← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 115

Sashe 89

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan uwar ki mijin naki kike wa rashin kunya abunda kika ga jatimar ki ta nayi shine zaki masa to wallahi bazan lamun ta ba...

Mama dake karasowa tace A'a karka zage ni inzakayi mata fada kayi mata amma ai wannan zagina kake yi Nice mara kunya Ko...

Sheik cikin Jin haushin Mama yace Aishatu wallahi inhar Salma bata koma gidan mijin nata a yau dinnan ba a bakin auren ki duka igoyiyon su tsinke....

Azabure Mama da Salma suke kallon Sheik dake kokarin wucewa sashin nasa cikin bacin rai....

Bakin mama n'a rawa tace '' Salma kinji abunda yafada kuma tunda muke betaba mun irin wannan furucin ba....

Salma cikin gigita tace mama ni gaskiya bazan koma ba...

Tass kakeji mama ta wanke ta da mari yau n'a tabbatar ke banza ce Salma akan ki igiyar aure na '' 'n'a neman tsinkewa shine zaki ce' '' bazaki koma ba '' kenan inbar gidan nan kike so...
To wallahi baki isa ba...

Salma rike da kuncinta hawaye shar a Idanun tace mama yau da kanki kika sa hannun ki kika mare ni...
Yaya Abubakar ya mareni..
Abby ya mareni..
Kema kin mareni..
Kusan lokaci daya yau n'a tabbatar ba'a kauna ta agidan nan..

Mahaifina n'a korana ke kuma dan ya miki barazana tome A'ciki Dan ya sake ki din..

Mama batasan sanda ta doki takalmanta taringa bugawa Salma ba '' tana ihu '' sossai mama ke bugun ta '' ' ta ko' ina..

Sheik yazo daidai fita yaji yanda take bugun Salma cak ya tsaya ganin Ànty tafito hakan yasa shi kallon anty cikin bacin rai yace Sa'adatu koma daki nace Ko..
Babu musu ta koma tana Girgiza kai...

Shiko Sheik karasowa wajen Mama yayi cikin Daga Murya yace Aishatu ki sakar mun ya....
Dan ke bakida hankali saiki buge ta..

Mama cikin takaici tace yarinyar nan ta rainani waini take gayawa zancen banza...

Sheik yace kwarai kuwa ta gayamiki ai Salma kawar ki ce...
Dan me bazata fadi son Ranta ba ni tafadamun mana wargi waje yasamu...

Daga haka yasakai yafice Daga gidan yana Girgiza kai...

Ranar mama bata bar Salma ba '' kiran Al'amin tayi tace yazo daukan Salma cike da Jin dadi Al'amin yaturo yayar sa Mariya...

Koda Mariya ta iso gidan '' cike da girmamwa ta gaisa da mutan gidan...

Ànty tace badan ban nemi izini ba '' d'ana raka ku har gidan ki..

InshAllah innasamu dama zamu kawo miki ziyara nida Asiya...

Sossai Salma ke kukan zuci wai yau mama ce ta hada mata kayan ta..
Babu rarrashi babu magana me dadi neman kawai take tabar gidan....

'' 'Mariya' tarar me napep tayi tareda taimakon Abdul jalil aka saka kayan Salma cikin napep din.....

Kwatance mariya tayiwa me napep din unguwar da za'a kai su...
Ita Ko Salma zaune take zuciyar ta na tafasa..

Sam taki kula Mariya data rakota banda hararan ta ba abunda takeyi...

Suna isa gidan '' Mamaki ne yakama Salma ganin wani shahararren gida n'a gani da na fada.
Kamar gidan daya da gidan Samad saidai nasu bekai nashi haduwa ba..

Mariya dake kokarin kama hannun Salma domin shiga gidan..
Nan da nan taga Annurin à fuskar Salma..

Waigowar da Salma zatayi Al'amin ta hango cikin wata bakar mota Mercedes cike da zallan Mamaki take kallon sa har yayi parking A gaban su...

Bakin Salma n'a rawa tace.........

