Sashe 11
Ciwon So Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gidansu ya kwana uku sai washe garin rana hudu ya shirya da wuri ya dawo Masarautar saboda yana son magana da Mai Martaba, he got lucky lokacin Mai Martaba be fita ba sai dai yau din ma ba girkin Anty ba ne na Hajiya Kilishi ne, be shiga bangaren shi kadai ba sai da ya saka Anty a gaba, daman can ba saba zuwa yayi magana da Mai Martaba daga shi sai shi ba sai Anty ta masa iso, wannan ne karo na farko da zai saka bakinsa a alamurran gidan domin duk abunda ake babu ruwansa a ciki saboda Mai Martaba ya ware shi dabam, sai this time yana jin ba zai kyale ayi am Kanensa auren dole ba. A karamin falonsa suka zauna Anty akan kujera shi kuma a kasa, Mama Lami ce ta fara fitowa sannan Mai Martaba tana takawa a hankali tana washe hakoranta da ta kawata da hakoran zinari na Makka guda biyu, daman haka take yar barikin macece indai Mai Martaba yana nan to bata da gurin zama sai inda yake kullum tana can tare da shi ta kalallame kamar ta fi kowa sonsa da tausayinsa ko da kuwa ba girkinta ba ne, wani lokacin ta kan dagawa Anty Amarya kafa saboda tana nuna mata bata so, ba kamar Hajiya Kilishi dake mata kawaici ba saboda kansu a hade yake.
Sai da ya zauna sannan ta zauna tana tana kallon Abiey domin sun gaisa da Anty tun shigowarsu kamin ta kira musu Mai Martaba amman Abiey be gaishe ta ba daman kuma be saba gaishe ba. Abiey ya masa kusa da Mai Martaba ya kwashi gaisuwa Mai Martaba be masa komai ba be kuma yi wata alama dake nuna ya amsa gaisuwar ba. Har Abiey yayi kamar ya ce da Mama Lami ta bashi guri zai yi magana da mahaifinsa sai kuma wata zuciyar ta raya mishi yayi maganar a gabanta domin ita ma ya shafe ta.
“Allah ya kara maka lafiya magana nake son na yi, shawara ce wanda nake ganin kamar ita ce mafita a gurin Aisha da kuma mu gaba daya”
Mai Martaba ya dan karkato kadan ya kalleshi. Abiey ya dora daga inda ya tsaya.
“Mai Martaba kai uba ne ga kowa balle kuma a garemu mu da ka haifa, kuma na san ko ni da baka kauna ba zaka zaba min abun da zai cutar da ni ba balle kuma sauran yan'uwana”
Sai da Mai Martaba ya hade yawu a lokacin da Abiey yake furta kalmar ko ni da baka kauna.... Ya sauke numfashi a hankali
“Mai Martaba akan kawo maka karar wani ka yanke hukunci balle kuma cikin gidanka, daga wani gurin wata yar zata iya zuwa ta kawo maka koke kuma ka duba mata, Mai Martaba a game da mijin da aka zaba ma Aisha da Narjis ne dukansu basa so, Aisha tana da wanda take so Narjis kuma ba ma aurene a gabanta ba yanzu, na san ni ba kowa ba ne a gurin Mai Martaba amman hakan ba zai hana na fada maka wani bangare na abun da na fahimta akan abun da ake kokarin hadawa ba, ba wai ina ganin rashin dacewar hakan ba ne kawai ina ganin kamar a bawa ko wace hakkinta shi ne mafita kuma za a samu zaman lafiya”
Mai Martaba ya kalli Mama Lami sai dai kamin yayi magana ta yi dariya ta kalli Anty ta ce.
“Zuwarai kenan, yanzu wannan maganar ce ba zaki iya yi tsakaninki da Mai Martaba ba har sai kin sako Abiey a ciki? Haba dai wai yaushe zaki waye ne sai kace Mai Martaba wani dodonki ne”
Anty ta kalleta.
“Ba zan iya musa hukunci Mai Martaba ba shiyasa ban tukare shi da maganar ba, shi ma sun kuka masa ne shiyasa yayi shahadar yin haka”
Mai Martaba yayi gyaran murya.
“Ban cilastawa kowa a cikin yayana auren wanda basa ra'ayi ba, kuma ba zan cilastawa kowa ba shawara ce da Hannatu ta kawo ban kuma ce a cilastawa daya daga cikinsu ba, Narjis ance shi mutumen ya ga yarmu ne yana so Aisha kuma ita ta Hannatu ta kawo shawarar kuma ina tunanin kamar hakan zai dace, amman idam har basa ra'ayi ba zan cilasta musu ba”
A take fuskar Anty ta cika da farinciki Mama Lami ma haka sai dai kowa ya ga nata ya san na bakinciki ne.
“Allah ya saka da alheri, abun ai be kai ce da kin same ni da maganar ma da mun warwareta tsakaninmu”
Mama Lami ta fada Anty dai bata ce komai ba, bayan tabe baki da ta yi Abiey ma farinciki yake domin be yi zaton jin haka daga gurin Mai Martaba ba.
“Kai ma ai ya kamata ka fito mana da matar aure ka girma Abiey”
Mai Martaba ya fada ba tare da ya kalleshi ba, kusan a rikice Abiey ya dago ya kalli Mai Martaba yana jin kamar ba daga bakin Mai Martaba maganar ta fito ba, not just him Anty da Mama Lami ma mutuwar zaune suka yi mamaki ya cika su. Sai dai hakan be hana Mama Lami karfin halin furta.
