← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 115

Sashe 18

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banda bauta babu abunda Rahama za taje yi a gidan.
Murmushi salma tayi azuciyar ta fadi take kema mama mai farar kafa tasiye ki..

To wlh koda yar aiki zata je yi gidan adamsy bazan bari ta aureshi ba bare zaman aure.

Afili tace Ayya mama karki damu ni tun yaushe ma nacire tunanin adamsy araina.

Mama Cike da Jin dadi salma tasauko tace Allah yayi maki Albarka da amin ta amsa.

Mama ta dan canja ne tunda mahaifiyar ta takira ta awaya ta zageta tsaf ta nuna yakamata ta jawo Rahama ajikin ta.

Kishi da ànty zatayi tacire yarta aciki dan suna tarayya da ànti.
Da wannan fadar da akayi mata tafara son yar ta har tana hira da ita.

Tana kokarin taga taraba ànty da Rahama amma Sam ànty taki bata dama intai maganar ai yar tace sai ànty tabata amsa da itace ta raineta tun tana karama kuma anbata ita aure kadai ze rabasu da Rahama..

Rakiya sukai masu har sheik shima baa barshi a baya ba 'suna kallon motar tasu ta tashi sai Daga masu hannu suke suna fadin Allah yatsare.

Gidan gabadaya Cike da kewa suke tafiyar Rahama dan bakaramin sabo sukai da ita ba.

........

Asiya hannunta dauke da dinkuna Cike à leda tazo Cikin girmamawa tagaida jama'ar gidan.

Kallon mama da ànty tayi tarasa wa zataba dinkunan acikin su..
Tana gudun tayi laifi dan tasan zaman da suke yi..

Murya cen kasa tace ànty gashi Rahama tace à baki ki ajiye mata..

Asiya n'a kokarin mikawa ànti mama ta taso ta ta kwace kayan tace banda shishigi kayan Rahama ai ni zan ajiye mata..

Anty tace Asiya kindai kawo sako Ko kina iya tafiya mun gode.

Asiya ta juya tanata girgiza kai.

***************

Kan hanyar su ta makarfi sunyi nisa sossai dan ma befi nan da mintuna a shirin ba suka sauka.

Cike da kwarewa drever ke tukin motar.

Rahama tuni barci yayi awon gaba da ita 'banda kallon ta babu abunda salma takeyi.
Tana tunanin yanda zatayi tunowa tayi akwai kudin da adamu yaba Rahama dasu ta taho ahankali tajawo jakar a kan kafafun Rahama durkusawa tayi acikin mota Saboda kada drever ya hango ta tacikin madubin mota.

Kirga kudin tayi taga dubu hamsin ne sabine kudi ne Daga gani à banki ya ciro su.

25k ta zara cikin jakar tareda saka wa cikin brezia dinta.

Komawa kan kujerar mota tayi tana kokarin maida jakar Rahama inda ta dauke su.

Rahama da batasan wainar da ake toyawa ba..
Har suka iso tana ta barci.

Cikin barci salma taringa bugun ta tashi ànty mun Iso.

Idanun ta tasoma murzawa tana bude su ahankali mika tasoma hade da hamma.
Idanun ta sun nuna tasha barci à mota.

Suna shiga gida sunsha tarba mekyau wajen matar kakar su.
Gidan iyayen sheik suka fara sauka nan nan da su tai tayi dasu matar kakar su.
Abinci me rai da lafiya ta girka musu.

Da yamma sheik kabeer yashigo Cike da fara'a yace yau wa nake gani kaman amare n'a.
Rahama tace aisune tunda kishi yahanaka zuwa kanon ganin mu.

Kallon salma yake yace uwar miskilan ci haryanzu kin saura da halin ki 'Allah yataimaka bani ne zan aure ki ba.
Danni kam nayafe mishi Al' amin din.
Dariya salma ta saki harda shewa tace naji din dandai kasan ba samu zakai ba shiyasa kace ka yafe.
Sunsha hira sossai da kakan su.
*******
Bayan sallah magrib Salma n'a idar da sallah tacewa Rahama bara inje shago insai wani abu.

