← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 115

Sashe 104

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rahama cike da Jin dadi tace mama nayi kewar ki sossai '' uhmm muna tare da baki '' mama firdausi kanwar mahaifiyar Abdul Samad 'da yan uwan sa mata....
Mama tace Ah sushigo mana..
Lala Mama karki damu Abby yakai su masaukin baki farkon gida baki wajen ba yanda ya tsaru har abinci komai ankai...
Mama sake da baki tace to waye yayi girkin Ko daman abincin sune naji jiya yana cemin in dafa n'a baki ne na zata n'a bakin sa ne da suka fito Daga wata uwa duniya nace ya nemo me dafawa...
Rahama bata rai tayi tace Mamaaaaa ta ja sunan wai yaushe zaki gane abunda nakeson kina ganewa ne...
Abby fa mijin ki ne kinfini sanin hakkin mata akan mijin ta biyayya dasai ki dafa masa ki jefa masa aniyar sa kinga anzauna lafiya 'mama banason kowace mace tazo gidan nan yafi ki matsayi inason matsayin ku yazo daya Ko ma ki d'ara su...
Mama ki duba anty mana bata damu ba..
Sau nawa Abby ze mata abunda bata so akan ki kuma ina gani amma wallahi bata taba nuna masa kaza da yayi mata be mata dadi.
Saidai tacemin tamasa uzuri amatsayin dan Adam agizi ne tasan da ganganci baze mata haka ba...
Irin haka shike karasawa miji ya yarda dakai dari bisa dari...
Nidai sonake ki hada kai da Ànty sossai wallahi matar nan tana kaunar ki sau nawa Abby ze yunkuro yace ze sake ki 'Inkin takura masa tareda kawar ki Suwaiba Ànty take tausasa tana gayamasa in har yabiyewa zuciya ze kaisa ya baro dayake yana Jin shawarar ta data fadi yake dauka kuma ya gode...
Inason yardan da Abby zeyi dake yafi n'a kowa cikin gidan nan..
Dan Allah mama ta kinji Ko...

Tabe baki Mama tayi tace uhmm naji zanduba Muje in kaiki daki Ko..
Ah ah mama ba dakin ki zan sauka ba.
Wajen uwar dakina zan kwana haka kurum ga inda zansha lele....
Mama bata rai tayi tace haba Rahama nice bazaki sha lele ba wajena ni fa mahaifiyar ki ce...
Nasani Mama anty itace ta raineni haihuwa ta kawaii kika yi kin fita matsayi amma bazan juya mata baya ba.
Ki duba yanda tasha wahala dani agidan nan Keko Salma kadai kika sani..
Mama ni kinga tafiya ta Abby ya aika kaya sama..
Zan fito anjima bayan na huta da Asiya tazo kice mata ina sama ta sameni Daga haka tasakai cikin hanzarin ta....

Mama rike da baki tace kam buhu amma yarinyar n'an ta mugun gamawa dani Rahamatullah chab....
Sallamar Yarima Samad suda Faruk Da Aminu yajawo hankalin ta akan su.....
Cike da fara'a tace lale lale ga waje ku zauna ta nuna musu kujerun suka zazzauna.....
Babu bata lokaci tasa yan aikin gidan suka kawo musu lemu da ruwan Swan...
Dakyar suka sha...

Yarima Samad kallon Maman Rahama yake ta kasan idanu yace Ah lallai dole mata ta tayi kyau watau kyau ne da kyau suka hadu ita da Sheik Imam..
Bayan sun dan gaisa ne suka nemi ayi musu jagora zuwa gidan su Asiya kai lefe dan Marwan da Ahmad suna waje basu shigo...
Mama tace me saukine drever.....

Basu bata lokaci ba suka tafi kai lefe harda Rahama da mama firdausi 'da Ahmad din dasu Faruk da Aminu' marwan......

Sun Samu tarba mekyau Daga gidan su Asiya '' cike da farin ciki ake bubbude lefen harda busan Algaita akayi musu n'a sarakuna...

