← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 115

Sashe 16

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shirune yabiyo baya.
.
Daddy yace nasan bakasanni ba '
Girgiza kai sheik yayi alamun hakane hankalin sa da nutsuwar sa yamaida kan zancen Daddy.

Daddy ya ce suna n'a Dr Abdullahi Auwal ambassador libya ne ni.

Ina zaune à katsina nida iyalina.
Dana Adamu nan yake bautan kasa.

Har Allah yahadashi da yar ka.

Amma cemana yayi wai kayi mata miji.

Bayanin abunda yasamu Adamsy ya bashi da dalili zuwan su kanon.

Sheik Girgiza kai yakeyi har Daddy yakai karshen zancen sa.

Gyaran murya yayi yace a gaskiya n'a tausayawa halin da adamu yashiga akan yata.
Ina me baku hakuri dan Allah.

Akwai wani dattijon Arziki salihu wanda ta dalili sa ne yau nake zaune cikin gidan nan 'duk dai baibasu labari tsakanin su.
Amma yanuna masa baba salihu ya taka rawar gani acikin rayuwar sa.

Shiyasa beki amince wa wajen bawa dan sa auren Rahama da zeyiba.

Iname baku hakuri nariga nayi Alkawari kuma harya tafi garin n'a su dan bikin nan tareda dansa zasu dawo.

Mommy tace Allah gafarta malam yarka ance tana son Adamsy wanda zaka ba Beko taba ganin Rahama ba itama bata sanshi ba.

Yin haka sainake ganin kamar cutar da zukata ne.
Adai duba lamarin nan
Harda sheshekar kukan ta.

Sheik ya numfasa tareda Maida kallon sa akan ta.
Yace biki saura sati biyo kikeson à fasa amaida kan dan ki ?

Yin haka babu son kai aciki kuwa.
Daddy yace babu son kai saidai taimakawa yaran zamuyi.

Sheik rasa me zecemusu yake gashi yana musu kallon mutane masu kamala.

Yace in babu laifi akwai kanwar ta Salma tacemin shi takeso me ze hana amaida auren akan ta.

Cikin kuka Adam yace sheik ni babu soyayya tsakanina da salma kanwa n'a dauketa.

Amma ina neman wata Alfarma sheik guda daya dan Allah.
Sheik yace inajin ka Allah yasa zan iya.

Inhar baba salihu be dawowa ba ana bikin saura kwana uku zaka Maida auren akaina.

Sheik yace n'a amince dan yasan baba salihu befi nan da kwana uku yadawo ba.

Cike da mutuntaka Suka bar gidan suna yaba hankali da dabarun sarrafa harshe da magana cikin hikima irin ta sheik.

.......

Bayan sati daya

Kasar Ghana

Baba salihu à kasar Ghana wani babban hôtel yakama nan yake kwana

Hôtel din da sai yayan sarauta kadai ne sauka ciki.

Motar dayake hawa mercendez bakaramin kyau yayi ba dan Sam bazaka taba ganeshi ba.
Fatar shi tayi fresh hasken Fatar yafito sossai kana kallon sa zaka tsatsan kamannin da suke yi da yarima Samad.

Wani fili yaje du bawa inda zefara ginin gidan sa.
Tuni yabiya contrat din gidan.

Zaune yake cikin motar sa ya kunna kira à idanunsa à lumshe.

Tunowa yayi yaufa saura kwana bakwai bikin Rahama hankalin sa yayi mugun tashi.

Zuciyar sa n'a masa radadin bakin cikin da sheik zeji inbe ganshi yazo da Samad kuma bekara ganin sa ba.

Wayar sa yadauko kirar iPhone 13 max ya danna kira bugu biyu aka Daga

Dagacen bangaren yace ranka yadade ina nan ina bincike akan komi sannu à hankali zan kamala maka ayyukan ka.

A jiyar zuciya baba salihu yasauke yace bawanan ba ina Yarima Samad yake ne ?

Mutumin yabashi amsa muna nan tare dashi.

OK bude whsap dinka muyi magana yanzu.
Da to. Ya amsa masa tareda katse wayar.

Shiga whsap yayi ya rubuta masa sako kamar haka.

