← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 115

Sashe 51

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yawwa gwamma da kuka taru Anan gobe ne tafiya ta nida Aminina, dan Allah ku tsare gida da mutunci.
Har Allah ya dawo dani.
Ke kuma Ànty yakamata ki je asibiti su dauraki akan magani kinsan mata irin ki n'a bukatar hakan.
Insha Allah zanje ànty ta furta tace" daman nazo muyi magana akan Rahama.
Jin ta Ambaci Rahama yasashi maida hankalin sa akan ta..
Mama dake kallon su Ranta yakai kololuwa wajen baci.
Ànty cike da nutsuwa take ba sheik labarin lefen da ke gidan Rahama.
Sheik yace" To ai inhar Saboda ita aka kai tana iya amfani dasu tunda dai ba ita ta nema ba, Iyayen Adamu ne suka aiko.
Maganar gold dasuke cikin akwatunan ta tazuba a wadrope din.
Ànty tace saura daya.
Murmushi yayi yace" fadi inajin ki.
Cikin yin kasa da murya tace" Gidan Rahama nake son zuwa Insha Allah Ko nan da jibi ne.
Sheik yace" Masha Allah zaki je dubo Y'ar taki Allah yakaimu, inzaki je kisa drever yakaiki yadawo dake..
Cikin gamsuwa da bayannan sa tace to.
Sheik kallon Mama yayi da kiris yarage ta fashe yace" ki gayawa Salma ta rike mutunci auren ta tazauna waje daya banda yawo da auren wani akan ta..
Mama cikin bacin rai tace kullum baka kyawawan zato akan Salma, wai me ta tsare maka ne haba ai wannan tsana ce, Ko ince kiyayya ce.
Tunda take zazzaga ruwan masifa sheik ya mike tsaye yana kallon Ànty, yace" Sa'adatu yau dakin wa nake acikin ku..
Ànty tace dakin ta yake OK to saina dawo yafice adakin dan kwata kwata beson biye mata.
Ita Ko Ànty fuskantar mama tayi tace haba Aishatu kina ban mamaki Wallahi Rahama diyar ki ce ta cikin ki amma kike nuna mata rashin kauna..
Me laifina dan Rahama tana Y'ar daki n'a?
Wallahi duk abunda zakiyi saide kiyi Wallahi bazan taba Jin ina tsanar Rahama ba, koda kuwa ita Rahama ta nuna bata yi Uban ta ya damka mun Amanar ta karkiyi tunanin kinayin haka ne dan naji haushi, 'Ko yau Allah yabarni ban haihu ba bazanyi bakin ciki ba tunda ina da Rahama...
Tsaya kiji dakyau Wallahi tallahi rantsuwar musulmi nafison Rahama akan Abdul jalil kinko san da cikina n'a haife shi..
Wallahi zakiyi kuka da idanun ki kirubuta ki ajiye.
Tun zuwana gidan nan nakebin ki da lalama burina mu zauna lafiya.
Sheik dai yana mutunta ki sossai dan na lura yafi sonki akaina hakan be taba batamin rai ba Saboda nasan taré naganku, amma kuma mutuntuwa fa yafi ganin mutuncina akan naki ,Saboda kin zubar da girman ki antake shi.
Kinba Y'ar ki mummunar Tarbiyya Wallahi da hannuna Salma ta zauna nasan Allah shine mai shiryawa da Wallahi ansamu saukin tabarar da take yi " Ta k'arashe zancen tana kokarin barin dakin.
Mama ce ta dakatar da ita cikin isa ta k'araso gaban ta tace" ke Sa'adatu kike Ko tsiya.
Ai ke baki isa kice banda Tarbiyya ba shiyasa Ya'ta Salma batada shi ba.
Mu bama bin bokaye da malamai ba dole sheik ya mutuntaki ba
Kuma....
Sallamar Salma da Abubakar ne yasa Mama yin shiru.. Cikin b'acin rai taga Abubakar tasan wa'azi ze tsaya musu barin wajen tayi kamar zata bangaje Ànty....
Salma banda harara babu abunda take jifan Ànty dashi.
Har zata juya Abubakar cikin tsawa yace Salma zo nan .Jiki babu kwarai tazo cikin tsoro..
Kallon banza yake binta dashi yace" Wannan ba Uwar Ki bace kike hararen ta, Matar da duk wata matsalar ki tazo itace kan gaba itace me nuna jajircewa akan ki, duk da rashin hankalin da kike nuna mata.
Maza ki duka ki bata hakuri Ko inyi kasa kasa dake.
Ànty Murmushi tayi tace" Haba Abubakar Yarinya ce fa haryanzu ka kyaleta karka damu Ko taki taso ni uwar ta ce.
Cikin zumbure zumbure baki ta dur kusa cikin muryan takura tace" Ànty kiyi hakuri Daga haka ta Mike tayi sashin Uwar ta..

Abubakar hakuri yake ta ba Ànty yace" Tayi hakuri shibesan irin Mama ba.
Amma wataran zata gane gaskiya.
Ànty tace" karka damu d'ana Allah yadada shiryamu dukan mu..
Da ameen suka amsa dukan su....

************************

Samad kwance yake kan kujerar falo 3str Idanun sa a lumshe zakai tunanin kallo yake ,amma Sam yayi zurfi a tunani har barci yafara daukan sa nan take wajen yayi barci.
Cikin barcin yafara mafarkin wannan zanen tashi daya zana.

Tafiya yake cikin ciyayi inda wajen zagaye yake da fulawowi masu ban sha'awa gwanin burgewa.

