← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 115

Sashe 109

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamy wani wawan runguma tayi masa Sam bata damu da wayanda ke wajen ba..
Ta kara kankame shi '' tana fadin ya Allah Ya Allah kai kace mu rokeka mun roka ka Amsa mana Allah nayi Al'kawarin zanyi Azumin sati daya bisa godiya akan ni'imar da kamin ka dawo min da mijina cikin koshin lafiya...
Kukan nata sossai yake shiga jikin sa 'Jin kukan yake kamar irin wacce aka t'aso mata cutar data dade da kwanciya..
Shafa fuskar ta yayi yana goge mata hawaye.
Yace Habiba yau gaki ga Salihu' 'nima yau gani ga Habiba..
Ganin sun kasa barin junan su Yarima yazo wajen yana fadin to yakamata mu wuce gida..
Mai Martaba yace Salihu kazo mu zauna mota daya...
Abban Marwan da yayi Mutuwar tsaye yana kallon yayan nasa' 'shima aguje ya rungume sa..
Yarima Samad yace Ah Ah mai Martaba mota daya Abban mu da Mamy zasu zauna kajira Muje masarautar sai kayi yanda kake so dashi...
Mai Martaba murmushi yayi yace anyi mai wuyan ai Muje kawai...
Babu bata lokaci suka fara kokarin barin filin airport din..
Sécurité nan da nan suka budewa Mamy da Shugaban Adalai mota suka Shiga.
Mai martaba shima yashiga tashi motar tareda mataimakan sa.....
Yarima da tawagarsa motoci duk suka kwashe su...
Inda Asiya da Rahama da Karima da hauwa 'mama firdausi kusan motocin su nabin juna..
Saratu kuwa tana cikin motar Yusuf Sani yaro.
Tareda matar sa.
Babu bata lokaci motocin nasu suka baro airport din direct Masarautar gheuzo ta nufa...
Baba Salihu rike da hannun Mamy wacce suke sauke ajiyan zuciyoyi kusan a tare..
Kan su isa Masarautar labari ya isa gabadaya jahar Sarkin Adalai ya bayyana.
Dayawa barin Ayyukan su sukayi dan zuwa ganin tabbacin maganar da ake yayatawa à gari.
Wasu har garin da suke suka baro suna hanya 'gani suke motar tasu baya gudu yanda yakamata....
Babban Al'ajabi hatta gwanoni n'a kasar duk sun turo mataimakan su dan su tabbatar da gaskiyar lamarin....
Mataimakin shugaban kasar kwatano duk sun hallara Saboda suna ta wasi wasi anya za'a sake ganin wannan shugaba Adalin.
Ministoci kuwa 'kam ba'a cewa komai sunce sai sun ganewa Idanun su abunda ke wakana...
Koda motocin nasu ya kunno kai Alayin tareda bata kara piiiii da karfi alamun abasu hanya..
Saboda cinkoso kai kace ranar Sallah Idi ce.
Motocin nasu gabadaya sukaja birki kasantuwa babu hanya..
Yusuf Sani Yaro sai kallo yake anata fama dasu akan su bada hanya sun tsaya suna yan surutai wai su kanun labari suke nema.....
Ransa amatukar bace yafito bakin sa na rawa cikin kakkausar Murya yace inna kirga daya biyu zuwa biyar baku bude mana hanya ba....
Uhmm dukan ku saina ankwashe ku..
Bekarasa fadin abunda ze fada ba kowa wajen ya matsa Daga gefen titi kallo daya sukayi masa suka gane koshi waye basai sun bari ya tabbatar musu da ainihin sa ba.....
Ganin anabasu hanya nan da nan suka karasa shiga layin cikin kalilan lokaci suka isa Masarautar dake cike makil da jama'a hatta bayi duk sun jeru kamar an saka su...
Koda suka fiffito Daga motocin nasu..
Gabadaya wajen suka fara kabbara suna Fadin ALLAHU Akbar.
Shugaban Adalai karasowa cikin jama'ar sa yayi yana Daga musu hannu alamun Jin dadin ganin su..
Bakin su narawa suka fara fadin Barka da zuwa Shugaban Adalai Sarki mai Adalci.
Sarki mai tausayin talaka.
Daga musu hannu yakeyi yana mai cigaba da tafiya tuni tawagar sa suka take masa baya...
Koda Mataimakan gwanoni suka karaso cikin masarautar.
Anan farfajiyar aka dakatar dasu..
Mai shigar da sako yace nasan Daga gwanati kuke shugaban Adalai ba daya yake da sauran sarakuna ba..
Yau yadawo yana bukatar hutu..
Kuna iya ajiye ranar da kuke son ganawa dashi asa sunan ku saman list..
Mataimakan sukace babu komai dan mu tabbatar ne kuma mun gansa da Idanun mu....

