← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 115

Sashe 105

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin Ahmed tafara lale lale da zuwan Angon Asiya...
Sossai ya fadada murmushin sa yace pls antina dan Allah kibamu waje zan danyi magana da ita.....

Rahama tace Salma tashi Muje mudawo ango ze gana da Amaryar sa....

Suna fita Ahmad yadawo da kallon sa Akan Asiya dake chattin data nuna bama tasan dashi ba..

Tabe baki yayi yace ke Asiya kike Ko menene sunan naki ni sam bana haddace sunan ki....

Dago kai tayi tana kallon da Idanun ta da suka kada jajir da kuka...

Suna hada idanu jiyayi ta sauya masa tayi bala'in kyau '' kawai de daka kalle ta zakasan bata cikin walwala...

Tabe baki yayi yace uhmm ke kowace Amarya tana kyau ranar daurin auren nata amma. Bandake...

Shiru tayi tareda maida hankalin ta akan wayar ta..
Hakan bakaramin bata masa rai yayi...
Hannun yasa ya Dago ta... Cikin zafin nama...
Saida yakai ta bangon dakin..
Zazzare idanu tasoma tana son tace lafiya kuwa....
Gani tayi yasa hannun sa yana...................

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:57 - Nuriyyat: KANWATA

09069080725

https://youtube.com/channel/UCCb-59DLAXr2BDMl3XJQvIA

Dan Allah channel dîna KYAUTA TV nan à sama kushiga ku danna mun subcribe 👆🏻

Saina jiku Masoya n'a...

Akwai Sabon Littafina wanda ze zomu ku da Zafi zafin sa..

Mai Suna *RUDANI* kai Dagajin sunan kunsan akwai akwai abubuwan masu ruda kwakwalwa 'dakuma ban Al'ajabi..
Wannan littafin tsaf n'a shirya wajen baje basira ta..
Kunsan Alkamila baya rubuta shirme.

KYAUTA DAGA Allah.

Shalelen Jarumai writ associat...

9️⃣7️⃣

Yasa hannun sa daidai wuyar ta yana shafawa..
Uhmm kinji tsoro ko kinyi tunanin wani abu zanmiki.
Ba'abunda zan miki Asiya..
Yawwa maza ki fito mu d'au hoto kinsan zuwa gobe kina hannuna Ko dafatan kin shirya karawa dani dan ninan ba kanwar lasa bane.......
Murmushi tayi tana ganin zallan yarinyar da ke dibansa cikin sassaita muryan sa tace uhmm aini ban isa inkara da mijina ba '' wake wasa da wuta.
Fada da Aljani aiba dadi 'babu nasara...
Cike da mamaki yake nazarin kalaman ta yace duk kiyi kigama me kamata kiyi laushi ba...
Cikin d'Anne fushin ta tace dole ne inyi laushi in ina gaban ka' 'sanin danayi maka Ada daban yanzu kai mutum mafi daraja ne awajena karka damu duk abunda zakayi zan jure lada nake nema agun ubangiji n'a...
Wanda yace duk wanda ya zalunce dan uwan sa InshAllah baze kyaleshi ba..
Dan baya yafe hakkin wani akan wani...

Sossai maganar ta yashige shi cike da mamakin ta betaba sanin tanada hankali ba saiyau to jiji da kan da take nuna masa agida n'a menene rasa me basa amsa yasashi Fadin Allah yakyauta yanzu Muje muyi hotuna so yake ya watsar da kudurin sa saboda kalaman da tace Allah baya yafe hakkin wani...
Wata zuciyar tace kai harka saurare ta wacce take ce maka drever...
Barin wani tunanin yayi yaja hannun ta suka nufo cikin jama'a..
Sossai jama'ar wajen suka ringa Fadin waouh Amma fa Amarya da angon n'a sun mugun dacewa 'jibi fa..

Wayannan kawaye biyu Rahama da Asiya' sunada Farin jini Samun attajirai.
Haka akayi ta fira sossai agidan bikin akan su......

Yana sunsha hotuna sossai yayi daidai dazuwan su mama Firdausi da Yarima da su Faruk harda Abban marwan da sauran à bokan tafiya sunzo da motoci guda Ashirin n'a daukar Amarya....