Sai fadi yake ina kike ne hasken zuciya ta yau raina a b'ace yake, pls dan fito mana kidaina boye mun wannan kyawawan fuskar taki kullum cikin nikaf kike, amma bankasa kazo zanen naki à nikaf din ba.

Dariyar yaji wanda yasa shi juyowa yana kallon ta tana tahowa cikin wani irin tafiya mai daukar hankalin, tasha ado kamar Matar basarake stil dai wannan nikaf din n'a fuskar ta..
Fuskar ta dauke da Murmushi tace........

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah

Yawwa comment yawan typin
3/21/22, 07:44 - Nuriyyat: KANWATA

LITTAFIN NAN KUDI NE INKIN GANSHI A WAJEN GROUP DÃŽNA NA SATA NE.
INKIN BUKATA GA NOMBA
09069080725

5️⃣3️⃣

Tace yakai Amjad din zuciya madubin dubawa ta hasken idaniya ta.
Tabbas ni ta kace kuma uwar yayan ka haryanzu baka gamsu bane tana Murmushi mai kayyatar da masoyin ta.
Samad cikin shakuwa yake nuna mata ta kalli sama kusan atare suka Daga kai suna kallo.
Yace kinga yanda sararin samaniyar nan ke haskawa haka kaunar ki take karuwa acikin zuciya ta '' pls Abar sona ki gayamin gidan naku Ko ince inda zan same ki.
Kinmin Alkawari zaki tsaya mun akan komai n'a rayuwa ta.
Kwabe fuska tayi cikin wasa tace kai Amjad dîna kasan dani kaje kayi aure.
Kallon yake cikin kasa da murya yace nayi aure kisani batada gurbi acikin zuciyata kece muradina ita Zabin iyayena ce ki fahimce ni.
Kallon shi take kallo mai daukan hankali 'kallo mai nutsar da zuciyar ma'abota soyayya.
Wacce ka aura bazan iya zaman kishi da ita ba.
Yarinya mai kamala ma'abociya addini ce saurin katse ta yayi da fadin kamarke haka take !!
Ki fadamin sunan ki da unguwar kinada ga cikin dalilin zuwa n'a kano.
Kince innazo zanga mahaifina nazo Amma shiru ne bangan shi ba..
Kallon shi take tana nazarin kalaman sa.
Ahankali take motsa labban ta tace kaine kake ganin bakaga mahaifin ka ba.
amma shi yasan da inda kake kuma yanada labarin ka.
Alkawari daya zaka min duk rintsi karka wulakan ta matar ka.
Koda kuwa bakason ta.
Banason ka aikata aikin d'ana sani InshAllah nakusa bude maka wannan kyawawan fuskar da kake ambata kana son gani..
Tashi tayi zata fice.
Da sauri Samad yasha gaban ta yace yau ba zamuyi yawo cikin jejin nan bane.
Girgiza kai tayi Alamun A'a.
Ganin tana ta zuba uban sauri yana ihu dan dakata mana.
Faruk tsaye akan sa rike da kugun sa hannun yasa yasoma bugun kafar sa firgit ya farka Idanun sa yasauka akan Faruk..
Faruk yace haba yaushe rabon da kayi mafarkin nan tun kan kayi aure.
Shikenan mun shiga uku mafarkin yadawo wlh Samad harda Aljanu ke damun ka..

Tashi Samad yayi Daga kwance yana mika hade da hamma cikin muryan barci yace nifa banason sa'idanu ina ruwan ka da mafarkin inbanda gulma n'a cinka.
Faruk rike da baki yace wallahi matarka saida ta toshe kunnen ta yanda kake ta ihu kana fadin ki tsaya karki tafi dan iska tashi kabita mana amma ba anan zaka baje mana kana kashe mana kunnuwa ba.....
Aminu ne yakaraso falon yace Faruk dafatan dai ya farka Ko caraf Idanun sa suka tsarke cikin juna shida Samad dake hararan sa yana tsaki.
Barin su yayi cikin sauri yake hawa kan matakalan step direct dakin sa ya nufa...

Faruk da Aminu kallon shi suke harya shige dakin.
Faruk yace gaskiya mu nemo masa magani karya Aljana ta aure shi..
Aminu yace kuma hakane amma dole ne mu nema mishi magani....

Samad n'a shiga dakin kan gadon sa yafada yana mika hade da kara rufa lausasan bargon sa ajiki..
Adu'oi kariya yafara karantowa yana gama adu'a ya tofe jikin sa..
Kallon inda Rahama ke kwanciya yayi ganin wayam babu ma kayan ta awajen Abunda yafaru dazun ne yafara dawo masa cikin kan sa.
Jikin sa a mace ya furta ya Salam wai me damun sa ne meyasa yaci zarafin wannan kanwar Rahama wata zuciyar tace yarinyar ce batada hankali '' amma duk da haka yana ganin kamar yayi kuskure hana Rahama rakiya cike da tunani barci yayi awon gaba dashi...

Itakuwa Rahama zaune kan dadduma tana waya da Asiya cikin Jin dadi tace kice gobe ina manyan baki.
Asiya tace kwarai kuwa gayamin me zaki dafa mun me dankaren dadi.
Rahama jujjuya Idanun ta tayi wanda ya bayyana cikar Idanun ta tace uhmm ke ai nidake babu shamaki tsakanin mu duk abunda kike so zan dafa miki ko ki dafa da kan ki..
Asiya tace ke dai Allah yakaimu Aminiyata.
Da ameen ta amsa mata.
Asiya tace Rahama wai meyasa bakya yawan hawa online ne Ko mijin naki beso ne ?
Chapter 51 · 0% Book details