← Book details Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 115

Sashe 19

Kanwata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaka rike da baki Ta maimaita tazarce to badani ba ehee kan mage yawaye..
Dukansu fita sukai suna mata dariya.

Sheik kabeer dakansa yajasu à motar sa.

Yaita zarya da su gun yan uwansa akai ta samusu Albarka.
Gidan zubaida ya ajiye su.

Inda nan m'a suka samu tarba n'a mussaman aranar dai sunsha kyautuka naban mamaki dangin mama sunyi abun ayaba musu..

Rahama tadauko jakar ta tafara kirga kudin da tazo dashi ganin babu rabi hankalin ta yatashi tace to kudin nan daukar su akai taya za'a dau rabi abar mata rabin su.

Kallon salma dake kokarin fita waje tayi harta yafa gyale.

Cike da nutsuwar takaraso kusa da ita ido cikin ido take kallon salma tace.
Salma meyasa kika daukar mun kudi baki gayamin ba.

Rau Rau salma ke kallon ta ta yatsine fuska bangane nadaukar miki kudi ba.

Sharrin sata zaki daura min.
Rahama tace Ko shakka babu ke ce kika dauke shi dan babu wacce zata dauka saike kuma tare muka kwana.

Wallahi ànty Rahama ki kiyaye ni daman kiyayyar da kikemin yakai haka bansaniba kuka ta saki wanda yajawo hankalin jama'ar gidan akansu.

Kowa sai tambayar abunda akai mata take ta zabga uban kuka haka.
Rahama tace karku damu wai dan ina tsokanan ta ne shine take kuka batasan wasa ba..

Mutanen gidan suka ce ke kuwa Rahama ba yayar ki bace kuma tace wasa take miki.

Da ga haka kowa ya watse yabar su.

Salma cikin huci sama sama tana hura hanci tace Wallahi Rahama saina saki kuka kuma saikin yi nadaman kasancewa yayan mutum daya nidake.

Kalaman ta bakadan ya Girgiza ila'iriin jama'ar dake gidan ba.

Dawowa sukai wajen kanwar mama ta wanke salma da mari tace ke wawiyar inace me yayi zafi da har zaki ringa jifar yar uwar ki.
Da mugayen kalamai.

Rike da kuncin ta salma ta dago kai ta kalle ta Idanun ta cike da kwalla tace ni kika mara ?

Kanwar mama tace anmareki kozaki rama ne ?

Kanta gama rufe bakinta saiji tayi tass salma ta wanke ta da mari.
Mamaki kwance kan fuskar Rahama.

Rahama da takai kololuwa wajen bacin rai.

Tace Wallahi salma kinyi asara wannan fa kanwar uwar ki ce.
Yanda kike kallon mama to ita ma haka take amma dan kina wawiya sha sha sha shine kika mare ta.

To bari kigani.

Maruka uku ta wanke salma dashi Ko kuwa n'a kokarin barkewa tsakanin su.

Dakyaar aka rabasu Rahama banda kuka babu abunda take ita bakin cikin ta marin da tayiwa kanwar uwar su.

Zuwa gun kanwar uwar su data zabga uban tagumi cikin rarrashi taringa bata hakuri kakar su zubaida ita Kanta ta Girgiza akan wannan rashin idon salma.
Kowa wajen yanata Allah wadai da halin ta.

Salma ficewa Daga gidan tayi tasamu wuri tazauna marin da Rahama tayi mata bakaramin sa mata ciwon kai yayi ba.
Tanata shafa fuskar ta.
Ciro wayar tayi Daga cikin jakar ta tayi tareda kunna ta.
Wayar n'a kawo haske ta danna nombar marwan.

Yanata ring ba'a da gaba dan marwan yana zaune kusa da yarima Samad yarasa yanda zeyi ya Daga wayar gashi Idanun yarima Samad yadawo kan wayar sa dake ta ring amma yaki dagawa.

Banda bari babu abunda jikin marwan yake.

Kokarin daukar wayar yake 'Samad yarigashi dauka Daga wayar yayi yasa hansfree Jin muryan mace yasa shi zare idanu..