Da to Rahama tabita dashi taci gaba da azkar din ta.
Salma tana fita shagon siyar da waya taje.

Mai shagon cikin Jin dadin ganin salma dan sun San Juna washe baki yake yace yau kune à gari.

Murmushin salma tayi tace ai yau ma dalili yakawo mu kasan mutumiyar ka ranar juma'a daurin auren ta.

MashaAllah MashaAllah amma Ko ina taya mijin daze aure ta murna dan wlh yayi babban kamu yarinya so silence ga kyau ga ilimi ga tarbiyya.

Salma cikin dakiya tace hakane dan walwalan t'a yarage Jin yanda yaketa yabon Rahama.

Mai shagon yace bismillah zauna ke kuma yaushe zakiyi auren ne.

Sai ranar da Allah yayi tabashi Amsa.
Allah yakawo lokaci yafurta mata.

Kallon wayoyin shagon tashiga yi ta nuna masa airtel touch yadauko mata.

Kallon wayar take tana tambayar sa Ko Android ce.
Yace kwarai kuwa itace ga kyau ga rikon caji...
Farashin sa 20k ne.

Bata nemi ragi ba tasai wayar tareda siyan layi mai rajista.

Saida ta tabbatar komai normal n'a wayar tasa yatura mata whsap..

Bata bar shagon dako kwandala ba.
Duka kudin ta kashe gun saka Kati.

Lalubo Katin marwan tayi acikin brezia tareda daukan nombar sa.
Tasa wayar ta.

Kira ta danna masa wayar tanata ring ba'a daga ba..

Kusan mis call shidda tayi masa.
Be Daga ba
Tana kokarin shiga gida taji wayar ta soma vibrer.
Alamun kira yashigo.

Komawa da baya baya tayi tashige wani lungun layin su.

Ta Daga Dagacen bangaren yace dawa nake magana ne naga mis call..

Murmushi salma tayi tace kako gane ni kuwa.

Nice wacce mu kazo airport nida yaya ta.
Har suka fadi itada uban gidan ka.
Bakaine kadauke su hoto à wayar ka ba.

Oh oh oh nagane ki yabata Amsa tun lokacin naita tsumayen ki saiyau kika neme ni.

Ajiyar zuciya salma tasauke cikin sanyin murya tace dan Allah wannan hoton daka dauke su yana nan à wayar ka kuwa.

Marwan dariya ta subce mishi yace to ita wannan me zatai da hoto kuma dukan Alamu ya nuna wacce yagansu tare yayar tace.
Akwai tsatsar kamanni da suke yi.

Amma tafita kyau sossai dan baza'a hada ba.

Dawo dashi Daga duniyar tunanin daya fada tayi tace kayi shiru koka goge ne ?

Ban goge ba turon lambar ki t'a whsap inmiki send dinsa yanzu.

Wani tsalle salma tayi tace ai da wannan nombar nakeyi inajiran ka.

Babu bata lokaci ta bude data.
Farkon abunda tayi tozali dashi kan whsap shine.......

Akwai channel dîna a YouTube mai suna
KYAUTA TV za'a fara daura audio din littafina n'a kaikajawa kanka.
Idan kunshiga ku danna mun subcribe.

Taku. Har kullum kyauta Daga Allah.

Saura page daya ingama free.
3/20/22, 22:34 - A'ish: *🌟🌟 KANWATA🌟🌟*

Paid book ne

300 vip

500 spécial

Àcct 3115484026 ikilima adamu fist bank

Ko kuma Katin MTN
Ta wannan lambar

09069080725

IKILIMA ADAM

KYAUTA DAGA Allah

Last free page domin cigaban labarin ku tuntubeni.

Page d'in sadaukarwa ne ga kungiyata jarumai writ association.

2️⃣5️⃣

Shine hoton da marwan yadauka a filin airport wani kayataccen murmushi ne kwance akan fuskar ta take kallon hoton waouh ta furta ta ayyana aranta yanda wasan ze kasance inhar Adamsy yaga hoton nan.

