← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 115

Sashe 42

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zazzakar muryan ta yaji tana fadin eh kallo nake sannun ku da zuwa ya gajiya tana magana hankalin ta nakan TV.
Aminu yace kalau muka dawo Madam Samad.
Yarima Samad tsaye yake kasa zaune danna wayar sa yakeyi.
Wayar sa yafara ring ganin Maman Maryam yasa yadaga babu bata lokaci.
Cike da nutsuwa yake yake gaishe ta yace ummy kina araina ya kike ya mutan gida ina Abban maryam yake da makawfta duk ya jero mata tambaya.
Dagacen bangaren Murmushi tayi tana zaune kan kujerar mulki tace kowa n'a lafiya lau Abdul Samad amma baka tambayi Maryam ba.
Ransa ne yabaci saiya dake yace kash narigaki a zuci kin rigani abaki.
Aidole in tambayi yar kanwata mana.
Dafatan tana lafiya Ko tareda neman guri yazauna kan kujera 1str hankalin sa nakan TV.
Maman Maryam tace tana lafiya lau saide bata gida taje unguwa inta dawo zan hadaku waya.
OK toh yabata amsa dan abar zancen.
Maman Maryam tace D'ana.
Naam ya bata Amsa tareda maida hankalin sa kan wayar dasukeyi.
Maman Maryam cikin iya bariki tace daman sonake ince maka ina Matar taka take ka hadani da ita mugaisa mana wai ita bata tambayar d'angin mijin ta ne koko feleke ta iya.
Murmushi yayi saida kucin sa ya lotsa yace kiyi hakuri zata San ku ne wataran.
Dagacen bangaren maman maryam tace Samad bangane zata san mu wataran ba ina matsayin uwar mijin ta.
Shiyasa auren yayan Malamai wallahi matsala ne kardai ta shanye maka kurwa.
Samad Murmushi kwance akan fuskar shi yace babu kodaya ummy n'a InshAllah zan gyara kokarin katse hiran yake dan shi kwata kwata beson korafi.
Uhmmm Ummy n'a inbazaki damu ba anjima zankiraki yanzu fita zanyi ne yana kallon agogon hannun sa.
Maman Maryam ta hada rai sossai kamar yana gaban ta tayi tsaki amma beji ba.
Tace daman sonake kazo da Matar taka mu ganta tunda rowar ta kake mana Ko hoton ta bamudashi.
SAMAD YACE Ummy n'a ina me baki hakuri bazan zo da ita kwatano ba.
Saboda auren nan dai Auren biyayya ne ''.
Kallon Rahama yake wanda shi take kallo itama tana jinjina kalaman auren biyayya daya furta...
.
Cigaba da magana yayi kinga bazan kawo ta cen kasar mu ba..
Harsai ta Mallaki hankalin kan ta.
Maman Maryam cikin fushi tace wani mallakan hankalin kai daya wuce auren ka da tayi.
Ai tasan komai kaine kake mata kallon yarinya.
Nidai ka taimaka inzaka zo shari'ar da za'ai nan da kwana shidda kuzo taré tunda ance befi kayi sati ba ka juya saiku juya tare dan Allah narokeka.
Tagama kashe masa jiki cikin Sanyi murya yace InshAllah zanzo da ita.
Sai dai bazan barta à kasar ba.
Cikin Jin dadi Maman Maryam tace eh kan yayi kaga zamu kulla zumunci.
Daga haka sukai Sallama.
Ita Ko Maman Maryam suna gama waya da Samad rawan murna take ta yi yar aikin ta tafito tana dariya tace maman mu abun farin ciki ne yasamu.
Cikin Jin Dadi tace eh wallahi kedai d'ana ne ze zo da Matar sa kinga dole in taka.
Yar aikin tace mama nima ina tayaki murna Daga hk tashige daki dan goge goge da mopin.

