← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 115

Sashe 55

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dattijo rike da kugun sa yace ya shugaba na.
Wannan ai shahararren Malamin Addinin nan ne muna kallon wa'azizunka sa
kasan shi kenan da dukan Alamu..
Baba Salihu kallon shi yake da rinannun Idanun sa da suka kada zuwa ja.
Yace eh nasan shi mana shine wanda nake baka labarin sa nazauna gidan sa a kano.
Dattijo yace gaskiya shugaba n'a dole ne yadau zafi duk da besan dalilin ka ba..

Baba Salihu yace hakane kana tunanin ze sauko ta ruwan sanyi ne.
Dattijo yace kwarai kuwa inka hadashi da Allah da manzon sa ze saurare ka.
Murmushi Baba Salihu yayi yace nagode da shawara zo mu koma gida tafiya tasha ruwa..
Kai tsaye wajen motar sa suka nufa.
Suna shiga sukabar airport din..

****************************

Asiya kama hannun Rahama tayi suka je dakin nata rike da ledan da tazo dashi.
Rahama cikin Jin dadi tace kinje super market ne kinsiyo mun biscuit ne kinsan inason cin sa Ko.
Uhmm wanda ake ajewa a gidan nan Sam bayamin dadi.
Asiya kallon ta take tana Murmushi tace Rahama kenan kedai haryanzu kinki ki girma Ko.
Wai intambayeki mana.
Rahma tace inajin ki
In kika kuskura kikamin tambayar banza zaki sani ne..ehee tana turo baki gaba.
Murmushi Asiya tayi tace naji dai koma meye ai sai ki tsaya ki saurara Ko ?
Gyara zaman ta Rahama tayi tareda baza kunnuwa dan Jin abunda zata ce..
.
Asiya tace Rahama n'alura kamar babu shakuwa keda mijin nan naki kallo daya nayi muku n'a fahimci hakan banson ki boye mun komai takarashe zancen tareda hada rai tamau babu Alamun wasa..

Rahama ganin Asiya ta daure yasa ta daukan maganar ta serious.
Cikin yin kasa da murya taba Asiya labarin komai tun zuwan ta gidan.
Asiye zare Idanun waje tayi da Rahma takai karshen labarin.
Tace yanzu kina nufin tun zuwan ki gidan nan babu abunda ya taba shiga tsakanin ku keda shi.
Rahama shiru tayi tarasa Amsar da zata bata..
Asiya tashi Daga zaune tayi tana ta buga hannayen ta..
Tace uhmm Rahama kinban mamaki fa da karatun da sanin ki da komai amma kike take sani..
Rahma cikin kunan rai tace Asiya eh da karatuna nasan abunda nake.
Taya zeringa Fadin auren Sadaka ce kinkosan yanda kalamin nan yake min ciwo acikin zuciyata kuwa banda wanda zan iya gayama abunda ke bata mun rai saike Asiya...
Da wannan kalamin nasa n'a gwammace yabugeni zefimun sauki.
Sannan niban hanashi kaina ba kinsan banda karfin sa duk da bani so.
Shima kamar yana zama dani dan dole ne.
Asiya 'ki fahimceni cewa yayi auren biyayya ne banzo gidan nan ba dan in kuntata masa ba.
Nadauki aure n'a dashi Kaddara ce.

Asiya cikin Jin tausayin Rahama ta zauna gefen ta rike da hannayen su cikin juna.
Tace Rahama kema kinsan Allah yayi miki canji mafi Alkhairi shine ya mallaka miki Yarima.
Wallahi kundace kedashi duk wanda ya ganku.

Ki saki ranki ga kayan gyaran jiki nan Ànty ta hado miki dan batasan cewa har yanzu a leda kike ba ba'a bare ba.
Nasan dasai ta kusa Zane matar Samad.
Rahama Murmushi tayi tana fiddo kayan dake cikin ledan.