Sossai unguwar ta cika makil...
Yarima Samad karasowa yayi ciki ganin Ahamd da marwan yace ya Salam yan iska daman kuna nan nake ta neman ku...
Ahmad yace haba Yaya nifa angon Asiya ne kake zagina...

Yarima Da Faruk rike baki sukayi suna kallon juna sukace ah ah to gayamana tunda bamu sani ba...
Baza idanu yake ina ze hango Rahama...
Hango ta yayi tana kokarin shiga dakin Asiya ya dakatar da ita tahanyar kiran sunan ta..
Yace kai mata ta kizo mana tunjiya kinmun wuyar gani..
Uhmm zomu dauki hotuna dasu Mama firdausi amma je ki fitowa mana da Amarya....
Murmushi ta sakar masa tace yawwa to ina zuwa yanzu zamu taho taré da ita.....

Suna fitowa aka fara daukan zafafan hotuna masu daukar ido...
Asiya sossai ta sake à kasha hotuna..
Harda Ahmad suka d'au hotunan....
Basu wani bata lokaci ba sukace zasu tafi da Amarya gidan Sheik zata kwana har zuwa goben...
Sossai kakkanin Amarya da iyayen ta suka mata Rakiya....
Hakan yasa aka bude motoci kowa ya shiga ba'a zarce Ko ina ba..
Sai gidan Sheik Abdurrazak..

Koda suka isa nan da nan aka shiga yiwa Amarya da ango fada akan tsoron Allah harda mahaifin Asiya yana gidan sheik sunzo tayashi murna karin auren sa...

Hakan yasa yazaunar da Ahmad da Asiya yayi masu fada sossai mai ratsa zukata.
Ahamd d'uk wani mugun tunanin sa yafara canzawa beyi tunanin akwai abunda ze hana shi yiwa Asiya wulakanci ba...

Tasha kuka sossai harda shesheka sossai Ahamd yaji tabashi tausayi harna zargin kansa anya badan ya kwacewa Faruk bane take kuka ba..
Sai yanzu yakejin haushin abunda yayi...
Itako Asiya tana kukan rabuwa da iyaye 'da kuma tunanin wani irin rayuwa zatayi a hannun Ahmad...

Abban Asiya yana gama masu nasiha sheik da abokansa suka daura da nasu' 'dan bakaramin Aya sheik ya jawo ya fassara ba......
Yakara kashe musu jiki..
Haka dai akayi cikin gidan da Asiya da taimakon yan uwan nata...

Cikin gidan ba'a barta abaya ba nasiha akayi mata sossai harda mama da Ànty.
Salma tana gefe tana cika tana batsewa wai ita à la dole abby ya mata wulakanci...
Rahama bayan kowa yawatse takai Asiya dakin nata...
Salma take masu baya tayi tace yawwa anty Rahama inason ganin ki....
Hakan yasa Rahama fadin gani Salma ya akayi ne naga taré muke tundazun....
Eh mana inason Inkin fito nan kizo sashin Mama maganar sirri ce....
Rahama cikin rashin kawo komai aranta tace to zanzo InshAllah dana gama......

Sheik waya yakeyi da baba Salihu akan suna airport yanzu Jirgin nasu ze wuce amma suna tareda Yar ta Hauwa wacce zata wuce kano....
Dan ta kuma shidawo Gabon tareda yayar mamar sa da zata rako su..

Sossai Sheik yaji dadin bayanan shugaban Adalai.....

Hassana cike da mamaki take tace Sheik tundazu be nemeta ba tunda yaji andaura aure...
Danna masa kira tayi hakan yasa ya Daga wayar tana hannun sa..
Cike da Jin dadi Yace Amarya ce dakanta.
Tace eh nice 'wai ace tundazun baka kirani ba..
Haba honey..
Murmushi yayi yace kedai hassana dan yana cikin mutane be iya kiran ta da wani sunan...
Taron jama'a sai à hankali kinji dalili n'a yi hakuri....
Jin kamar anfara kiraye kirayen sunan masu tafiya kano...
Tace to gashi zamu t'aso yanzu InshAllah...
Sheik yace Allah yatsare ya kuma kawo min ke lafiya dake da yan rakiya ameen ta furta cike da jin dadi.......
Babu bata lokaci duk suka Shiga a jirgi daya tashi dasu sararin Samaniya....

