← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 127

Sashe 123

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ya isar min ai, sai dai a lahira ayi wannan shari'ar, a cikin yayansu waye na kwarai? Matan ne kawai suka samu gurin zama mai kyau amman mazan daga masu neman bata masa suna sai wadanda ke jiran ya mutu a raba gado a ba su, ni ko ki dubi ni Zuwaira ba fariya ba Allah yayi min komai a cikin yayana babu lalatacce, dukansu suna aiki kuma suna arzikin da za su iya gogawa da masu kudi ko masu mukami, a cikin yayana ina da sojan sama da na kasa ga babbar likita a kuma Aliyu babban dan kwallon da duniya ma tana ji da shi, to me Allah ya rage ni da shi? Alhamdulillah, shiriyar yaya ai ita ce babbar shiriya iya haka ni Allah yayi min komai, balle kuma yanzu da Allah ya bawa ďana matar da yake so kuma ya shirya tsakaninsa da Mahaifinsa”

“Haka ne, idan Allah ya hana ka wani abun sai ya baka wani, hanyoyin Allah yawa ne da su, Allah ya karkato da hankalinsa ya dawo dake cikin gidan nan, hankalin Abiey zai kara kwanciya”

Ammy ta yi murmushi bakinciki still hawaye na kwaranya a idonta.

“Aliyu ai be rasa uwa a gidan ba, ke zaman wa kike ba ďana ba? Wallahi ko mutuwa na yi a yau na san Aliyu ba zai yi maraici ba saboda ke, ke ma kuma lokacin jindadinki ne ya zo a yanzu a da can sun kame gida babu mai iko sai su, yanzu kuma komai ya wuce, ni kam sai aljanna idan Allah ya ba ni ikon zaben abokin rayuwa, amman zaman aure tsakanina da Mai Martaba ya kare har abada, yanzu aure ba ya burge ni ai sai dai mu yi ta bawa yaya shawara”

Da tausayin Ammy Anty Amarya ta yi sallama, domin an raba aurensu ne a lokacin da suke matukar kaunar junansu kuma suke da kurciyar zama a tare, a zaton Anty Amarya Mai Martaba yayi ma Ammy saki uku ne da babu gyara shiyasa ba take fadar cewa zamanta da Mai Martaba ya kare a duniya.
[12/9, 7:56 PM] Oum_Nuwaira🥰: 7️⃣4️⃣

ONE MONTH LATER...

ZAHRA POV.

Abubuwa da yawa sun faru a wata nan, a cikin akwai tarewa ta a gidan mijina kuma masoyina wato Abiey, da kuma tarewa Mama a gidan da Abiey ya gina dake fuskantar na mu na da, wanda ya cilasta mata zaunawa a ciki duk da kasancewar Mr Bashir yayi mana kyautar gida na alfarma. An yi bikin nadin sarautar da ya amsa nadin sarautar da aka dade ba ayi irinsa ba. Domin an kashe naira kuma cikin ya samu halarta manyan mutane daga bangaren Ammy da Mai Martaba sai ka rantse sabon Sarkin Kano aka hada ba dansa a matsayin Galadima ba.

Hakika na ga kauna da soyayya daga gurin Mai Martaba a ranar da aka shiga da ni Masarautar da sunan gaisuwa kamin ya a kawo ni gidan da zan nake da tabbacin shi ne na zamana har aljanna. Mai Martaba ya tara iyalansa ciki har da yayansa da matan biyu wato Hajiya Lami da Anty Amarya jawabin maraba da ni a cikin zuri'ar bayan ya kira da sunan Mahaifiyarsa, kyautar tsadadiyar Alkyaba yayi min a take aka saka min ita a gurin aka cire yan kunena na zinari aka saka min wasu na zinarin da Mai Martaba yayi min kyauta da su na miliyoyin nairori, ranar yayi mana nasiha ni da Abiey sannan aka yi addu'a tare yi mana fatan zaman lafiya, turaren da aka feshe ni da shi sai ka rantse da Allah a gidan aka kafa kamfanin turare. A lokacin da zamu fita gidan Anty Amarya ta bada sabuwar motar da aka kawata da balon balon da fulawoyi da kuma jan kyale. Ni kadai aka dauka a motar wasu motocin suka shiga gaba wasu a baya masu busa na ta aikinsu har muka isa gidan da aka kawata da kusasasun dawankan Abiey guda Hudu. A ranar na ga taron mutane sosai ashe Ammy ma tana da yan'uwa da yawa domin sun yi ta zuwa gidan ganin Amaryar ďanta a cikin har da matan yayun Abiey Wato Yaya Auwal da Sani, ta bangaren Mai Martaba ma na ga yaya da yawa wanda ya kara tabbatar min da lallai na shiga babban gida mai cike da zuri'a da kuma sarauta, kowa a unguwar sai da ya san matan Abiey aka kawo kuma surukar Mai Martaba saboda busa da aka cika kofar gidan da shi da kuma shigowar manyan motoci. Na ga baki kala kala wasu am har na manta rabon da na ga fuskarsu, wasu tsofin abokaina ne wasu kuma makonta mu yan'uwa har da na nesa, suna ta zuwa bawa idonsu abinci. Sai dai duk wannan cin daka ayi aka cinye Hajiya da Bahijja ba su tako ba, balle na yi zaton samun albarka daga gurin Baba. Walimar da Mama ta shirya a ba su halarta ba kuma ta gayyace su. A daren da aka kai ni, na samu kaina a cikin wani farinciki da ya saka ni hawayen, mun raya daren kamar Annabinmu ya koyar da mu, wato da sallah da kuma abinci da sha, sauran abubuwan da suka biyo bayan wannan kuma ina tunanin kamar bana bukatar bayyana sirrin mijina domin sanannen abu ne da ba sai na fito duniya na fadi abun da ya faru ba. Sai dai na dandana kudata sosai a daren domin na sha gyara irin gyaran da ban yi zaton da gaske bayan macen ta haihu zata iya komawa budurwa ba, tabbar kayan Hajiya Aisha 08032350261 babu algus daman tun kamin lokacin na ji canji a jikina, fitsari ma idan na tafi da wahala nake yinsa, ita da kanta ta hana ni tarewa a lokacin da Abiey ya bukata a haka na cilasta masa daga tarewar har sai bayan an yi nadin sarautar da sati biyu, a gidan ta na karasa satin daya saboda na samu biyan bukata, wanda ke min dilka ma sai dai ta same ni a can ta yi min. Cikin satin uku na zama wata yar shala daman can ni din ba mai jiki bace balle kuma yanzu da jikin ya sha gyara kuma zuciya ta samu kwanciyar sai na kara kyau da haiba, kana kallona zaka san Amaryar babban mutum ce ni.
Har yanzu kirjina ciwo yake min domin wahalar ta zo biyu yayen da na yi na Amir da ya daina shan nono tun a ranar da aka sallamo shi daga asibiti, saukina daya na sha kayan gyaran nonon da na siya a gurin Hajiya Aisha wanda ya kara maida nonon nawa a tsaye kamar daman can ban taba shayarwar ba, ciwonsu ya dawo min sabo a lokacin da na yi zaton Abiey zai tausaya min, ashe mugun kansa ne ta wannan bangaren da baya iya tausayina ko da na kwayar zarra, sai dai ba ni kadai na wahala ba har da shi.

