← Book details Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 127

Sashe 88

Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban sake ce masa komai ban kuma daina binsa ba, har muka samu wani fili muka zauna a guri ni dai kamin wani lokaci bachi yayi gaba da ni, ban farka sai da safe ina bude ido na zabura na tashi zaune ina waige waige can na hango shi zaune yana ta daga waya sama da alama network yake nema, da sauri na tashi na karasa inda yake zaune.

“Ka kira gida ne?”

“Network din ne sai ya kawo ya dauke gurin nan ba network daman ke na ke jiran ki farka mu tafi”

Na waiga ina kallon ko'ina na dajin, irin dajin nan ne mai kama da tsohuwar gona idan an cire amfanin gonar babu komai a ciki sai haki da ciyayi.

“Abiey a ina ka kawo ni?”

“Ya za'ayi na sani? Ki kabe kanki akwai kasa”

Na kabe dogon gashina da ya gama hautsinewa saboda wahala dankwalin da mayafin ma ban san inda suke ba daga ni sai doguwar rigar lace din da aka dinka min jiya, kama hanya muka yi muna ta tafiya cikina sai kukan yunwa yake min ga gajiya, daker da tsudin goshi muka fara hango mutane, kamin mu karasa gurinsu na yi kuka har Abiey ya gaji da ba ni hakuri ya saka min ido.
Mutanen kauyen mutane masu karamci da son mutane sosai sai da suka fara ba mu abinci da ruwa, Abiey yayi fir shi ba zai ci ba, ni kan na zauna kamar a gidan mu na kwashi tuwona na ci na koshi ba wani kyama na sha ruwa sannan suka ba mu guri muka yi na yi sallah, bayan na gama na dawo kusa da shi na zauna.

“Abiey ka je ka yi sallah?”
“Na yi sallah tun a inda muka kwana na yi taimama a gurin na yi sallah, yanzu kuma na kira Ammy na fada mata muna garin Bagar (Fake name)”

“Ya aka yi ka san sunan garin?”

“Mutanen garin suka fada min, kuma na yi browsing na gani”

“To yanzu tafiya zamu yi?”

“Aa a nan zamu jira su har su zo”

“Amman dan Allah idan mun koma gida ka je gidan mu kace musu sace ni ka yi ka ji?”

Ya wara ido yana dariya.

“Na saka kaina a bala'i kenan? Ya aka yi ma muka zo nan? Ko ina motata?”

“Waya sani, ashe kenan wannan yarinyar da muka bi tafiyar da ta yi da ni har mun iso nan kenan? Kai kuma ya aka yi ka zo?”

“Shi ne abun tambayar ai”

Na waige na kalli mutanen da suka ba mu masauki a gidansu, sannan na juyo na kalli Abiey na ce.

“Idan sun tambaye ka kai mijina ne ka ce musu eh, ni ma idan sun tambaya zan ce musu kai mijina ne ni matarka ce”

“Saboda me?”

“To ai idan ba mu fadi haka ba, za a mana kallon yan iska ne ace miya kuka zo yi ba miji da mata ba”

“Ni kin min kankanta ba zan iya aurenki ba, kuma ban shirya auren yanzu ba ma”

“Ni ma ba da gaske na ke ba, saboda na kare mutuncina ne, kar ayi min kallon yar iska”

Na fada ina zare masa ido yo ina ruwana da mukaminsa ko wani kudinsa ko girma na da yayi to me age it's just a number.
[11/21, 4:26 PM] Oum_Nuwaira🥰: 5️⃣6️⃣

Da Ammy aka zo daukar mu, ta yi musu godiya sosai ta yi musu alheri sannan muka shiga motar da direbanta tare da wani dan'uwanta yake ja, muka kama hanyar gida. Babu kalar fadan da Ammy bata mana ba a motar musamman ma Abiey shi ta fi dorawa laifi, muna isa gidan ta ba ni bandaki na yi wanka ta dauko min wata doguwar riga da ta yi min yawa na saka. Sannan ta kawo min abinci na zauna a kasa ina ci ina kuma tana zaune a saman gadonta tana min wani sabon fadan.

“Yanzu kin tashi hankalin Mamanki Allah kadai ya san halin da ta shiga, tace karki je biki amman kin kama kafa kin tafi konda yake ba lafinku ba ne laifin Aliyu ne”

“Ato ai na fada masa laifinshi ne amman be yarda ba, ai da be kai ni gidan ba da ba haka be faru ba”

“Kun tashi hankalinmu na kira wayarshi a kashe, yau da safe kamin mu tafi ma Mamanki ta aiko gidan nan gurin neman ki na fada mata cewar ba ku ma garin nan”

“Ammy dan Allah ki rufa min asiri karki ce ni na taho da kafafuwana, ki ce Abiey sato ni yayi”

“Aa akan me zan lakawa ďana sata? Ke kika aikata ai dole a miki hukunci”

Duk yadda na so Ammy ta shirya karya ta yadda za a wanke ni a gurin Mama Ammy bata yarda ba, haka ta saka ni gaba muka tafi har gidan ita ta fara shiga, ina lafe kofar gidan sai ga Deen ya fito da saurinsa yana ganina ya dafa zuciyarsa ya zauna a dankali dake kofar gidan ya rufe ido ya dafe kai.

