← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 115

Sashe 17

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda salma tadawo gida take ta safa da marwa yanda zata hadu da Adamsy kawai take tunani

Iyayen Al'amin sunzo sheik cikin mutuntawa ya karbesu dan mutanen arziki ne.
Gasu makotan arziki.

Sheik be fadama musu abunda yaron nasu yake aikatawa ba shida salma Saboda yasan rufa asiri dan Adam yanada cikin kyakkyawan dabi'un mutanen kwarai.

Al'amin dake tsunkuye da kai tsoro da fargaba ne yakamashi kada à tona masa asiri.

Sheik cikin gyaran murya ya sanaar da Iyayen Al'amin diyar shi salma tace babu wanda takeso sai Al'amin.

Gaban Al'amin saida yayi mummunar faduwa azuciyar sa sai maimaita innaliahi wa'inna ilai rajun yake.

Me zanyi da salma wacce batada kamun kai dadai yayar tace amma anhadani da alakakai.

Cike da farin ciki da Jin dadi Iyayen sa suka ce sun amince tunda yace beson komai sai sadaki suka nemi Alfarma koda andaura Salma tazauna n'a kwana biyu kafun su nemi inda zasu taré da mijin nata.

Sheik yace babu matsala wannan ai munzama daya..

Al'amin gaza magana yayi dan yana tsoron yace wani abu Abba ya tona masa asiri.

Daga haka sukai sallama da Iyayen Al'amin jiki babu kwari Al'amin yakoma gida....

....

Kannen ànty suka zo sunyo ayari dan tayata murna zata aurar da yarta Rahama.

Kanwar ànty tazo da kayan gyaran amare masu kyau su turaren wuta humra dilka.
Sossai anti tayi farin cikin gudumuwar da suka kawo.

Dakin baki aka sauke su.

Aranar Rahama saida tasha gyaran jiki gun kanwar ànty

Salma Sam taki yarda ai mata gyaran jikin saima tarufe su da masifa.
Dole suka kyaleta.
*******

Adamsy labari yaje masa anbashi Rahama murna awajen sa baya misaltuwa.

Shago yaje yasiyo sabuwar wayar Samsung galaxy edge 7 yakawo mata hade da layi ranar sun sha hira ta waya.

Cikin farin ciki yace Rahama kinga ikon Allah Ko Allah yace ke matata ce gashi saura kwana shidda à adaura wayyo zan zama baban baby
Nakosa inzama Daddy nima.

Kunya yakamata
Hannayenta tasa tarufe fuskar ta kamar yana ganin ta

Cikin zazzakar muryan ta tace adamsy n'a.
Idanun ta a lumshe wani ni'ima da kwanciyar hankali suka ziyarci zuciyar ta lokaci daya.

Allah yayi zan zauna karkashin inuwar ka ina mai godiya ga mahallicina.
Wani hawayen farin ciki ne ya lullube fuskar ta.

Adamsy dake jinsa a sabuwar duniya yace kinga bara inkashe kinsan tunda su Daddy suka samu labarin anbani ke zama be gansa ba.

Yanata gayyatar manyan mutane Daga kasashe.

Cikin su harda sarkin kwatano zezo daurin auren mu..
Rahama banda dariya babu abunda take tace aini ma nan Abba ya gayyato manyan malaman addini n'a kasashe ketare dana cikin gida Nigeria harda abokanan sa larabawa da sukai zaman saudiya duk zasu halarci taron.

MashaAllah Adamsy ya furta yace lallai ranar juma'a akwai kallo.

Daga haka sukai ta firan su cikin nishadi.
Ta sanar masa gobe zasu je makarfi amma kwana biyu kacal zasuyi ba haka yaso ba amma yace Allah yakaiku lafiya zamu ringa waya.

Kinga saida safe zan kira Daddy ne kan lefen auren ki 'kinsan babu jira lokaci yakure.
Daga haka sukai sallama.

********kwatano

Mai martaba zaune shida mama karama ya sanar mata bikin da zasu je ranar alhamis bikin dan Dr Abdullahi Auwal ne.

Mama karama cikin Jin dadi tace tome zehana in bika tunda nima bantaba zuwa kanon ba.