Kasa mana munason zantawa dashi tareda gwanoni nan da Sati daya kenan InshAllah...

Mai shigar da sako yan rubuce rubuce yayi yace InshAllah bakuda matsala..

Yan jaridu suka zo kan layi suma suna neman Alfarma a saka musu ranar da zasu gana dashi dan wannan sojan ya hana su rawan gaban hantsi...
Mai shigar da sako yace wannan kam sai shi da kansa inya yarda ze gana daku kunsan aikin tambayoyi ku dawo nan da kwana uku duk yanda yace zakuji....

Cen cikin Masarautar kai tsaye Fadar Sarki aka nufa duk suka zazzauna masu mamaki nayi 'masu murna bakin su yaki rufuwa..

Sarkin Adalai samun kujera yayi kusa dana baban sa..
Ya zauna' cike da nuna zallan farin cikin sa yafara yiwa Allah godiya daya kawo shi cikin Ahlin sa..
Kowa wajen sai Fadi suke Barka dazuwa shugaban Adalai Sarki me koyi da sunnah manzon Allah Saw.
Shigowar shugaban kasar niger ne yasashi fadada murmushin sa..
Koda ya shigo runguma yakaiwa baba Salihu harda guntun hawayen sa yace Ashe rai kan ga rai..
Shugaban Adalai yace kwarai kuwa gashi Allah yasa ke hadamu anan InshAllah har gidan Aljanna zamu ringa haduwa....
Cikin farin yace nagode sossai daka halarci bikin khadija..

Karka damu Shugaban Adalai Khadija yata ce 'naji dadin d'ana zo daukar iyalina kana garin' 'zuwa karfe bakwai zamu bar kasar nan n'a yamma....

Baba Salihu yace haba wani irin a yau dinnan zaka tafi nida nakeson ka kai jibi..

Kayi hakuri shugabana ina uzuriruka ne'.
Baba Salihu shiru yayi yana nazartan kalaman sa yace Amma bada Karima zakaje ba...

Kasaitaccen Murmushi yayi yace ai Karima yar ka ce inkace karta kara zuwa niger din ma na amince...

Ah Ah bama zan hana ta zuwa niger ba..
Nama ta miji anan garin kuma InshAllah nan bada jimawa ba za'ayi auren....
Sarki yace MashaAllah Salihu wani mai sa'a ne wannan ze auri Karima..

Faruk shine mijin d'ana zaba mata.
Shikuma Aminu zan bashi hauwa..
Marwan daman yanada wacce yakeso n'a samu labari komai n'a tsara yanda ze tafi...

MashaAllah MashaAllah kowa yaringa Fadi awajen...
Cike da murnan dawowar 'Mamy dake gefe suna sauraren abunda yake fade cikin cire kunya tace Shugaban Adalai yakamata kaje daga ciki kasamu Ko wanka kayi....

Gabadaya kowa dawo da kallon à kanta sukayi..
Mama Karama data rungumi Baba Salihu tana kukan farin ciki tace d'ana tashi kaje kaji abunda matar ka tace..
Sossai wajen sun Fahimci Mamy tanason kadaita da mijin nata.
Kuma sunsan tanada gaskiya shekara da shekaru 'kowa keda bukatar haka amma suka d'Anne sun San nata dalilin yafi nasu karfi.....

