← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 115

Sashe 88

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zama yayi bakin gado yana tuna irin Alkhairan sheik gashi faran daya yabashi mata ya karba batareda ya musa....

Dattijo ne ya shigo bakin sa dauke da sallama yana sanye cikin farar shadda..

Kansa aduke yace shugaban Adalai Barka da wannan lokacin..

Kai muke jira mu tafi..
Baba Salihu cike da farin ciki yake kallon dattijon yace uhmm kaga wannan Aminin nawa sheik Abdurrazak bansan da wani kalma zan gode masa ba...

Matar da takeso taje har gidan mu tana bincike dan sanin sirrina shine naga gaskiya taje tabinciko sirrin namu bata aure ni ba nasan yadawa zatayi duk da babu rashin gaskiya a tattare da hakan...

Shiyasa na zabi in hada ta da sheik in kanta n'a rawa ne ze sata ahanya..
Kuma naji mijin nata marigayi mutum kirki ne...
Kuma itama an shede ta shiyasa banyi kasa a gwiwa ba..

Banson nayiwa Habiba kishiya '' shima sheik dan ya tara biyu ne shiyasa zankara masa da daya ya iya rikon gida...

Niko fa Inde akan mamy ne bazan iya yiwa wata matar Adalci ba...

Sossai Dattijo ya jinjina bayanan baba salihu yace shugaba n'a maganar ka dutse....

Shi aure anayin sa ne inhar mutum zeyi Adalci tunda ka nuna hada mata biyu anan zaka gaza dole ne ka janye...

Uhmm yawwa kagane nufina tashi yayi Daga zaunen babu bata lokaci suka fito Daga gidan....

Koda suka isa aka kai goron baba Salihu yace uhmm Nine zankai Amarya garin kano '' bikin nake jira sanna in tafi...

Sossai suka yaba da halin mutuntaka irin n'a sarkin adalai.....

Baba Salihu sanarwa sheik labarin yanda akayi komai yayi sossai sheik yaji dadi taré da masa Albishir tunda Amarya zata taré zasu koma sabon gida...

Yanacen anata gyare gyare Daga haka sukayi sallama....

Shiko Sheik cikin hanzarin sa yasa aka gyarawa anty dakin nata da yayi kura komai aka gyara mata tsaf har tukwane saida yasa duk aka wanke mata su....

Mama dake kallon shiga da fitar sa tace uhmm mijin tace anata hidima gimbiya zata iso....

Cak sheik ya tsaya yana jinjina kalaman ta...
Waigowa yayi tareda isowa kusa da ita yace...

Ai ban girma ne kazama matar ka duk abunda tace shi zakayi wannan ba haramun bane dan ance min mijin tace....

Dan bakiyi karyaba sai abunda tace shinakeyi nima sai abunda nace shi take yi kinga ita matar nace take nikuma mijin tace ya kike ganin sunan yada ce d'amu Ko....

Yar uwar ki zata zo amma kinkasa tsinana mata komai dan bakin hali..
Da kaina zan shiga kitchen indaura masu girkin Ko inkira kanwar Asiya '' tazo ta dafa musu koda taliya ce dadin abun harda yar ki acikin su.....

Kwabe baki Mama tayi tace uhmm yata tana ciki n'amata girki ita da Asiya wannan bakar Aljanar ka itace bazata ci ba..

Alhmdulilah ya furta tunda ita bakar Aljana ce ke kuma bakar zunubi Ko..
Ba girmana bane in tsaya ina biye miki ba...

Amma kisani wallahi Aisha n'a gaji da halin ki.....
Nagaji shiyasa nakosa wannan Amaryan da zanyi Sa'adatu tasamu abokiyar shawara da sauran su wacce zasuyi taimakeni in taimakeki bawai zaman dutse irin naki ba....

Ran Mama yayi mugun baci waini yau Sheik yake fadawa bakaken maganganu...

Wuce ta yayi domin shirya dan jirgin su Ànty n'a gab da karasowa..

Wayar Mama ce ta soma. Ring tana dubawa taga bakuwar lamba ce kuma ta kwatano shiyasa bata ki dagawa ba.....

