← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 115

Sashe 53

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuyanga tace jakadiya tace à kawo ta gun ki Daga haka tawuce.
Karima tace bismillah tareda bata wuri ta zauna.
Shiru ne ya ratsa dakin n'a wani lokaci.
Hassana tace Karima ance ke baiwar Samad ne.
Eh 'ni baiwar sa tabata amsa ataikaice tareda yin shiru n'a rashin sabo da ita..
Murmushi tayi tana kallon Karima tana nazartan yanayin ta.
Tace yawwa Karima inason in zama abokiyar hirar Ki inbabu matsala.
Karima tace wannan me sauki ne.
Fita nake shirin yi dan Shugaba n'a yakusa dawowa kuma tareda Matar sa Amaryar sa..
Hassana tace kina nufin daman Matar tasa bata taba zuwa masarautar nan bane..
Karima gyara zama tayi tana fuskantar hassana.
Tace eh betaba kawo ta ba Asalima wannan matar da ya aura gidan nan babu wanda yasan ta sai Mamy da mai martaba da Abban Marwan..
Hassana rike da baki tace Ko zaki gayamin ya haka ta kasance kuwa da mamaki Yarima dan Sarki jikan ace yayi aure batareda duniya taji ba..
Karima tace ai wannan karan duniya zata ji dan zuwan ta ba karamin Girgiza masarautar nan zeyi ba....
Hassana tace kamar ya kenan ?
Karima tace zan miki bayani bakuwa ki bari anjima inna nutsu.

************************

Fulani ta shiga babban tashi hankali bokan jeji ya tabbatar mata kada su bari Rahama ta tako kafar ta cikin Masarautar nan yin haka ze wargaza komai sabanin da da ake so tazo...
Yanzu kuma ya lura zuwan ta ze bata komai ne ba gyara ba dan yarinyar tanada taurin kai.

**************************

Maman Maryam cikin tashin hankali take magana da Abban Maryam dake fadi mata maza maza ta dakatar da Yarima tunda itace tace yakawo ta.
Maman maryam cikin zafin nama tadau wayar ta ta dannawa Samad kira...
Har wayar takusa tsinkewa ya Daga.
Cikin bangirma yace mommy n'a dafatan kina lafiya.
Lafiya lau tabashi amsa atakaice.
Tace Samad naam ya furta tareda gyara zama akan kujerar 1str n'a falon sa yana sauraren ta.
Inason kafasa zuwa da matar ka ?

Zumbur ya Mike tsaye yace banji dan........

Taku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:44 - Nuriyyat: KANWATA

LITTAFIN NAN KUDI NE INKIN GANSHI A WAJEN GROUP DÃŽNA NA SATA NE.
INKIN BUKATA GA NOMBA
09069080725

5️⃣4️⃣

ZUMBUR YA MIKE TSAYE YACE BANJI BA MOMMY KIKACE KADA INZO DA ITA.
MOMMY TACE EH HAKA NAKE NUFI YARIMA KA FAHIMCE NI.
Maryam ce take kuka akan son da take maka tace baka Daga wayar ta kwata kwata ina tsoron kazo da matar ka Jinin ta yahau takarashe zancen tana kukan karya.
Samad dake sauraren ta lumshe Idanun sa yayi yace mommy naam ta amsa cikin tsaigaita kukan ta.
Inason kisan cewa n'a haramtawa kaina auren Maryam hakuri zatai Inde akan Maryam ne bazan iya fasa zuwa da ita ba.
MOMMY kiyi hakuri dan Allah nariga n'a gaya mata taré zamu tafi banason raini ya shiga tsakanina da ita dan tana bani respect daidai yanda Allah yace.
MOMMY ta hada rai kamar yana gaban ta '.
Tace yanzu Samad duk kukan nan da nakeyi dan yata Ashe bazaki ji tausayin ta ba
Samad sassaita muryan sa yayi yace mommy ina me baki hakuri nariga nayi kudiri da niya kuma har mai Martaba yasan da wannan batun.
Tun farko kece kika samun sha'awar zuwa da ita sabanin da.
Da ban kawo hakan araina ba..
MOMMY cikin Jin haushin sa tace Samad kaban mamaki yanzu in Mamy ce zaka ce mata tayi hakuri.
Cikin gyara zaman sa yace kwarai kuwa har Mamy zan fadawa tayi hakuri shari'a bata yarda kaci zarafin iyayen ka ba.
Yi musu biyayya abu ne mai kyau.
Amma Saboda ke kadai bazan bata ran mutane dayawa ba.
Yi hakuri mommy Daga hk ya katse wayar ransa abace cikin Daga murya yace wai ita wannan matar meye matsalar ta ne.
Murmushi yayi uhmm koda yake batasan kallon ta nake ba Muje zuwa.

