← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 127

Sashe 75

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su waye team Abiey ni dai har gobe ina team Deen 😍
[11/15, 9:53 PM] Oum_Nuwaira🥰: 4️⃣9️⃣

Abiey na fita Dr Zainab ta dauki wayarta ta kira mijinta kamin ya daga kiran kafarta ta gama zagaye dakin jikinta har rawa yake.

“Assalamu Alaikum Madam”

“Ranka ya dade kana kusa?”

“Lafiya?”

“Ba lafiya ba, wani aikin ne ya taso na gaggawa ina son idan kana kusa ka raka ni mu tafi tare idan kuma baka kusa ina son ka yi min izini na tafi?”

“Ina? Wane irin abu ne haka?”

“Ba zan iya maka bayani a waya ba, bana son a kwana ban aiwatar da abun nan ba, domin ba ni tabbaci zan kai safe na san rai a hannun Allah yake amman wannan case na san za a iya aikata komai domin ganin maganar ta rufe”

“Gani nan zuwa yanzu, idan kin san you're not safe ki bari na kira police, and ki rufe gidan nan kar yarana su fita ko'ina”

“Okay amman karka fadawa police komai ka dawo da yanxu please”

“On my way”

Ta sauke wayar, sannan ta kira Ammy ta nufi karshen gadonta ta zauna, Ammy ta amsa wayar da sallama.

“Wa'alaikissalam Ammy barka da dare”

“Barka dai Dr ya yaranki?”

“Alhamdulillah Ammy ke kadai kike?”

“Kullum a gidana ni kadai nake ai, sai dai idan na yi baki miya faru?”

“Wani abun na ke son na tambaye ki amman ban san yadda zaki ji kuma ban san ta yadda zaki fahimci abun ba”

“Miya faru Zainab? Fada min mana”

Dr Zainab ta yi jimmm na dan lokaci sannan ta numfasa ta ce.

“Abiey ne yanzu ya fita daga gidan nan, ina mashi magana akan Mai Martaba sai yake ce min Mai Martaba is no longer his father abun ya ba ni mamaki kuma ya ba ni tsoro ta ina Abiey ya samu wannan magana haka? Ko dai sherin su Hajiya Kilishi ne ko kuma tsanar da Mai Martaba yayi mashi ne yake ganin kamar ba Mai Martaba ya haife shi ba?”

Ammy dake zaune rike da plate din apple ta mike tsaye da sauri plate din dake cinyarta ya fadi kasa.

“Waya fada mashi wannan magana?”

“Ban sani ba ban kuma san dalilinshi na yin wannan tunanin ba”

“Ina yake?”

“Ya fita ina zaton gida zai zo”

Ammy ya sake wayar daga kunnenta ta katse kiran da sauri ta kira line Abiey, da farko line busy ta ji wayar daga baya kuma ta sake kira aka sanar mata mai number yana kan amsa wani kiran ta jira, ta katse ta sake gwada kiran be amsa ba sai a karo na hudu.

“Hello”

“Aliyu kana ina?”

“Ina compound”

“Shigo yanzu cikin ďakin na ka same ni”

“Toh”

Kamin ya hau sama ya shigo dakinta har ta matsu, ita da kanta ta sauko kasa sai kuka hadu a falo, tsayawa yayi yana kallonta. Ammy da hawaye suka cika idonta har suke zuba ta tambaye shi.

“Why did you learn this?”

“What?”

“Cewar ba Mai Martaba ne mahaifinka ba? Waya fada maka haka? Zahra?”

“Zahra bata fada min komai ba, ban tambaye ta komai ba kawai na bi ta salo ne da hikima na gane komai”

Ammy ta dafa shi ta shafa kanshi tana kuka sosai kamar ba ita ba.

“Na rantse da sarki Allah kai ďan Mai Martaba ne jininsa ne kai, amman babu yadda zan iya wanke kaina domin na riga na dabawa kaina wuka, amman ka yarda da ni uwa da uba ne suka kawo ka duniya, dan halak ne kai ďan sunna”

Ta sake shi ta juya mishi baya tana kuka sosai.

“Toh mi ya saka Mai Martaba ya tsane ni? Me kike boyewa?”

“A yanzu ka fallasa yar'uwarka ma da bata san komai ba ka fada mata a yanzu, sauran duniya ta ji amman ina fatar kamin lokacin ajalina ya riske ni ta yadda zan samu na manta da komai kuma yaya ba za su kyalle ni su ji kyamar ganina ba”

Cikin kuka ta karashe maganar, Abiey ya taka ya shiga gabanta.

“Me mika aikata Ammy?”

Ta nuna kanta.

“Taya mahaifiya zata iya bawa ďanta labarin abun da ta aikata Aliyu? Taya kake tsammanin zan baka iya baka labarin abun da na san ba zai taba iya fita daga kwakwalwarka ba? Abun da zaka dade kana kallona da shi?”

“Idan baki fada min ba? Waye zai fada min? Mai Martaba da kanshi? Ko kuma Zahra? Ko kuma so kike na yi ta zama cikin kwankwaso da tunani kala kala? Idan kuma na yi zato ki ce ba haka abun yake ba? Babu dalili da zai saka Mai Martaba ya tsane ni tsana irin wannan idan har ni ďanshi ne, idan kuma da hanyar halak kika same ni Ammy duk wani abu da zai biyo baya mai sauki ne, kaddara ma da ba hanyar halak kika same ni ba ina da wani abun da zan yi ne? Zan iya canja abun da ya riga da ya faru ne? Haka kuma ba zai saka na tsane ki ba ko kuma na juya miki baya domin ke uwata ce kin dauki cikina tun ban san da zan zo duniya ba har kika haifo ni, Ammy har na girma ban san wani abu gatan mahaifi ba na ki na sani, to akan me zan tsane ki ko da kuwa ta hanyar banza kika same ni?”