Dagacen bangaren cike da murna harda buga uban tsalle adaki bakin ta awashe tace wayyo Mama n'a '' Rahama ce....

Mama kallon wayar taki da kyau Jin dai ba Mafarki take ba..

Tace Rahama yau kece kike kirana dan kinga anty taki ta baro kasar Ko....

Nan da nan jikin Rahama yayi mugun sanyin cikin kasa da Murya tace mahaifiya ta kodaya karkiyi fushi dani wallahi tunda nazo kasar banda layi sai yau nasamu...
Ki tambayi Abby ran nan ma da yake son magana dani kiran Abdul Samad yayi ya hadashi dani...

Haba Mama kinsan in inada waya da layi bazanki nemar ki ba....
Kece uwa ta karki yi fushi dani dan Allah...

Mama cikin Jin dadin kalaman Rahama tace uhmm n'a zata kin canza uwa ne...

A'a Mama banda kamar ki aduk duniya dagake sai Abby sai Ànty n'a...

Jin ta Ambaci Ànty nan da nan hannurin dake kwance kan fuskar mama ya bace bat...

Tace dan uban ki meye n'a kawo zancen Sa'adatu agabana...

Rahma sossai takejin haushin Rashin kaunar da mama ke nunawa Ànty '' ba'a canza uwa ne data canza haka zuciyar ta ke raya mata....

Afili kuma hakuri tashiga bawa Mama tace ina yaya Abubakar yake ne tasan intace ina Abdul jalil yanzu zancen ze lalace...

Mama tace yana lafiya lau nayi kewar ki yata tun ranar da kuka zo Asibiti duba Salma keda mijin naki bankara sanyaki a idanuna ba...

Rahama cike da bukatuwa ganin uwar ta tace InshAllah mun kusa zuwa zanzo gida inyi kwanaki Mama n'a..

Sun taba hira sossai Rahama taba Mama labarin su Mamy sossai Mama taji dadin karamci n'a Mamy tace Rahama ta turo mata lambar Mamy d'ana Samad '' 'babu bata lokaci Rahama ta tura mata Daga sukayi sallama....

Mama tabe baki tayi tace uhmm yata tana gidan daula' 'daman ba'a son ka fito gidan dadi kaje gidan wahala ba irin n'a Salma ba dole yau zamu rikita Al'amin......

*************************

Shiko Al'amin zaune yake gaban malamin nasa..
Yace malam inada mata ta amma n'alura sotake ta rabu dani..

Nikuma bangama latsar Zuman ta ba..

Malamin yace uhmm ai hâr mijin dazata aura sun fitar mata...
Amma mijin dan karya ne suka hada baki da Aminiyar uwar ta dan acuce ta yanda zasu samo kudi ta hannun su....

Al'amin jinjina Al'amarin yayi yace uhmm nidai gaskiya bazan sake ta...

Badai karyan Arziki takeso ba uhmm kwanan nan zan Faso gari wallahi zatayi mamaki Ko yanzu n'a fara samun kudi...

Malam yace yawwa kayi kokari kabar gidan da kake ciki kasamu miliyan daya kaba uwar ta..
Ita kuma yarinya basai n'a fada ba...

Karkayi wasa inhar kasan kanason ta...
Dan inhar baka nuna mata kudi masu yawa ba n'a tashin hankali ba akwai matsala....

Al'amin cike da yarda da shawaran da Aka bashi yace InshAllah zangwada

Sai kusan karfe daya jirgin su Asiya yasauka a babban filin airport n'a kano....

Sheik da kan sa yaje dauko su Ànty tareda drever kasancewa Abubakar baya zama gida Ayyuka sun masa yawa shike kula da komai n'a baban sa.....

Cike da jindadi ya tarosu yana ganin sun sauka a jirgi...

Ànty sai Washe baki take taga mijin nata shima din murna agun sa baya misaltuwa yau gashi ga sanyin zuciyar shi...

Basu bata lokaci ba suka shige mota direct gida suka zarce...