Har a yanzu ba zan ce na saba ba, duk kuwa da kasancewar ba wannan ne aurena na farko ba, amman wannan ne jarumin maza kuma gyaran da Hajiya Aisha ta yi min ya saka na fi jin azaba a yanzu fiye da can ma, domin Abiey ya zama tamkar karamin yaron da hausawa suke cewa ba a lasawa zuma a dan yatsa, shi yake ta shan rawar kafa baya barin na huta, sai dai ni na yi ta fama da wahalar.

Karamin tawul ne a jikina da nake kokarin cirewa bayan na gama shafa mai na saka sabbin tufafin da lefen da Ammy ta hada min su da kanta, domin naki yarda mu tafi honeymoon kamar yadda ya bukata balle na hada lefen a can, ba dan kuma bana bukatar zuwan ba sai dan na san zuciyata ba zata iya jurewa ba idan aka daura aurensa da Yasmin yace zai tafi da ita kamar yadda ni ma ya tafi da ni. Bayan na saka tufafin na tsaya a gaban madubi ina kokarin saka dankunnen, ta cikin madubin na hango ya bude kofar dakin ya shigo, wani sako idanuwansa suke aiko nawa idanuwan ta jikin madubi, kamin murmushi ya samu muhalli a fuskata. Kasancewar dikin atamfar da na saka irin ta matan auren nan ce dake bayyana kafadu waje, sai ya dora bakinsa ya sumbanci kafar tawa ya sake sumbantar wuyana.

“Good Morning Hiayatee”

Na juyo na ya rika fuskarsa na sumbanci bakinsa.

“Morning Love”

Sai ya saka hannayensa ya zagaye kumkuruna da su yana shafa bayana zuwa mazauna na da dayan hannunsa, goshin ya hade da nawa cikin siffar da ke nuna daren jiya be wadace shi yake tambayar.

“How was your night? Fada min kin yi mafarkina?”

Ya sumbanci bakina.

“To ai baka bar ni na yi bachi ba ma balle na yi mafarki”

“Ah... Hiayatee na ban da sheri fa”

Ya saka hannayensa ya dauke ni kamar yar baby ni kuma na saka nawa hannayen na zagaye wuyansa da su ina runtse ido. Falo ya fito da ni ya zarce dinning na yi zaton zai sauke akan kujerar da ya saba dora ni idan zamu karya ko kuma akan ciyarsa amman a yau sai ya dora akan dinning din yaja kujera a gabana ya zauna, ta gefena ya hada komai ya saka hannunsa yana dauka yana saka min baki idan na ci sau biyu sai ya ci sau daya. Hannu na mika zan dauki tissue sai yayi saurin rike hannun nawa.

“Hey Princess wait your prince is here”

Da kansa ya dauko tissues ya goge min baki, sannan ya bar ni na sauko dinning, da sauri ya mika hannunsa ya janyo ni na fado jikinsa sai ya rumgome.

“Come hare fada min me zamu dafa da rana?”

Na tabe baki a shagwabe na ce.

“Zamu da fa kuma?”

Ya ja zirin hancinta.

“Yes dole ne mu koyi girki, Ammy tace ta gaji da ciyar da mu, ai ya kamata mu koya ko dan jawabin da ta yi mana ko?”

“To waye zai koya mana?”

“Mu zamu koya mana, ai akwai waya yanzu ina dawowa zamu fara”

Na kara kwanta a kirjin da idan na rabe shi nake jin kamar an gafarta min zunubaina.

“Ina zaka je”

“Sauban ne yake nema, daman ke nake jiran ki farka mu yi breakfast sannan na fita”
Chapter 123 · 0% Book details