Kano

Yarima Samad zaune adakin da suka sauka yana chat da Yusuf Sani yaro akan gobe yasa à kawo Saratu airport..

Yusuf yace ah ah dakaina zan kawo ta kuma zanzo da mata ta zamu raka ku kwatano inyi muku Allah yasanya Alkhairi tunda bansamu zuwa daurin aure ba..
Sossai Yarima Samad yaji dadin haka..

Yace da so samune da katsaya ayi shari'a dakai Yusuf...
Yusuf yace ni ba lauya ba wannan ai aikin naku ne.....
Yarima Samad yace yawwa akwai wata kanwar mata ta nan yashiga bashi labarin duk abunda yafaru ya kuma tura masa wannan video da Cctv camera dinsa ya dauka yace....
Wallahi ina tsoron kada ta cutar mun da ita bare yanzu suna waje daya..
Yusuf n'a kallon vidéo yace subuhannalah wannan ai makira ce saita kashe mutum...
Har vidéo biyu wani tana Barbade wani kuma abinci zata zuba magani...
Hoton roban poisson din daya amsa hannun ta ya tura masa...
Yusuf yace yanzu ya kake so ayi kabada damar à kamata ne...
Yarima Samad yace uhmm banason mahaifin ta yaji haushina zan sanar masa da komai inhar ya amince à kamata à hukuntata koda na sati daya ne....
To zanma waya anjima.....
Yusuf yace gaskiya koya ce baza'a hukuntata ba.
Ni sainayi kwana uku kadai ya isheta ladabi da hankali da nutsuwa....

Yarima Samad Murmushi yayi yace nasan ka bakada wasa nawan sai kajini Daga haka sukayi sallama...

Kwatano....

Shugabar Kasar Niger yazo shida matar Amarya...
Gaban su akayi daurin auren...
Cewar su jibi zasu juya 'dan gobe su Karima zasu dawo..
Sossai yaji dadi sossai ganin matar sa Firdausi ta warke tsab kamar ba ita ba...
Ganin ta yasa ya mance wannan Amarya yatare adakin nata.....

Cewar shi tarée zasu kwana' 'Sam taki aminta tace haba' 'nan fa ba gidan ka bane..
Kabari saimun koma Niger din...

Cike da Jin dadi yace Ah Muje mu kama hôtel Alkur'an baki isa ba.... Tanaji tana gani yafito da ita Daga dakin....

Kai tsaya fadar Sarki ya nufa nan ya zayyana masa cewar matar sa ce..... Cike da mamaki Sarki yace wannan baiwar Mamy ce da Salihu yakawo...
Murmushi yayi yace ba baiwa bace Nina turo su dan amusu maganin hauka kuma Alhmdulilah sun samu waraka naso ace nayi tozali da sarkin Adalai....

Mai Martaba fashewa da kuka yayi yace yanzu kana nufin matar ka ce muka ringa mata kallon baiwa....

Iya Firdausi tace eh mai Martaba mijina ne kuma Yarima Samad da Abban shi sun ce kada mu taba bari asan Asalin mu..
Hakan zeja mana magauta...

Sarki Share hawayen sa yayi yace kuma gaskiya ne hakan '' kubari zuwa jibi kuntafi gobe Yarima Samad zasu dawo harda kariman kenan dasu zaka koma...

Shugaban kasa ya murmusa yace kwarai kuwa..
Nakama. Hôtel dîna iyalai n'a àcen zamu kwana...
Sossai mai Martaba yayi mamakin wannan Al'amarin....
Iya Fidausi koda suka fito tace masa su jira ta zata je ta sanarwa Mamy zanje kwana hôtel din..

Dole yabar ta tafi yana tsaye yana kallon takun tafiyar ta cike da nutsuwa hakan yakeji babu kamar acikin mata...

Koda yafito iske su bodygar dinsa yayi Alamun shi suke Jira..
Sossai maganar ya karade masarautar harda wajen gari cewar Karima diyar Shugaban kasar Niger ce uwar ta matar sa ne...

Anata kuskus labari yaje gun yan jaridu nan da nan suka fara wallafa bayanan da Aka basu agidan redio...
Chapter 105 · 0% Book details