← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 115

Sashe 29

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

MAMY tsaf suka SHIRYA zasu wuce khadija fuskar cike da damuwa zasu tafi subar Rahama '' Ahmed yace Mamy muyi sauri kada mu makara fa.
YARIMA Samad suka hango yana saukowa Daga kan matakalan step da sassarfa cikin shigar shi ta wani tsadaddan boyel yasaka hula bakaramin kyau yayiwa Mamy ba harya tuna mata da mijin ta.
Inakwana mamy yafada fuska a sake lafiya lau tabashi amsa Khadija da Ahmed suka gaishe cikin saikin fuska yace au duk kun Kosa ku tafi Ko.
Nima din nakusa zuwa yafada yana lacakan bakin khadija.
Khadija cikin shagwaba tace Mamy kina gani Ko.
Mamy tace babu ruwana kullum yara kuke komawa shida yayi aure yakamata yafara hankali.
Hade fuska yayi yanajin haushin furucin Mamy.
Mamy tace wai ina Rahama ne banji duriyar ta taci brek din da aka kai mata kuwa.
Eh Mamy tacinye duka harda side kwanun yafada cikin sanyin murya.
Mamay tace bara inje dakaina in sauko da ita kasan inason ta saki jikinta tafada tareda bin hanyar matakalan step.
Hankalin Yarima Samad yayi mugun tashi dan yasan Rahama tana zaune kan wannan bargon da ta kwana jiya.
Mamy n'a gani komai ze iya faruwa.
Cikin sauri yabi bayan Mamy da hannun ta yakai kan handle din kofar zata bude tashiga.
Kama hannun Mamy yayi à hankali atashe ya.....

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/20/22, 22:34 - A'ish: KANWATA

Akwai channel dîna KYAUTA TV kushiga ku danna mun subcribe.

Littafin kaikajawa kanka
Audio yana kan channel dîna saina jiku.

Littafin nan kudi ne.
Inkin ganshi a wajen group dîna na sata ne
Inkina bukata ga nomba
09069080725.

3️⃣4️⃣

Kama hannun Mamy yayi hankali atashe.
Mamy kallon sa take da mamaki tace yadai lafiya kuwa tana mai kallon hannun ta daya rike..
Murmushin yayi yana sosa keya yace namance ban gayamiki ba tashiga wanka nasan yanzu tana kokarin shiryawa yakarashe zancen cikin tsoron kada ta bude.
Murmushi Mamy tayi tace kuma kafini gaskiya dole ne sai n'a nemi izini kafun nashiga bara n'a
koma kasa in jira tagama dan Allah shiga ka gayamata tayi sauri.
Juyawa tayi tana kada kai mamakin Yarima takeyi yanda taga tsoron ta a Idanun sa murmushi tayi tace saida haka ake zama lafiya dasu.
Shiko Yarima Samad dakin ya shiga babu sallama iske ta yayi bata nan Jin karar ruwa yasashi sanin tana toilette.
Kwankwasa kofar toilette din yayi.
Rahama gaban ta ne ya fadi Jin buga kofa da akai.
Kayan data cire ta maida tareda fitowa Daga toilette din duk kayan jikin ta damshin ruwa yasa sun dan jike.
Kallon ta yake tunda tafito yanda take raba gefen sa.
Cikin bada umarni yace. Keee kadangaruwa yi maza kishirya Mamy yau zasu wuce '' tanason ganin ki yanzu'' gyada kai tayi alamun gamsuwa.
Ganin takasa aikata komai yace ba magana nake miki bane cikin Daga murya nace jiranki ake ki canja Muje Ko yakarasa zancen cikin Jin haushin ta.
Cikin muryan ta mai dadin sauraro tace dan Allah ka fita zan canja kaya.
Uhmm yayi yana kallon ta hannayen sa cikin aljihun rigar sa yafice Daga dakin dan shi ya manta da yafita din saida ta tuna masa.
Mamy tace yanaga kataho kai kadai ina take ne bata gama rufe baki ba tahango Rahama n'a kokarin saukowa Daga kan matakalan Stép sanye take da doguwar riga material mai Stone marron color ta yafa mayafin ta maroon kafar ta dauke da takalmi flat cike da nutsuwa takaraso falon gaishe da mamy tayi a ladabce tareda gaida Ahmed da khadija cikin sakin fuska.
Mamy cikin Jin dadi ganin Rahama tace diya ta yau zamu koma kasar mu sai Allah yakawo ki
Rahama duk yanayin ta ya canja tadawo kalan tausayi Mamy ta lura Sam batason Tafiyar tasu hakan yasa Ta kalli Abdul Samad ta tace to mudai zamu tafi karka manta in bana nan akwai Allah.
Mamakin furucin Mamy yayi cikin son kawar da zancen yace mu je Mamy kada mu latti.
Khadija n'a kuka Rahama n'a kukan Rabasu da za'ai.
Shiko Yarima kallon ikon Allah yake yaushe suka San juna da har suke kuka.
Cikin sauri sukabar gidan Rahama tana kallon motar su yatashi wanda mijin ta ne ke tukin.
Kukan zuci take tace yau gidan nan zemin zafi cikin sanyin jiki takoma gidan tana tunanin abunda zatayi.

