Sashe 99
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Zahra na san ina daya daga cikin mutanen da suka haifar da damuwa da bacin rai a zuciyarki, wannan dalilin ya saka na dauki alkawarin kuranye wannan damuwar na share hawayenki na mantar da ke duk wani hali na bakinciki da kuka taba shiga, na yi kudirin abubuwa da yawa akanki Zahra a farko a kyautata miki da kyautata mu'amala da ke da son duk wani abu da kike so, sannan na yi kudurin aurenki duk kuwa da na san ba lallai ne ki karbi soyayyata ko ki amince da ni ba, a duk lokacin da zan yi yunkurin nuna miki soyayya sai zuciyata tace be dace na yi haka a yanzu ba, saboda ina ganin kamar mijinki be dade da mutuwa ba, kuma ga halin da kika shiga a yanzu wata kila ba ki shirya karbar soyayya ba, ta dayan bangaren kuma ina tsoron irin kallon da zaki min, wata kila ma zaki yi zaton ko kanwata ce ta saka ni ko kuma ina son na aureki ne ba dan Allah ba sai dan na kara rufe sirrin dake tsakaninmu, wadannan abubuwa suka zame min wata tsarka data daure ni na saka duk wani motsi da ya kamata akanki, ashe dai rashin rabo ne ke ta tare ni amman Allah ya sani Zahra na so ki, domin kina da siffa da kyaun da duk namiji mai hankali da sanin rayuwa zai so ki kasance a matarsa”
Tare da dogon numfashi ya karashe maganar, ni ma numfashin na ja na sauke a yanzu dai ba zan ce ina tausayinsa ba domin idan har akwai wanda zan ji tausayinsa to kaina ne na fi kowa zama abar tausayi a yanzu, tabbas tunaninsa be bashi karya ba ba dan cilastawar Sauban ba, da ban shirya wani aure ba ko da a nan gaba balle kuma a yanzu.
“Wani lokacin abubuwa suna faruwa ba a yadda muke so ba, sai a yadda Ubangiji ya tsara za su faru, wata kila ni din ba alheri ba ce a gurinka shiyasa Allah be mallaka maka ni ba, domin Allah yana zabawa bayinsa abun da ya fi dacewa da su ne”
A cikin kalamaina babu na kuka, amman hawaye na ke kamar an sanar da ni awanin da suka rage min a duniyar nan, kuka nake sai na rasa dalilinsa ciwon zuciyar dake neman kaine kasa ne ko kuma auren Sauban da ya zame min dole kuma kaddara.
“Haka ne, ina miki fatan alheri Allah yasa mutumen da zaki aura ya rike ki amana, gaskiya yayi sa'a shi ne Abiey?”
“Abokinsa ne”
Ya kada kai.
“Na gane shi, daman zuciyata ta raya min son ki yake ashe kuwa haka ne, bari na wuce kar ya tarar da mu a nan ya fara kishi”
Da murmushi ya karasa maganar, sai na saka hannu na share hawayena.
“Na gode”
Na juya ina tafiya cike da nauyin kafa har na shige BQ be tunna motarsa ba balle na yi tunanin ya bar gurin.
The following day Sauban ya kira wayata yana tambayar ko akwai abun da nake bukata kamin a daura auren, na amsa masa da babu, sai ya sanar da ni zai balaguro a gobe kuma ba zai samu dawowa ba sai ranar da za'a daura auren, idan ya furta zancen aure sai na ji kamar ya soke ni da mashi a kahon zuciyata, kalmar tana min daci sosai kuma tana sakawa zuciyata bugawa, Jumma'ar da zata zo ma fargabar zuwanta nake domin kuwa jin ta nake kamar jumma'ar mutuwata, ko wane kallo Abiey da yan'uwansa suke min a yanzu oho, wata kila mayaudariya ko yar cin amana, wata kila ma za su ce na bi kudi ne na auri Sauban, haka dai na wuni da tunanin irin kallon da mutane za su min. Ana gobe za a daura aurena na shiga bawa Amir nono kamar yadda na saba na kan ba shi na safe da rana da kuma dare, ina a dakin Hajiya Jamila a zaune na saka masa nonon a baki yana sha idona na kansa sai ruwan hawaye ta taru a ciki har ya zubo akan fuskarsa.
“Zan yi aure Amir amman bana jindadi da farinciki ba, zan yi ne saboda na rufa asirinka kuma na rufa nawa domin ban san da wane bakin zan amsa maka ba idan ka tambaye ni miyasa na aikata haka, wata kila a gurinka da gurin wasu mutanen hujjata bata isa ta zama hujja ba, na san na aikata kuskure mafi girma, amman duk haka zan so na ga girmanka, zan so ka kalleni ko da a matsayin wanda ta shayar da kai ne, sai dai bana da tabbacin zan rayu har zuwa lokacin da zaka yi wannan wayon, amman ina son ka sani cewar ina kaunarka fiye da komai a duniyar nan ina son kasance da kai sai dai babu hali”
Ina shafa gefen fuskarsa da yatsana sai yayi min murmushi irin na yaran da suka shiga wata na uku da haihuwa.
“Amarya Amarya”
Shine abun da Hajiya Jamila ta shigo dakin tana fada, sai na yi saurin saka hannu na tare fuskata har sai da na share hawayena cikin hikima sannan na dago ina murmushin karfin hali.
