← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 115

Sashe 73

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dawo da. Kallon tayi akan sa cikin kalan tausayi tace yanzu tunda kaga khadija tadawo nan sashina tare zanringa kwana da ita..
Wani kallo yake binta dashi masu cike da baki isa ba..
Yace uhmm Rahamatullah dauko hijab dinki mu. Tafi Saboda Sallah Asuba..
Rahama tace ya zanbar khadija ita kadai..
Uhmm nidai Muje yafada yana kokarin Jan hannun ta...
Ganin zata bata masa lokaci yasa hannayen sa ya dauke ta..
Sai zazzare idanu take tace Amjad meye hakane idan khadija ta gan mu ahaka fa girma yafadi...
Uhmm yace be bata Amsa ba kai tsaye dakin nashi yakai tareda sauke ta Akan gadon sa..

Yana ajiye ta yadawo tsakiyar dakin kokarin cire kayan jikin sa yake''ganin tana kallon sa yace bazaki tayani cirewa ba....

Kaida kasa abunka kaine kasan yanda zaka cire su takarashe zancen tareda Jan bargo zata lullube jikin ta...
Yarima beko tsaya sauraren ta ba..
Ya shiga yayi wanka yana fitowa Daga shi sai boxer gashin jikin sa luf suka kwanta Saboda damshin ruwa..

Bakin gadon n'asa yazauna tareda dauko wayar sa yana bin sakonni dake shigowa takan whsap din sa...

Duk sakon dayaga New number ne baya shiga ciki sai inhar yaga profile din wanda yasani ne...

Sakon ya shigo masa akan hassana dake gidan sarauta ba aiki yakaita ba....
Ta dalilin Salihu Turaki tazo dan tasan sirrin sa...
Kuma son Salihu Turaki take dan har haduwa suke yi...
Kallon number data turo masa sakon yayi yaga nomber Gabon ce...

Shiga cikin message d'in yayi yana kara karanta wannan sakon...
Maganar zuci yake yace eh tabbas tace Gabon take inhar mutumin n'an dayayi masa magana yanada.masaniya akan hassana Kenan yasan inda Shugaban Adalai..
Batareda yabashi Amsa ba ya kashe datar sa..
Tagumi yayi Daga zaune yana nazarin yanda ze dauko lamarin da warware sa ganin babu mafita yasashi ajiye wayar gefen gadon nasa tareda jona ta a caji...

Kallon Rahama yake ji yasan ba barci take ba amma ta lumshe Idanun ta...
Hawa gadon yayi yana kokarin jawo ta jikin sa tareda kai hannun sa saman boob din ta...
Zumbur ta tashi tazauna cikin muryan wacce ke shirin kuka tace wayyo nace maka ban warke ba..

Tunda baki warke bara induba wajen ingani..
Ganin yana kokarin cire mata pant tarike masa hannun cikin tsoro tace haba Amjad kayi hakuri mana da wasa nake maka n'a warke..
Au kin warke kikace

Gyada masa kai tayi cikin Kosawa da tambayar sa..

Banyarda ba saina gani da idona..
Duk yanda taki yarda ta kasa kwatan kanta saida yakwantar da ita tareda duba wajen gani yayi kamar babu rauni tsabar raki ne ke damun ta.....

Dawo da kallon yayi akan ta ganin tarufe fuskar ta da pillow yasa shi murmusa.
Haba Amarya meye n'a Jin kunya Daga ina duba wajen kada asamu matsala kuma naga babu wata illa a wajen dan haka pls kidan bani inkara namiki Alkawari bazan wuce awa daya ba cikin marairaice fuska....
Rahama zazzare idanu tayi tasoma hawaye shar tace wayyo Allah Ànty ki taimakeni dan Allah kayi hakuri wallahi har yanzu ban koma daidai ba yanda take kukan iya gaskiyar ta yasa shi darawa yace ok kin amince Mala'ikun Rahama suyi ta tsine miki Albarka..