Ita Ko maman maryam tsine masa taringa yi tace shege dan akuya ni ze gayawa zancen banza.
Abban Maryam yace Kinga matsalar yaron nan Ko ya zamuyi ne.
Maryam ce tafito Daga dakin ta sanye take da riga da wando cotton sossai yakama jikin ta kowani sassa n'a jikin ta yana motsawa.
Cikin hanzari takaraso Idanun ta cike da kwalla tace Mommy ya amince baze zo da ita ba Ko ?

Kallon Maryam take tace inafa ya Amince dan iskan yaro.
Maryam tace haba mommy kidaina ce masa dan iska agabana inajin ciwon haka.
Abban maryam yace ke shasha ce duk wannan abun munayi dan ke ne.
Inkin ce kin fasa baki son sa.
Zamu cire hannu akan lamarin sa '' kema kinsan babu abunda matar sa ta taré muna Ko.
MOMMY TACE gayamata shasha kawai.
Maryam cikin kuka tace mommy kuyi hakuri wallahi inason Samad duk abunda yadace kuyi.
Nabishi ta lala m'a yaki kulani nazo ta karkashin kasa nan m'a abu be canza ba..
Abba zama yayi kan kujera tareda zaunar da Maryam din.
Cikin muryan rarrashi yace ki barta tazo din InshAllah Ko babu boka babu mallam akwai tugun da zamu kulla mata wanda zesa akore ta Daga masarautar gheuzo.
Cikin Jin dadi takwanta jikin Abba tace wai dagaske kake Abba n'a..
Kwarai kuwa Maryam dita.
Kisha kurumin ki yata sai inda karfi n'a yakare InshAllah zaki zama uwar yayan Samad.
Murmushi tayi tace Abba nagode Allah yabaka sa'a.
Da Ameen mommy da Abba suka Amsa.
Mommy tace ina nan fa ina neman wani malami da akace mun yana aiki kamar yankan wuka.
Kawata keban labari InshAllah zanje cen mugani..
Abban Maryam yace wannan shine daidai in hagu taki à koma dama....

_________________________

Mamy cikin dakin ta take tana dan gyara kayan wankin da suka bushe da tafiso ta gyara su da kanta kafun tabayar ayi mata guga...

Shigowar khadija yajawo hankalin ta akan kallon ta take cikin sakin fuska tace daughter har kin gama kallon ne ?

Cikin turo baki gaba tace bashi bane ba.

Mamy tace wa kenan ?
Sallamar Yarima Ahmad ne yasa ta fadin ke dashi ne kuke fada Ko.
Yarima Ahmad zama yayi kusa da Mamy tareda cire hulan kan sa yace wallahi Mamy yarinyar n'a n taraina ni dayawa kiringa bani daman ina dan casa t'a.
Mamy rike da baki tace chabdi Amma d'ai wuyan ka yayi kauri duka da nawa ka girme ta.
Wai ma tukunna ma laifin me tayi maka ne..
Gyada kai khadija tayi tace atoh shine abunda ya kamata kiji.
Tana hararan sa ta kasan idanu.
Shiko cikin isa ya hada rai Alamun babu wasa cikin maganar sa.
Yace Mamy koda taré muka zo duniya nida ita dole ne fa in gayamata mata gaskiya.
Wayar ta nadauka wlh batada kawaye sai zallan Arna.
Whasap din ta nashiga bakiga irin fitsarrarun kawayen nata ba.
Cikin su harda wata wai ita salomon shegiyar kafura wanda rabin nonon ta awaje hoton data daura akan Dp din ta..
Gasu nan dayawa basai n'a fada.
Tashi yayi Daga zaune yana fuskan ta khadija cikin bacin rai yace wallahi Mamy wayar khadija bazan bata ba sai tayi hankali.
Boko hauka ne Ko wacce intazo da rashin kunyar ta sai ace ai yar Boko ce
Nidai bazan zuba idanu ba Allah ya gani hakkina n'a ne inkula da ita.
Samari m'a haka kowani kare yanada nombar ta.
Kai har m'a kawayen ta musulman bakiga fitsarrarun da take hulda dasu ba.
Nidai banaso banaso banaso yakarashe zancen kamar ze take khadija da kafafun sa wanda haka yasa aguje ta Haye gadon....

