← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 115

Sashe 70

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin Rawar murya tace dan Allah kiran mene bazamuyi shi àcen ba saida kuka kawo ni nan....

Yarima yace inason ki gayamin Daga ina kike kuma ina ne garin ku..
Kuma meya kawo ki masarauta...

Nan da nan taji wani Zufa ta keto mata...
Cikin karfin hali tace bangane wannan tambayar ba..
Yarima dake kallon Agogon hannun sa yace karki damu kibamu Amsa..
Ahmad kada kai yayi Alamun ita suke jira tayi magana...

Cikin Rawar murya tace ni yar Gabon ce..
Banda aure.
Kuma nazo garin nan ne dan ance tafiya mabudin ilimi ne...
Yarima yace shiyasa kikazo masarauta..

KADA kai tayi Alamun hakane.
Good ya furta yana nazarin kalaman ta...

Yaushe zaki koma kasar ku ?
Hassana tace korata kuke yi ne..
Yarima yace A'a akan me saikace wajen mu kikazo kawaide rakiya zamuyi miki muga gidan naku...

Uhmm bazan wuce sati daya ba InshAllah dan nakosa inje gida yaya n'a suna bukatata.....
Ahmad tabe baki yayi yace kinada yaya kika zauna anan kamar bakida kowa lallai matar nan kina ruwa kusa da kada....
Nan dai sukayi iya kokarin su dan ganin sun sa tabar gidan...

Yarima yana tsoron ajiye baki a masarauta inya tuna da abunda suka wuce abaya...
Akarshe dai hakuri suka ba hassana kada tabari Mamy tasan sun kirata gefe..
Tayi musu Al'kawarin InshAllah bazata fadi ba........

************************

Gabon 🇬🇦

Sheik da Aminin sa Agajiye suka dawo Daga wajen taro inda manyan jami'an tsaro sukayi masu jagora har masaukin su.....

Baba Salihu ganin jami'an tsaro da yan jaridu sun rako su Sheik har gida.
Yasa shi buya a cikin daki saida suka gama daukan duk wasu bayanai Sannan suka wuce....

Baba salihu fitowa yayi bakin sa dauke da Murmushi yace ya Sheik dîna har kun dawo ya gajiyar ku.
Alhmdulilah suka bashi Amsa.
Sheik yace uhmm kaga gobe zamu koma InshAllah to ya zamuyi kenan kasan dole ne saida rakiyan manyan kasa Ko....

Baba salihu yace uhmm kude kuyi gaba zantaho Daga baya InshAllah.
Karku damu da wannan..
Yanzu de kuban labarin taron naga yanda kayi wa'azi mai ratsa zukata....
Sheik Murmushi yayi yace uhmm Baba Salihu yanzu tashi ka dubomun lemu masu sanyi hade da ruwa Ko.
Sai musha labari...
Ganin Baba Salihu ya tashi cikin hanzarin zeje dauko masa lemun.
Sheik yayi maza ya tare shi yace Shugaban Adalai tsokanar ka nake.
Murmushi baba salihu yayi yace nifa yaron gidan ka ne koka mance ne haryanzu ina nan awannan matsayin wlh komi kasani zan maka.....

Sheik yace nidai kabar shi zan dauka da kaina..
Firij din baba Salihu da sheik suka rike gam.

Sheik yace baza'a bude ba shikuma baba Salihu yace gaskiya shine zedauko lemun nan..

Malam Isa dake kallon su yana d'ariya yace to tunda abun yazama haka...
Duk Ko koma ku zauna ni zandauko lemun inkaiwa Sheik...
Sheik yace nayarda kai ka kawomun...
Malam Isa yace dan ni karaina ni Ko kaga wajen kwana n'a..
Shieik yace kaga yanzu banda lokacin ka kuma ina tareda surukina...

Ba yanda suka iya dole suka saki Firij din..
Shugaban Adalai yace nidai yau ka hanani samun lada..
Sheik yace hanyoyin samun sa dayawa suke..