*************************

Yarima Samad yana gama wayar da Maman Maryam dakin sa ya nufa kai tsaye dan shiryawa zasuje yawon neman baban sa dakuma hoton Mafarkin sa.
Wanka yafito yana daure da towel iya kugun sa....
Gaban miroir yatafi yana kallon kansa a madubi tareda daukan mayukan sa masu dankaren kamshi ahankali yake shafawa ajikin sa.
Kallon jikin sa yake yanda Ko ina da gashi ne kwance luf luf gwanin ban sha'awa.
Sumar kansa yake kokarin tajewa dan yana dan tara su kadan.
Kallon kansa yake ta cikin madubi yace Uhmmm..
Bara inyi sauri n'a fita Ko Allah yasa mudace a yau dinnan.
Kayan da zesaka suna a gefen sa..
Wando Jean ne da riga maroon.
Saka kayan yayi bakaramin kyau yayi ba.
Shi kansa yasan yayi kyau hakan yasa yayi wa kansa selfie.
Yana daukar hoto yaji sallamar Rahama tashigo dakin.
Ko kallon inda take beyi ba yaci gaba da daukar hoton sa.
Cikin hanzari ya zura takalmin sa komboss tafiya yake cike da izza da takama.
Haryakai bakin kofa yaji muryan ta.
Tan'a fadin Abba n'a yace in gayamaka ba'a ga hoton nan ba amma yace da zaran angani za'a turo Abdul Jalil da sako.
Jimm yayi kamar me nazarin wani Abu..
Be bata Amsa ba yasakai yafi ce Daga dakin.
Itakuwa hakan be dame t'a ganin yanda ya bata dakin dan shigowan da yayi tace ikon Allah badai bata waje ba.
Jibi yanda ya hargitsa dakin nan kayan da yacire yanda ya watsar dasu a dakin take kallo da mamaki.
Cikin hanzarin ta tashi ta gyara tareda maida komai a muhallin sa...
Nan da nan tagyara dakin har bandakin tashiga ta wanke shi tass..
Jin karar wayar ta yasa tafito cikin sauri domin Dagawa.
Tana amsa kiran tace wacece ne.
Dagacen bangaren tace eh lallai n'a yarda kin aure Rahama murya ta kika mance..
Murmushi tayi saida kuncin ta ya lotsa hijab din dake jikin ta tacire tareda nikaf din..
Tace Haba Asiya wace ni inmace dake kawar Arziki.
Asiya tace ainagani kin canza layi baki nemeni ba amma nida n'a damu dake har gida naje gun ànty tabani takarashen zancen cikin Jin dadi..
Rahama tace kiyi hakuri inada niyar in kiraki natuba kawata..
Asiya tace yawuce ya mijin naki yake ne ?
Rahama tace kalau yake yafita ma.
Wai yaushe zaki zone nayi miss dinki.
Asiya ajiyar zuciya tasauke tana Lure da Rahama duk sanda tayi mata maganar mijin ta basar da zancen take tahanyar dauko wani firan.
InshAllah Zanzo cikin Satin nan aikina WhatsApp da layin nan Ko ?
Rahama tace eh dashi nakeyi mu koma kan whsap kawai Daga haka sukai Sallama.
Itako Rahama kayan ta take hadawa zata koma dasu dayan dakin dan tagaji da kwana kasa babu kwakwaran dalili bawai rasa wajen kwanan akayi ba mulki dai ake nuna mata..

************************

Yarima Samad yana saukowa kasa samun su Faruk yayi har sun shirya.
Kallon Faruk yayi yace inafatan ka fito da wannan zanen hoton.
Faruk yace ya za'ai in manta da ranka yana Murmushi..
Aminu yace ina fatan yau bazamu dade ba Ko.
Kan wannan hoton wlh saikaita bamu bakar wahala kai wallahi mafarkin ka munafuki ne taya ze nuna maka mace à kano be nuna maka gidan su ba..
Faruk yace kuma fa hakane wlh saidai yayi ta bamu dan banzar wahala haba.
Samad da duk suka cika mai kunne da hayaniya sunsan abunda yatsana kenan surutu.