Har airport yakaisu suna zuwa yayi daidai da jirgi ze tashi babu bata lokaci suka shiga '' yarima n'a kallon su har jirgi nasu ya tashi.
Komawa yayi inda motar sa take 'cikin sauri yabar filin airport.

*******************

Mama da kawar ta Talatu suna shawaran yanda za' akai kayan Salma.
Talatu tace mun je munga gidan gaskiya dakin yayi kadan haba yarasa inda ze kama haya sai wajen gari gaskiya yaron nan beda Adalci.
Mama tasauke nauyayyen ajiyar zuciya tace yazanyi talatu n'a gayawa uban ta yakama musu haya koda babban gida ne nasu sukadai yace Sam besan wannan zancen ba waishi hakkin Salma yafita akan sa abunda yazama wajibi akan sa yariga yayi mata.
Uhmm talatu tace tana mai gyara zaman ta tace ina hankalin ki yake ne.
Mama tace bangane mekike nufi hankali yana kanki.
Uhmm gaskiya baya kanki céwar talatu.
Ke baki lura ba a gidan nan kece babba fa amma sheik duk abunda Sa'adatu ta fada wlh baya mu sa mata da itace tace a kamawa Salma haya wlh saiyayi shi koda kuwa beso.
Da jimm Mama tayi tayi tagumi tace aini tariga ta shanye shi ta wanke ta bashi yasha ai Allah yahadaka kishi da fulani wallahi kabani.
Talatu hararar mama tayi tace ke bazaki tashi tsaye ba ki kwatar wa kanki yanci ba '' ba ina nufin kishiga malamai ba.
Yaki zakiyi acikin gidan ki. wallahi matarbarki da kimar ki yadawo Idanun Sheik.
Sallamar Ànty ne yasa talatu yin shiru tana me sakarwa ànty murmushin yake.
Maman Rahama ke ce ?.
Eh Nice inna Talatu'' ànty tabata amsa.
Tana me kallon Mama da ta juya musu baya.
Cikin sanyin murya tace Maman Salma wajen ki nazo.
Mama tajuyo tace inajin ki Ranta abace take magana hakan da takeyi ita anty Ko ajikin ta.
Dama batun kai kayan Salma ne wayanda basu zama dole sai tayi amfani dasu ba ajiye su zamuyi a store dan dakin nata bashida girma '' Sannan kibada kudin da za'aje adauko mai makeup kamata yayi akai Amarya tsaf tsaf da ita gwanin ban sha'awa tafada tana kallon talatu.
Talatu tace kwarai kuwa maman Rahama maganar ki dutse.
Mama ta waigo tana kallon ànty tace babu matsala zan aiko da kudin abaki.
Cikin Gamsuwa ànty tace saina jiki tareda barin dakin.
Mama da talatu suka kalli juna atare.
Talatu tace baga irin ta nan ba wlh babu asirin da matar nan take miki ''..
ta iya kissa da kisisina jifa yanzu tazo tana tambayar kudin makeup.
Uban Salman shima wani abun daban zata ce ana bukata ahaka zata siye miki miji ke kina zaune wai kishi Allah natuba wa ke ta kishi yanzu kishina sutura ta wlh ki daura dammara kawata.
Shewa suka buga Mama da kawar ta '
Shiyasa nake son ki talatu kanki yana ja InshAllah zan bi shawaran ki.
...

Salma suna zaune itada Aminiyar ta Amina suna shawaran yanda zasu yiwa Al'amin asiri dan ya sake ta.
Amina tace kyalemu dashi ai yau zaki taré Ko nasan da wuya ki samu magani yau ki jira cikin satin dakaina zanje miki.
Amma haryanzu kin tsaura kinason Adamsy kuwa tana kallon Salma.
Salma ta numfasa tace kedai me zanyi da Adamsy ga Abdul Samad.
Cikin zazzare idanu Amina tace bangane ga Abdul Samad ba.
Mijin yayar taki.
Salma tace kwarai kuwa shinake nufi.
Tashi tayi Daga zaunen da take tareda jujjuyawa tana kada kugun ta tace kalleni Amina dan Allah banida diri ne Ko kyau ne bandashi.
Tun Ranar d'ana fara ganin mijin Rahama naji ya kwanta min.
Amina cikin bacin Rai tace haba Salma meyasa bazaki sassauta wa Rahama ba jibi abunda kikai mata akan Adamu.
Sai Allah yabata wanda yafishi ni kinga badani za'a lalata aure ba dama ace be aure ta bane sai mu Rabasu '' cikin bacin rai Amina ta d'au jakar ta zata fita '' a guje Salma tarike hannun ta tace haba Daga ina miki wasa saikiyi zuciya.
Tsaki Amina tayi tace ai aure yawuce wasa.
Salma Dakyar ta rarrashi Amina ta hakura tazauna jiran lokacin daukar Amarya.
Chapter 29 · 0% Book details