Al'amin ina kasamo mota ne...
Murmushi ya sakar mata cike da jin dadin ganin ta '' yace Amarya mushiga Daga ciki wannan motar d'ana tuko mallakkin kine nawa yana cikin gidan..

Hannun yayi musu yace Muje Ko..
Ba musu suka bi bayan sa yayi musu jagora har cikin gidan.....

Mai gadin Barka da zuwa yake ta fadi '' soya ke yayi magana da Al'amin ya tambaye sa Ko itace matar sa '' yana gudun kada ya kwabsa masa......

Hakan yasa sukai cikin gidan...
Wani katoton falo '' sossai mai girman gaske..

Anzuba daula a falon '' kujeru yan waje forein '' komai spécial hatta carpet din dake malale tsakiyar Falon shima abun kallo ne...

Salma tazama kamar wata bakauya badan bata taba gani ba saidan mamaki ne yakamata wai nan gidan mijin ta ne....

Ita kanta Mariya cike da mamaki take dan a tunanin gidan haya ne..
Saita ga sabanin haka so take ta zanta da kanin nata amma babu dama ganin Salma n'a wajen.....

Salma dube dube tafara acikin gidan tana leka lungu da sako n'a kowani gidan....

Ganin Salma tabar falon yasa Mariya fuskantar Al'amin tace kai ina kasamo wannan gidan '' da kudi da kake ta fantamawa nifa abun yafara bani tsoro.....

Al'amin tabe baki yayi yace kema zakiyi irin abunda baba yayi ne nacewan baze ci kudin ba '' saiyaji kwakwaran sana'a ta...

Toke bazan boye miki ba kuma dan Allah karki tona min Asirin nashiga kungiyar Asiri n'a mafiya....

Mariya cikin gigita take kallon sa tace haba Al'amin meya kaika kasan hadarin dake cikin wannan kungiyar..

Uhmm Mariya kenan nifa bazan bada Jinin kowa ba saina Salma...

Azabure Mariya ke kallon sa tace bangane Jinin Salma zaka bayar ba...

Matar ka ce fa...

Murmusawa yayi yace mata ta ce amma batasona dukiya takeso fiye da komai zanbata dukiya taci a karshe inmika ta....

Innaliahi wa'inna ilairajun Mariya take ta maimaitawa tace Al'amin kaji tsoron Allah dan Allah karka cuce ta '' tana dauke da cikin ka...

Ànty Mariya saita haihu zanbada Jinin ta '' kinga tabar tarihi kenan.
Narokeki karki tona mun Asiri yarda ce tasa nabude miki cikina..

Isowar Salma yasashi yin murmushi yace yadai Amarya gidan yayi miki ko ''

Kada kai tayi tace gaskiya gidan yayi kabari sai n'a haihu saika canza mana gida....

Kuma ina bukatar yan aiki...
Mariya cikin dauriya da tausayin da Salma tabata tace uhmm.zaki samu yan aiki har ki gaji dasu yar uwa ta...

Nan dai ya nunawa Salma dakin ta..
Da komai yanda suke..
Sossai taji dadin hakan...
Tana murna sotake takira mama marin da tayi mata da duka yasa tace uhmm bazan kirata ba..

Saidai taji agari ina fantamawa da naira badai ni ta wulakanta ba..

Koda Mariya zata wuce''' Al'amin duba dari yadauko yamika mata amma taki Amsa tace kabar shi nagode...

Salma ta yatsine fuska tace haba anti ana baki kina kin Amsa..

Murmushi tayi tace aiya bani kafun inzo sun isheni haka...
Al'amin yace hakane to anti mariya Muje in raka ki.....

Har bakin gate ya rakata yana kara jaddada mata karfin Al'kawari data dauka..
Cike da yarda dakai tace Al'amin baza'a jishi a baki n'a ba..

Komawa yayi cikin gidan yabarta anan tsaye..
Itako tsaye take tana lissafin anya zata iya barin akashe rai..
Taci Alwashin inhar salma ta haihu zatasan dabarun dazatayi ta ganar da ita gaskiya batareda ya sani ba..

Da wannan tunanin tabar kofar gidan....

Kwatano

Fulani cikin tashin hankali take kallon bokan jeji tace kana nufin bakin Aljani ya fallasa sirrin mu..