Jin motsin mutum à lungun yasa cikin hanzari tayi hanyar gida daidai shiga gidan marwan yakara kiran ta awaya dan gefe ta matsa ta Daga wayar murya cen kasa tace naga hoto yayi kyau sossai kabari gobe zamuyi waya kashe wayar zanyi.

Marwan dake kwance kan makeken gadon ya shafa gemun sa yayi yace toni me zaki bani wannan kyautar danai miki.
Cikin kosawa salma tace pls kabari gobe zan kira ka fada min sunan ka.

Marwan sani turaki yabata masa.

Suna me kyau tafurta tareda katse wayar.
Kashe wayar tayi gabadaya ta tura cikin brezia..

Kai tsaye ta cusa kanta cikin gidan hango Rahama tayi da kishiyar kakar su 'suna hira Rahama n'a dariya.
Da dukan alamu labarai masu Jan hankali take bata.

Kallon Salma sukai dake shigowa.
Kakar su tace haba salma baa San Amarya da yawo fa tundazun ina kikaje ne ke bakya Jin gajiya ne.

Salma turo baki tayi gaba tace gajiya kuma aita bi jiki yanzu banda ikon inje insai wani abu tana kokarin zama kusa da Rahama.

Rahama ta murmusa sai da kuncin ta ya lotsa tace uhmm yaudai naga fadan kishiyoyi 'maida kallon ta akan salma tayi tace my qanwaty wai ina kika tsaya ne Abba yakira waya yana son magana dake nace mai kina sallah banson yamiki fada.
Tafada cike da kulawa.

Gaban Salma saida yabuga rass.
Tace ikon Allah Ko me Abba ze cemun ne yake nema n'a.

Rahama tace nikam ina zansani tsakanin uba da ya ne.
Kaka tace ai gaskiya ne.

Rahama dauko wayar dake ring tayi ganin nombar Abba ne ke yawo akan screen din wayar.

Cikin hanzari tadaga.
Assalamu alaikum ya Abby.

Dagacen bangaren amsa mata yayi yace salma ta idar da sallah kuwa.
Duban salma take data kura mata idanu Alamun duk hiran da suke tanaji muryan n'a fita.

Eh Abba gatanan taré da mikawa salma wayar.

Cikin tsoro tace Abba inayini bayan sun gaisa yace yawwa maganar lefe ne kinsan bana amsar lefe agidana da duk wani abunda yazama Al'ada dan haka n'a ware kudi dubu dari biyar keda yayar ki zaku siye duk wani abunda kuke da bukata.
Sadakin ki yana hannuna.

Bayan daurin aure InshAllah zan damka miki à hannun ki.
Sannan jibi sammako zaku yi.
Cikin sanyin jiki tace Allah yakaimu.

........

Washe gari.

Bayan sun karya sunyi wanka tsaf suka shirya dan kaiwa mahaifiyar uwar su ziyara ' sheik kabeer da yafito Daga dakin sa' yana sanye da farar jallabiya.
Kallon su yake yanda suke ta dokin fita.

Rahama cike da ladabi tagaishe shi tace my ango sai yanzu kafito tun asuba daka shige Ko sanyi ne ke ratsaka nasan ka da tsoron sanyi.
Kayataccen murmushi yayi yace dadina dake Rahama akwai ganuwa.

Har kunshirya kenan zakuje gidan zubaida 'salma dake kallon sa tace cen muka nufa maza Muje kaimana rakiya.ta furta

Angama ranki yadade tunda umarni ne Muje to.
Yana gaba suna biye dashi abaya.

Matar kakar su rakiya tayi musu tace aida goben zaku kai yamma da taré muka je danni ban amso dinkuna n'a ba.

Sheik kabeer ya waigo yana kallon matar shi yace ai kuna iya tafiya 'tunda jibi zanzo kinga saina wuce miki dashi..

Tace takwana gidan sauki Allah yasa telan nan karta kwafsa mun tamin dinki me kyau yan zamani.

Salma data kosa subar gidan tace to kaka wani irin dinki zamani kuma za' ai miki.
Yawuce tadinka miki tazarce.
Chapter 18 · 0% Book details