Zazzare idanu tasoma tace uhmm nidai bazasu tsinemun ba dan bada ganganci n'a hana ba...
Yanda take zaro zancen sossai ya shagala da kallon karamin bakin ta...
Hakan yasa shi lacuto bakin nata yana kokarin hade shi da nashi.

Yace uhmm amma dai zaki barni in rage zafi Ko dan dai. Gaskiya ban iya kwana hakanan..
Babu yanda ta iya duk yanda t'aso tayi barci Yarima yaki bata damar haka...
Sossai ya raya daren ba tareda ya kusance ta ba..
Tun tana kaucewa har ta biye masa...
Kusan karfe ukun d'are Sannan barci barawo yayi awon gaba dasu dukan su......

Asuba tagari

Kasar Gabon....

Karfe tara daidai jirgin sheik da Aminin sa ze tashi zuwa garin kano...

Tun karfe bakwai n'a safe yashirya tsaf komai nasu harda siyayyan da suka yi..
Sheik harda kayan baby masu kyau ya siya à cewar sa yayi kewar yan kananan baby yanzu gashi zesamu....

Texte din Ànty ne yashigo wayar sa yana dubawa yayi Murmushi yace madam kina raina..

Dagacen bangaren tace ya Abban Rahama dafatan kuna ta shirye shiryen koma.
To Allah yakaiku lafiya.
Damar so nake in rokeka wata Alfarma..

Jin ta ambaci Alfarma yasashi bata damar ta fadi abunda take bukata...
Ànty tace tunda muke dakai bantaba kawo maka wani abu sabanin hankalin ka ba..

Sheik yace Sa'adatu hakane zancen naki ki fadi kai tsaye Alfarma InshAllah zan miki..

Cike da tsoro da Fargaba tace inason dan Allah ka raba mana gida nida Maman Salma..
Cikin tsananin mamakin furucin ta yace to Saboda me Sa'adatu zan raba muku gida...

Ànty tashiga bashi labarin wayar da salma tayi da Mama agaban ta...
Numfashi ya fesar yana nazarin kalaman ta...
Yace yanzu watan cikin ki nawa ?
Wata hudu tabashi amsa tana mamakin meya kawo zancen ciki bayan ba maganar suke ba...

Sheik yace Sa'adatu kiyi hakuri kibari watan haihuwar ki nakamawa zan canza muku gida..
Amma kowa da part din sa..
Sai kunso zaku ga juna hakan yayi miki sabon gida sabon baby....

Sossai tayi dariya tace hakan yayi nagode da Fahimta.
Suna gama fira da Ànty...

Yakira Mama awaya cikin gadara tace harka iso ne...
Sheik yace babu zancen gaisuwa Ko Allah yakawo mu lafiya wai ke Aysha yaushe zakiyi hankali ne..
Bama wannan ba ina Abdul jalil yake..
Hankalin mama ya tashi Jin wannan tambayar inda inda tasoma tace yanzu yafita Daga gidan...
Sheik yace au sammako yayi kenan.
To ki aika akirawo shi yadawo gida yanzu nan..
Banson n'a iso ban same shi ba....
Mama rike da baki tace uhmm nasan Algunguma ta fadamai ne shine ze fake da siyasa...
Ni yanzu ma ina nasan yaron nan yakwana tashi tayi tadau hijab din ta..

Tana ta shiga makota cigiyar sa duk inda taje sai ace ba'a gan shi ba..

Cike da takaicin yaron tace amma dai wannan yaron mugun dan banzan yawo gare shi ace yau kwanan sa biyu be kwana gida cike da damuwa take bin layi kwararo neman sa duk inda taje sai a je ba'a gan sa ba....

Wayar tazare cikin jakar ta tashi ga kiran layin Abubakar.....

Har ta kusa tsinkewa ya Daga..
Cike da damuwa tace ABU wai ina Abdul Jalil tun shekaran jiya da safe bankara sashi a idanuna ba..
Abubakar dake tuki yace aikuwa gida yakwana jiya ma inaga sammako yayi nasan sai d'are kibari zan dubo shi kila yana gidan su Asiya ne..

Mama kwata kwata ta mance taje gidan su Asiya hakan yasa tayi hanyar gidan cikin hanzarin ta isa gidan su Asiya....
Bakin ta dauke da Sallama..