Asiya cike da gajiya tace nikam nayi gidan mu..
Sheik yace A'a babu inda zakije kin dawo da zama agidan nan bakisan mun bayar da auren ki ba...

Gab gab haka zuciyar Asiya yashiga dukan uku uku....
Dago kai tayi tana kallon Sheik dake kokarin shigar da kayan su dakin Ànty...

Ita Ko Salma dakin mama ta tafi cike da takaicin wannan rashin nasara data samu.......

Ita Ko Asiya Mutuwar tsaye tayi tana kallon Sheik dake fira da Ànty yana bude mata kulolin abincin da Aka aiko Daga gidan Asiya....

Mama
nunawa tayi batasan da zaman anty ba bare tayi mata barka da isowa

Ànty tana gama shirya kayan su ta tashi ta nufi dakin mama cike da ladabi tace Maman Salma mun dawo...

Mama tabe baki tayi tace uhmm nasan kindawo to Barkan ki.....

Ànty tace yawwa godiya nake..
Tareda komawa dakin nata.....

*************************

Bayan kwana uku rayuwa nata tafiya yanda akeso...

Al'amin yazo da niyar daukar Salma su tafi '' Mama ta bata wani kullin magani da zata shaka miki inhar yazo...

Cike da hanzarin taje ta tarbeshi har tana wani shafa shi '' lura da bayanin da malamin yayi masa yasa yafara ja da baya baya.

Ita Ko tana kokarin ta kamo shi..
Yana zille mata.....
Ganin akwai abu a hannun ta hakan yasa yakama hannun nata ya murda saida ta saki kara dan Azaba yace uhmm wallahi baki isa yau dinnan zaki zo Muje sabon gidan mu...

Yarfe hannayen ta takeyi cike da Azaba tace ahaka zanbika..
Babu inda zanje ka kama kanka...

Yayi daidai da shigowar Abubakar daidai wajen nasu ya tsaya yana kallon yanda Salma ke rashin kunya....

Cike da mamaki ya daka mata tsawa tareda kai hannu ya wanke ta da mari.. Cikin fada yace mijin ki yawuce raini Ko bakisan girman miji bane...
Wannan ba tarbiyyan gidan mu bane..

Kallon sa ya maida akan Al'amin yace kayi hakuri kadawo anjima da anyi lasa'ar kadauki matar ka.
Ku tafi..

Al'amin cike da Jin dadi yace yaya Abu nagode Allah yasaka da Alkhairi....

Itako Salma sossai marin da yayan ta yayi mata yayi mata zafi..

Yana shiga cikin gidan ya iske Mama da sheik zaune a dakin nasa.
Da Alamun korafi take masa akan wannan auren da zeyi '' shikuma sai fadi yake mata sunyi yawa dole ayi ta rage su...?

Mama tace wai wannan matar à ina take ne..
Yace Gabon

Girgiza kai tayi tace wani munafuki ne yahada wannan auren '' dan nasan baka zuwa nema '' saide abika dashi....

Kokarin bata Amsa yake ganin Abubakar yashigo yasa shi yin shiru '' dan yanzu soyake ya kora mama makarfi '' tunanin mahaifin nasu yake '' yaki bashi daman ya koya mata hankali ta hanyar tura ta makarfi tayi koda shekara daya ne...

Abubakar da ransa yake abace yace Abby wallahi Salma batasan darajan aure ba..
Kaga yanda take zagin mijin ta Shiko yana tsaye yana kallon ta....

Ran sheik yakai kololuwa wajen baci hakan yasa miki tsaye cikin zafin nama yabar dakin..
Koda ya isa zaunen be iske su Salma ba.....

Cikin gidan yakoma tareda zuwa dakin su Salman iske ta yayi zaune zata bude data....

Dago kai azabure tayi ganin yanda...........

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:54 - Nuriyyat: KANWATA

Littafin nan kudi ne Inkin ganshi a wajen group dîna na sata ne
Inkina bukata ga nomba
09069080725

8️⃣4️⃣

Dago kai Azabure tayi ganin yanda yake kokarin kai mata mari...

Cikin gigita tace Abby lafiya kuwa...
Chapter 88 · 0% Book details