya zage ka ba..
Bare duka' ina neman Afuwa....
Chapter 77 · 0% Book details