Nanda dai sukayi ta hira cikin nishadantuwa..

*************************

Kano..

Mama zaune tsakar gida sai tunanin girkin da zatayi wa sheik takeyi dan gobe ze dawo cike da murna tace wannan shegiyar Sa'adatu bata nan zan sake agida...

Aminiyar ta ce tashigo hannun ta dauke da leda..
Lale Lale mama ta tarbe ta cikin fara'a...
Samun wuri sukai suka zauna taré...
Aminiyar mama tace naga kamar gidan babu kowa wai haryanzu basu dawo bane..

Babu wanda yadawo dagani sai Abubakar da Abdul jalil dan shegiyar matar cen....

Aminiyar ta dariya tayi sossai tace harda kaya aka barmiki kedai sha kurumin ki..
Maman Rahama kamar kin cemin cikine da ita Ko...
Mama tace eh cikine da ita...
Aminiyar tace akwai wani magani da nazo miki dashi kiyi mata girki me kyau ranar da zata iso ki tarbe ta dakyau..
A'cikin abinci zaki zuba mata bayan Awa uku jini zai balle mata Daga nan saide tayi barin sa..

Dariya suka bushe dashi dukan su...
Mama tace jibi shegiyar mata duk yanda nayi in hanata haihuwa gidan nan saida tayi daya.
Nade ci gari da bata haihu da wuri.
Har sheik yasamu damar daukar yata yaba ta...

Aminiyar tace kedai kibar ta yanzu m'a.
Ba haihuwar zatai ba saide ta saura da dan ta daya wlh......
Dan dai Rahama ba yar ta bace..
Kece kika yi sake wlh da mun rabasu ita da Rahama...

Mama tace kinsan banason abunda ze cutar da Rahama shiyasa kwanaki da kika ban magani ban zubawa anty ba..
Nasan karshen ta tareda Rahama zasu ci..

Aminiyar ta numfasa tace kuma hakane amma ai yanzu tayi aure bata gidan..
Komai kikai mata daidai ne..
Yawwa Akwai wani Alhaji bushasha Ibrahim kwangila...

Mama tace Alh Ibrahim bushasha kwangila shahararren dan kasuwan nan ance baya zama kasar sai ya shekara bezo Nigeria ba..

Aminiyar tace kedai ban aron kunne ki kisha labari...
Shidai Alh Ibrahim din n'a samowa Salma nasan batason mijin ta dan talaucin sa me nakasa yaci bare yaba nasama..
Sheik yana sane yahada auren Saboda anty tashanye shi..

Inason mu San yanda za'ai à raba auren nan..
Shikuma yace ze Auri Salma.
Kinga kenan mijin Rahama Sarauta da kyau kadai ze nuna masa ba tarin dukiya ba...

Mama tazare idanu tace taya kike ganin zan iya Raba auren nan..
Bayan kinsan sheik baze yarda ba..
Aminiyar tace nidai kibar komai hannuna amincewar ki kawai nake nema...
Daga haka sukayi ta shirye shiryen abunda zasu aikata....

************************

Kwatano...

Bayan isha'i
Samad. Yana idar da Sallah ya shige ciki..
Iske Rahama yayi zaune tana goge Jan baki a leben ta..
Murmushi yayi tareda karasowa kusa da ita yace la la Amarya ta kullum kyaun ki karuwa yakeyi meye sirrine..

Rahama Jin sa take taki magana kokarin ajiye Jan bakin takeyi tana neman hanyar guduwa...
Ji tayi ya kamo ta yarike ta gam tareda hade ta da jikin sa suna kallon juna..
Duk yanda t'aso ta kauce yaki bata dama..
Cikin sanyin muryan sa yace Hubby meyasa kike guduna dan kawai n'a karbi hakkina haba love bakisan Ko wace mace da hakan ta fara ba..

Turo baki tayi gaba cikin shagwaba kamar zatayi kuka tace uhmm..
Ko wace mace daman haka ake mata wannan mugunta babu tausayi...
Yarima Murmushi yayi yana Jin kansa a shauki..
Yace aike din ce Rahama Allah yayi miki ni'ima nakasa control din kaina ne please kiyi hakuri Muje yanzu muga wajen koya warke dan banki in kara ba...