Yaji tana fadin jiya n'a kashe wayar Ko' uhmm kaidai gidan mu ba'asan ina rike waya ba.
Naji kace dame zanbiyaka kyautan dakamun.
Gayamin me kake so dan kabiyani komai à rayuwa wlh..

Jikin marwa yadau rawa Saboda wani mugun kallon da yarima Samad ke jifan shi dashi.

Idanu yayi masa daya d'au wayar 'cikin hanzari yadau wayar tareda cire hansfree din yabar falon.

Da Idanu yabishi dashi yana Girgiza kai yace lallai saina sa idanu akan yaron nan kenan neman mata yasoma a garin nan.

Marwan wani corridor daze sadashi da babban falon gidan' n'a su yabi waya n'a kunnen sa.
Soma share Zufa da ya keto masa à fuska yayi da hankicin.

Salma Jin shirun yayi yawa Daga cen bangaren tana gyara zaman ta tace hello marwan bakajina ne.

Marwan bekuma bin takan wayar ba dan ya tsorata sossai da abunda yarima yayi masa dan ma Allah yataimake sa.

Su faruk basu nan da sun gane lagon sa.
Numfashi ya fesar yana tunanin ta inda zefara.
Dan sun tsara shida Abban sa sai mai martaba yazo kanon zasu kai hoton gidan jaridu 'amma kafun nan yana son yasan yar wacece me matsayin mahaifin ta.
Dariyar mugun ta yayi yace kajira ranar juma''a
Wannan barazanar da kake mun zekare ne.

**************

Yau takama ranar talata su Rahama tunda asuba suka shirya tsaf tareda kyaututukan da a ka basu.

Drever Abba karfe takwas ya Iso makarfin.
Tareda matar kakar su.
Zasu juya kanon.

Adamsy sai kira yakeyi ba arziki rahama ganin kaka yasa takejin kunyar daga wayar dan suna gaf da juna zaune cikin motar.

Salma data lura Adamsy ne ke kira murmushi tayi tace au naga angon naki nakira amma kinki dagawa lafiya kuwa.
Tana me tsareta da idanu.
Rahama tace babu komai
Tare da kame bakinta tayi shiru.
Kakar t'asu talura kunyar ta takeji murmushi tayi tana jinjina alkunya irin ta rahama Sam Sam wayewar ta cike yake da hikima da hangen nesa.
Kafun ta furta zancen saita tauna shi ta fidda mekyau sannan ta isar dashi.

********

Kusan karfe daya suka Iso kanon dabo tumbin giwa 'salma banda murna babu abunda takeyi cikin zumudi tafito Daga motar tana kokarin shiga Daga ciki cin karo da Abba tayi dake kokarin fita zuwa massalaci da fara'a fuskar shi yatare su' Abubakar ya kwada kira shida hussain nan da nan suka fito kaya ya nuna musu da sushiga dashi.

Sannu ku da zuwa inna tareda durkusa ya gaisheta cikin ladabi.
Cike da farin cikin haduwa dashi ta amsa masa gaisuwan.

Hussain yana kallon innar tasu yace su Hassan yaushe zasu zone ya jefo mata tambaya.

Tace ai inaga gobe sammako zasuyi harda abban naku.

Cike da farin ciki suka shiga gidan wanda tuni gidan hargitse yake da jama'a anata hada hadan kai kayan amare...

Ànty da duk ta rude bata nutsuwa zuwa tayi tasamu sheik a zaure tareda baki.

Ta ce tana son magna dashi ya taso ya sameta cike da kulawa yake kallon ta kuma da dukan alamu sauri yake yakoma wajen bakin nasa yaraba hankalin sa gida biyu.

A nitse tafara magana tace daman zancen kai kayan amare ne abari bayan daurin aure mu zamuje kai kaya.
Saboda kaga har yanzu kujerun dakin su basu karaso ba.
.
Au to babu matsala ayi yanda kika ce din yabata amsa yakara da cewa wannan raguna guda shidda da saniya guda biyu gobe in Allah yakaimu za'a yankan su.