Ahmad ne kadai be fito Daga Motar ba kallon gidan su Asiya yake babu laifi suma gidan nasu babu raini hadadde ne saidai bekai nasu Rahama ba.
Yace oh Ko me ruwana da zancen gida iyakata in koya mata hankali.....

Yaso ya ganta a yau haka bazeyu bane yasa ya kyale.... Gobe suna taré tunda tare za'a juya zuwa kwatanon........
Asiya sai kukan farin ciki take irin mutuntawa da dangin Ahmad sukayi wa iyayen nata.....
Sossai aka hada su da kayan ciye ciye a motar tasu....
Ita Ko Rahama da zasu wuce tacewa Asiya matar kanina '' Daga yanzu respect zaki ringa bani ehee...
Darawa Asiya tayi tace to anti babba...
Sossai suke sukayi kamar kada su Rabu à ranar Rahama tabi dangin mijin nata suka juya....

Marwan tsiya yakewa Ahmad yace dan Iska ka damu kaga Asiya Ko....
Tabe baki yayi yace toni me zangani anan wajen chab

Marwan yace bangane chab ba banson gulma fa..
Uhmm kaidai yi shiru kawai bazaka bane..

Uhmm naji tunda haka kace
..

Kwatano...

Ambassador Abdullahi shida tawagar da matar sa da yan uwa da à bokan arziki suka isa garin kwatano

Kai tsaye sashin Mai martaba suka je shida uban nasa..
Sauran bakin aka tafi dasu masaukin su dan suna taré da gajiya...

Mai martaba cike da Jin dadi yace kaga Ambassador yanda Allah ke ikon sa Ko..
Ka bamu 'mun baka..
Ambassador ya murmusa yace to ya za'ayi da hukunci Allah...
Sossai suka shagala da hiran yaushe gamo..
Shiko Adamsy cire kunya yayi yace a nuna masa sashin Mamy zeje yaga khadija...
Mai martaba yace gaskiya kam gara kaje kaga sarauniya dukar da kansa yayi kasa yace uhmm zanje a rakani Daga haka ya fice Daga dakin cikin hanzarin.

Ambassador da mai martaba kallon sa suke suna Girgiza kai..
Shiko kai tsaye Kwatance sashin Mamy bayi suka yi masa dan sunsan Ko ya akayi shine angon....

Allah Allah yake ya isa sashin Mamy gani yake kamar baya sauri....
Koda ya isa sashin Mamy.

Bakin sa dauke da Sallama ya shiga dakin...

Iske Mamy yayi da khadija suna hira '' Mamy lale lale Barka da zuwan Adamu har kun iso...
Jin haka yasa khadija Dago kanta.
Caraf Idanun su suka tsarke cikin juna.....

Saurin dukar da kanta kasa tayi..
Shiko cikin hanzarin sa yakaraso falon tareda nan waje ya zauna yana kallon Mamy cike da ladabi ya gaishe ta Amsa masa tayi cikin Sakin fuska tace ina mamar taka uhmm suna cen masauki sunce sun tara gajiya sai anjima zasu leko...

Ah Ah bara intashi ni zanje dakaina irin wannan bakin haka...
Ihun kiran wata baiwa tasoma tace maza adauko abincin baki akai masu masaukin su da duk wani abunda da yakamata..
Cike da ladabi baiwar tace angama Shugaba ta...

Mamy ganin Adamu ya kurawa Khadija idanu hakan yasa tace yawwa ina zuwa bara inje inji da bakin dake cikin daki....

Mamy n'a ficewa yasoma mata magana yace please dijat dan Dago kanki in ganki mana wannan lalle da akayi miki bakaramin kyau yayi da fatar jikin ki ba..

Duk da bantaba ganin ki ba saiyau dasai ince ke ta mussaman ce...
Dijat Dago kan ki inga kyakkyawa fuskar da ake min rowa....

Dago kanta tayi '' sake da baki yace waow MashaAllah Allah mai halitta..

Cike da zakewa yace bara in rera miki waka.....
Kamar haka....

Dama dake nafara haduwa danayi aure tuntuni '' wayyo soyayya n'a dadi '..