Wani roban Zuman yaji hadi sossai ta fiddo tace wannan Zuma ce.
Asiya tace kisha kiji mana abu yana hannun ki amma kina tambaya ta..
Bude murfin roban Rahama tayi tareda da dan lakutowa da hannun takai bakin ta.
Lumshe Idanun ta tayi tace Asiya wannan Zuman badai dadi ba har wasu kwa kwa nake ji a ciki...
Asiya tace uhmm nasan ke uwar kwadayi ce saiki shanye t'as yanzu amma fa kibi à hankali kisha Rabi yanzu.
Sauran kibarshi sai munje kwatano kinsha.
Rahama tace haba wlh ni duka zan shanye bazan iya bari sai munje cen ba.
Dariya Asiya tayi sossai harda rike ciki tace ina ruwana ki shanye mana Ai Samad yana gari kika matsu ze rage zafi cikin ruwan Sanyi batareda yasha wahala ba...
Hararan wasa Rahama tabita dashi kinga ba dakin mu daya ba nidashi ba.
Yana tashi ina tawa.
Kidaina mun mugun baki banaso.
Kafa roban Zuman tayi a bakin ta saida ta shanye shi tass ajiye roban.

Asiya rike da baki tace wlh zaki gane bakida wayau au wannan ba simple din Zuma bace kema kin sani Ko amma Saboda tsabar kwadayi kin shanye jiki magayi ina ruwana..
Rahama cikin turo baki tace nafa gayamiki ba dakin mu daya ba.
Kuma bazemun komai ba banson kina mun mugun baki fa..
Asiya tace Tom nayi shiru yanzu dai kinga sauran kayan harda su gumba garurruka duk yanda zaki sha su ga sunan ànty ta rubuta a papper.
Rahama tace uhmm nifa duk bazan sha ba Zuman ce kadai ta mun dadi.
Asiya tace wlh inbaki sha ba à gabana ba saina gayawa Ànty wlh...

Asiya da kanta tadauko madarar peak a frij din kitchen tazo ta hada mata magunguna tabata ta shanye.
Sai yamutsa fuska take kamar zatai Amai.
Asiya tace kardai ki kuskura kiyi Amai kamar yanda kikai kafun bikin ki dan anbaki magani saiki amayo
Rahama tace nidai wlh magungunan nan sun cika min cikina haka zan kwanta banci komai ba..

Nan da suka je kitchen tareda da taimakon Asiya tayi girki.
Tuwon semovita da miyan ganye wai wannan girkin bakaramin daukan ido yake ba abaki ma ba'a cewa komai.
Asiya ce ta bude miyan dayaji kifi manya manya tace uhmm Rahama nidai girki zaki koyamin dan anan wajen ban kamo kafar ki ba.
Dibar miyan tayi takai bakin ta tareda lumshe Idanun ta wani dadi ne ya ratsata sossai.
Asiya tace Rahama in babu damuwa ki koyawa fans din KYAUTA Daga Allah yanda kika hada miyar nan dan wlh tahadu iya haduwa sai ma Yarima yaci ze baki note..

Rahama tayi Murmushi tace wai fans din KYAUTA Daga Allah insunce suna so zan fada musu meye aciki ai karuwa ce..
Kusan atare suka fito da manyan Wamer flask cike da abinci suka jera komai a dîner table.

Faruk Da Aminu cikin sauri suke saukowa Daga kan matakalan step din.
Aminu yace Ah ashe manyan baki gare mu.

Asiya ta murmusa tana kallon su cike da ladabi ta gaishe su.
Suka Amsa cikin sakin fuska.
Faruk yace Madam Samad wai ina Yarima yake ne ?
Rahama tace uhmm yadai fita amma bansan inda yayi ba...
Takun shigowar sa yasa ta yin shiru karasowa falon yayi yace daman ina zaki San inda naje yana kallon ta kauda kansa yayi Daga kallon ta yadawo kallon Aminu da Faruk yace sai yanzu kuka fito nasan yanzu ma yunwa ce ta sauko daku.
Faruk yace wlh kuwa kamar kasani amma naga ga abinci nan madam ta girka mana..
Dîner table suka nufa Faruk da Aminu.
Shiko Samad kallon su yake ganin Rahama da Asiya awajen ya kasa motsawa Daga inda yake..