Dan Allah masu kula da bangaren abincin suyi mana farfesu nama yayi kyau kingan n'a taron daurin aure ne.
Yayi magana cike da nuna muhimman cin abun.
Tace babu matsala za'a kula tareda juyawa cikin gida shima yakoma gun bakin nasa.

************

Dr Abdullahi shida matar sa banda zumudi babu abunda suke yi wai yau saura kwana uku kacal dan su ya angwance farin ciki à fuskar su baya misaltuwa.

Bangaren Adamsy sossai yake ta shirye shirye yahada mata akwatuna takwas harda akwatin zinari karama.

WAOUH MASHAALLAH MASU BUDE KAYAN LEFEN SUKAI TA FADI SUNA GUDA.
DAN SOSSAI GIDAN YACIKA DA JAMA'A.

Adamsy ya shiga damuwa inya kira Rahama bata dagawa hakan bakaramin Daga masa hankali yake ba.

Shiryawa yayi cikin boye blue yasa takalmi half cover bakaramin kyau yayi ba sai baza kamshi yake.
Abokin sa hamza yaimasa jagora zuwa gidan su Rahama..

Dakyar tafito takasa hada idanu dashi 'yace yau rowar fuskar taki kike min ne Rahama yana me tsareta da idanu yana murmushi.

Hamza yace kaga bara inbaku wuri kila batason magana a gabana ne.

Barin wajen yayi hamza

Adamsy yace pls wannan kunyar taki tana bala'in cutar dani ki Daga kai Ko saudaya ne ki kalleni.

Dago kai tayi takalleshi Idanun su suka tsarke cikin juna sauke Idanun ta tayi tace Idanun mutane akan mu pls kabari zamuyi waya..

OK ya bata amsa yace akwai abunda kike bukata ne n'a biki.
Girgiza kai tayi Alamun babu...
Adam yace ai ranar juma'a gida n'a zaki kwana gado daya nidake zancire miki kunyar nan inhuta yana kallon yanayin ta.

Maganar sa yasa takasa Tsayuwa domin faduwar gaba da kunya suka dirar mata lokaci daya.
cike da nutsuwa tajuya tace masa sai anjima..

Shiko Adamsy yana ganin tashige yakira hamza suka tafi.

*********

Yau takama Alhamis gobe daurin aure.

Kasar kwatano.

Me martaba shida iyalan sa a airport hade da waziri.

Mamy da Ahmad 'da khadija..

Fulani bata biyo su ba.
Amma mijin ta dashi za'a je.

Mai martaba yace lallai wannan bikin yayi kai gashi mun taho da yawan mu..

Karfe daya jirginsu yasauka à kano.

Yarima Samad cike da farin ciki yanata baza idanu yanda zehango kannen sa.
Da mahaifiyar sa.

Marwan yace haba Samad ka tare mana gaba kai kaidai ne kake zumudin ganin su kenan bandamu kenan.

Faruk yace kash marwan yanzu ina gaban daya tare maka.
Samad yace kyaleshi dan rainin wayau mana baka ga Ko kallo be isan ba.

Yana magana hankalin sa nakan masu fitowa Daga jirgin.
Aminu yace ammaa basa cikin jirgin nan fa.

Kamar ance Samad air plan personnel suka shiga.

Yarima Samad dake kallon sa yace gaskiya hakane waigowar dazeyi suka hango su Daga cen nesa suna tunkaro su.

Cike da zakuwa Yarima kamar karamin yaro yaje ya rungumi mamy.
Ta nata murna tace d'ana gashi yau Allah yakawoni kanon nima.
Yace eh wlh mamy kamar kinsan nayi kewar ki yana magana cikin shagwaba kaman karamin yaro.
Kallon khadija yake yabude hannayen sa.
Alamun tazo aguje taje ta rungume shi cike da farin ciki yace yau gani ga kanwata a kano uhmm.

Ahmed yabata fuska cikin wasa yace nidai Ko !
Samad dake kallon yanayin sa yace kaide Ko me akai maka sarkin rigima.

Zumbura baki Ahmad yayi yace bakai bane to.

Bani bane nayi me yana kokarin yaja masa kunne à guje yaje bayan mamy yabuya yana ma Samad gwalo.
Chapter 19 · 0% Book details