“Zahra kin daga min hankali”

Na matsa baya, na san hukunci mai kauri ne ban daga masa hankalin ba ma ya hukunta ni balle kuma na daga masa hankali.

“Ina mutumen nan ya kaiki? Miya faru?”

“Babu abun da ya faru, hannuna kawai ya rike sau uku be amman babu abun da ya faru”

Ya mike tsaye a fusace ni kuma na fada masa gaskiyar ne saboda ban iya karya ba, kuma kar yayi tunanin ko wani abun ya faru yace zai min hukunci mai tsauri.

“Wuce mu shiga cikin gida”

Da gudu na shiga cikin gidan, sai na samu gidan na mu cike da Uncles dina da Hajiya da kuma Yaya Maryam, juyawa na yi zan koma saboda mugun kallon da Mama take min sai Deen ya riko ni riko bana wasa ba ya saka kafarshi ya buge nawa kafafuwan na fadi kasa ba kwari sai ihu ya biyo baya, a take ya cire belt dinsa ya fara dukana da shi aka rasa wanda zai ce uffan ko ya ta so ceceni a hannunsa sai Ammy dake kokarin tara jikinta ta maida ni bayanta

“Haban bawan Allah wannan mugun dukan kamar wanda ta yi kisan kai, wannan ai sai ka ji mata ciwo”

Deen kamar jiranta yake sai yayo kanta yana kokarin sauke haushin ďanta a kanta.

“Ina ruwanki lokacin da zata bi ďanki miyasa ba ki hana ba? Yarinya kamae Zahra ace ta iya bin namiji suje su kwana a wani guri?”

Ammy ta kalleshi da kyau ta girgiza kai.

“Daga ganin idonka yaron nan baka da tarbiya, taya zaka kalli idona ka fada min wannan maganar? Ai ko ban san Zahra ba idan na ga zata yi abun da be kamata ba ba zan barta ba balle kuma ace da ďana zata aikata haka?”

Sai da Hajiya ta taso ta shiga tsakani sannan Deen ya shafa min lafiya, Ammy ta fice rai a bace, daga ranar ban sake zuwa ko'ina ba kullum ina gida gidan na daga ďaki sai daki idan na fito waje to fitsari zan yi ko na zagaya bandaki, Mari Deen ya saka min saboda kar na sake zuwa ko'ina ba sai dai idan zan yi fitsari ko bayan gidan Mama ta kan bude ni naje na yi idan na dawo sai na miki mata kafafuwana ta saka min.
Wata rana ina sanye da marin ina alwala kawata Hafsat ta shigo muka sha hira da ita da zata tafi bata sakon gaisuwar yan makarantar mu na Islamiya da kuma boko, har ina fadar na yi marmarin makaranta. Bayan ta tafi na tashi ina tsalle cikin marin na shiga daki na yi sallah, sai na kwanta a gurin na yi shiru ina ta tunanin abun da na jawa kaina da ina da yanci na je duk inda nake so amman ban da yanzu da aka saka min mari a cikin gidan ma ba ni da wani walwala, gashi babu mai cewa komai babu saka baki ya ba da hakuri yace a cire min. Ina tsaka da kukana Deen ya shigo da yar ledarshi kamar yadda ya saba min idan zai shigo ya kan shigo min da wani abun ci saboda ya san ni da kwadayi gashi kuma ya saka an saka min mari bana da gurin zuwa.

“Kuka me kuma kike?”

“Na gaji da wannan marin Yaya Deen dan Allah ka cire min, Wallahi zan rika jin magana ka yi hakuri dan Allah”

Fuskar damuwa yayi yana kallon fuskata dake zubar da hawaye.

“Ni ma bana jindadin ganinki cikin marin nan Zahra, amman rashin jin maganarki ne yake damuna, bana son yadda kike shigewa Maza, wani zafi zuciyata take min idan ana kallonki ma balle kuma ace alaka ta shiga tsakaninki da wani”

“Ba zan sake ba, idan na sake ka fille min kai, dan Allah ka cire min wannan abun ya ishe ni”

Yadda na marairaice fuska kadai ya isa ya saka shi tausaya min, daman can kuma na san akwai tausayina a tare da shi.

“Zan cire miki, amman zaki min alkawarin babu ruwanki da kowa dan Allah duk rashin da zaki yi ki yi amman ban da kula maza”

“Toh ba zan yi ba, cire min”

Na janye zanena na mike masa fafaren kafafuwana, ina jin motsin Mama na yi saurin janye kafafuwan domin fada take min idan ina sakin jiki a gaban Deen.

“Deeni ne?”

“Eh Mama ya gida?”

“Lafiya Kalau ina su Hajiya”

“Suma suna lafiya, suna gaisheku”

“Ina amsawa”

“Mama na ce yanzu kam za a cirewa Zahra marin nan mu ga ko zata natsu ”

“Na natsu ma Wallahi ba zan sake ba”

“Allah yasa”
Chapter 88 · 0% Book details