Asiya daukar abincin nasu sukai sukai dakin Rahama dan su basu waje.
Suna barin wajen Samad ya isa kusa da su Faruk yace yan iska kawai waya hanaku kuyi aure..
Faruk dayanzu yakai loma daya a bakin sa yace wai wai kaji wani gardi da dadin abinci nan kuwa.
Aminu yace tunda nake bantaba cin abinci me dadin wannan ba.

Samad dake kallon su yace uhmm kuyi aure mana gwaurayen banza kawai.
Faruk yace ai banbancin mu dakai daya ne.

Samad yace bangane banbancin mu daya bane meye nufin ka.
Zama yayi kan kujerar yana kokarin zuba abincin a plate..

Faruk yace eh mana Saboda kai da sunan kanada aure ne amma bakasan Dadin auren ba..

Aminu yace tabe tabe.
Faruk yayi Murmushi shima yace tabe tabe mana n'a gasken ma..
.
Samad yace ai duk wani dan iska acikin ku kar nake kallon sa.
Nasan dani kuke tabe tabe meye ma'anar haka ?
Aminu yace zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne.
Kawai dai ka tsargu ne tokai kana tabe taben ne.
Mun ce maka film ne muka kalla kaki yarda Ko in kunna maka ne ..
Samad yace dan iska kunna mana mugani.
Murmushi Aminu yayi yace to bara ingama cin Abincin karka bari n'a kware.
Sossai suka ci Abinci yayinda Samad yanaci yana lumshe idanu ji yayi kamar taita girka masa irin wannan abincin yanacin sa dan yanason irin abinci haka..

Kusan Magrib Asiya tasauko da niyar tafiya gida.
Sossai Rahama tashiga damuwa akan tafiyar ta dan wunin da sukai ji tayi kamar su dawwama taré.

Aminu da Faruk zaune suna kallon Ball.
Asiya tace to ni zan tafi ina angon Rahma yake ne ?
Dagacen zaunen kan dîner tablé yana chat yadago kai yana kallon ta.
Yace kice ina Abdul Samad yake aini bankai matsayin ango ba..
Daga Asiya har su Faruk darawa sukai.
Ajiye wayar yayi ya iso wajen Asiya yace ki bari Farruk yakaiki har gida..

Aminu yace kwarai kuwa bari mukai ki kinga mun samu mu nuna miki wani abu da muke nema à unguwar ku.
Asiya tace babu matsala Muje.
Gaba sukai ita da Rahama.
Samad ganin Rahama n'a kokarin fita Daga Falon yayi saurin fadin.
Ashe banhanaki wuce iyakar falon nan ba inkikai baki ba indai bani ne nace ba
Cak ta tsaya cikin Jin zafin haka tarasa dalilin sa.
Asiya ta juyo tana kallon Rahama tace ki koma ai yanada gaskiya babu hijab zaki fito haraban gidan..
Murmushi Samad yayi dan ya lura Asiya akwai ganuwa a fili yace.
Asiya kiyi hakuri fa karki ga laifina..
Asiya tace ba komai InshAllah zakaji amsa ta wajen Rahama..
Daga haka tasakai tafita '' Faruk da Aminu suka bi bayan ta dan kaita gidan su..
Rahama dawowa falon tayi.
Jin yanayin ta yasoma canzawa saman kujera ta zauna 3str idanunta a lumshe wani bakon yanayine yake ziyartan ta.
Mutsu Mutsu tasoma Daga kwance wanda yajawo hankalin Samad dake kokarin hawa kan matakalan step din..
Dawowa yayi a falon yana tsaye akan ta kallon ta yake yanda Idanun ta arufe suke amma sai nishi take fitarwa mai fidda sauti.
Hannu yasa ya taba jikin ta yaji jikin nata harya d'au zafi sossai.
Subuhannalah ya furta yana kokarin.......

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:45 - Nuriyyat: KANWATA

LITTAFIN NAN KUDI NE INKIN GANSHI A WAJEN GROUP DÃŽNA NA SATA NE

Inkina bukata ga nomba
09069080725

Writin By Sa'adatu

5️⃣6️⃣
Chapter 55 · 0% Book details