Dakatar dasu yayi da hannun cikin halin Ko in kula da zancen nasu.
Yace akwai wanda n'a daure acikin ku ne.
Duk wanda yaga be iya zuwa ya koma dakin sa yazauna.
Mikawa Faruk hannun yayi Alamun yabashi zanen.
Faruk yace dan Allah malam mu tafi in mun barka ka tafi kai kadai bacewa zakai arasa gane inda kashiga..
Gaba sukai Faruk da Aminu.
Kallon su yake yana ciza yatsa lallai suncika yan rainin wayau...
Binsu yayi abaya cike da dan saurin sa
************************
Rahama tana kai kayan ta dayan dakin Idanun ta yasauka akan lefen da Samad yadauko Daga gidan su Adamsy wanda tunda ya ajiye mata su.
Bata bi takan su ba..
Kallon akwatunan take tsadaddu akwatina ne wanda Daga ganin su zasu kai à kalla dubu dari biyar.. .
Bude babban akwatin tayi taga uban kaya turame guda dari n'a Atamfofi ikon Allah tafada yayin da taga wasu a ciki an dinkasu daidai size din ta.
Saita tuna lokacin da Adamsy yazo yadauke ta yakai ta gun tela da su auna size dinta.
Murmushi tayi me kama da ciwo tace Uhmmm haryanzu Adamu bandaina sonka ba..
Bakin cikin rabuwa da Adamu take tace wayyo ni Rahama Allah kai kasan daidaii ina rokon ka akan falalar ka kasama zuciyata hakuri da dangana..
Jiki Asanyaye tabude sauran akwatunan.
Su lesss da matériel.
Hartakai kan karamin akwati da gold ne zalla a cikin su.
Mamaki ne yacika ta tace me zanyi da uban kayan nan harda kayan darirukan milyoyi.
Wayar tadauka tareda dannawa Ànty kira.

Dagacen bangaren tace my Rahama dafatan kina lfy.
Rahama tace kalau nake uwata ta kaina..
Murmushi anti tayi duk sanda taji Rahama tace mata haka to akwai magana mai muhimmanci da zatai mata.
Rahama tace antina akwatuna lefe ne aka ajiye mun adakina wanda Adamsy ya hada ne shine Abban Adamsy yabashi yakawo nan gidan da sunan nawa.
Ànty tace wa 'akaba.
Rahama tayi shiru batasan yanda zata fadi sunan sa ba..
Ànty tace haba yata yimun bayani wa' aka ba nace.
Cikin yin kasa da Murya tace me nan gidan.
Murmushi Ànty tayi tace Haba Rahama ki maida hankalin ki waje daya nasan kinada tarbiyya kokarin da kikai n'a zama gidan miji bakowa bane ze iya ace Daga wajen daurin aure a canza à baka wani daban kinyi namijin kokari Rahama ta.
Abunda nakeso dake ki dauki komai ba komai bane kamar yanda naga mijin naki yanada saukin kai ga girmama n'a gaba dashi ki kalle shi da kyau Rahama duk inda ake son namiji yakai kyakywa mai Addini ga nutsuwa.
Hamdala zakiyiwa ubangiji ki..
Kema kam duk abunda n'a lissafa akan sa Allah yabaki '' cancantar kune yasa Allah ya hada auren naku '' ' uhmm Rahama ki kama mijin ki dakyau ni uwa ce bani ce zan koyar dake yanda ake kama miji ba.
Amma InshAllah zanturo *KANWATA* da Asiya suna dan saki ahanya koda ta whsap ne inyakama suje gidan ki zasu je.
Kinga Asiya kawar ki ce ina tabbacin bazata ci Amanar ki ba itama Kanwata haka.
Cike da nutsuwa taringa Jan hankalin Rahama...
Tace su wayannan kayan da suke adakin naki wanda Adamu ya hada zan gayawa baban ki.
Muji abunda ze ce akai..
Rahama tace Ànty nagode sossai samun uwa irinki sai Antona.
Cikin Jin dadi da Begen juna sukai Sallama....
Rahama maida kayan gefe daya tayi tareda gyara dakin dan yayi kura kasantuwa ba'a kwana ciki..

***********************
Chapter 42 · 0% Book details