← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 115

Sashe 1

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

KANWATA

*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌�*

Marubuciyar
*Amince Dani*

*KAIKAJAWA KANKA*

Yanzu kuma gani dauke da
*KANWATA*

Paid Book ne
Vip 300
Spécial 500

Acct nomba 3115484026 first bank ko kuma Kati MTN
Banason vtu

Idan kinbiya ta bank kina iya turo shaidar biyar ki ta wannan 09069080725

Dasunan Allah mai Rahma mai jinkai Allah kasa yanda nafara lafiya in kare shi lafiya wannan labarin yafaru da gaske dan kusan Book Dina da nakeyi true life ne saidai inyi masa kwaskwarima dan abun yafi Bada citta

Wannan shafin nakine maman nusaiba yar mutan makkah bazan manta kokarin ki dakuma bani karfin Gwuiwa ba Akan littafin kanwata

Bazan manta dakuba Yan uwana n'a jini dakuka nunamin inci gaba Allah Yana taredani
💃💃

Kunji kanwata kaunarki n'a cikin Raina kuma bazani dainaba har abada ......

Ku biyoni kusha labari .

Book 0️⃣1️⃣

Tafiya suke a k'asa Rahama sai zuba Uban sauri take batason tayi latti.. 'Waigo war da zatai ta hangon k'anwar ta Salma cen baya t'ai, 'tana fira da wani Atiku sai washe baki tace cikin jin haushin haka.

Rahama ta d'aga murya da karfi yanda zata iya jiyo ta 'tace salmaaaaa!

Wacce Aka Kira da Salma b'ata rai tayi tace na'am.

Kinsan lecture d'in mallam Hamza garemu amma kika tsaya surutu tana magana da d'an b'acin rai.

Salma turo baki t'ai Ta ce" kina iya tafiya Kona hanaki ne ehee.

Aikuwa cigaba da tafiyarta Rahama t'ai 'dan taso ta makara shiga aji.

Mallam Hamza yashigo aji 'dukan dalibai suka tashi dan gaishe shi.

Hannun yai musu da su zauna 'kowa ya nemi wuri yazauna 'tsit kakejin ajin .

Gyaran murya Mallam yai Ya ce" Wazai gayamin inda muka tsaya wancen satin?

Kowa yayi tsit shiru kakeji .

Rahama ce 'ta daga hannu.
Bismillah Ya ce mata...

Cikin muryan ta 'da nutsuwarta ta fara fad'in awancen satin mun tsaya ne Akan inda kake mana bayanan amfanin ruwa ajikin d'an Adam...

Mallam Hamza kallon ta yake yana nazarin tarin ilimin Yarinyar Yace Ku tafa mata class kowa yadauki tab'i..

Kina iya zama 'Rahama .

Cikin dan b'acin rai Ya ce" yanzu tun wancen satin mukai lecture kan amfanin ruwa jikin d'an Adam ,amma wai babu Wanda yarike sai mutum daya.

Meyasa sau dayawa bakwa daukan Abun da ze amfane Ku da muhimmanci?

Gaban allo ya koma ya soma rubutu kamar Haka

*Amfanin ruwa jikin dan Adam ''*

*Ruwa yana taimakawa wajen gudanar da jinin jikin mu*

Da kuma....

Sallamar Salma ne ya dakatar da shi da rubutun dayakeyi.. 'Kallon ta yake yana kallon agogon hannun sa.

Keee daga ina Haka? .ya nuna ta yatsa da hannu wannan ba Yayar ki bace? Ya akai tarigaki zuwa?

Dukar da kanta k'asa Tayi tagaza magana.

Kowa class sai kallon su suke suna kwabe baki .

Ita ko Salma ganin idanun class kowa akanta 'turo baki gaba t'ai 'Ta ce" Mallam bansan lokaci yawuce ba.

Get out .... Yace mata ransa abace.
Cikin bacin rai ta kalli Malam. Ta ce" Mallam ka kosan waye babana agarin nan kuwa kake korata'?

Rahama ta Mike cikin fushi Ta ce" haba Salma bazaki bashi hakuri ba 'bayan kinyi laifi! Saiki tsaya zakimasa rashin kunya.!!

Harara ta watsawa Rahama Ta ce" oho dai ai ban kasa dake ba .