Bokan jeji cike da takaici yace baduka bane dan ya kwantar mata da hankali yace '' wace ita data San sirrin namu saidai taji n'a Farida...

Ajiyar zuciya Fulani ta sauke cike da Jin saukin Asirin ta be tonu ba..
Tace bokan jeji yakamata mijina à sake masa sabon jiko jiya naga kamar yana fadin '' ina zega Salihu koda sau daya ne........

Bokan jeji yace ina baze ga Salihu ba''' kuma kisan yanda zakiyi kibashi magunguna yasha '' shikuma yaba baban shi...
.
Kasaitaccen murmushi cike da takama tace '' watau abun naka aike aike ne...

Kwarai kuwa cewar bokar jeji..
Sun dade suna tattauna Daga karshe sukayi sallama..

Ta fito cikin ciyayi nan tareda nufar motar ta......

Rahama zaune take tana gyare gyaren dakin '' mijin nata..

Taji wani iska me karfin gaske ya kada '' nan take tafara adu'oi....
Wannan iskan n'a tsaigaitawa Idanun ta suka sauka akan.....
Takarda dake kan gadon nata.

Cikin Azzama hannun ta na rawa tadau takardan

Koda ta warware takardan ganin rubutun tayi dan Jan biro aka rubuta shi ta harshen larabci '' hakan yasa hankalin ta yayi mugun tashi cike da aro jarumta take son ganin meye A'ciki...

Sallamar Samad ne yasa ta kokarin boye takardan amma ina yariga da yagani '' kusanto inda take yayi cikin hanzari yana mata kallon tuhuma
Cikin tsaita nutsuwar sa '' yace Hubby me kike boye mun ne bakyason ingani...

Bakin ta na rawa tace uhmm kai me ka gani..
. Hannun ta ya kamo ya hade da nashi yana kokarin amsar takardan...

Girgiza kai tasoma tace A'a Amjad dan Allah karka amshi wannan takardan Idanun ta nan da nan yakawo ruwa''Sam batason yakaranta abunda ze Girgiza shi...

Kallon ta yake yana nazartan ta''' miko mun ya furta cikin kakkausar murya tareda hada rai kamar bashi ba...

Ganin yanda ya canza launin sa' 'yasa ta tsoro ta
Babu musu ta mika masa

Zama yayi bakin gadon yasoma karantawa''' a fili.

Kamar haka....

Rahamatullah hakika haduwa ta dake bemun dadi ba' 'nasan kinada sirrin adu'a da zaki iya dawo dani cikin dakin ki inhar bancika Al'kawari ba.....

Bokan jeji ya karkade ni kada in sanar miki da komai nace masa naji..

Amma ban dauka ba...

Rahama nafara baki labari to yanzu zanci gaba Daga inda natsaya aranar kin tambayeni laifin mène uban mijin naki yayi...

Abun da yafaru da sa hannuna ni Aljani Sultan..

Sarkin Adalai Sarki ne mai gudanar da mulkin sa akan ka'ida da dokokin musulunci '' babu yanda Fulani da Farida basuyi ba dan asauke shi ba...

Ita Farida tanason yasauka ne dan tun farko be aure ta ya auri kanwar ta da Aka bashi zabi '' wannan bakin cikin yana nan aranta...

Ita Ko Fulani ta nemi da Sarkin Adalai da yayi Alfasha da ita...

Ya nuna mata Sam shi baze iya cin Amanar kanin sa ba..

Watarana safiyar wata juma'a Sarkin Adalai yafito Daga sashin nasa zanshi Fada '' yahadu..........

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:54 - Nuriyyat: KANWATA

Littafin nan kudi ne Inkin ganshi a wajen group dîna na sata ne

09069080725

8️⃣5️⃣

Yahadu da wata baiwar Fulani mai suna Saratu '' cikin gigita tana ihu tace Shugaban Adalai dan Allah ka taimaka mun kwarto ne acikin dakina....
Cikin gigita yake kallon ta yace Saratu kwarto adakin naki kuma...
Chapter 89 · 0% Book details