“Gaskiya kam ni ma na so na yi magana domin na lura Zuwaira kamar abun be dame ta ba”
“Ina masa maganar ai matar ce har yanzu be rika ba, kin san ďana babu ruwansa da sha'anin kula mata ba shi da wata wanda yake so a yanzu”
Anty ta fada baki har kunne saboda jindadin Mai Martaba yayi maganar Abiey.
“Ga yan'uwa ga mata a gari ai sai a nema masa, ko yarinyar da ta zo nan kwana kin baya ai sai a nema masa ita idan yana so yar gidan Mr Bashir Auta”
Abiey ya kalli Mai Martaba baki sake yana kokarin ce masa akwai wanda yake so, sai dai wa? Ai ba zai ina cewa Zahra ba domin takaba take, sai dai space din yatsun hannunsa da na zuciyarsa na Zahra ne kawai saboda haka dole ya sama wa kansa mafita kamin Mama Lami ta kulla masa wani sherin.
“Akwai wanda nake so”
Anty ta kalleshi da mamaki Mama Lami kuma ta yi murmushin yake.
“Maa Shaa Allah yar dangi ce ko daga nesa aka dauko, ashe ko zama be gan mu ba Abiey ya sake yin budurwa”
Sai ya samu bakinsa da furta sunan yarinyar da be hada komai da ita ba.
“Yasmin”
“Maa Shaa Allah aiko ka zabo mai tarbiya Wallahi, dan Yasmin tana da mutunci”
Wannan karon Anty ce ta yi maganar sannan ta fara yi ma Mai Martaba bayanin din Yasmin din da Abiey yake nufi domin kar Mai Martaba ya dauka Yasmin yar dan'uwansa, Anty ta ji dadi sosai daman ta lura kamar suna shan inuwa daya da Yasmin da Abiey, tun bayan rasa Zahra sai a yau Abiey ya furta yana son wata macen.
“Zamu nema maka aurenta da yardar Allah”
Mai Martaba ya fada, Abiey be san lokacin da ya kai hannunsa ya dafa kafafuwan Mai Martaba ba not because of yace zai nema mashi auren Yasmin, saboda ya nuna mashi kulawa wanda be taba nuna mashi ba.
“Allah ya kara maka lafiya, na gode kwarai da kulawa”
Mai Martaba ya dauke kai fuskarsa a hade kamar ba shi yayi furucin ba. Abiey da Anty suka fito bangaren Mai Martaba cike tsananin farinciki da suka dade ba su samu kansu a ciki ba.
“Ban sha fada maka ba Abiey wata rana komai zai wuce Mai Martaba zai kaunace ka kamar sauran yan'uwaka koma fiye da sauran daman can ni na san Mahaifinka yana sonka, na tabbatar da ba kai ka yi masa maganar su Aisha ba wata kila da be saurari kowa ba, domin zai ga kamar an same shi da maganar ne kai tsaye ba tare da an raba ta gurin matansa ba”
Abiey yayi murmushi yana kokarin zaunawa kan royal cushion din Anty.
“Ban yi zaton haka da sauri ba”
“Ba'ayi sauri ba Abiey shakara nawa ka yi a duniya kamin Mai Martaba ya kalleka ya furta maka wata magana mai dadi?”
“Tun da aka haife ni sai yau, kuma dukan abun da ya faru a yau ya faru ne saboda ke da Ammy, Thank you so much Anty you're such a wonderful mom beautiful wife”
Anty ta yi murmushi tana saka hannu ya tare hawayen daya cika idonta ganin hawayen Abiey dake sauka, ta kwalawa Aisha kira.
“Humaira fito yayanki ya miki yaki”
Abiey yayi saurin mikewa tsaye ya share hawayensa, sai ga Aisha ta fito da gudunta, Anty na labarta mata abun da ya faru ta rumgume Abiey cike da murna da farinciki.
“And abun farinciki na biyu Abiey ya fitar da matar da yake so”
Aisha ta nufo Anty cikin murna.
“Wacece Anty?”
“Yasmin step sister din Dr Zainab”
Aisha ta daka tsalla ta dire tana ihu, sai Abiey yayi saurin sakatarda ita.
“No.... Wallahi babu komai a tsakanina da Yasmin kawai na fadi sunanta ne saboda na kare kaina gudun kar Mama Lami ta min jaye jaye”
“Amman a gabanka fa Mai Martaba yake fadar za a nema ka aurenta Abiey? Be kamata ka yi haka ba, bayan ka fadi kana sonta sai kuma ka zo yanzu kace mana ba haka ba, shi ma ai ba zai jidadi ba”
“Kwantar da hankalinki Anty zan samu Yasmin zan yi magana da ita, na san yadda zan shirya komai lemme go and Ammy abun da Mai Martaba ya min a yau, jiki da zuciyata Zahra nake ajewa nata ne ita kadai”
“Allah ya baka Zahra nan Anty ta fada min mijinta ya rasu”
Aisha ta fada sai ya amsa yana jindadin addu'arta.
“Amin My Sweet Sister”
Cikin farinciki da mamaki Abiey ya bar gidan, kamin ya isa gurin Ammy har ya motsu saboda daddadan labarin dake bakinsa, daf da entrance din kofar falon Ammy ya faka motarsa ta miliyoyin nairaro ya fito ya shiga falon, Zaune akan laulausan center carpet ya hango Ammy plate din guava a gefenta, Jummai na zaune nesa da ita suna hira, da sauri karasa kuaa da ita ya kwanta a gurin ya dora kansa akan cinyarta, Jummai na ganin haka ta tashi ta ba su guri.
“Me ya same ka na farinciki yau?”