Gidan sheik Abdurrazak nakeson kuje akwai bikin yarsa da za'ayi gudummuwa zasu aika masa n'a million goma.

Da sunan tallafi ne Daga saudiya akabashi dan yayi zama à kasar kuma kada ka kuskura Yarima samad yagane komi tattare dakai.

Daga haka sukai sallama.

*****,********

Kasar kwatano

Maryam ce tazo gaida mamy Cike da farin cikin ganin t'a.

Mamy ta rungume ta yaushe rabo yata da gidan nan gaskiya nayi fushi tunda Samad ya tafi shikenan kikai mana yaji.

Cike da kunya tace haba mamy koba samad dole inzo 'zama sukayi suna hira yaushe gamo.
Khadija tashigo fuskar ta dauke da fara'a yau manya baki gare mu tana kallo Maryam.

Dake sakar mata murmushi ' mamy da kanta takawo mata lemun kwali da pepper soup din kaza.
Ta ce ajiye gabanta bismillah yata kuma surukata nan gaba InshAllah.

Kamshin abincin ya barade dakin gabadaya.
Cikin sakin jiki taringa ci.

Mamy tace bara inkira Mutumin ki.
Waiko kuna waya ke dashi kuwa.

Annuri dake kwance fuskar Maryam yadauke.

Mamy tace inajin ki kinyi ...........

Taku har kullum kyauta Daga Allah
3/20/22, 22:34 - A'ish: *🌟🌟 KANWATA🌟🌟*

Paid book ne

300 vip

500 spécial

Àcct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ko kuma Katin MTN
Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

2️⃣3️⃣

Asiya ta ce What
banganeba Rahama wai kina nufin har yanzu bedawo ba chabdi amma saina ke ganin da Adamsy akaba auren naki zefi kwanciyar hankali kinga yana mugun son ki.

Rahama kema kina son sa.
Ajiyar zuciya Rahama tasauke tace ni fa banda zabi wanda yawuce n'a iyayena komai sona da abu komai kin abu danakeyi.
Amma wlh Asiya da so samu ne in auri Adamsy.
Zuciyata tafi aminta dashi dari bisa dari.

Abba dake tsaye kofar dakin mama duk abunda suke fade akan kunnen sa.

Cike da tausayin Rahama yabar wajen.

Yana shiga dakin sa ya shiga nazarin yanda ze bullowa Al'amarin zuwa yanzu ya gama sarewa akan dawowar baba salihu.

Anty yakira awaya yacemata tazo dakin sa ta same shi 'babu bata lokaci sai gata tashi go sanye take da doguwar riga Atamfa takashe daurin dankwali sai kamshi take zubawa
Barka da warhaka baban Rahama.
Ta furta fuska a sake.

Fuskar sa babu walwala ya amsa mata.
Shigar ta bakaramin daukar hankalin sa yayi ba.

bata izinin zama yayi.

Zama sukai yana fuskantar ta yace nayi tunani akan Rahama nalura baba salihu ba dawowa zeyi ba.
Allah kadai muka barwa sanin gaibu.

Kuma kinga yarinyar nan ta mana biyayya akan amincewa zata auri dan baba salihu batareda ta san shi ba.

Nayanke shawarar bawa Adamsy auren Rahama koya kika gani ?

Ànty cikin murna tace wallahi ni hakan yayi min dadi sossai kaga ka taimakawa masoya.

Wani hanzari ba gudu ba koda Baba salihu yadawo zan ba dansa diyar Hassan kanina.

Shine kawai kwanciyar hankali n'a kuma mutanen nan yanzu zankira su in sanar musu kawai su kawo sadaki n'a basu Rahama dan haka ki gaggayawa mutane makota araba alawa daurin aure ranar juma'a.

Itakuma salma nata me sauki ne dan saurayin da suke tanbadewa tare shi zan hadasu aure.
dan uban sa koyanaso Ko baya so saiya aure ta.

Cike da farinci ànty tace hakan ma yayi bara in tafi in sanar cikin gida.

Cike da farin ciki ànty taje tsakar gidan tanata guda.

Kowa saida yafito har bakin da suka fara zuwa Daga makarfi sun fito.