Kuka ta fara tace shikenan yau ma zesani barcin wuya please Amjad dan Allah narokeke ban warke ba...
Dariya tabashi sossai yanda yaga tsoro à Idanun ta..
Yace karki damu damar zolaya ce yanzu de Muje muci Abinci amma fa sai fa kin bude mun wajen nagani dan insan wani magani zan baki...
Kasa magana tayi tana fadin ikon Allah wayyo ni Rahama n'a bani daman Yarima bashi da kunya take fadi batasan maganar ta fito fili ba....

Eh Yarima bashida kunya amma akan Rahama ta..
Oya Muje inbaki iya takawa zandauke ki..

A'a kabar shi zan iya tafada tana ciza labban ta cikin tsoron kada ya dauke ta tabi shi sukayi part din sa.

Salma sannu ahankali tafito Daga dakin ta zata je sashin su Rahama hannun ta dauke da magani har ta iso bakin kofar ta bude le dan tana shirin zuba wa..

Taji Tsayuwar mutum a bayan ta arazane tajuyo suka..........

Ta ku har kullum kyauta Daga Allah
3/21/22, 07:51 - Nuriyyat: KANWATA

09069080725
+22953726162

6️⃣9️⃣

Arazane ta juyo suka hada idanu da Karima cikin gigita tace uhmm wai kece..

Karima tace Nice mana naga kintaho sashin Shugabana bayan doka ne ba'a shiga sashin sa 'saida izinina dakuma sanin sa.....
Dan Allah kiyi hakuri ki koma inda kika fito..
Tafada cikin nuna da gaskiyar maganar ta..

Salma sake da baki take kallon Karima tana kokarin boye ledan dake hannun ta tace bangane inzamu shigo nan ba sai mun nemi izinina ba.
Nida dakin yaya ta bazan shiga ba Ko bakisan yanda muke bane da Rahama bane...

Karima cikin hada rai da sanin makaman aikin ta tace ni wannan ba damuwa ta bace umarnin da Aka bani dole ne inyi biyayya '' daman Saboda taron biki ne yasa kikaga wajen free kowa ke shiga amma daga gobe bayi masu tsaron sashin Yarima zasu fara aikin da suka Saba dafatan dai kin fahimta ta.
Hannun tayiwa Salma alamun su tafi..

Hankalin Salma yayi mugun tashi
Tace amma dai bakida mutunci wlh kinkosan ni wacece kuwa..
Karima tace wannan damuwar ki ce.. Ba tawa ba dan haka ki fice nace Ko cikin tsawa...

jiki babu kwari ta juya Karima n'a biye da ita a baya......

Koda suka baro sashin su Yarima.

Karima cikin karfin hali irin nata tace bansan me kike boyewa ba inda abu me kyau ne bazaki yi shi bayan duhu ya shigo ba..
Koma menene dai kiji tsoron Allah.

Salma cikin hasala tace kaji shegiya uwar Sharri sai in sa asauke ki Daga mukamin da kike ciki baiwar banza baiwar wofi...

Dariya mai fidda sauti Karima tayi tareda takowa kusa da Salma har suna Jin numfashin juna..
Tace inkika fasa sawa asauke ni ba Sunan ki Salma ba '' babu ruwana da ciki daya kuka fito keda shugaba ta..
Ya zan ganki kina shirin aikata barna duk da bansan meye manufar ki ba..
Amma nasan dai ba abun Alkhairi bane.
Dan n'a fiddo ki Daga Sashin su shine zakiji haushi n'a indai Nice yanzu aka fara wlh...
Mtsss taja tsaki tareda rufo kofar dake sada mutum da Sashin su Yarima.

Barin wajen tayi tana wake waken habaici...

Sake da Baki Salma ke kallon ta har ta fice mata da gani..
Chapter 70 · 0% Book details