Faruk cike dajin dadi anbashi Karima yafara godiya awajen shida Aminu...
Marwan yace wayyo Ashe nakusa zama ango nima..
Kusan kowa dariya yasa..
Ita Ko Karima cike da Jin kunya taje ta rike hannun Abban ta ''tace baba n'a Allah yayi zamu gana dan Allah kabari zuwa gobe da safe saiku tafi tunda badani za'a je ba....
Cike da gamsuwa yace naji daman n'a janye tunda naga shugaba n'a bayaso..
Sossai suka d'ara Jin furucin sa.

Sarki ne yayi gyaran Murya yace tunda Dana yadawo ni Daga yau zan ajiye mulkin..
Azabure baba Salihu ya kalle sa yace Ah Ah banaso tun Farko ma tursasani akayi n'a hau karagan mulkin nan yanzu kuma ataimaka a barni inzauna normal kamar kowa....

Wajen gabadaya suka cika da tashin hankalin Furucin nasa akan bayason Mulkin...
Gabadaya wajen kuka suka soma sukace Ranka ya dade muna murna mun ganka kuma zaka yanke mana kauna da irin mulkin ka mai cike da abin burgewa...

Dan Allah kataimaka kacigaba da Mulkin nan mun rokeka...
Idanun Baba Salihu kadawa yayi jajir yace inhar kuka cigaba da takura mun akan wannan Mulkin zan bar kasar nan..
Saidai Aba Yarima Samad duk abunda zan iya shima ze iya nasani ne...

ZUMBUR Yarima ya tashi yana haki cikin zallan tsoro da Fargaba yace Ah Ah wallahi banaso banaso '' daukar takalman sa yayi a hannun sa yabar Fadar cikin hanzari..

Da mamaki ake kallon yanda uba da dansa suke gudun Mulkin nan.....
Sarki yace karku damu zamuyi zama n'a mussaman akan haka..

Sannan Aje araba abinci ciki da waje dan murna dawowar d'ana kafun ranar da za'ayi bikin dawowar sa...

Mama Firdausi tace Sarki me Ran karfe ga Amaryan Ahmad nan munzo da ita..
Hakan yasa yadawo da kallon sa akan Asiya da kanta ke a duke yace MashaAllah MashaAllah..
Aje afiddo Khadija.
Kuma a kira mijin nata Adamu....
Akira mahaifan sa...
Kai kuma Ahmad saika zauna anan za'ayi komai agama asamu akai Amarya dakin nata tahuta..

Ahmad yace kwarai kuwa d'an kowa ya tara gajiya Tsoho..
Mamy tace uhmm nizan shige ciki.
Mama Firdausi tace haba ki tsaya inace tare keda Shugaban Adalai zaku shiga ciki..

Babu bata lokaci à kazo da khadija 'Adamu da iyayen sa cikin hanzari suka karaso falon..
Aguje khadija taje ta rungumi Abban ta tana kuka cikin Rawar murya tace Abba n'a kai nake gani koko idanu n'a ne ke min gizo....
Murmushi yayi tareda dagota yana kallon fuskar ta data sha makeup sumbata yakai mata a goshi yace yar auta ta.
Ni dinne kike gani nayi kewar ki sossai '.
Baki yaki rufuwa gun dijat dan murna hakan yasa tafara kukan farin ciki tace nagode Allah da ban bar kasar nan ba Sannan ka bayyana ba...
Baba Salihu yace yata kin kara girma sossai hankali yazo MashaAllah....
Zaunar dasu yayi yaringa musu Adua zaman lafiya taré yake da gajiya tattare dashi hakan yasa ya Mike dan tafiya sashin nasa....

Ambassador yace MashaAllah Sarki ina tayaka murnan bayyanar wannan babban Arzikin.
Sossai suka zauna tareda Abban Karima sukayi lifaya da ciye ciye dan murnan babban rana...

Mamy kusan taré suka bar Fadar itada mijin nata..
Mama firdausi da yan uwa da Abokan Arziki suka zaga da Asiya cikin masarautar ''...
Kowa nata sa mata Albarka da yaba kyawun ta.....
Ahmad yace Ah yakamata taje tagaishe da Mama Fulani...
Kai tsaye sashin gidan yari suka nufa...

Koda suka iso 'sun iske Fulani zaune tana Aman jini..
Cikin tashin hankali sukace lafiya kuwa..
Bakida lafiya ne...
Chapter 109 · 0% Book details