Maman Asiya hajiya hussaina cikin washe baki har fararen hakoran ta dake dauke da hakorin makkah suka bayyana...

Cikin sakin Fuska tace Maman Salma yau kece agidan namu lale lale..
Mama cikin tabe baki tace eh Nice dafatan dai kuna lafiya..
Lafiya lau tabata amsa tace mu shiga Daga ciki mana...

Mama tace Ah ah basai na shiga ba akan hanya nake.
Abdul Jalil nake nema Ko yazo gidan nan kuwa...

Maman Asiya tace yana ciki kamar Abinci yake ci..

Maman Ranta dubu yabaci cikin d'Anne fushin ta tace Ayya idan yagama yazo gida ya sameni yau baban su ze dawo....takarashe zancen tareda juyawa...

Ita Ko Maman Asiya da mamaki take kallon ta tace uhmm haryanzu dai Aishatu kinki canza halin ki.

Mijin ki ma beji dadin ki ba bare yaya bare makota uhmm Allah yasa ki gane takarashe zancen tana karkada kai tareda shiga dakin ta iske Abdul Jalil harya gama cin abinci duk hirar da suke yana jinsu...
Kallon Maman Asiya yayi yace nasan Abba yau zedawo bara inje inshirya indan gyara masa daki...

Maman Asiya tace to kadaiyi hakuri duk abunda zatayi maka.
KADA kai yayi yace babu damuwa.....

Wajen karfe daya n'a Rana su sheik suka iso garin Kano...
Abubakar ne yaje yadauko su yasauke Aminin sheik agidan sa..
Shi kuma sukayi nasu gidan kai tsaye.....

Sheik cike da hamdala yace Allah yayi mun dawo kasar tamu..
Abubakar dake tuki yace Abba da bakanan kaida Ànty gidan babu dadi...

Murmushi sheik yayi yace to ina maman taka take bata tayaka hira ne..

Tana yi yabashi amsa atakaice yana cigaba da tukin nasa....

Kano

Tunda sassafe Fulani tashirya tsaf cikin shigar ta na Alfarma hannun ta rike da wata bakar leda mai cike da mugun sirri da bokan ta ya aiko mata
Cike da izza da takama take taka kasa iya Firdausi tana bayan ta sai kirari take zuba mata...

Barka da Fitowa gimbiya Fulani takawan ki lafiya uwargida agun Sani Turaki.
Ba gaba da gaba ba kota baya sai anshirya shuga ta...
Kasaitaccen Murmushi tayi tana cigaba da takun ta izuwa Sashin Yarima.
Har ta kusa kai kofa taji muryan Karima n'a fadin..

Gimbiya Fulani dakata !
Cak Fulani ta tsaya cikin tsananin mamaki ta wai..................

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:52 - Nuriyyat: 7️⃣3️⃣

Cikin tsananin mamaki ta wai ga tana kallon Karima..
Dake kokarin isowa gareta kan aduke tace.

Gimbiya Fulani Yarima yasa doka hana kowa shiga Sashin nasa saida izinin sa....

Wani kallo mai wuyar fassara Fulani ke jifan Karima dashi cikin tsananin bacin rai tace ke shasha dabba karya mara hankali kaskantaciyyar baiwa har kin isa ki gayamin doka bayan mune masu bada doka da oder to bari kiji ingayamiki badai takamar ki Yarima ba to zansa asauke ki Daga kan mukamin ki.
Zaki shigo cen cikin bayi kina aiki..
Shasha dan Allah matsa kiban hanya maza kisa key ki bude mun...

Karima dukar da kanta kasa tayi tace ina kara baki hakuri Gimbiya bazan iya bude miki kofar nan ba...

Iya Firdausi dake bayan su cikin tsoron abunda zeje yadawo tace haba Karima Gimbiya Fulani ce gaban ki......yakamata ki gyara kalaman ki..

Karima cikin karfin hali tace mama nasani kawaide bazan iya budewa bane...
Chapter 73 · 0% Book details