“Yau kuma tsokana kike ji ke da kanki?”
“Ai na fi kowa murna da farincikin auren nan da zaki yi ne Zahra, Allah dai ya sa gurin zamanki ne”
“Ameen”
Na amsa sannan na kalli wayarta dake ringing, da sauri ta karasa gurin wayar ta cikin zumudi da far'a ta karba kiran da nake kyautata zaton Mr Bashir ne ya kira.
“Hello Hubby, ahhhh i miss you da gaske? Awww i can't wait wannan jumma'ar ta gobe, Okay Allah ya kawo ku lafiya”
Ashe kuwa na canka a daidai domin yanayin yadda take amsa masa da kuma sunan da ta kira ya tabbatar da haka har wani tsalle take kamar yar yarinya tana ta zumudi.
Ni dai ban ce komai ba na cire Amir daga nonon na kwantar da shi na mike tsaye na fice daga dakin ina jin wani irin kaunar ďana yana fizgata. A ranar na wuni da tunani da kuma damuwa marar misaltuwa na dan samu sukuni ne a lokacin da Hajiya Jamila ta kirani na fara tayata aikin da zata shiryawa mijinta abinci gobe ta nan na fahimci zai dawo a gobe kenan bayan doguwar tafiyar da yayi, wani abun tun a ranar muka kallama shi, sannan na fito na dawo bangarenmu ina shigowa na rufe windows din da Mama ta bude saboda hadarin da ya taso iska na kadawa da karfi, ina kokarin kwantawa wayata ta yi kara bakuwar number ce cikin fargaba na amsa kiran.
“Zahra'u kuna lafiya ina Mamanki?”
Ina jin muryar na fahimci Inna ce kanwar Mama, sai na mikawa Mama wayar suka yi magana, bayan sun gama Mama take fada min cewar wai zata zo gobe ita da wata kanwarta.
“Allah ya kawo su lafiya”
Kawai na iya fada na cire tufafin jikina na saka na bachi na yi addu'a na kwanta.
[11/26, 10:50 PM] Oum_Nuwaira🥰: 6️⃣2️⃣
Jumma'atu Babbar Rana, sai dai ni zan iya cewa ta zame min ranar tashin hankali domin na farka da kuka kamar yadda na kwana da shi, ina sallah ma kuka nake a boye saboda bana son Mama ta gani zuciyata ta rike gam kamar an daureta dan motsi kadan sai na ji kamar raina zai fita saboda ciwon da take min, Mama ta shirya abun karyawa amman na kasa cin komai sai ruwa na ke ta sha. Misalin karfe tara na safe Inna ta kira wayar tace tana waje na zo na shiga da ita saboda masu gadin sun hana su shiga. Kamar marar lafiya na fito BQ din na fita gate domin shigowa da su a lokacin ne suka budewa Mai gidan Gate direbansa ya shigo da motarsa ni da su Inna muka rabe gefe har sai da ya wuce sannan na yi magana da masu gadin suka bar su suka shigo.
Bana tunanin yayi awa daya da shigowa gidan Hajiya Jamila da kanta ta shigo BQ din da kanta kirana.
“Allah yasa ba laifi na yi ba”
Ta yi dariya.
“Babu laifin da kika yi kawai dai yayi maganar Amir ne sai na ce masa zan sanar masa da wani albishir daga Nannyn Amir amman waka a bakin mai ita tafi dadi zan kira ki fada masa da kanki, shi kenan fa ya tashi hankali sai na kira ki ko abinci be karasa ci ba”
Hankalina ya dan kwanta da jin haka, na san da ace ba a aurena za a daura ba da bazata fadi haka ba har tana yakar hakora. Haka na bi bayanta muka shiga bangarensa sai dai na same shi a zaune a falon da Ummiter ta taba yi min iso lokacin da ya aikata ta kira ni. Na shiga kaina a kasa na zauna a makamancin gurin da na zauna a wacan lokacin, ita kuma ta karasa kusa da mijinta ta zauna tana murmushi.
“Gata nan sai ta maka albishir din”
“Toh Madam ai sai kin bamu guri kin san dai ban saba magana da ita a gabanki ba”
Kunnuwa suka ji sautin muryarsa zuciya kuma na raya min cewar idonsa yana kaina.
“Ahhh ni ai bana da shan kai ga ta ga ka”
Ta mike tsaye ta fice tare da jan kofar falon, tsit falon yayi kamar babu kowa baka jin komai sai sanyin ac dake tashi.
“Matata tace akwai wani abun alheri da ya same ki, sai dai bata sanar da ni ko minene ba shiyasa na ce ta kira min ke na ji daga bakinki, abu na biyu kuma kin san ba ki karasa min labarinki ba har yanzu ban gama sanin wacece ke ba, tafiyar da na yi a kwanan baya ban yi zaton zata dauke ni wadannan kwanakin ba, sai dai yanayin aikina ko kuma na ce kasuwancin na ya saka dole na dade a turkiya, a jiyan ma ban saka ran dawowa ba sai gashi kuma mun iso nigeria a jiya din cikin amincin Allah, sai dai ban samu karaso gurin iyalina ba sai a yau, saboda mun dawo late sai na tsaya na kwana a Abuja”