Kuma zanga maigidana yarima Samad.
Inga Ko akwai wacce zata iya ta kwace min shi.

Tana dariya mai martaba ya numfasa yace ki shirya Muje ranar Alhamis kinga tareda Samad zamu dawo dan yanada zama kotu ranar litinin anan garin namu.

Cikin gamsuwa da bayanan sa tace Allah yakaimu.

********

Yarima Samad zaune yake a falon sa.
Hannun sa dauke da remote.

Faruk yashigo hannun sa dauke da leda yace kanada masaniya mai martaba zezo bikin dan Ambassador shida mama karama.
Waziri ze rakosu.

Samad da hankalin sa ke kan kwallo da ake bugawa À TV batareda ya kalle sa ba yace inada masaniya ai duk tare zamuje daurin auren.

Nuna masa kusa dashi yayi yace kaga wannan shaddunan anko zamuyi nida ku abawa telan nan dake mana dinki kai kasan wanda za'amin tunda daurin aure zamu je.

Kasan dole muyi kara dan uban angon tun muna yara yake zuwa kwatano gidan mu yake sauka akwai shakuwa sossai tsakanin sa da mai martaba kaga dole mu zage.

Aminu dake gefen sa kwance kan kujera 3str yace gaskiya ne yarima Samad Allah yakaimu
Da Amin suka amsa dukan su banda marwan da ransa yake a bace.

********
Washe gari

Salma tanata tunanin ya zatayi ta hadu da adamsy ne gashi yau zasuje makarfi.

Wata dabara ce tafado mata gun Rahama taje cikin murmushi tace anti wai ina yaya Adamsy ne.

Rahama tace ai yanzu zezo 'wayar ta yasoma ring murmushi tayi tace kinga salma gashi cen yazo yana waje.

Aguje Salma tabar Dakin.

Dariya Rahama tayi dan a tunanin ta salma tasauko tana kaunar farin cikin ta.

Salma daidan wajen zauren gidan su ta tsaya tana.....

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah

Saura page biyu InshAllah ingama free
Masu bukatan cigaban labari zaku iya biya acct n'a sama
3/20/22, 22:34 - A'ish: *🌟🌟 KANWATA🌟🌟*

Paid book ne

300 vip

500 spécial

Àcct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ko kuma Katin MTN
Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

Saura page daya ingama free wayanda basu siya ba ku hanzarta kubiya.

2️⃣4️⃣

Ta tsaya tana kokarin fiddo maganin Daga jakar ta.
Abubakar da buta ke hannun sa yafito toilette sake da baki yake kallon abunda take shirin yi.

Tsayuwar sa taji akan ta bakaramin firgita tayi ba har tana neman faduwa.

Azabure tana sakalo murmushin dole tace yaya kaine cikin muryan ta dake rawa.

Kallon yake yana nazartan yanayin ta yace au baki ganni ba tundazu me kikeyi ne.

Me wannan à hannun ki
Cikin inda inda tace tozali nane nake dubawa Ko yana nan.

Sai anan zaki duba ya jefo mata tambaya.
Yana mai tsareta da idanu.

A'a yaya kawai de inadubawa ne.

OK to ina zakije ne ?

Yaya adamsy ne yakirani zanje mu gaisa yanzu zandawo batareda tajira amsar shi ba tafita jiki n'a rawa.

Tana fitowa kofar gida ajiyar zuciya ta soma saukewa tace azuciyar ta.
Da wannan uban nacin yaga abunda zanyi shikenan daya tonamin asiri gashi ta dalilin shi bansamu nayi ba.

Oh my God ta furta ta dunkule hannayen ta tabugi iska.

Adamsy dake tsaye jikin motar sa yaci kananun kaya sanye yake da wando jeans riga teashot hash kala ba karamin kyau yayi ba sajen shi kwance lub à fuskar shi.

Da fara'a dauke a fuskar shi yake kallon salma yace *kanwata* ya n'a ganki à birkice haka.

Kaman wacce tayi wasan gudu.
Haushin shi taji danma ya raina mata wayau ita ze fadawa haka.