Ammy ta kalleshi da duba irin na uwa mai alfahari da samun ďa mai tunani da tarbiya irin nata, rikata yayi ya zauna a kujerar dake kusa da su.

“Ba zan cilasta ki ko fada min ba, amman ba zan taba samun salama ba har sai na san komai, domin kin raba min tunani gida biyu ne a yanzu”

Ya saka hannunshi ya share mata hawayenta.

“Ko na kasa da ni ba zan bari ya zubar da hawayen bakinciki saboda ni ba, balle kuma mahaifiyata dan Allah ki yi hakuri ki daina kuka Ammy”

Ya mike tsaye ya nufi kitchen ta dauko ruwan da cup ya dawo kusa da ita ya zauna ta zuba mata ruwan ya mike mata ta karbar ta sha sannan ta share ragowar hawayen dake zubo mata, ya karbi cup din ya aje bayan ta sha ruwa sannan ya mike tsaye rike da ita suka haura sama har dakinta ya shiga da ita ta zauna saman gado shi kuma ya duka ya dauki plate din apple din da ya fadi dazun ya fara tattara apple din.

“A wani kokaci can baya, na yi soyayya da mahaifinka soyayya sosai kamar ba za a rabu ba, sai dai Allah be kaddara aure a tsakaninmu ba, kasancewar al'adar masarautarsu ďan sarauta ko yar sarauta ba sa zabar abokan zama, sai dai a hada dan wannan masarautar da wacan ko kuma ďan cikin masarautar, amman ba sa yarda a auro musu bare na hadu da Mahaifinka a gidanmu domin kakanta da mahaifina abokan juna ne, ta wannan hanyar muka san juna har muka kulla soyayya, ya sani a dokar masarautar ba a auren bare a wacan lokacin ni ma kuma na sani kowa ma ya sani amman a haka muka cigaba da son junanmu, kwatsan wata rana sai mahaifina ya shigo gida ya sanar da Umma ma yace ta sanar min cewar ya ba da ni ga abokinshi, mahaifinka kuma aka yi mashi mata a masarautar wato Hajiya Kilishi yar Sarki Rano a wacan lokacin”

Ammy ta saka hannu ta share hawayenta, Abiey kuma ya dago ya kalleta bayan ya gama tattara apple din.

“A wacan lokacin mu yaran da, muma da tsananin biyayya ga iyaye, ba ko wace budurwa ake bawa damar zabar miji ba sai dai iyaye su duba wanda ya dace su aura maka, mu kuma biyayya da kawaici ba zai iya bari mu tsabawa iyayenmu ba, ko da baka son mutum idan iyaye suka zaba maka shi zaka amsa ne kawai ka yi na'am, to haka ce ta faru da ni ban iya musawa mahaifina ba har aka daura aurena da abokinshi, ba zan iya kiran mahaifinsu Zainab da tsoho ba kuma ba zan ce da shi yaro ba, iyakar abun da na sani shi din abokin mahaifina ne sosai ni kuma ni ce ta biyu a gurin mahaifina, a wacan lokacin ana mana aure ne da kananan shekaru ba kamar yanzu ba, na yi sa'ar aure duk da kasancewar bana son shi amman Alhaji Falalu Na'ala mutum ne mai matukar adalci da tsanin ya kamata da mutunci, ya rike ni amana ba zan iya tuna wata rana da ya bakanta min ko kuma ya musguna min, sai kuma na yi sa'a da abokiyar zama ta gari mai saka ni a hanyar kwarai, mahaifiyar Yasmin ta rike ni kamar kanwarta bata taba nuna min tsana ba, bata taba nuna min cewar ni kishiyarta ce ba, sai dai ta kira ni da kanwarta duk wani zuga da taegumi bata dauka ba, muka zauna a gidanshi kamar yaya da kanwarta, Alhaji Na'ala babban mutum ne mai arzikin da abu ne mai wahala ka lissafa mutun biyar a masu kudin kudin arewa baka saka da shi ba a wacan lokaci, na zauna a gidan babu tashin hankali babu tsoron komai sai gata da girmamawa ya rike ni amana kamar yadda yayi wa mahaifina alkawari, mahaifinka kuma ya zauna da matarshi Hajiya Kilishi be dade ba ya auro Mama Lami wanda ita ma yar sarautar ce a lokacin ne mahaifinshi ya kwanta dama sai a ba shi sarautar garin Kano, aka nada shi a matsayin sabon Sarkin Kano, lokacin da na haifi ďana na farko Auwal yana yaya hudu a lokaci domin sai da na shekara biyu sannan na haihu shi kuma matanshi biyu kuma suna haihuwa kamar suna gasar juna, na yi na biyu mahaifin Zainab ya saka mishi sunan mahaifinsa waton Muhammad Sani, daga lokacin haihuwar sai ta dauke mana ni da Momy abokiyar zamana, daman na tararda ita da yaranta biyu a lokaci, ita ma yarinyace kamar ni domin ba ita ce matarshi ta farko ba ,sai dai ta zama kamar ita ce uwargida kasancewar matar da ya aura da fari ta rasu ta bar mashi yara uku duk maza”

Ammy ta daga kai ta kalli air-condition dake ďakinta.
Chapter 75 · 0% Book details