Batasan sanda ta murmusa ba tace uhmm nidai banson Zuga fa..
Haba Dijat dîna kinfi karfin Zuga duk abunda nake fada Daga cen kasar zuciya ta ne...
Banki inwuni ina kallon kyakkyawa fuskar ki ba...
Dijat uhmm wani Abu sai jibi nasan goben ba barina zasu yi inkare miki kallo ba..

Amma jibi InshAllah ina tareda ke dan barin kasar zamuyi 'domin zuwa honeymoon cike da Jin dadi da son yawo tace dan Allah da gaske kake..
Nan da nan yaga farin ciki akan haka...

InshAllah dagaske baby n'a ranar Lahadi zamu wuce banson à takura mana..
Uhmm Allah yakaimu ta furta..

Kashe gari

Ta kama yau Juma'a gabadaya masarautar ta cike da dumbun jama'a kasancewa sai anyi sallah juma'a za'a daura auren.....

Cen ma Kanon sai bayan juma'a za'a daura.....

Sossai Khadija tasha makeup gun kwararriyar ma'akaciya...

Maman Adamsy ita da yan uwan nata zuwa sukayi wajen dijat domin daukar zafafan hotuna da ita..
Sossai ta saki jiki suka dauki hoto da Ita.
Shima Adamsy zuwa yayi akayi hoton dashi......

Lokaci n'a karatowa....

Ana idar da Sallah juma'a.
Jama'a suka cika domin sheda wannan daurin auren.....
Sossai aka cika wajen inda naji Ana fadin andaura auren Khadija Salihu da Angon ta Adamu Abdullahi akan sadaki dubu dari biyar.....

Sossai wajen aka fara busan sarewa da Algaita..
Nan dan nan aka fara wasan dokuna.
Na yayan sarauta yan jaridu sun samu aiki dauka suke babu kakkautawa....

Adamsy cike da murna abokan sa da suka zo ranar daurin auren sukayi ta masa congrat har hawaye yayi beyi zaton za'a daura wannan auren bece yafasa.....

Nan da nan aka shirin taron Walima bayan lasa'ar..
Adamsy kai tsaye wajen su Mamy da yan uwan ya nuna sabar cikan da akayi dakyar mutum ke tura kafar sa...

Ganin babu hanya yafara neman yanda zeyi suga dijat domin daukar hotuna da ita....

Wata baiwar tace anty dijat tana Sashin yayan ta Yarima Samad cen take sittin da kawayen ta...
Haka yasa yace a nuna masa kai tsaye suka nufa...koda suka isa sashin bayi basu hana su kasancewa in ana sha'ani manyan mutane ba'a hanasu shige da fice da anbaza caméra ta Ko ina shiyasa Sarki be hana ba....

Bakin su dauke da Sallama suka isa sashin inda suka iske Dijat atsakiyan kawayen ta ana selfie...

Tunda ya tsura mata idanu kasa sauke su yayi...
. Cikin hanzarin su suka Shiga dakin '' babu bata lokaci akasha hotuna zafafa harda rungume ta 'tana ta kaucewa ganin bashida kunya gaban mutane.......

Kano......

Kusan karfe uku aka daura auren Ahmad da Asiya..
Kasancewa ranar anyi daure daure aure dayawa....

Nan da nan aka d'au shela andaura auren Ahmad salihu da Amaryar sa Asiya Muhammad....
Bisa sadaki dubu dari biyar...

Sossai Yarima Samad da Ahmad suka ringa hotuna n'a tarih.
Su Faruk da Marwan da Aminu ba'a barsu abaya ba..

Sheik sossai yake cike da farin ciki...
Shima wajen suna ta masa Allah yasanya Alkhairi kasancewa andaura auren nasa àcen gabon tun misali karfe biyu......

YARIMA Ahmad Jan Marwan yayi bayan sun bar wajen daurin auren..

Kai tsaye gidan su Asiya suka nufa...
Iske Rahama sukayi awajen sun sa kaya iri daya sunsha makeup.
Salma n'a zaune gefen su sai tabe baki take tana taunan cingam....
Chapter 104 · 0% Book details