Karasowa gaban shi tayi tace yaya n'a ai antina ce muke rige rigen waze fara ganinka.
Dariya yayi yace ai ita basai tayi rige rigen ganina ba.

Dan zamu kasance taré n'a har a bada.

Kekuma Al'amin zakiyiwa wannan tseren dan kiga fuskar abun ki.
Koba Al'amin naji ance sunan shi ba.
Yana kashe mata idanu cikin tsokana..

Salma ranta yakai kololuwa wajen baci tace ayya hakane kuma ai shima Al'amin din yanzu ze zo.

Jiki asanyaye tace ni zanshige Girgiza mata kai yayi yana kallon ta harta shige.

Baza idanu yayi yaga ta inda tauraruwar sa zata Bullo.

Yayin da iska take busowa yanajin shi cikin shauki da begen abun son sa.

Cike da nutsuwar ta da kasaitar ta tafito kamshin turaren ta ya doki hancin sa.
Sai asannan yadago kai yake kallon ta babu Ko kiftawa.

Sarki ya tabbata ga ubangiji kyakaywa.

Murmushi tayi cikin girmamawa ta gaishe shi.

Kasa cire idanu yayi akan ta saida ta soma tsarguwa da kallon da yake binta dashi.

Turo baki tayi gaba tace wannan kallon fa.

Murmushi yayi yace menene dan n'a kalli fuskar matata.
Uwar yaya n'a ?

Girgiza masa kai tayi tace babu laifi amma ka rage.
Kallon shigar da tayi yakeyi.
yace gaskiya dole inbiya wankan nan.

Sanye take da abayas doguwar riga égyptien yasha stonne gaba da baya tayi Rolling dankwalin akan ta.

MashaAllah ya furta tareda dauko wayar sa ze masu selfie.
Yayi juyin duniya Rahama tace Sam bazatai hoton ba.
Beji dadi aransa ba amma ya dake yace idan kinzo gidana zanga tayanda zaki hana muyi hoto.

Dariya tayi mai sauti bazan dade ba kasan yau zamuje makarfi so muke Muje dawuri.

Adamsy yace Ko zaku bari ni inkaiku ne.

A'a kabarshi drever Abba ne zekaimu jibi ze koma yadauko mu.

Bandir din dubu daya yabata dakyar ta amsa tana mai masa godiya.
Sunkai mintina goma

Kafun suyi sallama Cike da begen juna.

**,********

Salma tana shiga daki kuka tasaki mai cin rai tace yanzu shikenan burina baze cikaba wata zuciyar tace ai zecika tunda jibi zaku dawo ana saura kwana uku daurin aure.

Murmushi tayi tace ai har yanzu ina nan akan bakata wlh dan saina wulakanta ku.

Zan auri Al'amin InshAllah Rahama saide à daura auren naki da dan gamai ruwa n'a miki alkawari ni salma abdurrazak zansaki kuka ranar daurin auren ki.

Badainiba shibanda munafukine adamsy nifa ya fara gani yabiyo dan yahada ido da mai farar kafa yace ai ita yabiyo.

Cijje labban ta tayi tace Muje zuwa wanda ya fasa badan halak bane.
Shegu taron matsiyata har ita ànty.

Sallamar Rahama ne ya katse mata surutan da takeyi..

Cikin Jin dadi Rahama tace salma kinga kudin da adamsy yabamu.

Murmushi dole salma tayi tace kai amma wannan adamun yana mugun ji dake Rahama.

Eh wlh Rahama ta furta yi maza ki dauko mana jakar kayan mu.

Abba yace mufito mu ake jira bara inshiga ciki muyi sallama da su mama da ànty tareda jama'ar gidan.

Tana fita.

Salma taringa watso mata harara Jiki asanyaye tadau jakar kayan nasu tafito.

Rahama saida tayiwa kowa sallama suka bisu da Adu'ar Allah yatsare hanya.

Mama taja salma gefe tace karki damu yata ai Al'amin dinnan yayi degree yana samun aiki zaki Faso gari yata karki damu shi Adamun beda halin kirki iyayen sa 'mutanen banza ne.
Chapter 17 · 0% Book details