Mama tace wannan gudar fa n'a menene.

Salma tace uhmm tana murna ne Yar dakin ta zata auri dan me gadi.
Dariyan mugun ta tayi tana me kallon anti.

Maganar tayiwa Rahama da Asiya zafi aransu..

Ànty kara yin wani gudar tayi tace MashaAllah MashaAllah tana dafa Rahama tace congratulations my daughter tare da rungume ta sassanyan kiss tayi mata à goshi.

Tace yau Allah ya amshi rokona Rahama.

Mama da ranta yasoma baci tace to ai saiki fadi abun murnan muji.

Ànty tace nasan mama zakifi kowa farin ciki gashi yau Abba yaba Adamu auren Rahama.

Kwabe fuska mama tayi.
tace ba shakka abun farin ciki ne Allah yasa ayi damu Daga haka ta kama gaban ta.

Wani farin cikine ya lullube kowa cikin gidan duk wanda yasan shakuwar Rahama da Adamsy yasan akwai tsantsar soyayya.
Rahama kasa boye farin cikin ta tayi dukawa kasa tayi tayiwa Allah sujjada.
Tareda dago kai gaban kowa tace Allah ina godiya agareka.

Rungumar ànty Tayi tana murnan farin ciki.

Salma tunda taji maganar wai Adamsy ne ze auri Rahama hankalin t'a yayi mugun tashi.

Kasa tsayuwa tayi cikin kuka tashige daki ta danne kanta da filo tana kuka mai taba zuciya.

Rahama ta lura da yanayin salma sai taji tausayin ta yakamata bin bayan ta tayi.

Ta iske ta tanata rusa uban kuka jiki asanyaye ta Haye gadon jawota tayi salma n'a turjewa.

Cikin yanayin damuwa Rahama tace salma ke kadai ce kanwata ya mace pls meyasa bazaki soni ba koda kadan ne wlh salma inason ki fiye da komai banda iyayena.
Banda kamarki.

Salma dago kai tayi tana me Jin tsanar Rahama nakara ruruwa acikin zuciyar ta.

A fili murmushi mai kama da ciwo tayi tace ayya kukan da nake kaina ke min ciwo karkiyi tunanin wani abu cen kasan ranta tana ayyana yanda zata tozarta Rahama à fili kuma murmushi yake tayi mata wanda hakan yasa Rahama Jin dadin sun fahimci juna itada kanwar ta.

Rahama n'a fita.
Salma hijab dinta tasaka ta bayan gida tafita batareda kowa yasani ba.

Direct gidan Amina taje ta iske ta awaje wani me mota yasauke ta.
Tana masa bye bye.

Aguje taje t'a rungumi Amina cikin kunan rai take bata labarin auren.

Amina tace zancen banza zancen wofi wai ina maganin da malam isa yabaki kinkoyi aiki dashi kuwa.

Salma Girgiza kai tayi Alamun A'a
Amina cikin fushi tace meyasa salma kodan bakisan zafin kudi bane.
Insa kudi masu yawa in biya miki dan biyan bukatun ki

Amma kika ajiye bakiyi ba yanzu me kike son inyi miki tana kallon salma ranta à bace.

Salma hakuri tasoma bata tace wlh dan naga Abba yace dan me gadi zata aura shiyasa banyi ba.
amma pls miye mafita karki manta yau saura kwana shidda naji Abba n'a cewa wai Al'amin ze aura min kijifa.
Tana yatsine fuska.

Ina aibazan iyaba dan ambassador zata aura fa nikuma in kare da yaron dako sana'a bashida shi.

Amina tace yanzu inbaki komi Muje gun malam isa.

Haka suka kwashi juna suka je malam isa yaba salma maganin da zatayi tozali da adamsy inhar suka hada idanu tabbas zeso ta inkuma be sota ba alokaci to duk abunda tafadamai akan Rahama ze yarda koda karya ne.

Murmushi kwance kan fuskar salma tace ai gwara mu rasa dukan mu wallahi itama anemi Ko me ga ruwa ne abata ta aura ehee tana hura hanci sama sama

Cike da Jin dadi suka baro wajen malam isa.
Chapter 16 · 0% Book details