Mamy cikin sanyin jiki tace yi hakuri baba n'a kanada gaskiya kanwar kace kanada iko akan ta '' fuskantar khadija cikin bacin rai tace baki isa indaura akan hanya madaidaiciya ba wasu Arna da fitsarraun yaran musulmai susa ki kauce hanya ba..
Ki nutsu ki maida hankalin ki akan karatun ki.
Jiki magayi bazan kara hanashi ba inhar zebuge ki yana son ki bakowani dan uwa bane yake kula da sa'idanu akan dan uwan sa ba.
Wasu inkinga sunyi magana sai ta baci.
Khadija kuka take Daga zaunen.
Ahmad da kukan ta yana kara hasala shi yace Mamy da kinbarni n'a dan gyara ta koda n'a minti daya ne kinga ai tayi kukan da hujja Ko..
Mamy tace A'a kyaleta ai akwai gaba inhar bata gyara ba kayi mata yanda kaso.
Kara zama yayi kusa da Mamy yace yawwa Mamy Samad yakusa zuwa naga ana ta shirye shirye har katuna aka buga n'a ganarumin taro da za'ai n'a auren Samad.
Mamy Murmushi tayi tace to nacewa Mai martaba basai anyi ba tunda amma yace Sam ba wannan zancen dole ne yayi cewar shi jikan Fari abun soyuwar sa.
Ahmad yace oho kenan in mune baze mana wannan gatan ba.
Mamy tace ina zan sani kana iya zuwa fadar shi ka tambaye shi.
Ahmad Murmushi yayi yace ayi Samad ne kadai yake shiga fadar sa batareda anyi masa iso ba.
Mune aka raina Ko tonima auren nan zan nema gaskiya dan kada mu rasa gatan da ake yiwa masu auren.
Jin muryan khadija yayi Daga bayan sa cen karshen gado tace uhmm wace mata ce zata aure ka saidai à rashin Sani.
Juyowa yayi yana kallon ta yace idan n'a kawo ta ki hanata zama yar rainin wayau ai Saboda ke zan siye bulala n'a ajiye.
Tashi yayi Jin wayar sa na ring yace Mamy zanje indawo Daga haka yafice cikin tafiyar sa mai daukan hankalin yan mata..
Yana fita Mamy ta fuskanci khadija tace kinga banason kina masa rashin kunya kinsan dan yana ganina ne yake shanye wani abun ''badai kin rainasa ba ai ga uban gayyan nan zuwa zamu ga yanda zaku kare dashi kinsan halin sa babu sauki sai wajen Allah..
Khadija tace Mamy InshAllah zan canza kodan Mala'ikan mutuwa nan Yaya Samad..
Murmushi Mamy tayi tace Ko ke fa Dadina dake kina daukan shawara Allah Yayiwa Rayuwar ku Albarka da Ameen suka amsa atare.

______________________________

Karima à Nutse tayi aikin ta tagama tareda taimakon hassana sossai ta taya aiki sukai komai taré..
Hassana tace woww gaskiya dakin shugaban ki yahadu sai kace ba'a duniya ba Allah kasa ta Aljanna tafi wannan haduwa.
Ameen Karima ta amsa tana dariya tace ai Samad ne fa uban gidan n'awa n'a daban ne antina..
Chapter 53 · 0% Book details