Kai kuma Mallam kakiyaye had'uwa ta dakai!

Tsakiiii taja tafice cikin harabar makarantar tanemi waje ta zaunata tana ta gunani Wallahi Mallam Hamza zesan ya ta boni.

Mallam Hamza rike da baki yake mamakin kalamin Salma

Maida hankalin sa Yayi Akan rubutun da yakeyi...

Sai kusan karfe 11am yagama musu lecture

Mallam Hamza nafita ajin .

Salma tashigo ajin ,tazauna tanata cika tana batsewa Wallahi duk wani dan iska à ajin nan na k'ara Ganin Yana min kallon raini Wallahi zai san yata boni, munafukai kawai ... Rahama harta bud'e baki zatai magana saita fasa , sai kusan karfe d'aya suka tashi.

Tafiya suke ahanya suna hiran k'awar su da batada lafiya zasuje dubo ta.

Wani matashin saurayi kyakyawa saurayi ajin farko yanata cewa Yan mata ji mana.

Sai suka waigo 'Salma sai fari da ido takeyi irin an saida ita d'in nan.

Ya k'araso gaban su. Rahama kanta a duke Tace "pls in kanason magana da K'anwata ba a titi zaka tsaida ita ba.

Salma turo baki t'ai gaba irin yau ga rainin wayo.
Ko ina ruwanta da in an tsaida ita din.

Saurayin Ya ce" nidai 'sunana

Adamsy dan gidan ambassado d'in Libya d'azun nazo garin Kano .

Kuma Wallahi naji kin kwanta min a rai ya nuna Rahama da yatsaya .

D'ago Kai tayi ta kallesa Ta ce" nikuma ba K'anwata ka tsayar ba?.

No kece d'in nabiyo ba ita ba.

Ran Salma yakai kololuwa wajen baci .

A fusace t'ai gaba tanata buga Uban sauri 'har tuntube takeyi a hanya 'saida ta taka Kaya 'amma dayake ranta abace yake bama ta damu ba.

Rahama Ta ce" kaga karka had'a ni da K'anwata 'in kanason Yarinya gidan iyayen ta 'zakaje kanemi izini daga Haka ta wuce .

Yan Mata! Yan Mata!! ..
Yasake biyo ta 'baki fadamin sunanki ba?
Kallon sa ,t'ai takauda kanta gefe cikin gajiya da bin bayanta da yakeyi .
Rahma sunana Ta ce" masa a tak'aice tareda cigaba da tafiyar ta cike da nutsuwa .

Kallon ta yake 'Yace wow amma wannan Yarinyar sai kace ita tayi kanta komai Nata na musamman ne ,Allah yasa ta soni daman kyakyawar Macé aji gareta. Cije labbansa yai cikin son ganin yai magana da Rahama 'wani dan yaron Unguwa ya gani shima daga makaranta yake n'a sauri yaje gida.. Tsayar dashi yai Yace zonan abokina

Yaron tsayawa yai yatsareshi da idanu.

Dan Allah wacce Yarinyar c'en datai nisa a tafiya yanuna masa ita da yatsaya koka san Gidan su? Tace min sunan ta Rahama.

Yaron yai murmushi au Rahama kake nufi ?

Eh ita yabashi amsa yana kallon sa.

Yar gidan Sheik Abdulrrazak hizqeel makarfi ce 'wannan shahararren Malamin addinin 'nan Wanda yadawo nan Kano dazama '.

Kai haba Kana nufin Sheik Abdulrrazak hizqeel makarfi danasani ina sauraran wa'azin sa .

Gayamin layin gidan nasa.

Layi n'a uku ta hannu hagu zakaga wani gida me babban Gate kaf cikin Unguwar sune gidan su 'yafita daban .

Nagode sossai ya sunanka.

Sunana Aliya Haidar

To Aliyu godiya nake
Zaro dubu daya daga cikin aljihun wandon sa.

Ya Mik'a masa.

Karba yai'yana masa godiya cike da jin dad'in kyautar mutumin .

............

Salma tashigo gida kamar anjefota daga sama sai haki takeyi dan tasha gudu ahanya

Mama ! mama !!mama!!!

Take Kira

Mama Ta ce"
Lafiya Salma kike kwadamin Kira meya farune ?

Ta tsareta da idanu

Ina Rahma take ne kika dawo ke kadai.

Cikin bakin cikin da ke cinta 'tace Wallahi Mama wani Saurayi ne yajata a mota suka tafi.

Abban su dake zaune yake cin tuwo ya Mike cikin zazzare idanu yace mo....me?

Tace mota tana turo baki waje .

Innalilahi wa'inna ilai rajun Mama tashiga maimaita wa.

Nan take taji ji......

Littafin *kanwata* n'a kudi ne .

Kibiya ki karanta hankalin ki kwance cikin Salama

Domin Karin bayani
Ki tuntubeni Akan lambar waya kamar Haka

09069080725 whsap

Taku har kullum kyauta daga Allah
3/20/22, 22:34 - A'ish: *🌟🌟 KANWATA🌟🌟*

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo

*⚜️©J.A.W📚🖌�*

Marubuciyar
*Amince Dani*

*KAIKAJAWA KANKA*

Yanzu kuma gani dauke Da *KANWATA*

IKILIMA ADAM
(Kyauta daga Allah)

*Littafin K'ANWATA paid Book ne*
Vip 300
Spécial 500

*Acct nomba 3115484026 first bank ko kuma kati MTN*
*Banason vtu*

Idan kinbiya ta banki kina iya turo shaidar biyar ki ta wannan lambar 09069080725

Book. 0️⃣3️⃣

Allah yataimaki mai martaba yau fa nakeson infara cika burina .

Mai martaba *Sanusi *Turaki* kallon sa yake cike da tausayin yace Abdul Samad ..
Naji dadin jin Haka daga gareka Allah yabaka Sa'a .
Amma wace kasa zakaje ne?

Cikin dukar dakai kasa ya gyara kafafun sa ya tankwashe su waje daya .

Zazzakar muryan sa mai dadin sauraro yace wannan karan ( Nigeria kano) zanje ko Allah zesa indace da abunda nake nema.

Kuka ya kwacewa mai martaba har sautin kukan nafita yace Abdul Allah yataimakeka .

Inason duk halin da ake ciki karinga sanar dani Domin inringa sani lafiyar ka.

Ya batun Maryam ne Samad ya tsare shi da idanu .

Nan da nan duk wani annurin dake kwance saman fuskar sa ya dauke.

Mikewa tsaye yayi cikin halin ko in kula da maganar mai martaba cikin bata rai yace natafi .

Bai jira amsar mai Martaba yafito Kai tsaye .

Mai Martaba murmushi yayi Yana girgiza Kai yasan za'ai Haka .

Fadawa 'na ganin fitowar sa 'suka fara masa kirari

Tafiya yake cike da kasaitar sa da cikar haibar sa yai bangaren fulani yanufa dan yayi mata sallama ' bayi ya iske sunata mata hidima yayinda take zaune kan doguwar kujera .

Idanunsa yasauka Akan baiwar dake goge wa fulani kafa da ruwa da kyalle ahannunta cike da nutsuwa take mata wankin kafar.

Lale lale barka da isowa Samad Yana ga ka shirya kaman Wanda zebar kasar.

Bé bata amsa ba karasa shigowa dakin yai Yana kallon bayin dake mata bauta 'cikin jin haushin wannan banzar Al'adar su.

Ya kalli inda bayin suke umarni yabasu Dukan su 'sufita kuma beson yakara ganin su a dakin inhar Yana ciki.

Cike da girmama zancen sa
kowannen su yafita sadaf sadaf .

Kallon sa ya maida Akan fulani wadda shi take kallo cike da mamakin cin fuskar dayai mata .

Daman nazo in sanar dake zanyi tafiya saina dawo daga Haka bekara cemata komi yafita dakin .

Itako fulani ranta yakai kololuwa wajen baci kagamun dan iskan yaro
Ni zewa cin fuska agaban bayi .
Cije labban ta tayi cikin zafin rai tace wallahi Kaima saina ga bayan ka .
inshAllah inka tafi bazaka kara tako kafarka masarautar nan , wani dariyar mugun ta saki .

Bangaren mahaifiyar sa
Ya nufa

Mahaifiyar sa 'kwance ya isketa tana fitar da nishi mai wuyar fassarawa Alamun tana jin jiki sossai

Cikin hanzari yakarasa shigowa dakin 'sannu mamy jikinne yatashi?
Chapter 1 · 0% Book details